page 2
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE....
Love And scandal💕
Arewabooks@surayyahms
⏯️2️⃣
kallonta ammi karama ta dingayi baki bude cikin rasa nacewa kawai tagyada mata kai snn tabita sama domin taji dalilin wnn Ɗanyen hukunci da suka yankewa Ayaanah wanda ita kanta zuciyarta acike yake da fargaban irin mijin da zasu zabar mata a wann kuraren lokaci kuma acikin fusata da fushi....
Shekaru sha biyu (12yrs) BAYA KAFIN FARUWAR HAKA...
Garin majiya
karaye LGA,
North-West of Kano State.
wata lafiyayyar kauye ne acikin nisan dajin karaye me taken garin majiya datake kusa da wani tsauni mai suna Dutsen Gulbi wanda Aka riga aka san su da daukaka al’adu na gargajiya masu tsauri da girmama haihuwar d'a na miji dan kuwa yawancin su fatake ne, jajirtccun fulani sadaukai, malaman tsubbu da bokaye, tare da buzaye, suna zamane cikin bukka mai shinge da laka.
mutanen kauyen basuda wani yawa dan basufi dubu ba amma sosai suka tsare kansu da tsabar ilimin tsafi na usuli tareda kaurin suna wajen iya farauta a daji, makiyaya da fataken cikinsu suna yawan fitowa birnuka domin cinikayya da kasuwanci na abinci da dabobi har can can zuwa bordern qasar niger da chad da ake hada-hadan yau da kullum wanda har yajawo suka kukkula zuria da alakar aure tareda kyawawan matayen buzayen dana fulanin usuli.
Anan kauyen garin majiya, duk shekara ana gudanar da wata muhimmiyar biki mai girma da ake kira da Gangamin Gwaninta. a Wannan rana ce da ake fito da zaratan maza masu ƙarfi, yara maza masu kwarewa, su fito fili nuna bajinta a wasan dambe,mashi da wuka, wasannin doki, da kuma rawa ta gargajiya.
A wannan shekarar kamar koyaushe yauma al’ummar kauyen gabaki daya sun tarune makil a filin ƙaramar haraban mei garinsu, Kowa ya shirya da rawani da rigunansu na gargajiya. daga nesa zaka iya hango samari buzaye da fulanin nan kyawawan yan maza dogaye masu dogon hanci suna shigowa daya bayan daya suna ɗaga hannuwa da takobi, wasu kuma suna bisa dawakai suna baza taƙama.
Daga can gefe wani ginannen mutum ne mei suna malam Juma Maharouzo , asalin kayan buzaye yasaka ajikinsa data masa kyau dan shi kyakkwan mutun ne yana tahowa fuskarsa adan ɗaure, matarsa Falmata tambazaou doguwar cikekkyr ƴa mace ce kuma kyakyawan gaske, half breed ne na fulani da buzaye, wani irin yolo yolon baqi sidik in suma takeji dashi wanda har wuce gadon bayanta, akauyen an fi saninta da suna "Tàawuré" tana biye da shi a baya cikin sanyin yanayi, sai babban yarta inayah (innari) yar 12yrs yarinya ce me tsananin karfin zuciya da taurin rai, da karamar yarta me suna Ayaanah yarinya ce me sanyin hali da rauni wacce bazata wuce shekara goma ba da kaf kauyen akeyi ma inkiya da"annayo". tsabar yadda Allah ya zuba mata sassanya kuma kamilallen hali da rare beauty kyaun ayaanah irin me tsananin sanyin nan mesaka nitsuwa da kama zuciya, zakaganta always calm and peaceful like her healthy light caramel skin colour, sam bata fiye magana ba, tana rike ne da ƙaramar kwarya daf da mahaifyarta, inayah kuma tana tafe agefensu kanta na kallon kasa sabida tana da wani irin zuciyae zafi da kuma tsefaffen ido, har suka karaso cikin filin babu wanda ya tankasu face saida suka iso tsakiyar jama'a inda daga dosuwarsu wajen kai tsaye wani garjejen fatauki ya hau nuna su yana ihu yana tuntsinrewa da wata muguwar dariya cikin shakiyanci yana cewa
"yekuwa jama'ar gari, yeeehoooh haihuwar da namiji sai gwarzon namiji,.. ahalin maharaozou an gaisheku, jama'a nace sarki ya gaida cikakkun maza masu haifa ma kauyenmu yara maza gwarzaye. Toh, ga fa juma Maharouzo da ahalinsa mata duk sun shigo fili. Amma kamar kullum, babu ɗa namiji da zai tsaya musu a gasa.“sai dai da alaman kamar yau ya fitar mana da ƴaƴansa mata ne domin su shiga gasar rawar yn mata. fagen shaɗi, fatauci, da Dambe kuwa babu wanda zai wakilce shi.” hahahahaha
wani irin dariya aka fashe da shi awajen ana nunasu da yatsun hannu musmn inayah da ake ganin takai shekaru 12 amma haryau babu wanda ya nuna intrest akan aurenta sabida tsabar an tsangwamesu a kauyen. yadda zaka san jahilci yay ma wann garin illa babu mutum daya da baya musu dariya wasu har suna rike cikin su.
