PAGE 17.
by @sumy6163
💫💫RASHIN SANI 💫💫
STORY AND WRITTEN BY: Sumaiya M Tukur (the Charismatic).
Dukkan godiya ta tabbata gab Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta annabi Muhammad (SAW).
Godiya mai tarin yawa tare da jinjina ga 'yan' uwa marubuta da suka karfafa mini gwiwa wurin yin wannan rubutu, Allah ya Saka musu da alkairi ya kara daukaka su.
Wannan labari kirkirarre ne, idan yayi kama da rayuwar wani ko wata, to arashi ne.
PAGE 17.
Dariya sukayi, sannan Aisha ta tabo Aimana da ta daskare a wurin kamar statue tana karewa Kamal kallo, firgit tayi ta dawo duniyar mutane, cikin waskewa tace..
"Kun ganshi can, kuzo mu karasa".
Binta kawai sukayi ba tare da sunce komai ba, suna zuwa suka ja kujera suka zauna a table dinda yake.
Aimana ce ta fara masa magana da wani irin muryar da ita kanta bata san tana dashi ba, gaishesa tayi sannan ta gabatar masa da Sabin kawayenta, cikin sakin fiska suka gaisa, daga nan sukayi ordern snacks da drinks, suna sha suna dan hira.
Ana hira ne amma gabadaya Aimana ta tattare hankalinta akan Kamal, kallonsa kawai take cike da shauki, tana admiring yanda yayi kyau.
"Ya Kamal, kayi kyau", haka kawai ta samu kanta da furtawa ba tare da ta ankare ba.
"Allah ko my Aima, tunda kin yaba, wanka ya biya kudin sabulu".
"Kajika, sai kace dama don ni kayi".
"Don ke nayi mana, to wa zanwa duk cikin makarantar nan, tunda banda wata kanwa bayan ke".
"Hmm, Ya Kamal kenan, to nagode, duk da nasan fada kayi, amma dai I feel honoured".
Hira suka cigaba dayi, gabadaya sun manta da su Aisha da suke wurin, Aimana idan tana gaban Kamal mancewa da kowa takeyi, can Kamal ya kalli Aisha tace..
"To wai Sabin kawayen namu basa magana ne?"
"A'a yayanmu, ai magana kam sai ka gaji, kawai mun dan barku ku gama naku ne, kar mu shiga tsakanin, ko ba haka ba Aina'u?"
"Hakane sis, amma yanzu idan kun gama sai mu fara namu".
Duka Aimana ta daka mata tace, "Zakuji dashi ai, dama hiran namu daban naku daban ne, anyways kunga Yayana da kukace ina muku rowarsa, to gashi nan, ya kuka ganshi".
"Ba laifi, Yayan namu"cewar Aisha Kenan.
Kamal ne ya katse su da fadin, "karfe nawa kuke da class ne, kar dadin hira yasa ku rasa lectures".
"Kaidai ya Kamal, muna sane da time, sai karfe biyu, kaifa?", Aimana ta tambaya.
No ni yau banda class sai dai zamuyi tutorial anjima, kinsan munzo gangara, yanzu sai an maida hankali"
Aisha ce tayiwa Aina'u signal, sannan tace, mukam bari mudan zaga nan muna zuwa, suka mike suka basu wuri.
Ganin haka yasa Aimana ta ware, ta rika zuba masa shagwaba, tana wani kashe murya, shima kuwa sai ya biye mata, don yasan Aimana tun da shagwababbiya ce, hira kuwa sukayi sosai, har zuwa azahar suna wurin, karshe ma order abinci sukayi sukaci, daga nan suka wuce masallaci.
A can Aimana ta hadu dasu Aisha, har ga Allah ita ta manta tare suka je cafeteria, sai yanzu data gansu.
Dariyar shakiyanci suka shiga yi mata, Aina'u tace, "sai yanzu aka gama hiran soyayyar?".
"Wani irin hiran soyayya kuma Aina'u, kuma daga cewa bari kuje ku dawo sai kuka ki dawowa".
Aina'u tace, "Kaji yar rainin hankali, idan ba hiran soyayya ba to me kukeyi, ai shiyasa muka baku wuri, don naga kamar muna takura Ku".
"Kwaji dashi, da Yayan nawa zanyi hiran soyayya, yaya nane fa".
"Uhumm Aimana munji, ai muna nan, gaskiya zatayi halinta", Aisha ta fada, tana fara alwalanta.
Daga haka suka shiga masallaci, sukayi sallah, sannan suka koma hall dinda zasuyi lecture, karfe biyu kuwa na cika sai ga malamin nasu ya shigo, basu suka gama ba sai karfe hudu har kusan da rabi.
