MANARAH

15&16

by @meenatyandoma

MANARAH

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai miki a duk inda ki ke🫶🥰

PG 15&16

..."Subhanallahi Sir! Ko dai mu kira jami'an tsaro ne?

Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya karasa maganar tare da riko ogansu.

"Ku rufamin asiri a fito da yarinyar nan ba tare da wani abu ya sameta ba. Maganar jami'an tsaro kuma ku aje ta a gefe. Muddun jami'an tsaro suka shigo cikin maganar nan, kashina ya bushe wata ƙilama lokacin karayar arzikina ce ta zo"

"Amma Sir Baka ganin kome zai iya faruwa idan ba a kirasu sun fasa kofar nan ba? Tun dazu fa sai faman zabga ihu take ba tare da mun san me ke wakana ba"

Jin alamar an bude kofa ne ya saka ma'aikatan karasawa bakin kofar.

Sai dai Hisham ne tsaye da belt sai huci yake, kallo daya za ka masa ka gane a fusace ya ke.

"Bawan Allah lafiya zaka samu ma'aikaciyarmu ka ci gaba da jibga kamar Allah ya aiko ka. Anya kuwa kana da cikakkiyar lafiya?"

"Ka iya bakinka kafin ina fizgoka In hada da kai in mayar da dakin nan in rufe. Ku har kun isa ku ɓatar mini da jaririya sannan ku ce ina kyaleta? Ko dai ta fiddo min jinjira ko kuma duk wanda ke cikin Hotel ɗin nan sai ya yabawa aya zakinta"

Hisham ya karasa maganar tare da karayin bake-bake a kofa.

"ku taimamin ku fiddo ni daga cikin nan, wallahi ina kuka barni kasheni zai yi. Ban san da wata jaririya ba wallahi bani na dauketa ba Sir ku saka baki "

Shugaban wurin kuwa jin Muryar ma'aikaciyarsa na raye da karfin guiwa ya mike tare da karasowa bakin kofar.

"Bawan Allah ka dai duba amma na san Gloria BA Zata taba daukar maka jinjira ba"

"Ina ba ita ta dauketa ba wa kuke nufin ya dauketa, kunga ku fito mini da ɗiya tun kafin in aikata abinda zai janyo a rufe wannan Hotel ɗin"

A zabure shugaban Hotel ɗin ya sake kallonsa.

"Kada mu yi haka da kai, ka bamu hanya mu shigo za a fito maka da diyarnan. "

"Ina kuka shigo ba ku fito da ita ba kun yarda in dauki ko wane irin mataki ne?"

"Ba ma zata kai mu ga haka ba, kai dai ka matsa mu shigo"

Hanya ya ba su suka shigo sai dai ya tarbe kofa ta yadda babu wanda ya isa ya fita har sai In shi ya bada hanya.

Ɗaya daga cikin masu dubawar ne ya duƙa ƙarƙashin gado.

A firgice ya mike tare da nuna karkashin gadon.

"Sir wallahi wani abu"

"A ina!"

Hisham ya fada a hanzarce

"a karkashin gadon nan. Wallahi na tsorata ina dukawa ya kawo min hari da Faratansa"

Ya karasa maganar ya na haki.

Me Hotel ɗin jin abinda aka fada wata irin motsawa cikinsa ya yi. Lokaci ɗaya ya ji ya bada wani sauti ƙuuw!

"Joseph duka ka gani me ye"

Ja da baya Joseph ya yi tare da fiddo ido.

"Ni kuma Sir! Wallahi ba zan iya ba. In dai sai na duka a wurin nan ka koreni a aiki tun yanzu"

Ya karasa maganar tare da komawa bakin kofa.

Abin mamaki duk wanda aka ce masa ya duka ya duba sai ya tirje ya ja baya.

A fusace Hisham ya tunkari ƙarƙashin gado.

Ganin ya saka hannu karkashin gadon ya saka mutane da dama ja da baya suna jiran tsammani.

A dan rikice kowa ke kallonsa. Sai dai Gloria ta fiddo ido waje cike da mamakin yaushe ya saka jinjira cikin dakin.

Shi kuma Hisham mamaki fal a fuskarsa ya ke kallon jinjirar da ke wasa da hannunta cikin baki alamun yunwa take ji.

"Ka aje yarinya a ƙarƙashin gado amma ka na mana rashin mutumci. A kan haka za mu iya riƙe ka tare da maka ka ƙara a koto na bata mana suna da kaso yi"

Kallon baka da hankali Hisham ya yiwa Shugaban hotel din.

"Kotu fa ka ce? To don Allah ku gaggauta kai ni. In aje yarinya saman gado sannan daga in fita in dawo na taras da kun canza mata wuri zuwa ƙarƙashin gado. Zan iya maka ku kotu in ce kuna so ku salwanta mini da yarinya, wa ma ya sani ko tsafi kuka so yi da ita?"

Ya karasa maganar ya na rungume jinjirar a kirjinsa.

