Page 20
by @sanazty
•••SANADIN MAHAIFINA•••
Wattpad@SaNaz_deeyah
Arewabooks@sanazty
Facebook@Habibtyn Habibi
YouTube: ***
Tiktok: ***
Facebook Page
***
Karku manta ku shiga links ɗin nan ku yi following handles ɗina
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
'''Shafi na 20'''
"Akan Jannat yanzu kumatuna ya zama madakar ka ko yaushe?" ta faɗa hannunta na kan kuncinta, hawaye na zuba daga idanunta. "Akan Jannat za ki iya fuskantar ko wane irin ɓacin rai"
Tashi tayi tsaye ta kalleshi ranta a ɓace yake sosai, ta saka hannu ta goge hawayen idanunta "Ai yanzu ma bata ɓaci ba tunda kana tausayin Jannat ka sakeni sai ka aureta" wucewa tayi har ta buɗe ƙofa ta juyo ta kalleshi. "Kuma ka sani wannan cikin sai na ɓarar dashi wallahi, dan bashi da wani amfani" tana fita yayi saurin bin ta ya tari gabanta. "Me kike nufi da hakan?" "Ai kafi kowa sani" ta faɗa tana aika masa harara. "Farhan dama ashe ke kallon kitse nakewa rogo?" bata bashi amsa ba kawai ta wuce.
****
"Ka sani muddin kace za ka auri yarinyar nan wallahi sai na saɓa maka, kuma sai na hanaku jindaɗi" Mommy ta faɗa rai a ɓace. Rayyan dai shiru yayi ya kasa cewa komai.
"Ni wallahi abin har mamaki yake bani, sai kace wanda aka asirce" Khairat ta faɗa tana ajje waya kan cinya. Ranshi a ɓace ya ce "Idan muna magana da Mommy kina saka baki ranki zai mugun ɓaci"
"Ai ni ya kamata kazo ka rufe da duka sai in san kaji haushi Rayyan, ka huce akan Khairat, ai nina fara magana ita ƙarasawa tayi" bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya bar ɗakin.
"Shashasha" Mommy ta faɗa tana bin shi da kallo. "Wallahi Mommy ina ganin Yaya sai kin haɗa da addu'a, dan ba banza suka bar shi ba" "Da alama kam, dole sai na tashi tsaye, dan muddin ina raye ba zan taɓa bari ya auri wannan watsatstsiyar ba."
****
"Sannu Jannat, Allah yasa wannan abu ya zame miki kaffara" kallon Ummu tayi bata ce komai ba, sai Mommy da Daddy ne suka amsa. Khalil yana daga gefe kusa da Daddy.
"Yanzu baki buƙatar komai?" Daddy ya tambaya cike da kulawa. "Bana so na mutu yanzu" ta faɗa idanunta cike da hawaye. "Ba za ki mutu ba Jannat, insha Allah sai kin ga ƴaƴanki har ma da jikoki, ita cuta ai ba mutuwa bace" Ummu ta faɗa tana dafa kafaɗarta, Yayinda Mommy ta tashi da sauri ta fita, dan ji tayi
zuciyarta ta karye.
"Khalil mene ya hana Farhan zuwa?" Ummu ta tayi tambayar. "Itama bata jindaɗi ne, amma tace zuwa gobe in sha Allah za ta zo" ya shimfiɗa ƙarya ba shiri. "Allah ya bata lafiya" Ummu ta faɗa sannan ta maida kallonta ga Jannat.
Da Khalil da Daddy da Mommy ƙarfe 11 na dare suka bar asibiti, dan Ummu cewa tayi a wannan karon ita za tayi jinya.
****
Ta juya masa baya, magana yake amma sam taƙi ta tanka masa, har sai daya gama sannan ta juyo ta kalleshi. "Ka faɗa min gaskiya, mene tsakaninka da wannan da ake kira da Jannat" "Wace gaskiya bayan wacce na faɗa yanzu" "Sa'ad ni fa sam ban gamsu da abinda ka faɗa ba, domin yadda take magana kamar ka zalunceta ne"
Cikin zafi ya miƙe tsaye "To na zalunceta, ke mene naki a ciki da zaki zo ki titsiyeni da surutu" "Nawa a ciki shine kai mijina ne, kuma yana da kyau in san duk wani sirrinka" "To Jannat tsohuwar budurwata ce, sauran labari kuwa ki tuntuɓeta sai ta faɗa miki" ya ja tsaki ya fita ya bar gidan gaba ɗaya.