malam juma maharazou y'ay'a mata kawai ya haifa, babbar yarsa itace inayah ana cemata innaari yar shekara 12, da karamar yarsa Anayah da ake kira annayo yar shekara 10 cass, wanda dakyar ma Allah ya bashi su daga nan kuma sai Allahn bai kara bashi wani haihuwa ba.
Wannan dariyar da ake kwashe musu da shi atake ya ƙona zuciyar Juma. Ya tsaya cak, ya kalli wajen da aka fi tashin dariya. atake take fuskarsa ta hau kumbura idonsa ya dada ƙanƙancewa akansu sai dai babu abin da yasan zai iya yi har ransa, domin gaskiyar maganace ta fito fili duk yaransa mata ne bazai taba iya kaucewa wann babban abun kunyar ba kasancewar gidansa ba namiji face shi.
ana cikin musu dariyar wani samari acikin fulani irin bullies masu tashen balaga marasa kunya daga cikin masu rike sandan shaɗi ya daga sandansa sama yayo kansu da gudu yana tada musu kura anata dariya can yay wuf kamar zai gwada sandan akan ayaanah daya san cewa ta fi kankanta da rauni danyana so ne yaga yakara tsoratata ta razana ta firgita tay kuka dan kawai ayi dariya sosai, yana daga sandan kuwa caraf inayah tayi wuff ta cabe tareda kwacewa da karfi daga hannunsa ta rike anata hannun a zafafe yanayinta cike da gigin taurin kai da tsananin zafin zuciya da jarumta take kallon har cikin idonsa tana huci.
cak ido ya koma kanta ayayinda kunya ya rike ma saurayin kirji
wani huci yay yana kokrin daka mata tsawa kenan cikin datsar numfashinsa tazare mai manyan idanunta dake bushe tareda nuna shi da sandar a tsawace tace "kaiiii Garbati kar ka sake ka karayin mafarkin taɓamin ƙanwata annayo, idan bahaka ba saina dakeka anan wajen andau mushenka...
jarumtaccen muryan zaki me amon bacin rai datay maganan dashi yasaka kananan magana da dariyar da ake filin ya dauke cakkkk ganinta yar karamar yarinya me zafin zuciya irinna jajirtacun maza..
tsayawa duk akai aka dinga kallonta yadda idonta yajuya yay jaa kmr ruwa ga turirin zafin rai da ke fita a numfashinta koinanta na kyarma irinna jaruman maza ..