Wasu yawu masu ɗaci shugaban Hotel ɗin ya haɗiye.

Hakika in suka yi wasa wannan fa ya fi su bariki. Abin da ya fi shi ne su lallaba su rabu lafiya.

Don haka cikin hikima ya fara magana.

"Ka ga mun ɓata maka, amma kayi hakuri in Shaa Allah hakan ba zata sake faruwa a. A madadina da na Gloria mu na masu kara baka hakuri, sannan ko kwana nawa za kayi ba zamu amsa kudinka ba"

Ya karasa maganar tare da tattare duk wasu ma'aikatansa suka fice.

Bayan ya kulle dakin kwantar da ita ya yi ya zauna. Rana ta farko da ya fara tafka tagumi

"Me ke faruwa? Ko dai yarinyar nan ba mutum ba ce. Anya gobe da safe ba zai kaiwa Umma ita ba don ya san kaf duniya ita ɗaya ce zata fahimce shi"

Ina zai samu abinda zai bata wa zai kuka masa da ita? Da wadannan tambayoyi ya yi bacci.

Wani irin ciwon kai ne ya yi masa dirar mikiya tilas ya kwanta lokaci daya ciwon da ke ziyartarsa a mafi yawan darare ya afka masa.

Sunansa ya ji ta na kira daga nan bai sake sanin me ke faruwa ba sai da gari ya waye.

Babban abin da ya bashi mamaki shi ne yadda ya ga yarinyar idanuwanta ƙamas tamkar babu alamun tayi bacci sai faman tsotsar hannu take yi.

A gaggauce ya shirya ya fito. Ba karamar murna ma'aikatan Hotel din suka yi ba ganin sun rabu da ala ƙaƙai.

Kai tsaye gidansu ya nufa ya na jin gabansa na faduwa.

Inda Allah ya rufa masa asiri shi ne ba kowa a cikin falon, kai tsaye dakin Umma ya nufa.

Shigowar Hisham cikin ɗakin sai da ta saka gabanta yin mummunar faduwa. Ba shiri ta mike tsaye.

"Hisham! Me nake gani haka, daga ina?"

"Umma ɗiyar jeji ce Maranah ce wannan"

Ya samu bakinsa da furta wa ba tare da ya ba shi izini ba.

"Ɗiyar jeji kuma Manarah? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!"

Ta karasa yin maganar tare da yin zaman daɓaso a saman gado.

"Umma don Allah ki amsheta ki bata abinci ko madara ce a dama mata, sannan ban san yadda zan mata wanka ba shi ma duk ayi mata"

Wasu zafafan hawaye ne suka ɓallewa Umma, ganin yadda Hisham ke kora mata bayani ba tare da fargaban komai ba. Anya ya san me zuwa da jinjirar da bai san asalinta ke nufi ba a cikin gidan nan? Ya za su kare da mahaifinsa?

"Hisham!"

Ya ji ta kira sunansa da wata irin murya.

Jiki a sanyaye ya fuskance ta.

"Ka fadamin gaskiya ko dai wata ka yiwa ciki ta kawo maka diyarka? Hisham ka fadamin gaskiya"

Da mamaki ya ke kallonta.

"Ban ta miki karya ba ko da kuwa gaskiyar da na fada miki ba zata yi miki dadi ba. Umma diyar jeji ce amma in kin yarda"

Ya karasa maganar tare da sungumar Manarah ya miƙe.

Hajiya da ke labe tun lokacin da suka fara magana da sauri ta zabga da gudu ta sanar da Alhaji halin da ake ciki.

Ya na karasowa falo ya yi kicibis da Alhaji da Hajiya tsaye su na dakonsu.

Hankalin Umma kara tashi ya yi. Lokaci daya ta ji wani gumi ya hau wanke mata jiki.

Alhaji kuwa kallo daya za ka yi masa sai gabanka ya fadi sakamakon mawuyacin hali da ya shiga.

"innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Shi kenan Alhaji, sunanmu ya gama ɓaci ɗiyar shege a cikin gidanka. Da wane ido zaka lalle mutane?"

Hajiya ta karasa maganar ta na me fashewa da kuka.

A fusace Alhajin ya ci kwalar Hisham da ke rike da jinjirar.

"Hisham shegiya! Shegiya a cikin gidana. Na yi nadamar haihuwarka Hisham, Kashe ni kake so ka yi bakin cikinka shi zai zama ajalina"

Ga ni suka yi ya saki Hisham tare da dafe saitin zuciyarsa. Kafin su yi wani yunkuri Alhaji ya yanke jiki ya faɗi cikin ƙara i da kururuwa suka yi kansa....

KAMAR YADDA NA FADA BONONZA TA ƘARE LITTAFI YA KOMA AINAHIN KUDINSA WATO 500 ZAKU TURO TA WANNAN ACCOUNT DIN. 8133562798 Opa Amina Abubakar

COMPLETE PAGES SUNA NAN CIKI 👇👇

***