Zama tayi kan kujera tare da kafa tagumi.
Bayan kwana uku
Yana saka links sai ga ta ta shigo ɗakin. "Za a tafi gurin karuwar kenan" bai tanka mata ba, dan ya lura a kwanakin nan, sai faɗar magana take son ranta, gashi sam asibitin ma ba ta je ko so ɗaya ba, hakan ya tabbatar masa cewa lallai tana kishi da Jannat irin sosai.
"Ai dama na san baka kulani, saboda ka riga ka faɗa min cewa baka da zuciya." nan ma bai kulata ba, ya ɗauki hula ya koma gaban mirrow yana gyara karinta. "A gidanku da ka tashi baka taɓa ganin gyatumarka da kishiya ba, amma kai da alama da da hali wannan karuwar za ka aura"
Ranshi a ɓace ya kalleta ya ce "Amma ai ke taki gyatumar gidan wata ta shiga ta zauna, kuma ba a nuna mata kishi ba, sai ke kike kishi da macen da babu abinda zai saka ta zama kishiyarki" ƙara haɗe rai tayi ta nuna shi da yatsa. "Duk abinda za muyi kada ka sake haɗo da mahaifiyata" "Oh ashe ba daɗi ni kika yi wa tawa" "Eh nayi mata ɗin, ai haka ta zauna daram a gidan ubanka ba kishiya, ko kuma tana bin mazan titi ne ba'a sani ba kayo gado b......." bata san lokacin daya ƙaraso gareta ba, saboda kukan kura yayi ya damƙi wuyanta ya shaƙe, tare da mannata da bangon ɗakin. Nishi take idanunta duk sun yo waje, yayinda nashi idanun sukayi jajir. "Ba zan taɓa lamuntar cin mutumci daga gareki ba, ina ƙaunar iyayena yanda baki zato, ke wacece da zaki zagesu, yaushe aka yi ki Farhan? Kije kawai na tsinka igiyar aurenmu dake gaba ɗaya ukun, ba a kanta kike hauka ba? To na sakeki"
Cire hannunsa yayi daga wuyanta, ta zunduma ihu tare da zubewa a gurin tana kuka. Bai ko bi ta kanta ba kawai ya fita ya shiga mota ya nufi asibiti.
"Na shiga uku, wallahi ba zan taɓa lamunta ba, ni wallahi ban saku ba" kuka sosai take, ita idanunta gaba ɗaya sun rufe akan kishi, shiyasa har ta tafka kuskuren zagin mahaifiyarsa.
A ƙofar ɗakin ya tarar da Mommy da Ummu, gaishesu yayi, sam ya kasa haɗa ido da Ummu, duk da ya san a lokacin bata san anyi saki ba. "Khalil wai meyasa Farhan taƙi zuwa, idan na kirata sai tace za tazo kuma najita shiru, gashi yanzu za a wuce da Jannat ɗakin theater" "Za tazo itama" ya faɗa kan shi a ƙasa, a dai-dai lokacin aka fito da Jannat, da rigar theater a jikinta, aka turo gadon tare da Daddy.
A gurin aka tsayar da gadon, Mommy ta ƙaraso tana hawaye ta riƙe hannuwan Jannat. "Ki yafe min Mommy" ta faɗa tana hawaye. "Jannat na yafe miki, kuma in sha Allah za ki fito lafiya." kallon Abba, Ummu da Khalil tayi "Ku yafe min kuma ku faɗawa kowa ya yafeni dan Allah" "Ki daina faɗar haka Jannat, za ki karya mana zuciya" Ummu ta faɗa tana goge hawaye. Tare suka wuce har sai da aka shiga da ita sannan suka tsaya bakin ƙofar.
*****
Kuka sosai take tana durƙushe akan carpet gaban Mommyn Khalil. Shahina kam ta zuba tagumi kawai tana kallon Farhan cike da tausayawa.
Mommy tsaki ta fara a karo na ba adadi sannan ta ce "Ya san yayi laifi shine yaƙi ɗaga wayata" "Nima na kira bai ɗaga ba" Shihina ta faɗa tana ƙara dialing number Khalil.