A memakon hakan yay ma mahaifinsu dadi sai kuma yaji mugun haushi ya rike sa, dan aganinsa kara tozarta shi inayah tay data nuna rashin kunyarta da rashin tarbiyanta a fili wajen kkrin kare yar uwarta anayah.
a tunaninsa da kuma tunanin yan kauyen kowacce mace me rauni ce da kunya, mace bata daga ido ko murya wa namiji ko da kasheta za'ayi akan gaskiyarta.
da mugun bacin ran ganin abunda yarsa inayah tay ya juyo cikin huci ya kalle Matarsa taawure data sunkuyar da kai cikin jin mugun tsoro da nauyi tana jin kamar ƙasa ta buɗe ta shige.
kallo daya yay ma inayah wanda tuni inayahn ta saki sandan sabida suna mugun dajara idon mahaifin nasu Ayanah kuwa na nan tsaye a gefenta, batako motsi tsabar uban tsoron da ya lullumeta, bacin ran da mahaifinsu ya fara nunawa a filin ya saka idanunsu yacike da ruwan hawaye suna ji aransu kamar duk duniyanan ne ma ake ƙyamatar halittar su na ƴaƴa mata bawai ubansu kadai ba.
mahaifinsu Juma ya yi ƙoƙarin ɓoye ciwon abun aransa amma inaa da ihu ya ce musu ku fita kubani waje anan, kunji me ake cewa wajen nan wajen yaya maza ne bana mata ba, ke kuma innari kije gida kijirani yau sai na tsine miki albarka da kika karbi sanda ahannun namiji.
yana huci ya kalli idon matarsa tawuree cikin tsananin gigin jahilci da fushi yace " ki tafi da yan iskan yaran nan naki anan. daga yau kuma kar na sake ganinku a fili, dama kin matsa muzo da yaran ne dan ku taru ku kunyata ni abainar maza, kije can..sanda kikayi jarumtar fito da d'a namiji duniyan nan saiki dawo filin wasa.
dariya aka faray musu, kuka me sanyi ya kufce ma taawure tafashe dashi tareda janye hannayen yaranta duka biyun izuwa waje dan already habaice habaicen da akemusu awajen akan abunda inayah tay ynxu ya mugun kara raunatasu su sosai..
wani ikon Allah kaffff kauyen gidansu ne kawai akwai ƴaya mata har biyu snn babu namiji ko daya..
kafafunsu har na hardewa suka fice a filin sunaji ana musu habaici sosai, a zuciye juma ya kalli masu dariyan akaro na biyu snn yace “Kai jama'a! saidai Ku yi dariya ku yi ba’a akan yaya na mata, aje dai na fi uban kowa ƙarfin aikin noma a kauyen nan. Wani ma gashi da y'aya mazan amma bai isa ya iyayin noma irin nawa ba.”
duk da zafin jarumta dake tafe acikin maganarsa already gorin nan da ake masa akan yaransa ya gama ratsawa cikin zuciyarsa har yau yana tuna tsananin baqin cikin dayaji aransa da aka haife yarsa na biyu Ayanah a matsayin y'a mace ba d'a namiji ba..
wasa ta cigaba a fili amma gori da cin fuskar da ake ma juma maharaozu baiyi sauki ba musmn ma da sarkin fulani ya fito filin wasan da duka y'ay'ansa maza kusan su guda goma sha bakwai shine mutumin da yafi kowa haifan yaya maza a garin majiya gabaki daya kuma shine yafi kowa kuntata ma juma akan batun yayansa mata guda biyu. abu kadan sai kaga ya gaya masa baqar magana me hade da gori abainar jama'a haka za'ayita ma juma dariya duk dama yana daya daga cikin jiga jigan manomar garin dayadace ace ana ji dashi saidai rashin samun da namji koda dayane a ahalinsa yasaka gabaki daya ya zama baida wani daraja a idanun hakiman fulani dana buzaye dan har kwatance da shi akeyi a kauyen.
