SANADIN MAHAIFINA

Page 17

by @sanazty

•••SANADIN MAHAIFINA•••

Wattpad@SaNaz_deeyah

Arewabooks@sanazty

Facebook@Habibtyn Habibi

YouTube: ***

Tiktok: ***

Facebook Page

***

Karku manta ku shiga links ɗin nan ku yi following handles ɗina

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula ta gari]

*Wannan shafin naku ne masoyana na nesa dana kusa wanda na sani da wanda ban sani ba, ina ƙaunarku domin da bazarku nake taka rawa*🥰

                    '''Shafi na 17'''

Da mamaki Zulaihat ke bin inda Hanne ta bari. Ranta a ɓace ta miƙe tsaye "Tashi mu tafi kawai" ta faɗa tana kallon Murja. "Haba dan Allah akan wannan banzar za ki wani fusata" "Murja idan ƙanwar sa bata daraja ni ba, kina tunanin zanji daɗin zama dashi? Gaskiya bazan yarda ta wulaƙanta ni ba, tun yanzu zan nemawa kaina ƴan ci" "Hakane kuma." Tashi Murja tayi suka fita.

A tsakar gida suka tarar da Umma da Sa'ad. "A'a ba dai kun fito baku ci komai ba" Murmushin yaƙe Zulaiha tayi sannan ta ce "Ai munci Umma, yanzu Mama ta kira ta ce tana son ganina shiyasa zamu tafi" "To ki gaida ta da kyau" kallon Sa'ad tayi ta ce "Kaje sai ka raka su ko?" "To Umma."

A ƙofar gidan ta kalleshi cikin ɓacin rai ta zayyana masa komai, haƙuri yayi ta bata kuma ya mata alƙawarin in sha Allah zai wa tubƙar hanci.

                 ****

Suna fitowa daga pharmacy Rayyan ya kalli Khalil ya ce "Amma mene ya samu Jannat?" "Ba wani abu bane, kawai tana fama da zazzaɓi ne"  ya san ba gaskiya bane, kawai murmushi yayi.

Suna kai maganin Rayyan yayi masu sallama ya tafi.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Daddy kwananshi uku a asibiti aka sallameshi, Bikin Sa'ad da Zulaiha kuma an saka rana. Shirye-shirye yake abinsa bai san halin da Jannat take ciki ba, kuma bai nemi ya sani ba, domin bai ma san Safina ta rasu  ba. Ta ɓangaren Rayyan kuwa yana ta bincike yana so ya gano mene ya faru da Jannat kuma ya gano sai dai bai samu asibitin da take ba.

Bayan Wata Bakwai

Airport

Passengers ɗin da suka taho daga Florida zuwa Kano, sune suke ta tururuwar sauka daga jirgi. Yana sauke ƙafarsa yaji gabansa yayi mummunan faɗuwa. Sai da yayi addu'a sannan ya ƙarasa sauka. Mota daya saka a zo ɗaukarsa daga gidansu tuni driver yazo.

Da sauri driver ya karɓi trolley ya saka a booth sannan ya buɗe masa mota ya shiga. Ya zagaya ya shiga motar.

"Yallaɓai barka da sauka"

"Yauwa Sammani da fatan na sameku lafiya?"

"Duk kowa lafiya"

"Ma sha Allah, gidana za ka kaini"

"Maigida ya ce a kaika can, domin gidan na ka babu kowa"

"A'a Safina fa? Bata gidan?"

"Eh haka dai ya ce babu kowa a gidan naka" a zuciyarsa kuwa cewa yayi Amma meyasa aka ɓoye masa mutuwar matarsa?

Ba wanda ya ƙara cewa komai har suka ƙarasa gida. Yana yin parking Ahmad ya fito ya shiga ciki, yayinda maigadi ya tsaya yana ɗauko kaya.

                ******

Kuka sosai take hankalinta a matuƙar tashe, Mommy ta dafa kafaɗarta ta ce "Kiyi haƙuri Safina, baki da inda ya fi gidan mahaifinki, ni ma a baya nayi tunanin barin gidan saboda abinda yayi mana, amma kuma da yayi min bayani na fahimce shi, sannan kuma har rashin lafiya yayi duk akan wannan al'amari, ki yafewa mahaifinki"

Ɗago kai tayi ta kalli Mommy ta ce "Mommy meyasa a lokacin da nake ta roƙon Daddy kan ya fahimceni bai tsaya ya saurareni ba, ni yarinya ce am just 19 meyasa bai saka ni dole in auri Khalil ba?" "Haƙuri za kiyi Jannat ba za ki taɓa iya canza shi daga mahaifi ba"

Haka Mommy tayi ta rarrashinta, suna tafiya cikin mota, a haka har suka isa gida. Bata ma tsaya a falo ba kai tsaye ɗakinta ta wuce tayi wanka ta canza kaya.

