17&18
MANARAH
©️MEENAT A 'YANDOMA
Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***
DEDICATED TO
ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai miki a duk inda ki ke🫶🥰
PG 17 & 18
...Hajiya da Umma a gigice suka fara girgiza Alhaji da ke kwance wani irin kumfa na fitowa a bakinsa.
Hisham kuwa ko a jikinsa kujera ya samu ya zauna ya na rirrika Manarah.
Kan shi ya fara tambaya kamar haka
"Wa ya fada mini sunanta Manarah? Ko dai da gaske na fara zarewa, in haka ne bai kamata in ci gaba da renon jinjirar nan ni daya ba."
"Ka yi aure ta nan ne zaka iya kula da ita a cikin aminci. Amma matar da zaka aura zata yarda ce wa wannan ɗiyar ba mara uba ba ce? "
Wata zuciyar ta yi saurin tunatar da shi.
Jin karar mota da ya yi an fita shi ne ya ba shi tabbacin asibiti suka nufa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da kwalawa me aikinsu kira.
Mika mata ita ya yi a kan ta bata madara.
Ba musu ta amsheta ta nufi Kitchen.
Sai dai abinda ya tsorata me aikin ba karami bane, domin kaf madarar da ta dama mata ta shanyeta, jiki na ciri ta maido masa ita domin ita dai ko a tatsuniya bata taɓa ganin inda haka ta faru ba.
Wayarsa da ta fara ruri ce ya kalla, bai so dauka ba amma ba shi da yadda ya iya dole ya dauka
Umurnin daahaifiyarsa ta ba shi ne ya saka shi ajiye wayar ransa a matukar ɓace.
Daukarta ya yi suka nufi asibitin. Tun daga nesa ya hade girar sama data kasa, Babban aminin mahaifinsa wato Alhaji Lukhman mahaifin Yazid da ya hango ne tare da Yazid din ya saka shi matsala kusa da su.
Shi dai Yazid sake da baki ya ke kallon wannan ikon Allah. Kamar a mafarki Hisham ne rike da jinjira shi da ya tsani yara. In bai manta ba ya sha fada masa in ya yi aure ba zai yarda matarsa ta haihu ba, saboda yara liability ne.
"Me ya kawo ka? Nan ma ka biyoshi ne ka karasa kashe shi, Hisham Allah wadaran haihuwarka ka fice daga asibitin nan tun kafin in sanar da duniya halin da kake ciki"
Hajiya ta karasa maganar cikin ƙaraji.
Alhaji Luluman ne ya yi saurin tarbarta.
"Subhanallahi! Me yayi zafi haka ko ma me ya aikata bai kamata a tayar da maganar a nan cikin mutane ba. Ki duba ki gani daga fara maganar hankalin kowa ya dawo a kanmu. Kamata ya yi mu fara nemansa Alhaji lafiya in ta kama daga baya sai mu yi maganar"
Shuru ta yi amma ba haka ta so ba, ta so ta tara ma shi mutane ta yadda kowa ma zai san ainahin halin da ake ciki.
Ummu kuwa ba baka sai kunne. Tun ta na kukan da hawaye ta har ta koma yin kukan zuci.
Likita ne ya fito daga dakin ya na tambayar waye Alhaji Lukman? Da sauri ya amsa tare da mikewa tsaye.
Bayan likitan ya bi suka shige dakin.
Kallo daya ya yi Alhajin ya tabbatar ya na cikin matsananciyar damuwa gami da tashin hankali.
Alama ya yi da a kira Hisham da kuma mahaifiyarsa.
Ba don ya so ba sai don nuna ɓacin ran da mahaifiyarta ta yi ya saka shi mikewa suka nufi dakin.
Da dishasshiyar murya ya fara magana.
"Lukman ka shaida ni Alhaji Biliya na fitar da Hisham daga cikin..."
Saurin toshe masa baki ya yi ya na fadar subhanallahi!
"Me yayi zafi haka? Ina ga mu bar wannan maganar har zuwa lokacin da Allah zai baka lafiya. Tayar da maganar nan a wurin nan ba shi da wani amfani face mu tonawa kanmu asiri. Kai Hisham ka fada mana gaskiya me ye alakarka da jinjirar nan"
"Tsintarta na yi kuma gaskiya ko me za a fada ba zan yarda in rabu da ita ba"
"Ka ji ko? Kana jin irin abinda ya ke fada. To shi kenan ka je na barwa duniya kai, dama me kake tsinana mini in Banda ɓacin rai da bakin ciki"
"Assha! Amma banso wannan maganar ta na fita a bakinka ba. Hisham dai ɗan ka ne kuma duk lakacewarsa har abada da ɗan ka za a kira shi. Wallahi kai ma kana da matukar laifi na munana dan nan da kake yi, na rasa me ya sa duk soyayyar da ku ka nunawa juna a baya yanzu sam babu ita. La'anta ko kuma tsintuwa babu abinda za su kara masa face karasa lalacewa. Shawara daya zan baka ita ce ka yi masa aure indai kana son zaman lafiya da kwanciyar hankali. Sannan wannan ɗiyar daya tsinto a nawa ganin kawai a barta a hannunsa ai temako ne yayi"
"Kayya Lukman! Shi baka kula da tsabar kamannin da ke tsakaninta da Hisham ba? Sannan maganar aure ya na a haka wa zata yarda ta aure shi. Sai dai ya je nemo daya daga cikin karuwansa ya aura."
Alhaji ya karasa maganar a fusace.
" Relax Alhaji! Wannan me sauki ne domin na san ba zai rasa wadda ya ke so na. Kuma aure zai iya zamowa hanya ta nutsuwarsa in Shaa Allah. Kai kuma na dawo kanka, kana da wata wadda kake so ne?"
"Eh amma su biyu ne, don gaskiya biyu zan aura"
Da mamaki suke kallonsa jin abin da ya furta.
"Lukman ko mata hudu zai yi ba damuwata ba ce nan da mako ɗaya ka tabbatar an gama wannan aure. Sannan ku buɗe kunnenka da kyau ku ji ni ko wani dangina babu wanda zai halarci bikin nan. Na wakilta ka a kan komai."
Ya karasa maganar tari na sarkesa. Bayan sun fita waje Yazid ba karamin mamaki ya yi ba.
"Ta ya zaka ce mana sunanta Manarah sannan kuma ka ce ba diyarka ba ce. To wa ya fada maka sunanta?"
Kallon baka da hankali ya yi ma Yazid.
"diya ta ce akwai yadda zaka yi da Ni?"
"Haba ko da na ce"
Yazid ya karasa maganar ya me amsar ta.
Rass! Gabansa ya yanke ya fadi.
Wata irin kururuwa Yazid ya saki tare da yin jifa da Manarah ya yanke jiki ya fadi....
MASU TUROMIN 300 PLS NA RUFE BONONZA TUN KWANA BIYU. LITTAFI YA DAWO AINAHIN KUDINSA 500
GOBE FREE PAGE ZAI KARE. KU TURO DA KUDINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 8133562798 Opay Amina Abubakar
Meenat A 'Yandoma
***
KU YI JOIN WANNAN CHANNEL DIN DOMIN SAMUN LITTAFIN DAGA FARKO 👇👇👇
***