Dagata bangaren su taawure kuwa tunda tajanye hannun yaran ta suka bar filin wasa tafiya kawai sukeyi suna masu tsaga cikin jejin da zaibi dasu madaidacin rugarsu dake can can gefen babban rafin kauyen inda babn filin noman su da tsaunukan kiwon dabbobinsu yake kusa azagaye dasu, they are kind of isolated daga main mutanen kauyen ko abu zasu saya sai sun yi tafiya mai dan nisa suke isowa kasuwa kusan ince rugarsu ne karshe a kauyen kusa da hanyar barin gari gabaki daya, gabansu kuma babban ruwa da jejine me duhun gske dake zagaye su.
tafiya suke da sauri sauri tareda wani irin rauni da kuma fargaba acikin zuciyoyinsu, koina yay shiru dan kusan kowa a kauyen anacan fili wajen gagarimin wasa, cikin sassarfa da sauri taawure tariko hannun karamar yarta ayanah gam tana janta ahnkli nan inda bakajin karar komi a hanyar face sanyin iskan yammaci da kukan tsutsaye tareda dirar sautin ajiyan zuciyar taawure datake saukeshi akai akai jin raunattecen ajiyar zuciyar da ayanah takeja wanda yagama narkewa cikin tsoro da matsanancin damuwa. daga ita har mahaifyarsun a dame suke da tunanin irin hukuncin da juma zai zo gida ya dauka akan su da kuma inaayah.
ita kuwa inayahr ko ajikinta daf dasu take tafiyarta zucyarta karau dan tun basu karasa barin filin wasan bama tabi ta shanye hawayenta idonta yabi ya bushe tsabar wann taurin zuciyar da Allah ya bata wanda yasaka tuni ta iya hadiye duk wata damuwa da kukanta aciki. duk dama kowa cikinsu na jin dar dar da tunanon dawowar baban nasu gida ayau amma ita kam gaba gadi take tafiyatta da zucyarta daya.
sunyi tafiya na akalla mintina ashirin kafin suka kawo kofar madaidaicin rugarsu da gininsa yayi mugun jimawa sabida asali gidan gadone da wani uban gidan juma a harkan noma ya taba mallaka masa halak malak saboda tsbaar jajircewr sa a harkan kiwo da noma. duk da rugar ta jima saidai tsabar tsafta da tattali irinna taawure yasaka muhallin nasu yake da kyaun gani, nan suka tsaya a babban filin kofar gidan suna kan tattara buhuhunan da suka shanya wasu kayan abincinsu kmr tarugu, ganyen zobo kubewa, da gyada da wasu yan hatsi, inayah da kanwarta ayanah suka dukufa suna kan kwashewa taawure kuma tana zubawa acikin buhun tana dinkewa da allura da zaren buhu.
tsabar kawaici da kunya irinna bafulatanar usuli yasaka har iyanzu taawure bata budi baki tace uffan ma yayan nata akan abun da ya afku a fili ba, dake ma sunsaba da irin wann halintan ya saka koda wani abu yafaru inde batay musu magana ba suma sukeyin shiru saidai kawai kaga suna aikinsu da ladabi da kawaici.
gasu da hatsi,dabbobi da kaji amma diss din datti bazaka gani a tsakar gidan nasu ba koina an tandesa tass da tsintsiya yanayin yaran da uwarsu kadai kagani zakasan Allah ya zuba musu kwazo kunya da kuma sanyin tarbiya me tafe a jini.
bayan sun gama kwashe shauran abincin taawure da Ayanah ne agaba wajen kaiwa cikin ma'ajiya, ayayinda inaayah tay maza ta shiga ban daki, kai tsaye tayi tsarki ta taho tazauna akan dutsin dake kusa da madafi tahau alwala
Daga cikin daki kuwa suna shiga taawure ta cire mayafinta snn ta daga ido ta kalli yarta ayaanah dake rakube kan taburma ta rike saman kirjinta bata ko motsi, Tun haihuwar anayah suka fahimce cewa kamar tana famane da wani irin ciwo na raunin zuciya wanda baya tashi sai tana cikin halin tsoro ko tsananin baqin ciki da fargaba.
bayan mahaifyarsu arayuwarta babu abunda take kauna aranta kamar addarta inayah dan sun taso ne da wani irin kakkafar yarda da juna, shakuwa da kuma tausayin juna meyawa a tsakaninsu.
