SANADIN MAHAIFINA

Page 18

by @sanazty

•••SANADIN MAHAIFINA•••

Wattpad@SaNaz_deeyah

Arewabooks@sanazty

Facebook@Habibtyn Habibi

YouTube: ***

Tiktok: ***

Facebook Page

***

Karku manta ku shiga links ɗin nan ku yi following handles ɗina

KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

[karamci tushen mu'amula ta gari]

                    '''Shafi na 18'''

A zaune kan gado ta tarar da ita, ta jingina bayanta da fuskar gado tana kuka mara sauti. Tsayawa Mommy tayi tana kallon ta kafin ta sauke ajiyar zuciya. "Kin san cewa kina da hawan jini amma shine ba za ki fitar da damuwa a ranki ba?" bata ba ta amsa ba, ba kuma ta daina kukan ba.

Zama gefen gado Mommy tayi sannan ta cigaba da cewa "Yanzu hukunci ya rage gareki ki yafe masa ko kuma akasin haka" "Idan har na yafe masa Safina fa?" "Safina bata raye, sai dai bamu sani ba ko ta yafe masa a cikin ranta kafin rasuwarta." "Bana tunanin Safina za ta yafewa azzalumin nan" "Jannat kin san Allah yana son mai haƙuri ko?" kai ta gyaɗa alamar eh. "To ina so ki barwa Allah komai kiyi haƙuri ki yafe masa" jin haka ya saka ta sake fashewa da kuka da sauri ta dira daga gadon da niyyar barin ɗakin, akayi knocking.

Komawa tayi gefen gadon tana goge hawaye, ita kuma Mommy ta buɗe ƙofar. "Ina so inyi magana da Jannat please" shine abinda Khalil ya faɗa, da sauri Jannat ta ɗago kai ta kalli ƙofar. "Shiga tana ciki?" Mommy ta faɗa sannan ta wuce ta bar ɗakin, shi kuma Khalil ya shigo.

Gaba ɗaya ta kasa sukuni, ta kuma kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi, duk da ta na cikin tashin hankali a lokacin.

Stool ya janyo ya zauna a gabanta gami da ƙura mata manyan idanunsa. "Kin rame sosai, ko kin sake wani ciwo ne?" gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba, ta maze dai bata ce komai ba.

"Jannat...." ya kira sunanta muryar shi so calm. Bata amsa ba, ba kuma ta ɗago ta kalleshi ba. "Ina so nayi magana dake a matsayin Yaya ba matsayin Ex ba" jin haka ya saka ta ƙara fashewa da kuka. Hannu ta saka ta rufe bakinta dan kar kukanta ya fito fili.

"Jannat ina neman alfarmarki da karki taɓa yafe wa Ahmad, ina so ya girba abinda ya shuka, ina so ya zubda hawaye fiye da wanda kika zubda" sai lokacin ta samu ƙarfin faɗin "Yaya Khalil ina son ganin Sa'ad" ɗagowa tayi ta kalleshi karo na farko da tayi masa kallon eyes to eyes tun bayan rabuwarsu. "Na san Daddy ba zai bar ni ba, amma dan Allah ka samu abinda za ka faɗa masa, ina so naga Sa'ad" "Me za ki ma Sa'ad, bai zo asibiti ba, bai kuma zo ta'aziyya ba" "Wannan dalilan ne yasa nake son ganin sa, kuma na san za ka iya min wannan alfarmar" "Yaushe za ki je?" "Yau idan zai yuwu" "Da wannan hawayen?" hannu biyu ta saka ta goge shi, kallonta kawai yake cike da tausayawa. "Bari na je gurin Daddy" kai kawai ta gyaɗa, ya fita ta bi shi da ido.

                  *****

Driving yake ita kuma tana daga gefensa ta ƙurawa titi ido, ba hawaye a idanunta amma kallo ɗaya za ka mata ka gane cewa akwai damuwa a tare da ita.

Kallon shi ta ɗanyi ta ga damuwa ƙarara a fuskar shi, a ranta  ta furta Nayi dana sanin abinda na aikata. bata san lokacin da a fili ta furta "Ya Allah ka kawo min mafita" "Amin" taji ya furta. Kallon shi tayi suka haɗa ido tayi sauri sauke ƙwayar idanunta ƙasa.

A ƙofar gidan su Sa'ad yayi parking, ita ta fara fitowa kafin shi. "Zan jira ki anan" kai kawai ta gyaɗa sannan ta kutsa kai cikin gidan bakinta ɗauke da sallama da muryarta bata fita sosai.