Ya fiddo wayar ya ga missed calls na Mommy rututu, ya tabbatar Farhan ta faɗa mata, yana shirin kiranta sai ga Shahina ta kira. Ɗagawa yayi ya kara a kunne ba tare da yayi magana ba.
"Yauwa Mommy ya ɗaga" Shahina ta faɗa tana miƙa mata wayar. Karɓa tayi ta kara tare da rufe shi da faɗa kuma tace ko mene yake ya dawo tana son ganin shi. "Mommy wallahi wayata na silent ba da gangan naƙi ɗagawa ba, kin san yau za a yiwa Jannat aiki, kuma yanzu haka an shiga da ita ma" "Ni dai na sanar maka ka zo yanzu ina son ganinka" ta faɗa tare da katse wayar.
Ajiyar zuciya yayi sannan ya koma inda su Daddy ke tsaye. "Daddy anyi kira na a gida zanje na dawo" "To ba damuwa Khalil, Allah ya dawo da kai lafiya" "Amin ya rabbi."
*****
Cikin faɗa ta kalleshi "Ba shawara bace umarni nake baka da ka mayar da Farhan ɗakinta yanzu-yanzu" kan shi a ƙasa bai ɗago ya kalleta ba, ya ce "Mommy saki uku nayiwa Farhan ba ɗaya ba" mari ta wanka masa, ranta a ɓace muryarta da alamun kuka tace "Ni za ka tozarta Khalil? Yanzu duk irin halacci da yarinyar tayi maka, da wane ido kake so in kalli ɗan uwana, kaine zaka lalata zumuncin dake tsakanin mu"
"Kiyi haƙuri Mommy, zan iya lamuntar komai, amma bazan jure a zageki ba, ta zageki shiyasa idona ya rufe" Kasa ɗago kai Farhan tayi saboda kunya, bata taɓa tunanin Khalil zai faɗa ba. "Ai ni ta zaga ko? To na yafe mata, amma ka daina saurin yanke hukunci cikin fushi, yanzu da wane ido zan kalli mahaifinta in faɗa masa wannan batu duk da ya kasance ɗan uwa a gareni" shiru Khalil yayi bai ce komai ba. Sai kuma ya miƙe tsaya "Mommy zan wuce saboda nima bana jindaɗi" kasa cewa komai tayi har ya fita.
Yamma
"Za muje mu dawo saboda Sa'adatu ta ce tana gidan tana jira na, ina tunanin wani abu ne ya haɗa Khalil da Farhan, dan naji alamun kuka a gefenta, kuma naji tace muzo tare da ita Maman Farhan ɗin."
Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To Allah dai yasa lafiya" "Amin ya rabbi, amma dai da fatan ba matsala?" ya faɗa yana kallon Jannat dake kwance kamar gawa har a lokacin bata farfaɗo ba . "Eh babu, ai tunda anyi aiki lafiya to Alhamdulillahi"
"To za muje mu dawo in sha Allah da mun gama da ita, dan kar a barki ke kaɗai" 'Ba damuwa ai ƙawayenta naji sunce suna hanya, karku damu" Ummu ma cewa tayi "To bari muje Allah ya ƙara sauƙi" "Amin ya rabbi" Mommy ta bata amsa.
*****
Shiru Daddy yayi na ɗan lokaci sannan ya ce "Na san Khalil yana da hankali ba zai taɓa yin abu da ka ba, me kika masa?" yayi maganar yana kallon Farhan. "Ba...bab...ba...ba abinda nayi masa" ta faɗa tana share hawaye" "Karya kike" Ummu dai bata ce komai ba. Mommyn Khalil ta sake cewa "Rashin hankali ne kawai na Khalil, nayi masa faɗa sosai, taya zai saki yarinya har saki uku kuma a lokaci ɗaya, dan Allah ina neman afuwar ku kuyi haƙuri da wannan abu daya faru."
Ummu tsam ta tashi tayi side ɗinta, yayinda Daddy ya bita da kallo. "Na san dama dole taji ba daɗi, nima naji zafin abin bare ita da aka sakarwa ƴa" cewar Haj Sa'adatu. "Babu komai Allah yasa haka shine mafi alkhairi" "Ina fatan hakan ba zai saka zumuncinmu ya wargaje ba." "Haba Allah ya kiyaye, su ƴaƴa ai ba su suka haɗamu ba, kuma shima ina fatan hakan ba zai saka ya gujemu mu ba."