Suna fita sukayi masallaci, suka gabatar da salla, ganin bata da wani class yau yasa ta dannawa direbanta kira, yau dai tace da wuri zata gida, tana sauke wayar kuwa sai ga kiran Kamal.
Dagawa tayi tana sakin murmushi ta kara a kunnenta, sallama tayi ya amsa sannan yace..
"Ya class, kun fito ne, ko har kin wuce gida, nazo ban ganki ba"
"Dagaske ya Kamal kazo, ban tafi ba, muna ta wurin masallaci, amma ka jirani yanzu bari nazo".
"Ok to sai kinzo".
Ta juya ta tace wa su Aisha, bari taje ya Kamal ne yake kiranta, Aisha tace..
"To kenan yau Aimana baza ki tsaya mu duba abunda aka mana dake ba?".
"Ku duba mana kawai, nima zan duba a gida, idan Allah ya kaimu gobe sai mu sake dubawa", tana gama magana tayi gaba ko jiran amsarsu batayi ba sai ce musu tayi, "see you guys tomorrow insha'Allah".
Tana zuwa kuwa ta hangoshi zaune yana jiranta, karasowa tayi itama ta zauna tace..
"Gani ya Kamal, ashe da gaske kakeyi".
"Ai to da kin dauka da wasa nakeyi ne, mun gama tutorial namu ne nace bari nazo nayi sallama da kanwata, ai na zaci har kin tafi".
"Ai driver dinma bai iso ba, muna can haraban masallaci ne tunda mukayi sallah, dama zamu dan duba karatun mu ne"
"Baku gane karatun bane?"
"No kawai muna dubawa ne, inda bamu gane ba sai muyi jotting, so that mu tambaya next class".
"Ok, gashi na taso ki, ya za'ayi Kenan"
"Don't worry, nace su duba, idan naje gida zanyi nawa".
"Okay muga littafin naki".
Mika masa tayi, ya fara bi yana karantawa, introduction ne, yana yi yana mata tambaya, inda bata gane ba kuma ya mata bayanin, suna haka driver dinta ya iso, ce masa tayi ya dan jirata kadan, don taji dadin bayanin da yake mata.
Saida suka gama tas, ta kuma fahimta sosai, ya mata tambayoyi don ya kara tabbatar da ta fahimta, sannan sukayi sallama ta tafi.
Ita da tace yau da wuri zata gida, sai gashi yauma ana Isha suka iso, don magariba a gate din makaranta ya samesu.
Yauma kamar jiya, wanka kawai tayi, tayi sallolinta, sannan ta nemi wuri ta kwanta, ta jawo littafinta tana dubawa, kafin can Mama ta biyota da abinci, tana gama ci kuwa minti talatin tsakani taje ta kwanta.
Yauma kamar jiya haka suka dau lokaci mai tsayi suna waya da Kamal, saidai sabanin jiya, yau hiran duk akan karatu aka kareshi.
Washegari kuwa koda taje makaranta, kafin su shiga class sai da ta musu explaining duk inda basu gane ba a darasin jiya.
Aisha tace, "lallai ma Aimana, kice kekam kin gane komai, shiyasa kika yi tafiyarki jiya ko ta kanmu baki biba".
"Kudai ayi sha'anin kawai, ya kamata mu tafi class lokaci ya kusa", suka mike kuwa suka tafi, yau ma to 6 suka fita, don haka yauma komawar dare tayi.
Haka Aimana ta gama first week dinta a makaranta, kullum da safe take fita, sannan sai bayan magariba take dawowa.
Da aka shiga weekend kuwa, ran Saturday wuni tayi tana bacci, ran Sunday ne tayi dan abunda zatayi, sannan ta shiryawa Monday, Abdul ma ranan ya daga abunsa, sai Abuja.
Koda Monday tayi, Aimana ta cigaba da zuwa makaranta, kamar ko yaushe ne dai,ba abunda ya canza, duk lokacinda suka samu sarari kuwa suna haduwa ita da Kamal, duk da bai cika zama ba, kasancewar yawancin karatunsu yanzu a hospital ne, ko suna can suna wani practical din, da yake su sunyi nisa.
Kullum kuma da dare haka suke kwashe tsawon lokaci suna waya, idan kuma zasuyi karatu, sai suyi video call.
Sosai Kamal yake taimaka mata da karatunta, don yanzu su Aisha ma idan basu gane wani abunba wurinta suke zuwa, za kuwa ta musu bayani su fahimta, don idan aka musu abu, idan Kamal yazo sai ya kara buda mata darasin sosai.