ganin yanayinta na laulayi yasa cikin sauri taawure ta durqusa kasa tajawo wani babban kwarya daga kasan kujera ta bude shi, wani tsaftacen jikon maganine aciki marmaza tasaka ludayi tahau deban ruwan maganin tana zubawa cikin karamin kwarya inda ko rabi baikai ba tamika mata da yaren babansu na buzanci tahau tursasa mata shi abaki kiyi bisimillahi Annayo am, karkiyi raunin zuciya maza kisha wnn zai saka kiji karfii kinji?..
adan ragwabe ayanah tamike zaune ta amshi kwaryan da ladabi tafara sha kenan saiga inayah ta shigo gabobinta duk a jike da ruwan alwala
suna hade ido kallo daya taawure tay mata kafin nan ta mike tsaye da tsoro a muryanta tana cewa
"ke kuma muje in rakaki hanya innari, kijeki ki buya a garin tudu harsai nazo na nemeki, bana son babanki ya dawo gidan nan da fushinki aransa ya zo yayi miki lahani ko ya tsinemiki kibi duniya in shiga uku..
kafin inayah ta amsa taga mahaifyarta har tajuya tahau daga katifarsu da akayishi da ciyawar tim tim hannunta na rawa rawa ta dauko mata jakar buhunta inda suke boye littafan karatunta na boko da islamiya da ta jima tana turata yi acan anguwar tudu inda suke kasuwanci ta saka yaranta karatu a boye batare da sanin mahaifinsu juma maharaozu ba.
jakar karatun ta fara mika mata danta boye shi acikin rigarta snn ta jawo kullin kayanta tahau nade matasu a tsuman zani tana gama kullawa ta dora mata shi akai, tsabar zafin zuciya 'bari 'bari kawai jikin inayah yake dan bataga wani dalilin da za'a boyeta ba,aganinta ai kare yar uwarta kawai tayi a fili, kawaici da darajar da take mugun bawa mahaifyrta yasaka batace komi ba dan babu abunda yake cimata tuwo a kwarya kamar irin mugun tsoron mahaifinsu da taga taawure takeyi agidan, wanda inda anbarta dashi da tuni takara dashi dan ji take ajininta kmr itadin mace me kmr maza.
turjewa tay ayayinda taawure ta wafco hannunta zata jawota waje, suna hade ido da dan taurin kai ta tsaya tanata kallon cikin idanunta batay mata yaren buzancin ba sai tay mata da fulatanci tana cewa 'ummah miyyasa kike tsoron abunda baba zai min dan na kare yar uwata ayaanah a fili ko dama so yake wancan katon banzan ya kasheta da sandanshi dan ya nuna musu baya kaunarmu? ummah inkina jin tsoronsa wata rana za'a kasheki ko akashe annayo a filin nan, kidubeta bata da kwarin gwiwa kuma wnn jikon naku da ake bata kinsan zai sakata bacci me nisa zai kashe mata zuciya bazatay karatu ko ibada ba umma inde ciwon zuciya ke damunta ai akwai malaman asbiti a tudu
rufe mata baki taawuree tay da sauri tun kafin wani yaji abubuwan datake ambata musmn ma batun asibiti da karatu
hankli tashe cikin tsawatar mata tace ya isa haka innarii yanxu ba lokacin magana bane, kituna dake kawai na dogara dan ranar da mahaifinku yasan nasakaku kuna karatu a tudu zai iya kasheni ko ya batar dani, innari kece mini, nasan zaki zama karfina anan gaba, nasan koda na mutu kece kawai zaki iya rike ayanah tsakanin ki da Allah koda bana duniya, in nabari yaxo ya tsine miki yau ni aka cuta duniya da lahira, kawai kije ki cigaba da karatunki a tudu, nayi miki alkwari bayan ya huce daga fushinsa, zanzo saida nono wata sati zan dawo dake gida, snn nayi alkwakri wnnan karon da kaina zanzo da anayah tudu itama ta cigaba da karatunta acan naji ance anyi mata nisa kudin natan ne bangama tarawa ba. tun kan innari ta amsa idanunta ya cika da ruwan hawaye ganin yadda jikin mahaifiyrsu yake bari sosai yanayinta cike da fargaba me ban tausayi da tsanani.
