13&14
MANARAH
©️MEENAT A 'YANDOMA
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***
DEDICATED TO
ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai miki a duk inda ki ke🫶🥰
PG 13&14
...Tamkar tsayawar ruwan sama haka komai ya lafa hatta kukan da jinjirar ke yi.
Mikewa ya ke so ya yi sai dai ji yayi tamkar an ɗaɗɗaure ilahirin jikinsa, hannuwansa da ke rike da jinjirar ya ji sunyi sanyi da kyar ya samu ya miƙe.
Duk da duhun dake rufe da idonsa bai hana shi gane hanyar da ya shigo ba.
Gefen wata itaciya ya samu ya zauna ya na me sauke ajiyar zuciya.
Kallon farko da yayi mata sai da ya ji gabansa ya yanke ya fadi.
A maimakon ya ga fuskarta da alamun hawaye na kukan da take tsalawa sai ganinta ya yi ƙamas! Babu alamar kuka a tattare da ita face kafe shi da tayi da ido ko kyaftawa bata yi.
Kayan dake jikinta ya kalla fes da su overroll ce sai wani tsumman zane da aka nannaɗeta da shi.
"Wa ya haifeta ya 'yar? Aa ba ta yi kama da ɗiyar tsintuwa ba, ko dai iyayenta suka ajiye ta su je su dawo."
"Wace uwa ce zata aje ɗiyarta a cikin ƙasurgumin jejin?"
Wata zuciya ta yi saurin gargaɗinsa ta tunatar da shi.
Gabas, yamma, kudu da arewa ya kalla. Babu kowa face bishiyoyi da ke faman rangaji a cikin iska.
Rana ta farko da ya ji hankalinsa ya tashi ina zai je da wannan jinjirar? Alkawari ya yi shi da komawa gida sai dai in mahaifinsa ya nemesa da kansa.
Miƙewa yayi ya ci gaba da tafiya har ya karasa kusa da motarsa.
Buɗewa yayi ya saka jinjirar wadda bai raba ɗaya biyu ba sabuwar haihuwa ce.
Tayar da mota yayi ba tare da sanin inda zai nufa ba, kai tsaye gidansa ya nufa.
…Kwance take a bisa cinyar Mahaifiyarta suna raha. "Mama gani kike kamar abinda na fada ba zai tabbata ba ko?"
"Haba Shukura! Hisham fa kike ce wa zaki aura nan da mako ɗaya? Yaron da ko gidan nan bai baya zuwa karshe ma babu maganar da ta haɗa iyalai biyu wato maganar aure. Ke dai ki ci gaba da neman kudinki ki tara mana duniya kawai, sannan In kince aure za kiyi wa zai aureki. Shi kuma Mahaifin Deena ya za ki yi da shi?"
Mahaifiyarta ta karasa maganar cikin damuwa.
Mikewa Shukura ta yi tare da fuskantar Mahaifiyarta.
"Mama duk abinda zan faɗa ba za ki gane ba. Mahaifin Deena da kike magana kuma ai aure ba zai hanani yin tarayya da shi ba. Kawai dai ki zuba ido ki gani nan da mako ɗaya za a daura mini aure da Hisham."
Murmushi Mama ta yi.
"Hmm! Shukura Kenan. Ina so in ga ranar da wannan mafarkin naki zai tabbata, domin bai da maraba da mafarki. Ke dai kamar yadda na fada miki ki ci gaba da tara mana kudi tunda Allah ya raba mu da zafin talaucin dake bibiyarmu, dangin mahaifinki kuma su gane Kuskurensu na watsar da mu bayan mutuwar Babanki"
"Mama kenan! Ke dai ki sha kuruminki. Ni dai abinda nake so ki zuba ido sanin kanki ne duk abinda na ce zanyi to fa zanyi. Kin tuna lokacin da muke cikin zafin talauci na ce miki za mu yi kudi? Shin munyi kudi ko kuma ba mu yi ba?"
"munyi kuɗi mana! Abin da ke kudi ma kuwa. A ƙalla abinda na sani kin tara gidaje da motoci hatta gidan nan na alfarma da muke ciki in ban manta ba kince Mahaifin Deena ne ya mallaka miki shi."