A jikin mirrow ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, a zuci ta furta Gashi kamar ban yi yoyon fitsari ba, cutar ta rabu dani, kamar yadda budurcina ya rabu dani, kuma Safina ma bata tare dani

Faɗawa kan gado tayi tana hawaye a ranta take addua Allah yajiƙan Safina.

              ******

A gigice ya miƙe tsaye, kallon Mommynsa da Daddynsa yayi hawaye tuni sun ɓata fuskarshi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ya furta.

"Ka zauna ka nutsu ka ji abinda zan faɗa maka" Daddy ya furta muryasa so calm. Kallon shi Ahmad yayi cikin tashin hankali ya ce "Daddy mene zanji wanda baka sanar dani a yanzu ba? Meyasa baku faɗa min Safina ta rasu ba?"

Faɗawa yayi kan kujera ya dafe kai lokacin da wasu sabbin hawayen suke ƙara ambaliya a fuskar shi. "Mun ɓoye maka ne saboda a lokacin ina tsoron kar ka dawo su kama min kai" "Gara a kamani, ai na aikata laifin dana cancanci hakan, yanzu da wane ido zan kalli mahaifanta, ga abinda na aikata wa Jannat ga kuma mutuwar Safina da ko shakka babu baƙin cikin abinda nayi ne"

Sai lokacin Mommynsa ta ce "Haba Ahmad, mun ga hankalinka ya tashi a kan abinda ka aikata, duk da mun san laifi ne, amma haka muka danne muka turaka wata ƙasar sannan muka nunawa iyayen Safina mu bamu san baka nan ba, saboda muna tsoron wani abu ya sameka domin a lokacin ina ganin kamar akan abinda ya samu ƴar uwarta ne ta fita hayyacinta"

"Amma Daddy abinda ya faru ni ne sanadi, kuma ban taɓa tunanin cewa abin zai kai haka ba da ban gudu ba, shaiɗan ne ya ruɗe ni shiyasa har na gudu na bar garin, amma da nasan Safina matata zata rasa ranta, sannan da na san abin zai janyo wa Jannat yoyon fitsari da ba zan taɓa aikata abinda na aikata ba."

Zai zube gwiwoyinsa a ƙasa, ya dafe zuciyar sa yana jin wata ƙuna.

Cikin ɓacin rai Mommy za ta ce "Ka ga mu fa ba zaka zo ka rufe mu da faɗa ba, kenan gatan da muka maka baka gani ba ko?"

Bai basu amsa ba kawai ya tashi yayi side ɗin da aka sauke shi.

                ******

Zulaiha na tsakar gida daga gefen fanfo tana wanke-wanke, Sa'ad yayi sallama ya shigo gidan. Da sauri ta ɗauraye hannunta ta tashi taje gabansa tare da karɓar ledar dake hannunsa. "Sannu da zuwa mijina" ta faɗa tana murmushi, shima maida mata yayi sannan yace "Yauwa matata abar alfaharina, ya zaman kaɗaici" "Babu shi tunda ga ka ka dawo" "Na so ace gidana kusa da gidanmu ne da na san za ki riƙa ganin Hanne akai-akai" "Hmmm! Muje ciki ka ci abinci ka huta" shine abinda ta faɗa sannan ta wuce ya bita a baya.

Bayan yayi wanka ya saka kaya mararsa nauyi, abinci ya zauna ci itama lokacin ta gama aikin da take dan haka anan falo suka zauna suna hira cikin jindaɗi.

"Danginka ba laifi suna yi dani, sannan Mahaifiyarka tana so na, amma na rasa dalilin da yasa ƙanwarka bata sona duk da cewar ina ƙoƙarin jawota a jiki" "Waya faɗa miki bata sonki? Hanne muskila ce kawai" "Ko da muskilanci akwai ƙiyayya ina ganinta ƙarara a idon Hanne, yau sati na uku a gidan nan amma bata taɓa zuwa ba" "Kiyi haƙuri zan mata magana za ta gyara" "Ko dai akwai wadda take so ka aura ne?" "Hanne ba ita za ta zauna min da mata ba, dan haka ki bar ni da ita zan gyara mata zama" "A'a mijina ni fa ba na faɗa bane dan in haɗaka da ƴar uwarka" "Nima na san da haka."

             *****

Da sallama ya shiga falon mahaifin nasa, Mommy ta fara amsa masa sannan Daddy.

