MANARAH

19&20

by @meenatyandoma

MANARAH

©️MEENAT A 'YANDOMA

Wattpad: Meenat_A_Yandoma

ArewaBooks: Meenatyandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

MASU BUKATAR A TALLATA MASU HAJARSU SU YI MIN MAGANA A WANNAN NUMBER ***

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA (Jasmine) Alherin Allah ya kai miki a duk inda ki ke🫶🥰

PG 19&20

... Cikin tashin hankali jama'ar da ke wurin suka yo Kansa ana salati da sallallami.

Hisham kuwa rai a matukar ɓace ya dauko Manarah da ke ke yashe a ƙasa. Da taimakon wata Nurse aka shigar da Yazid ɗaki. Cikin ikon Allah ba a dauki dogon lokaci ba ya farfaɗo domin wani abu da ya firgitasa ne ya saka shi suma.

Tambayar duniya an masa amma amsa daya yake bayarwa.

"Ba za ku gane ba. Ku dai ku yi addu'ar kada Allah ya sa ku ga abin da na gani"

Tambayarsa Suke me ka gani amma shuru har suka gaji suka kyale sa. Hisham kuwa ya san wanene Yazid don haka dole akwai dalili, ruwa ba ya tsami banza"

Alhaji Lukman kuwa bai kawo komai ba a ransa abin da ya dauka shi ne kila ya na da wata damuwa ne da ya kasa sanar da shi.

Don haka a gefe ya ja Hisham ya yi masa kwatancen gidajen 'yan matansa. Gidansu Deena bai yi masa wuyar ganewa ba domin mahaifinta sananne ne. Gidansu Shukura ne dai ya so ya ba shi wahala.

A kofar gida ya aika yaro ce war ana sallama. Shukura da ke kwance ta na dannar waya mahaifiyarta ta kalla.

"Mama ki fito kila ma manemin aurena ne ya zo, ba dai gani kike duk tatsuniya ce nake miki ba"

"Haba Shukura, daga yin sallama sai ki ce manema aurenki ne suka zo. Ki dai jira in je in gani, na san me gadi bai dawo daga aiken da aka masa ba da a wurin shi za mu ji su waye"

Ta karasa maganar tare da ficewa.

Bayan sun gaisa ya sanar da abin da ke tafe da shi.

Ba ƙaramar kaɗuwa Mama ta yi musamman da ta ji da gaske Ɗan gidan Alhaji Mukhtar ɗan canji ne zai auri Shukura kuma nan da mako ɗaya.

Ganin jikin Mama na kyarma ya saka Alhaji Lukman ya ce su shiga daga ciki. A nan suka tsaida maganar zuwa gobe ta sanar da dangin mahaifinta zasu kawo sadak, sannan su faɗi kuɗin lefe nawa suke so sai a haɗa hada su.

Har bakin get Mama ta yi masa Rakiya.

Ta na shigowa falon Shukura ta ruga da gudu ta rungumeta.

"Yauxu dai kin tabbatar da nan da mako ɗaya amarya na ke ko?"

Ta karasa maganar ta na dariya.

"Ke 'yar nan! Wane irin Boka ne kika mallaka haka? Anya kuwa Shukura?"

"Ai Mama ba ki ga komai ba. Ta shi za kiyi in Kira driver ya Kai mu gidan kawu yanzu ba sai anjima ba"

"Yau ni na ga rashin kunya! Hada ke zamu tafi a sanar da maganar auren naki?"

"Me ye abin wani boyo ko jin kunyar mutanen can. Da ni za a tafi ta yadda in ma ba zasu iya ba ni da kai na In he in Nemo wasu iyayen"

“Wane su? Ai ba zasu iya ba kinga ta shi mu je"

Bayan sun karasa gidan sunyi sa a kawu Mati na gida bai tafi kasuwa ba.

Ya na hangosu ya fara watse baki domin ko ba komai ya san yau miyar gidansa zata canza.

Bayan sun gaisa take sanar da shi halin da ake ciki. Kawu Mati na jin Ɗan gidan Alhaji Mukhtar ɗan canji ne zata aura ai sai ya kara washe baki.

Luba matarsa da ke gefe tsoma baki tayi cikin maganar ba tare da sun sako da ita ba.