Karatu ya mika, semester yayi nisa, don har sun fara test, jefi jefi, gashi yanzu kullum sai ta dawo da assignment biyu ko uku, rana daddaya ne take dawowa da daya, yanzu take fahimtar yanda karatunsu yake da wahala.
A bangaren Kamal ma kusan haka ne, don har gara Aimana ma, basu cika haduwa ba, don yanzu mafi yawan zamansa a asibiti ne,in ya shigo dai to da abunda ya kawo shi, dayake Aimana ma kai ya dau wuta, sai rashin haduwarsu din bai dameta sosai ba.
Kwanci tashi ba wuya, su Aimana sun yi jarabawar first semester, kuma Alhamdulillahi ya mata sauki, ba kamar yadda ta tsammani ba,sauran jiran result.
Gabadaya hutun da suka samu wani iri Aimana take ji, don yanzu ita har ta saba da school life, zaman wuri dayan sai ya gundire ta, saukin ma Kamal yana nan, amma fa hutun nan shima baida wani zama sosai, saboda asibiti yake zuwa, saidai suna waya.
Abdul ma ya samu hutu, ya dawo, harda su Junior, wanda shima yanzu shekaran karshe yake, shi da Munnir.
Sosai Aimana ta canza, baza ma ace ita bace, duk wannan rashin ji da fitinar babu, ta zama wata miskila na bugawa a jarida, magana ma wahalar yi yake Mata, bare kuma wani takalan fada, amma fa kar ka tabota, nan zaka fahimci mai hali baya canza halinsa.
A wannan lokacinne kuma Nana ta haihu, abin yayiwa Aimana dadi, gabadaya suka dunguma suka tafi Abuja suna.
An sha shagali ba kadan ba, inda yaro yaci sunan kakansa, baban mijinta, suna kiransa da Aryan.
Bayan suna da kwana biyu suka dawo, amma Nana tace anan Aimana zata karasa hutunta, sabida haka ba'a koma da ita ba, da farko abin ya mata dadi, amma daga baya rashin Kamal a kusa yasa ta fara tunanin komawa.
Nana ce ta lura kwana biyu Aimana kamar akwai abunda yake damunta, amma tambayar duniya Aimana tace ba komai, sai kawai ta barta a haka, Saidai tsab Nana ta karanci kanwar tata, don duk wanda zai kwana ya wuni da Aimana sai yasan sunan Kamal a bakinta.
Watarana suna zaune a parlour, Aimana tana rike da Aryan tana masa wasa, hira sukeyi da Nana, can ta jefowa Aimana tambaya..
"Nikam Aimana, wai me yake tafiya ne tsakanin ki da Kamal?"
"Me kika gani adda Nana, ni ba komai a tsakanin mu sai mutunci".
"Aimana kenan, kallo ni nan, kinsan dai na baki shekaru ya kai goma, sannan na fiki sanin wasu abubuwa dayawa, ba abunda zaki boye min Aimana, ina lura dake sarai, don haka ki fada min, kar ki yadda ki boye min komai".
Tashi Aimana tayi taje ta kwantar da Aryan a kan gadonsa, sannan ta dawo ta zauna kusa da yayar tata, sunkuyar da kanta tayi kafin ta fara magana..
"Bansani ba Adda Nana, bansan ta ina ya faro ba, bansan yaushe ya faru ba, bansan kuma dalilin faruwar hakan ba".
"Meye din kenan ya faru Aimana?"
"Bazan boye miki ba Adda Nana, na dade ina neman wanda zan fadawa ban samu ba, wallahi Adda Nana ina son Kamal, ina masa wani irin so da ni kaina bansan adadinsa ba, ina jin tamkar Kamal shine rayuwata, ina tsoron randa zatazo babu Kamal, don na tabbata zai kasance babu Aimana", wani irin kuka ta saki mai ban tausayi sannan ta cigaba da magana..
"Kinsan me yake damuna kuwa Adda Nana, bansani ba ko shima Kamal yana min irin wannan so, wallahi Adda Nana ina tsoron rasa Kamal, zan iya mutuwa idan haka ta faru".
"Innalillahi wa inna ilahi raji'uun" shi kawai Nana take ta maimaitawa tana kallon Aimana, wacce take kuka bilhakki, can ta rikota sannan tace..
"Kiyi hakuri Aimana, kiyi shiru".
Cigaba da kuka Aimana tayi, ta kasa ma yin shirun.
"Kiyi shiru Aimana, muyi magana, amma kina wannan kukan nima kina daga min hankali, ki natsu muyi magana".