marmaza taawuren ta warware bakin zaninta ta ciro kudi da basu fi dari biyarba ta damka matasu duka a hannu tace" kirike wnn inkinje tudun kice ma goggo mei tuwo ina gaisheta, har da ma malaminku. ki kula da kanki Allah hokku barka am. inayah ta kasa cewa komi ganin yadda hankli da jikin mahairfyrsun gabaki daya yarikide dukkan hanklinta atashe yake sai leke leken waje take da tsoro daga ganinta kasan tana mugun tsorone kar ace juma ya dawo ya iskesu anan atare dqn bakaramin son yaranta takeyi ba.
hawaye kwalli daya ya sauka idon inaayah musmn da ta daga ido ta kalli mahaifayarsun snn ta kalli ayaanah dake kan kwance a tabarma ta kanannede kanta bata iya ko da motsi sabida jikon da aka bata tasha tuni ya sakata bacci..
tawuree na jan hannunta da kyar dai ta iya dauke idonta akan yar uwarta suka fice waje suna sauri sauri haka ta rakata har gaban babban rafi ta turata bisa hanyar tudu, ita kuma ta damke kayanta snn ta falfala da gudu tabi jejin, saida taga tay nisa snn ta dawo gida
taqumi tay ta zauna kurkusa da ayaanah dake kan bacci wasu maqudan hawaye na zuba mata ahnkli cikin tunanin safetyn yarta inayah, harcan saida aka kira sallan magrib snn ta tashe anayah sukayi marmaza sukayi sallolinsu suka ci abinci wanda dede lokacin ne aka taso daga wajen wasa...
fitila me kwai kawai ta kunna musu tay shiru tanajin ayanah tanata bitan karatun da addarta inayan ta koya mata game da sallah , tun suna zaune acikin dar dar din ganin shigowar juma gidan har dai suka hakura.
washe gari da asuban fari sukejin labarin cewa ashe baram baram aka tashi a filin wasa, sarkin buzaye dakansa yay jawabi akan tarbiya, yana mai kafa misali da rashin kunya da kuma tarbiya irinna inayah dahar ta karbi sanda a hannun namiji a filin wasa, dan haka tun anan juma maharozau yayi zuciya, sabida ance masa ya haifa musu y'ay'a mata marasa amfani ga cigaban kauyen snn kuma bai iya tarbiyatan dasu ba, acewar sarkin fulani in har innari ta sake musu tsaurin idon karban sanda a hannun namiji a fili zai saka matasa maza su giciye ta.
wayannn furucin yasaka juma tsananin fushi, bai dawo gidan sa ba ya wuce jeji dan tsabar zafin zuciya ma akan wata bishiyan mangwaro ya kwana
jin hakan bakaramin kara tsorota taawure yayi ba, dan tafi kowa sanin mugun zuciya da tsananin rashn son kaskanci irinna mijinta juma. dan da a raina mazantakarsa ko aci mutuncinsa a fili gara a maresa a fuska.
Juma Maharouzo ba asalin ɗan Dajin rini ba ne. Kakanninsa sun fito ne daga ƙauyen Maharouzo kusa da iyakar Tamesna wato yankin da ke tsakanin Nijar da Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sunan “Maharouzo” ma ya samo asali daga tsohon harshen Tamasheq wanda ke nufin “ɗan ƙura, mai ƙarfi a ƙaura”. ance Kakan kakansa bbn malamin addini ne wanda yayi suna wajen tafsiri da bayar da fatawowi musmn ga ƙauyukan kan iyaka amma babansa kuma jahili ne dake bautawa al'adarsu. yaki neman ilimi ne saboda kakan juman adacan ya ki shiga cikin yaƙin sarakunan Fulani a lokacin jihadin Shehu, sai aka koreshi da iyalansa daga garinsu. Sun yi hijira, suka shigo cikin karkarar Katsina duk ba'a kyale su ba, daga nan suka ratsa zuwa Rini inda aka basu ƙaramin fili don su zauna, Saboda haka shida ya taso sai baibi tafarkin ilimi ba har ya haifi babban dansa juma a maharazou cikin jahilci da tsananin son al'ada..