Zama yayi kan kujera ya ɗan yi shiru ba tare da yayi magana ba "Ina jin ka Rayyan kayi shiru baka ce komai ba?"

Ɗan sosa sajensa yayi sannan ya ce "Daddy dama ina so dan Allah na nemi wata alfarma a gurinka" "Allah yasa zan iya" "Amin, dam....dama Daddy ina so ne dan Allah kayi min jagora ka nema min auren Jannat, naji labarin abinda ya sameta na tausaya mata ku......." bai ƙarasa ba Mommy ta katse shi da faɗin "Allah ya sawwaƙa maka auren yarinyar da aka tsinka mutumcin ta tun a waje, wallahi baka isa ba, ai mu iyayen naka ba mahaukata bane da za mu baka aurenta" "Saurara da Allah" Mommy tayi shiru ranta a ɓace. Daddy ya kalli Rayyan ya ce "Ashe na haifo lu'u lu'un ɗa ban sani ba, naji daɗin furucinka, da ace za a samu samari masu jin ƙai kamarka da duniya ta zauna lafiya, kuma na amince da wannan aure domin Jannat yarinya ce mai haƙuri, kuma in sha Allah zan je in samu mahaifinta muyi magana" cikin jindaɗi ya ce "Daddy nagode Allah ya saka da alkhairi" "Wai kana nufin wannan mara tarbiyyar za ka aurawa ɗan cikinka" ran shi a ɓace ya ce "Eh" sannan ya kalli Rayyan ya ce "Tashi kaje" cikin jindaɗi Rayyan ya tashi ya bar falon, Mommy sai faɗa take tana faɗin ba zai taɓa yuwuwa ba.

             *******

Bayan an buɗe masa gate yayi parking, ya kalli Ahmad ya ce "Muje ko?" kallon sa Ahmad yayi sannan ya ce "Daddy dan Allah kar ka ce ka san na gudu na bar garin nan, idan har suka san cewa da sanin ka, to tabbas kimarka za ta zube a idanunsu" "Tunda yanzu na kawo ka za kuma ka amsa laifinka, mene amfanin ƙarya?" "Daddy ba ƙarya bace, kare mutumcin kai ne, ni ne da laifi kuma ba zan so laifina ya taɓa mutumcinka ba" yana gama maganar ya ɓalle murfin motar ya fita.

Cikin kuka ta riƙe hannayen Mommy "Mommy na tsani ganin fuskar Ahmad, meya kawo shi gidan nan, kuna me zan je nayi masa" cikin yanayi na rarrashi ta ce "Jannat ina so ki gyara ne, domin gaba, yadda mahaifinki yayi sanyi ke kuma bana so ki riƙa bijire masa kamar yadda aka sanki da kawaici yanzu ma ki zama haka, mahaifinki ya ce ba za ai magana da Ahmad ba dole sai kina gurin shiyasa yace na kiraki, dan ya kira Khalil ma ya ce masa yazo." "Mommy......." sai kuma tayi shiru tana goge hawayenta, ta ɗauki hijab ta zura suka nufi falon Daddy.

Da sauri ta sha gabansa cikin ɓacin rai ta ce "Babu inda za kaje wallahi" da mamaki ya kalleta ya ce "Farhan yaushe kika zama mafaɗaciya?" Mtsww "Ban sani ba, wallahi Yaya Khalil babu inda zaka je, na maka katanga da ganin Jannat" "To bari na kira Daddy nace kin hanani kiran da yayi min" "Hmmm ai na san kiran ba zai wuce akan Jannat ba" "Kin ga Farhan wai kin manta Jannat cousin sister na ce? Ko da ba ke nake aure ba dole in ta kama naje gurin Jannat, domin ko ba soyayya akwai ƴan uwantaka" "Cousins ɗinmu nawa? Ka ga na hana ka zuwa wajen su? Itama Jannat ɗin da dalilina" "Dalilin ai bai wuce ki ce soyayya ba, Farhan ina son Jannat kuma a musulunci ma ya halatta in sakeki in kuma aure ta" zaro ido tayi tana kallon sa, har ya wuce amma ta kasa ko motsa yatsa saboda furucinsa ya matuƙar girgiza ta.

Kan ta na ƙasa ta ƙi ɗagowa ta kalli kowa, mutuwar Safina ji take ta dawo mata sabuwa, dan haka babu abinda ke fita daga idanunta sai hawaye.