Dakyar ta samu ta tsayar da kukan, dama ta dade tana neman inda zatayi bata samu ba sai yau.
Matsowa Nana tayi, ta share mata hawayen fuskarta, sannan ta riko hannuta tace..
"Ki natsu Aimana, inason ki amsa min tambayoyin da zan miki".
Daga kanta Aimana tayi, alamun tana sauraren ta.
"Shin Aimana Kamal shi da kansa ya gabatar da kansa a wurinki matsayin masoyi?"
Girgiza kanta tayi tace, "A'a"
"Ya taba nuna miki alamar yana son ki?".
"Banace ba, saidai nasan yana kokarin faranta min, kuma ya damu dani, yana kuma bani lokacinsa duk sanda ya samu dama".
"To kenan ko a cikin hira bai taba baki wani kafar da zaki fahimci akwai wani abu a zuciyar sa game dake ba kenan, baya nuna miki wani alamu na soyayya saidai kulawa?"
"Kusan haka"
"Hmmm, tirkashi, lallai kuwa idan haka ne akwai matsala"
"Wani irin matsala Adda Nana?"
"Aimana kenan, har yanzu ke yarinya ce,da sauranki tukunna, kai tsaye bazance Kamal baya sonki ba, duba da yanda mu'amalarku take, amma shawaran da zan baki anan shine, kiyi kokarin ganin kin rage wannan soyayyar da kike masa, kar ki zurfafa, kuma duk rintsi ki rike wannan sirrin a ranki, kar ki yadda ki bari Kamal ya fahimci irin son da kike masa, ki bari har sai shi da kansa ya furta yana sonki da bakinsa, idan ba haka ba kuma, wallahi zaki kuka a gaba".
"Amma Adda Nana, don na bari ya fahimci yadda na daukesa a raina ai ba komai bane, watakila gano hakan yasa shi kara ganin girmana, ko don albarkacin soyayyar da nake masa, kuma naga ko a addinance ai babu laifi".
"Ba laifi bane Aimana, amma abunda nakeso ki fahimta shine mazan da dana yanzu ba daya bane, a yanzu idan kika nunawa namiji kina sonsa, to daga nan zai daina ganin mutuncinki, wani kuma haushiki ma zai fara ji, wani kuma idan akayi dace ya karbi tayinki, to abunda zai biyo baya wulakanci ne, baki isa kuma kiyi magana ba, zaice ai dama ke kikace kina sonsa, zai ta miki gori ne har abada koda kuwa yana sonki, misalan suna da yawa Aimana, bance duka ba mazan haka suke ba, tunda baza'a taru a zama daya ba, amma mafi yawanci haka ne yake faruwa".
"Yanzu Adda Nana ya kike so nayi, wani lokaci fa ji nake kamar in fada masa kawai ina sonsa a wuce wurin"
"Kul na gaya miki, kar ki yadda ki fara wannan kuskuren, nidai na fada miki".
"Shikenan Adda Nana, zanyi iya kokarina insha'Allah, saidai ku tayani da addu'a".
"Kullum muna miki Aimana".
Haka Nana tayi ta bata shawarwari, da nasiha, ta kuma kawo nuna mata illar abinda take shirin aikatawa, sun dauki lokaci mai tsayi kafin suka tashi a wurin.
A bangaren Kamal kuwa, karatunsa kawai yasa a gaba, baza'a ce baya missing Aimana ba, amma sam hakan bai shafi al'amuran rayuwasa ko na karatunsa ba, lafiya lau yake rayuwarsa, sabanin Aimana da ta daurawa kanta damuwa da tunaninsa.
Kwanci tashi, hutunsu ya kare, Aimana ta shirya don komawa gida, Nana ta mata shopping sosai na duk wani abun bukata, ta kara saya mata wasu sabbin kayan, ita Aimana a yanzu har bata san adadin yawan kayan da take dasu ba, wannan ma Mama tana dauka ta kyautar wa masu bukata.
Dan zaman da tayi da Nana, ta koya mata dabarun zama da Kamal, ta yanda zata iya takunta, kuma Aimana tayi mata alkawarin insha'Allah zatayi kokarin kwatantawa, don ko a yanzu ta nuna mata ta rage yawan nemansa a waya, kuma ta rage din, saidai abunda ya bata mamaki shine Kamal baiyi korafi ba, kuma bai nuna abun ya damesa ba sam.
Haka ta tattara ta koma, aka cigaba da gashi, tana komawa, Abdul kuma yana zuwa, don a gidan Nana yake Zama, daga nan yake zuwa school dake ba nisa, su Munnir kuma suna hostel.....