"To Mama ki saka a ranki aure ni da Hisham kamar anyi an gama ne. Bari ki ga in tashi in nufi wurin me gyaran jiki domin yau muka kulla za mu a fara mana, kin san amarya da wuri take fara gyarawa"
Ta na karasa maganar ta fada ɗakinta mayafi ta dauko ta fice daga gidan.
Umma da ke zaune me aiki ta kwalawa kira a kan ta zo ta miko mata ruwa....
...Deena da ke zaune abin duniya ya isheta, tunda gari ya waye take tunanin maganganun da mahaifinta ya fada mata.
Afra ta kira suka hade a inda suka saba haduwa.
"Ni kam lafiya kika kwala min kira ko dai Hisham ne ya mutu?"
Harararta Deena ta yi
"Ke kuma da mugunwar fata, to yanzu Yazid ya tabbatar mini da an sallame shi. Wai ni Afra me ya sa ba kya son Hisham"
Ya mutsa fuska ta yi kafin ta fara magana.
"Dalilin da ya sa kika kirani kiji ko kuma akwai wata magana me amfani da za mu yi?"
"Allah ya huci zuciyarki don naga yau a wuya kike"
"amin idan da gaske kike"
Ta karasa maganar tare da karbar lemun da ke gabanta.
"Afra kin kuwa san Shukura tare suke da Daddy?"
Tsabar firgita lemun da ta kurba ba shiri ta feso shi waje.
"Ban gane ba! Wane dadyn kike nufi?"
"Daddy dai mahaifina da kika sani"
Kaf abinda ya faru tsakaninsu ta sanar da ita. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke.
"Amma baki tunanin asiri ta yi masa. Ni dai a ganina gaskiya ki duba lamarin nan banza ta barshi ba"
"Ba wani asiri da ta yi masa Afra. Ina ma ta yi masa to kadan ne ya kama shi. Zargin da nake Daddy a cikin kungiyar asiri ya ke Shukura ita ce mahadin arzikinsa.
"What! Kin kuwa san abinda kike fada?"
"Na sani Shukura! Ina da tabbacin abinda nake zargi"
"Amma dai Deena a yau na tabbatar da baki da hankali. Yanzu da ma za ki iya zargin Mahaifinki a kan wata banza can, zargin Mahaifinki daidai ya ke da zargin nawa Mahaifin domin aminan juna ne komai a tare suke yi"
Shukura ta karasa maganar a fusace tare da mikewa tsaye.
"Subhanallahi! Wallahi ba nufi na bane haka. Ban kiraki domin in bata miki ba, kin san kaf duniya bani da abokiyar da ta fiki. Kiyi hakuri mu bar wannan maganar tuba nake"
"Deena bazan boye miki ba Wallahi kin bata mini rai matuka. Yanzu duk soyayyar da Mahaifinki ke nuna miki ki rasa sakayyar da za ki saka mai da ita sai wannan ƙage da sharrin haba Deena"
"Na gane kuskurena kiyi hakuri ba zan kara ba"
Hararar ta Shukura ta yi domin ta san halin kawar Tata...
Umma tun bayan tafiyar Hisham take kuka ta rasa me ke mata dad'i, anya kuwa Alhaji na cikin hayyacinsa.
Hawayen da ke fuskarta ta share jin motsin mutum zai shigo. Ƙafarsa da zai saka cikin ɗakin jibgegiyar damisa ce taso masa tamkar zata haɗiyesa.
"Wayyo Allah!"
Ya karasa maganar tare da faduwa kasa.
Umma da ke zaune a dan rikice ta miƙe ganin Alhaji a cikin irin halin da bata saba ganinsa ba. Kokarin magana take masa amma ina ganin ya fara rarrafe, hauhawar tashin hankalinta karuwa ta yi ta biyoshi ta na fadar lafiya.