Juma ya taso ne da ɗan tsakanin ƙabilu biyu, akwai al’adun Hausa fulani a jikinsa, amma shi asalin Buzu ne tsatson su na Tuareg har a halayyarsa. shi mutum ne mai ɗaukar hankali koda bai yi magana ba, Fuskarsa tana da faɗi, idonsa yan dede masu zurfin haske, daga saman Goshinsa akwai wani dogon tabo mai layi guda biyu wanda labarin tabon nan shi kansa yana da ban aljabi, dan ana cewa a lokacin ƙuruciyarsa ya tsallake dajin mutuwa lokacin farautar wasu macizai, wasu kuma sunce yabuge kansa ne da itace wasu na cewa alamar ruwan gadon hatsice daga kakanninsa shiyasa noma ta amshesa
Dogon mutum ne mai lafiyayyen kafadu masu faɗi, gashin kansa baƙi, gashin gemunsa kuma ya fara tsufewa. a sutura Ya fi son dogon riga mai launin ƙasa ko shuɗi, da rawani mai kauri wanda yake nadawa fiye da yadda maza kauyen suke yi, shi baida hakuri sam, kuma zuciyarsa akusa take, babu abunda yakeso aransa kamar al'adarsa, babu kuma abunda yafi ci masa tuwo a kwarya kamar haifan yaya mata dayayi, dacan sai kaga kamar yana mutuwar son matarsa taawure amma tunda ta haifa masa mata banda wutar tsana da tsangwama babu abunda ke shiga tsakaninsu. already ya hana yaransa komi na nishadi, da amfani, daga aikin gida, talle sai kiwo, baya basu kulawa, ko ciwo suke an haramta musu shan maganin da addini ta amince dashi, saidai uwarsu ta jika musu magani na asalin malamn gargajiya susha, snn ba a karatu kowani iri a gidansa, ya hana zuwa asibiti sabida shi asalin al'adarsu ba jahilcin garin yake bi badon komi ba sai dan kawai yaga shima ya zama me fada aji snn ya samu shiga a fadan sarakunansu both fulani da buzaye ana darajashi kamr sauran zaratan maza.
Kamar ko wani zagowar shekara yauma al'adarsu ta bikin gangamin gwaninmta baima Juma maharazou dadi ba. tun safe taawure taje jejin tana rokonsa, hakama wasu Maza abokansa Wanda sukadan damu dashi a garin sukazo babu irin rokonsa da basuyi akan yay hakuri ya sauka akan bishiyan nan ya koma gida ba amma inaaa, yaki magana da kowa yay zuciya harda abinci.
wasa wasa saida ya kara kwana washe gari taawure ta fita tanabi gidan dattijai tana magiya dakyar akazo aka tallafosa ya hakura ya sauko ya koma gida, yunwa duk ta watayashi sanda ya sha kuna yay wanka ya dawo hayyacinshi, tsabar zuciya haka bai magana da kowa agidan ba, har saida da yazo yaga babu wulgawar innarin agidan snn ya dan sake ransa, dama kuma mugun tsoron sa ayaanah takeji bata sakewa suhade ido ko su hade hanya in zata gaishesa da sanyin asuba take fitowa ta bi taawure itama haka za ta durkusa ta sunkuyar da kai can kasa a kofar turakarsa tay shiruuu koda taawure ta gaishesa daga nan waje ya amsata cikii ciki, ita shiru takeyi inbe amsata ba kuma komin jimawar da zatay a tsugune haka zata kasance har sai ya fito daga dakin ya ganta snn take iya tashi tabar wajen.
#SURAYYAHMS
AYI SHARING idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
AREWABOOKS
@SURAYYAHMS
WATTAPAD @SURAYYAHMS
WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
#SURAYYAHMS