Da Hanne da Umma gaba ɗaya suna tsakar gida anyi katari ranar Sa'ad ya kawo matarsa ta gaida Umma, itama tana daga gefe tana latsa waya.

Miƙewa tsaye Hanne tayi da sauri ta ƙarasa kusa da Jannat "Jannat kece?"  Umma tuni annurin fuskarta ya disashe. "Ni ce Hanne" ta faɗa sannan ta kalli Umma, sai kuma ta dawo da kallonta ga Hanne. "Ina Sa'ad?" "Am....." "Me za ki yiwa Sa'ad? Ba na faɗa miki cewar nayi miki katangar ƙarfe dashi ba, to Sa'ad ma yayi aure, kina tunanin dan kin warke zan yarda ne ya aure ki" "A'a" Jannat ta faɗa tana murmushi mai cike da takaici. Kallon Hanne tayi sannan ta ce "Na so ace da nazo baki nan, wallahi Hanne darajarki mahaifiyarki ke ci" Tasowa Zulaihat tayi a fusace "Dallah malama dakata, kin ga ke da kika zo nan me zaki iya ne? Ko kin ɗauka za a ji tsoronki" ɗan murmushi tayi wanda suka bayyanar da haƙoranta "Tofa, ke kuma wacece da za ki shiga maganar da babu ke a cikinta, baki san illar da suka min ba dan haka kiyi shiru in gama."

Yana ƙoƙarin shiga ciki da saurinsa, dan tunda ya hango Khalil yasan tabbas sun yi baƙi. "Malam ji mana" Khalil yayi maganar lokacin daya ke ƙoƙarin wucewa.  "Lafiya" "Amma ai ko gaba muke ya dace ace ka yi min sallama ko?"

Zulaihat kasa cewa komai tayi, Jannat ta kalli  Umma ta ce "A yanzu kam ɗanki ko ɗaura min shi akai a ƙafa zan kunce, amma ku sani kun zalinceni kuma Allah sai ya saka min, wanda na zo nema baya nan dan haka sai anjima" juyawa tayi ta fita Umma na faɗin "Sakayya ba dai akanmu ba, tunda ba abinda muka miki" Hanne dai ta kasa magana, idanunta gaba ɗaya sun cika da hawaye, da sauri ta bi Jannat, Umma na magana amma taƙi dawowa.

"In maka sallama? To ba zan yi ba sai me?" ya faɗa cikin ɓacin rai, a dai-dai lokacin Jannat ta fito. Kallon ta yayi sannan ya kauda kai, Khalil kuwa ƙura mata ido yayi ji yake tamkar yayi mata hawaye.

Gaban Sa'ad ta dawo, ya sake kauda kai. "Hmmm dole ka kauda kai, saboda ƙwayar idonka ba za ta iya kallona ba, Sa'ad ka cuceni, ka cuci rayuwata, ka cuci soyayyata, ka sakani a mawuyacin hali" "Jannat komai da kika ga ya faru dama muƙaddari ne" "Ƙaddara..." ta maimaita, sannan ta sake kallonsa "Meyasa a lokacin da kace kana sona na sanar maka ina da wanda nake so amma sai kuka dage sai na aureka, Umma ta kafa min karan tsana, ka hau rashin lafiya, a lokacin tausayinka ne ya saka na fasa auren Khalil saboda ina tsoron karka mutu dalilina, ba wai dan ina sonka ba, amma ni a lokacin ina gadon asibiti ina fama da ciwon yoyon fitsari haka mahaifiyarka ta wulaƙantani, a gaban idanunka Sa'ad" "Jannat kiyi haƙuri ba zan iya bijirewa umarnin mahaifiyata ba" kallon shi tayi baki a sake "Kaji azzalumi, ni kuma ka saka na bijirewa umarnin mahaifina, kuma a sanadinka komai ya faru, ba zan taɓa yafe maku ba, a dalilinka aka koreni daga gidan mu, aka min fyaɗe" ta fashe da kuka.

Khalil ya matso kusa da ita "Jannat mu tafi nan waje ne, bai kamata ki riƙa faɗar maganganu ba."  kallon Sa'ad ta sake yi ta ce "Safina ta rasu babu wanda yazo min gaisuwa a cikinku, Allah sai ya saka min zalunta ta da kuka yi, ba a taɓa min irin abinda kuka min ba" Ganin ba ta da niyyar tafiya Khalil ya fuzgi hannunta ya buɗe mota ya saka ta, sannan ya rufe. Kallon Sa'ad ɗin yayi da ya ƙame inda ta bar shi. Kai kawai ya girgiza ya shiga mota ya ja. Da gudu Hanne ta koma ciki tana kuka.