Kafin ta tafi sai da ta karɓi Acct number Farhan ta tura mata dubu ɗari kuɗin da za ta riƙa renon cikinta, tace kuma idan sun ƙare ta faɗa mata, Daddy yayi ta faɗa akan me zata tura, ai da Khalil da Farhan duk ɗaya ne a wurinsa.
Anan falo aka bar Farhan da ƙyar ta iya miƙewa ta shiga ɗakinsu tana kuka, kayanta ma a falo ta bari. Duk abinda take bata taɓa tunanin Khalil zai saketa ba, tunda auren dole ma aka mata, amma yanzu gashi ya ci amana ya saketa.
Daddy kuwa yana shigowa ya wuce side ɗin Ummu. A zaune gefen gado ya sameta. "Amma bai kamata muna cikin magana ki taso" "Taya bazan tashi ba, me kuma zan ji? Aikin gama ai ya gama, an dai cuci Farhan, yarinya ƙarama an ruguza rayuwarta, an mayarta ƙaramar bazawara, kuma saki da ciki, auren da ko wata shidda baiyi ba" "Ni sam bana blaming Khalil, domin ba zai taɓa yanke ɗanyen hukunci haka ba tare da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba" "Eh ai yanzu zaka ce haka, tunda yana ta ɗawainiya da kai da kuma Jannat, ni bana wuce ɗayan biyu, Khalil ya saki Farhan ne dan ya auri Jannat" "Amma matsayinki na mai hankali sam bai kamata ki kawo wa kanki wannan tunanin ba" "Dole na kawo, kuma bazan taɓa yafewa ba, an cutar da ƴa ta, ba zan ƙara ganin girman shi ba" ta faɗa tana share ƙwalla." Fita kawai Daddy yayi ya barta dan ya san a yanzu dai ba zata fahimce shi ba.
*****
General Hospital
Male Ward(Amenity room)
Umma na zaune gefen gadon da Sa'ad yake kwance, Hanne da Zulaihat suna daga tsaye, yayinda Doctor ma ke tsaye yana rubutu a file. Bayan ya gama ya ɗago ya kallesu. Sa'ad ma idanunsa akan Doctor yana jiran yaji abinda zai faɗa.
"Sannu ko?" "Yauwa Doctor" Sa'ad ɗin ya faɗa yana kallon sa. Kallon Umma yayi ya ce "Allah ya taƙaita bayan ciwon dake goshin sa bai samu wani rauni ko wani illa ba sai a guri ɗaya" tashi Sa'ad ya ke ƙoƙari yi amma ya kasa. Doctor ya ɗanyi shiru yana karantar fuskarsu sannan ya ce "Ya samu nakasa a private part ɗin shi, wanda hakan ya saka ba zai taɓa iya haihuwa ba" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Duk suka faɗa cikin tashin hankali.
"Doctor me kake nufi da hakan? Shikenan ba zan ga jini na ba?" "Ka godewa Allah daya taƙaita iya haka" "Haba Doctor gara ace na rasa ƙafa da hannu da ace na rasa haihuwa" ya faɗa lokacin da wasu zafafan hawaye suka fito daga idanuwansa." Umma ma kasa daurewa tayi ta fashe da kuka. Haka Hanne da Zulaihat ma. Doctor dai ƴan nasihohi yayi masu kan su ɗauki ƙaddarar da Allah ya ɗora masu.
Yana fita Zulaihat tayi saurin bin bayansa, sunan shi ta kira ya tsaya. "Doctor ni matar shi ce, kuma bamuyi shekara da aure ba, ina so a duba ni ko ina da ciki dan Allah" "Kina da file a cikin asibitin nan?" "A'a bani dashi" kwatance ya mata inda za taje ta yanko kati, da kuma inda zataje a duba aga ko tana da ciki.
Ta shiga tashin hankali lokacin da aka ce mata bata da ciki, a sanyaye ta koma ɗakin ta tarar da su duk sunyi jugum-jugum.
Zama tayi a ranta tana ayyana cewa ba za ta taɓa iya zama dashi a haka ba, dan itama tana son haihuwa.