Alhaji kuwa ji yayi gurnanin damisa na kara kusanto inda ya ke da dai Allah ya ba shi dai Allah ya ba shi sa a ya mike tsaye bai bata lokaci ba ya zabga da gudu. Take masa baya tayi sai dai lokacin da suka karaso falo yayi wuff ya shige cikin dakin Hajiya.
Hajiya da ke tsaye bakin kofa domin ta san haka zata faru da sauri ta fito ta na murmushi.
"Yaya mun shiga uku! Alhaji ba lafiya"
Umma ta karasa maganar ta na kokarin fadawa dakin. Da sauri Hajiya ta daga mata hannu.
"Babu matsalar da ya samu, lafiyarsu ƙalau game da dakin ki dai ne tsakaninki da Alhaji sai gani sai hange. Ba dai kince sai kin zauna a cikin gidan nan ba? Wallahi sai kin gudu da kafarki"
"Sai Gani sai hange kuma? Ban fahimci me kike son fada ba."
"Za ki fahimta nan ba da jimawa ba. Domin hausawa sunce gani ya kori ji, don haka ki zuba ido tsakaninki da shi sai gani sai hange"
Ta na karasa maganar ta shige daki ta bar Umma nan tsaye zuciyarta na son fahimtar da ita abinda Hajiya ke nufi...
Hisham da ke tsala gudu a titi canza shawara yayi a kan Hotel zai je kawai kila a can ya samu nutsuwar tunanin yadda zai yi da wannan tsintacciyar jinjirar.
Lokacin da ya kama daki da mamaki ma'aikatan hotel din ke kallonsa da jinjira amma babu uwarta. Kauda zancen suka yi da tunanin kila uwar ta na baya.
Bayan ya shiga dakin kwantar da ita ya yi saman gado. Ya zauna gefe ya na kare mata kallon, wasan ta take da idanunta buɗe tarr kamar ba jinjira ba.
Mantawa ya yi ya baro abu cikin mota, har ya miƙe sai kuma ya tuna wa zai barwa jinjirar.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan mata ya kira ya ce ta kula ma shi da dakinsa tare da miƙa mata key. Da mamaki ma'aikaciyar take kallonsa amma da ta tuna kudi zai biyata sai ta nufi dakin ta bude amma babu komai. Gabanta ta ji ya fadi sai ta ƙi shiga cikin dakin ta tsaya bakin kofa.
Bayan ya dauko wayarsa a bakin kofa ya iske ma'aikaciyar, kallonta yayi ya shige dakin. Sai dai kafin ya karasa ya ja tunga ya tsaya
"Ke ina jinjirar take ko goyata kika yi"
Da mamaki ta kallesa tare da juyawa ta kalli bayanta ta cikin mirror, domin ita dai tun shigowata ko mage bata gani ba bare kuma jinjira.
"Sir wace kuma jinjira? Ai babu komai cikin dakin nan tun da na shigo"
"Kada ki raina mini hankali mana. Ki fito da ita bana son wasa domin banyi kala da wanda za ki yi ma wasa ba"
Ya karasa maganar tare da hade girar sama da ta ƙasa.
"Sir wallahi banga kowa ba cikin ɗakin nan! "
Ganin zata raina masa wayo fizgota ya yi ya mayar da ƙofa ya rufe.
"Ko ki fito min da jinjira ko kuma a mutu har liman"
Jin abinda ya faɗa ya saka ma'aikaciyar fara zabga ihu ta na neman taimako. Ihun da take kwalawa shi ya fito da kaf ma'aikatan Hotel ɗin aka fara bugun ƙofa sai dai babu alamun Hisham zai buɗe.
Wata irin zufa ce ta ɓallewa me Hotel ɗin lokaci daya ya ji ƙafafunsa sun kasa ɗaukar sa. Idan aka yi kisa a Hotel dinsa ya maganar makomarsu, Kafin su ankara ya yi ƙasa...
DAGA GOBE LITTAFI YA KOMA AINAHIN KUDINSA 500 KU TURO 300 ZUWA WANNAN ACCOUNT NUMBER 8133562798 Opay Amina Abubakar
MASU NEMAN DAGA FARKO KU SHIGA NAN👇👇👇