"wannan wane irin aure ne za a ce nan da mako ɗaya? Ya dai kamata kuyi bincike"

"To munafuka! Ayi binciken me? Lokacin da muka hadu kin san da haduwarmu ne. Ba tun yau ba na san ke ce babbar algungumar da ta hana Kawu ya tallafe mu a lokacin da muke cikin zafin talauci. Wato yanzu ma kinji gidan da zani huta shi ne kike so ki hana mini zaman lafiya ko?"

Shukura ta karasa maganar tamkar zata kai mata shaƙa.

"Kinga luba ɓace mini da gani. Kada ki kuskura in Kara jin bakinki a wurin nan. Ke kuma ɗiyar albarka ai abin da ya wuce, ya wuce. Ba kyauta tuna baya"

"Yanzu dai Kawu ga wannan kudin ka siya dinkakkun kaya masu kyau kai da kawu dan Juma. Sannan a gidanmu zaku hadu da azahar, saboda na kula kaf gidajenku babu inda za a iya aje wani bako"

Baki ya kara washewa ya na zabga mata addu'a.

Umma kuwa bata iya hakuri ba, tun a asibitin ta sanar da Mahaifiyarta halin da ake ciki. Allah ya sani bata so auren nan na Hisham ba amma babu yadda ta iya. Addu'ar ta ita ce Ubangiji ya sa shi ne sanadin shiryuwarsa.

Hajiya kuwa ba karamin dadi ta ji ba domin ko ba komai a yanzu ne take da tabbacin rayuwar Hisham tana a cikin matsala, abu ne me wahala ya haye tudun da take shirin ɗora shi.

Kamar yadda ya fada washe gari aka kai kudin neman aure tare da sadaki da kuma kudin lefe. Nan suka tsaida ranar aure sanar da su asabar me zuwa.

Jikin Alhaji ya ji sauki washe gari aka sallamesu.

Duk yadda Yazid ya so a hada sharholiya wadda zata gigita duk wasu kwari, amma sam Hisham ya kafe babu abinda za a yi ga biki. Ko wace amarya in ta na so ta haɗa ita da kawayenta.

Da Yazid ya matsa sai anyi a nan Hisham ya sanar da shi kowacce a cikinsu gani take ita ɗaya zai aura, don haka ne ba zai yi wani shagali ba ta yadda zai hada su duka biyun. So ya ke sun iso gidansa su gane su biyu ne.

Wasu yawu Yazid ya haɗiye.

"Kana nufin boye masu ka yi ba su san da wannan maganar ba? Anya kuwa ka san hali da zafin kan Deena?"

"To ta yi haukan ta gani idan ban sawwake mata ba"

"Lallai Hisham! kana shirin Kunno wata irin gobara ne a cikin gidanka ta yadda kai kanka ba zaka iya kasheta ba."

Ya karasa maganar tare da cire hular da ke kansa.

"Kai ke wannan tunanin. Ni nan babu yadda zan bari wata daga cikinsu ta ɗaya min hankali. To tsaya ka ji hatta maganar Manarah ba su san da ita ba"

"Ka cire ni a cikin maganar yarinyar nan. Ni fa duk wani abu da zai kara kusanta ni da ita ka rabani da shi, domin banji da dad'i ba"

Yazid ya karasa maganar tare da yin gaba abinsa.

Kasancewar yau saura kwana biyu biki tuni dangin Umma suka cika gida aka fara shirye-shirye. Hajiya kuwa babu abin daya da ta yi wanda zai nuna ta na murna da bikin, duk wanda ke cikin gidan ko yau ya zo tuni ya shaida wacece ita.

Ta bangaren Shukura da Deena kuwa hidima ake gabatarwa tamkar babu gobe. Sai dai abin da Deena ta manta Shi ne mako dayan da Cinyedu ya ɗibar masu tuni ya ciki.

Rana bata karya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.

Al'umma da dama ne suka shaida wannan gagarumin daurin aure da aka daura na Deena da kuma Hisham.

Ana gamawa da nan suka nufi inda za a daura na Shukura.

Tun bayan da ta tabbatar an daura auren take farin ciki cike da farin cikin mallakar Hisham. A yanzu ne zata nunuwa Deena ainahin kalarta.

Abin da bata sani ba ita ma Dennar yanzu haka a matsayin matar Hisham take.