Bayan sati biyu
A cikin wannan sati biyun abubuwa da dama sun faru. Ummu bata ƙara komawa asibiti ba, saboda ƴan uwanta sun zugata kan lallai Mommy ce tayi asiri aka saki Farhan, dama ta Farhan ba'a magana dan bata taɓa zuwa dubiya ba. Haka Khalil bai ƙara zuwa asibiti ba, kuma ya kashe wayoyinsa.
Ta ɓangaren Sa'ad kuwa an sallameshi daga asibiti sai dai tuni Zulaihat ta kwashe kayanta tayi gidansu, kuma iyayenta dashi kan shi abokin nasa sai da suka masa rashin mutumci akayi hayaniya sosai, sannan Umma taga ba zata iya ba tace kawai ya saketa, dan ta dage a saketa ita ba zata zauna dashi ba shi kuma yace ba zai saketa ba, da abun ya ishi Umma ta saka dole ya sake ta. Kuma ta saka ya dawo gida da zama, saboda bai ƙarasa warkewa ba, kuma ga damuwa a tattare dashi.
****
Tunda suka shigo gidan suka zauna a falo, Jannat ta kalli Mommy cikin damuwa ta ce "Mommy shikenan kan gidan nan ya ruguje" "Jannat ya za ayi haka Allah ya ƙaddara, ke dai kawai ki cigaba da addu'a, kuma ki daina saka damuwa a ranki" Kai kawai ta gyaɗa mata.
Knocking da akayi ya saka Mommy tashi ta buɗe ƙofar "Sannunku da zuwa" shine abinda ta faɗa sannan ta basu hanya suka shiga falon "Gaidasu Jannat tayi dan ita kam ta shaidasu"
"Ai munji kun dawo shiyasa nazo da zafi-zafi" "Tofah, Allah yasa lafiya" Mommy ta faɗa tana kallonta. "Nazo ne akan ɗana, ina so ki gargaɗi ƴarki, ta fita a harkar Rayyan, ya dage sai ya aureta, ni kuma akwai tanadin da nayiwa ɗana ba kuma anan gidan bane"
Mommy da Jannat tare suka miƙe tsaye, a dai-dai lokacin Ummu na sakkowa daga ƙafar bene. "Ina gargaɗinta da kada ta aureshi, dan wallahi saina fitini rayuwarta, sai ta gwammace batayi aure ba" tana gama faɗa ta miƙe tsaye. "Khairat muje" Harara Khairat ta watsawa Jannat sannan tabi bayan Mommynta suka wuce. "Ikon Allah" Mommy ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. "Mommy yaushe nake soyayya da Rayyan? Mutumin da ko magana bamu taɓa yi ba" ta faɗa fuskarta da tashin hankali a cikinta. "Karki ɗaga hankalinki, zauna ki nutsu, ki shaƙi numfashi sosai" Ummu kam juyawa tayi ta koma, Mommy ta bita da ido kawai sannan tayi dialing number Alhaji Mas'ud.
Yana ɗagawa ta ce "Kana ina ne, ka dawo gida akwai matsala" daga can ɓangaren ya ce "Ai gani nan akan hanya ma, naje gidan Khalil kuma tare muke dashi" "To sai kun ƙaraso" ta faɗa tare da zama kan kujera.
30 minutes later
Daddy, Mommy, Ummu, Khalil, Jannat da Farhan ne zaune a main parlour, kowa yayi shiru bayan Mommy ta gama yiwa Daddy bayanin zuwan Mahaifiyar Rayyan gidan.
"Tabbas Mahaifin shi ya sameni da maganar, kuma nace masa ya jira zan shawarci mahaifiyarta da ita kanta, Rayyan bashi da matsala, amma dai kafin waccan maganar bari mu fara ta Farhan."