"Alhaji ku ɗan ƙara haƙuri muna jiran zuwan ɗana Khalil" "To babu damuwa, Allah ya kawo shi lafiya"

Ahmad shima ya kasa ɗaga kai ya kallesu saboda kunya, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi saboda wani lokacin sautin shashsheƙar Jannat tana fitowa.

Cikin mintuna 15 Khalil ya ƙaraso. Zama yayi ya gaida kowa, da mamaki ya nuna Ahmad "Daddy ba dai Ahmad bane wannan?" "Shine" ai a kiɗime yaje ya damƙi wuyansa gami da aika masa naushi a hanci, da sauri Alhaji Mas'ud yaje ya janye Khalil ɗin. "Dama jiran dawowar sa nake, yanzu zan kira ƴan sanda, sai ka ƙarashe rayuwarka a gidan maza" "A'a Khalil kar ka kira kowa, ka jira muji da wacce suka zo tunda sun zo har gida. Faɗa Khalil yake tayi ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Jannat a hankali ta ɗago kai ta kalleshi, wani furuci da yayi mata lokacin suna soyayya shi ne ya dawo mata. A ko wane hali kike, ba zan taɓa gudunki ba, kuma nayi alƙawari bazan taɓa bari ki wulaƙanta ba, zan tsaya miki a duk wasu al'amuranki. Wani sabon hawaye taji sun sauka daga idanunta, har a lokacin idanunta a kansa, yana juyowa tayi saurin kauda kai, dan bata ma so suka haɗa ido ba.

Ahmad kuma hanky ya saka ya goge jinin haɓo da Khalil yayi masa. "Dan Allah kuyi haƙuri, minti kaɗan bari nayi magana da Khalil" shine abinda Alhaji Mas'ud ya faɗa, sannan yaja hannun Khalil suka fita.

Suna dawowa ya zauna bai ce komai ba, amma har a lokacin ransa a ɓace, Mommy da Ummu ba wanda ya iya magana. "To Alhaji muna saurarenka, meke tafe daku?" har ya buɗe baki zai yi magana Ahmad yayi saurin katse sa, sannan ya durƙusa akan gwiwoyinsa ya fara magana "Daddy, Mommy da Jannat gani akan gwiwoyina a kuma gaban ku domin neman yafiyarku, na yarda da duk hukuncin da zaku ɗauka a kaina amma ni dai fatana shine ku yafe min, Daddy na rantse maka da Allah ban san Safina ta rasu ba" kuka ya fara, Khalil ya ja tsaki. "Abinda na aikata wa Jannat kuma Safina ta kamani ƙuru-ƙuru, sannan jini ya ɓallewa Jannat wannan kunyar abin dana aikata ne ya saka na gudu na bar ƙasar, kuma duka layikana na kashe su ban nemi kowa ba bare a sanar min, sai yanzu dawowar da nayi mahaifina yayi faɗa sosai har yaso ya fita daga sabga ta, nayi dana sani, kuma na tafi ne dan in komai ya lafa in dawo, saboda ni na san lafiya na tafi na bar Safina" "Ita kuma Jannat ɗin fa? Ba ruwanka da in ta mutu ko, tunda kayi abinda za kayi" Khalil ya faɗa rai a ɓace. Jannat ta runtse ido cike da ƙunar zuciya.

"Kuyi haƙuri, a lokacin hankalina ya tashi, ina kunyar kallon da iyayen Safina za su min, wallahi  sharrin shaiɗan ne, amma na zo na gyara kuskurena, ina neman afuwarku, kuma idan kun yafe min ina roƙan ku bani damar auren Jannat hakan zai saka na ƙara gyara a........." "Dalla dakata Malam" Khalil ya sake katse shi, ya kalli Daddy "Daddy kaji wata banzar magana fa, ni ka bani dama yanzu a tafi cell dashi"

Jannat ƙanƙame Mommy tayi ta ƙara fashewa da kuka. Ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce "To da farko dai ni laifin da kayi min bai kai wanda ka yiwa Jannat da Safina ba, Safina dai bata raye, bare muji ta bakinka, ni kuma a nawa ɓangaren idan Jannat ta yafe maka kuma ta yarda za ta aureka to nima haka, wannan shine magana" miƙewa Jannat tayi ta bar falon tana kuka. Da sauri Mommy ta tashi ta bita.

Ina jiran ta bakinku game da wannan shafin

Kuyi following ɗina a Wattpad @SaNaz_deeyah sannan ku riƙa vote a ko wane shafi na book ɗina. Sai kuma comment domin jin ra'ayinku.

Sannan ina mai baku haƙuri a bisa rashin posting kullum abubuwa ne sun min yawa amma insha Allah komai zai daidaita

SaNaz Ce✌️