Kanta yana cikin cinyoyinta tana shashsheƙar kuka, ta ɗago kai ta kalli Khalil dake driving cike da  damuwa. "Ka kaini gurin Farhan, bana son na koma gida a haka" ji yayi kawai gaban shi ya faɗi, yayi addu'a Allah yasa kada Farhan ta nuna mata komai.

"Jannat ki ƙaddara wannan abu daya sameki jarabawa ce, kiyi haƙuri ki cigaba da addu'a" Hawayen da bai daina zuba ba ta saka hannu tana gogewa. "Akwai da yawa wanda basu kai shekaruna ba, amma suna da hankali da zurfin tunani, ban taɓa sanin bani da hankali ba sai yau" "Kina da hankali, tausayinki ne ya jawo miki, amma Allah zai duba kyakykyawar niyyarki" "Ina mai ƙara baka haƙuri, a wancan lokacin nayi hauka, nayi saka ci, wannan shi ake kira da biyu babu, amma koma mene Sanadin Mahaifina ne, da bai ɗauki zafi ba a wancan lokacin da ace kuma bai koreni ba, da ace bai min baki ba, da duk haka bata faru ba, illar furucinsa ne wannan ƙaddarar da ta faɗa min. Amma ko babu komai yanzu na ga true colour na Sa'ad, kuma naga illar bijirewa umarnin iyaye" ya isa haka, kukan nan da kike zai iya haddasa miki ciwon kai, ki daina tuna komai" kwantar da kai tayi jikin kujera tana sauke ajiyar zuciya, yayinda hawaye ke fita a idanunta. Hannu ya saka ya goge hawayen idanunsa. Allah ya kawo miki ɗauki Jannat, ya baki miji nagari mai tsoron Allah, wanda zai riƙeki amana, da na san cewa rayuwarki za ta zama haka, da bazan auri ƙanwarki ba, da na jira har lokacin da za ki dawo gareni.

Horn yayi maigadi ya buɗe, tana jin haka ta buɗe idanunta da suka kaɗa suka yi jajir. Yana yin parking ta fita, shima ya fito ya rufe motar sannan suka nufi hanyar da za ta sadasu da main parlour. Knocking yayi sannan suka tsaya jiran a buɗe.

Ranta a ɓace ta buɗe ƙofar ta kallesu taƙi matsawa. "Farhan...." "Kin ga dakata" Farhan ɗin ta dakatar da ita cikin tsawa. "Farhan meke damunki ne?" Khalil yayi maganar cikin ɓacin rai. "Ai kafi kowa sani, dan cin mutumci shine ka kawo min ita har gida" Mamaki Jannat ta shiga ta kasa gane abinda ke faruwa. "Farhan ni ce fa?" "Kin ga dan Allah saurara, da mijina nake magana ba dake ba ƴar uba" "ƴar uba..." ta maimaita kalaman. "Eh mana, ai dama ance duk yadda kake da ɗan uba sai ya nemi ya tozarta ka, ke kika guje shi, amma kuma yanzu saboda kin rasa mashinshini shine za ki dawo ki liƙe masa, to wallahi baki isa ba" Hannu ya saka ya ɗauke ta da mari. "Dama ashe baki da mutumci? Bakin ki ne ke faɗar wannan furuci akan Yayarki?" hannunta akan kunci ta kalleshi "Dole ka mareni, tunda an barbaɗa a ruwa an baka ka sha, an riga an asirce ka, kuma bazan yafe mata ba, sai na ɗauki mataki" ɗan murmushi Jannat tayi mai ɗauke da ƙwalla. "Yaya Khalil ko dan larurar da take ɗauke da ita bai kamata ka mareta ba, ka san mai ciki lallaɓata ake" ta kalli Farhan ta ce "Ke kuma ki yi haƙuri, kin san ko giyar wake na sha ba zan auri Yaya Khalil ba tunda yana aureki da muka fito daga jini ɗaya, kuma in sha Allah zan nesanta kaina dashi gudun zargi" "Da yafi miki sauƙi, in babu aure akwai rayuwar bariki ai, ki fita harkar miji na" ɗaga hannu yayi zai sake marinta, Jannat tayi saurin riƙe hannunsa, sai kuma ta saki. "Dan Allah kayi haƙuri, zan fita a rayuwarku" da sauri ta juya ta fara tafiya. "Farhan duk son da Jannat ke miki yau ita kike faɗawa haka? Jannat fa?" murguɗa baki tayi kawai ta koma ciki.

#Follow

#Vote

#Share