Annurin fuskarshi ne ya ɗauke, ya kalleta "Kin ce baki masa komai ba, yanzu ya faɗa min abinda kika masa kuma abinda kikayi kin cancanci saki, Farhan wannan itace tarbiyyar da nayi miki?" shiru tayi bata ce komai ba, sai Ummu ce tace dashi "Ko kisan kai Farhan tayi ai bata cancanci saki ba, tunda taimaka masa tayi ta auresa"
"Babu wani taimako, nine da kaina nace zan haɗa aurensu" Daddy ya faɗa cikin faɗa. "To ai sai ka faɗi laifin da tayi, har ta cancanci saki har uku bama ɗaya ba?" "Ta cewa mahaifiyarsa karuwa, ni kuma a iya sanina kaf danginmu ba'a taɓa samun mara tarbiyya ba, ai ba Khalil kaɗai kikayiwa ba, har dani kika zaga" "Ai ruwa baya tsami banza. Hakanan ba za ta zagar masa mahaifiya ba" Ummu tayi maganar da faɗa.
"To ai ga ta nan sai ta faɗi abinda yayi mata kamar yadda shima ya faɗi dalilin sakinta" ɗago kai Farhan tayi rai a ɓace tace "Nima ai ya zagi tawa" "Bayan kin zagi tashi ba, amma yace mata karuwa?" shiru Farhan tayi. Daddy ya kalli Ummu ya ce "Ga tanan ki tambayeta abinda tayi masa, tunda haka kika zaɓa sai ki cigaba"
Miƙewa Ummu tayi ta kama hannun Farhan ta miƙar da ita. "Ba zan cigaba da zama anan ba, domin raina ne zai ta ɓaci, amma ka sani Khalil bamu yafe ba, ka cutar da ƙanƙanuwar yarinya" Janta tayi suka tafi Daddy na faɗin "Ka da Allah yasa ku yafe ɗin"
Dawo da kallon sa yayi ga Khalil "Ka da ɗan wannan abu ya ɓata maka rai, ni na fahimceka" kai kawai ya gyaɗa, Mommy dai tunda aka fara har aka ƙare bata ce komai ba, ita kuwa Jannat har a lokacin taƙi ɗago kanta.
"Yauwa ga me da batun Rayyan kuma, me za ki ce a ciki? Domin na faɗawa mahaifinsa sai kin amince sannan zan bashi damar ya fara zuwa hira, dan ku fahimci juna." sai a lokacin ta ɗan ɗago kai, suka haɗa ido da Khalil tayi saurin sauke ƙwayar idanunta ƙasa.
"Me kika yanke?" Daddy ya sake tambaya. A firgice ta ɗan ɗago, cikin sanyin murya ta ce "Ina so nayi shawara da Yaya Khalil" "Eh hakan ma yana da kyau, lallai kin fara hankali Jannat" Kallon Mommy yayi ya ce "Muje mu basu guri su tattauna ko" tashi Mommy tayi suka bar falon ita da Daddy.
Ɗago kai tayi ta ƙara kallon Khalil, still idanunshi a kanta. "Ko dai na canza maka kamanni?" ta furta a sanyaye. "Eh mana, kamar ana zuƙeki sai ƙara ramewa kike" "Hmmm to ya za ayi rayuwa ce. Yanzu dai ka faɗa min me zan faɗawa Daddy game da Rayyan" "Ki faɗawa Daddy baki son shi" zaro ido tayi tana kallon shi "To ko kina son shi?" "Ba haka bane, ni da bamu taɓa magana ba, taya ma na fara sonshi" "Akwai crushing ai" ɗan murmushi tayi sannan tace "Amma meyasa kace haka?" "Saboda mahaifiyar shi bata ƙaunarki, ko kin aure shi wahala kawai zaki sha, ko kuma tayi miki wani abun, tunda har ta iya takowa tazo nan tayi gargaɗi"
Ɗan dafe kai Jannat tayi tare da faɗin "To shikenan" "Jannatu...." ya faɗi sunan da salon da bai taɓa faɗa ba. Ɗagowa tayi ta kalleshi bata ce komai ba. Shi kuma ya cigaba da faɗin "Akwai mutum ɗaya, wanda shi kaɗai ne zai iya riƙeki da amana, kuma zai iya tunkarar ko wane irin ƙalubale a kanki, a shirye yake ya karɓi ko wane irin zagi da cin mutumci a dalilinki, a shirye yake ya bada ranshi domin ke ki rayu"
Kallon shi tayi cike da mamaki ta ce "Amma waye wannan? Kuma a ina yake?" ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ba kowa bane face ni, Jannat zan aureki" Cikin tashin hankali da tsananin firgici ta miƙe tsaye.
#Vote
#Share
#Comment