Gidan shi da mahaifinsa ya mallaka masa a nan aka kai Deena.

Sai dai abinda ya ba Umma Rabi ƙanwar Magaifiyar Deena mamaki shi ne. Tunda suka kawo Deena ta fahimci gidan tsakiya ne ka shigo karon farko ne Dakin Deena a saman ne ya ke Amma ƙasa ma ta fahimci dakin wata ne domin har jere an gama.

A sirrance take tambayar Deena sai dai ce mata ta yi dakin Hisham ne. Guɗa da shewar yan kawo amarya ya saka Deena da Umma Rabi kallon juna. Su da sauran jama'ar da ke dakin ba shiri suka yo waje.

Lokacin da suka sauko har su Shukura da ke lullube da mayafi sun karaso tsakiyar falon.

Afra ce tayi karfin halin fara magana.

"Kunga bayin Allah! Lafiya za ku shigo mana gida kuna faman shewa, baku kula da amaryar da ke cikin gidan ba? Ko dai kun saɓa hanya ne?"

Kawar Mahaifiyar Shukura me suna Cidau ce ta karɓe zancen.

"Wane irin saɓa hanya? Bayan a yau ne aka daura auren 'yar mu Shukurah da Angonta Hisham. Ina tunanin dai ku ne kuka saɓa lamba ta hanyar kawo amarya wadda ba gidanta bane"

Sunan Shukura da aka ambata shi ya saka Afra da Deena fizge gyalen da ke fuskar Shukura.

Su duka biyun mutuwar tsaye suka yi cike da mamakin ganin juna.

"Me kika zo yi a gida na. Ko na gayyaci ki ne? Tun muna shaida juna ki fice daga gidan nan kafin in Saba miki kamannii"

Deena ta karasa maganar tare da nunata da yatsa.

"Gidanki ko kuma gidana. Ke ban son haka ki dawo cikin hayyacinki saboda wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa."

Rufe bakin Shukura ya yi daidai da tsinketa da mari da Deena ta yi.

Kafin ka ce me gida ya koma filin dambe babu abin da kake jiyo wa face ihu mata.

Hisham da Yazid shigowarsu kenan gidan suka taras da wannan rikici. Wuff Hisham ya mayar da get ya saka makulli ya rufe. Gefen shirka ya hango wani tiyo da ake ba shuka ruwa. Da karfin tsiya ya fizgesa daga cikin injin.

Yazid so ya ke ya taro shi amma ina, ya na zuwa ya afka falon ya ci gaba da jibgarsu a kan me uwa da wabi.

Duk wadda ya samu sauke masu bulalen ya ke a jiki.

Lokaci daya gida ya rikice da iface-iface. A guje suka rika fitowa su na nufar get sai dai a kulle ya ke. A wajen ma biyosu ya yi ya ci gaba da jibga tamkar Allah ya aiko sa.

Ihu da kururuwar mata shi ya saka makwafta kawo masu ɗauki aka fara dukan get din tamkar zasu ɓalle shi....

1. WACECE MANARA

2. ⁠INA MAHAIFIYARTA TAKE?

3. ⁠WANE IRIN ZAMA DEENA DA SHUKURA ZA SU YI?

4. ⁠ME YE MAKOMAR TSAFATACCIYAR ƊIYAR ROBAR DA HAJIYA TA AJE A ƊAKIN UMMA?

5. ⁠INA MAKOMAR ALAƘAR DAKE TSAKANIN SHUKURA DA MAHAIFIN DEENA?

6. ⁠SHIN HISHAM FUSKA BIYU GARESHI DA WASU KE MASA KALLON MUTUMIN KIRKI?

7. ⁠ME YE MAKUMAR TSINTACCIYA MANARAH?

8. ⁠INA MAKOMAR HAJIYA

9. ⁠SHIN ASIRINTA ZAI TONU?

10. ⁠DEENA DA MAKO GUDA YA WUCE BA SU KOMA WURIN BOKA BA ME ZAI FARU?

WADANNAN AMSOSHI WANDA YA BIYA 500 NE KADAI ZAI SAME SU.

8133562798 Opay AMINA ABUBAKAR

JOIN THIS LINK FOR MORE PAGES👇👇👇👇

***