ABUNDA KE 'BOYE...

3

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE....

Love And scandal💕

Arewabooks@surayyahms

⏯️3️⃣ Duk zafin zuciya da taurin kan inayah tsanar dayake mata baikai wanda yake ma Ayanah ba, dan akanta ne yafara samun rugujewar burinsa na samun ɗa namiji sabida shi dakyer ma yake iya samun haihuwa. a kauyen mutane da yawa sun haifi mata a fari saidai abinda yake biyowa baya maza ne, shima sosai yaci burin ace ayanaah tafito masa a matsayin ɗa namiji sai kuma ta fito mace kyakkwan gaske kuma me dauke da ciwo na raunin zuciya wanda saida aka sha wahala ma kafin ta rayu.

ranar koda aka cemai mace aka kara haifar masa tsabar bakin cikin dayaji aransa ko daukarta as a baby a hannunsa bai taɓayi ba,he despises ayanah ryt frm the very minute she was born dan haihuwarta ya jawo masa ababen gori bana kadan ba shiyasa har yau kuma baijinta aransa dan banda hantara, tsawa da tsananin dokoki babu abunda ke giftawa tsakaninsu.

yau shekaranta goma amma bai taba amsa gaisuwarta ba, kowani safe saidai tabiyo bayan mahaifiyatta cikin nuna biyayya haka zatazo ta durkusa masa abakin kofar turakarsa ta tsunkyar dakai kasa tay shiru bata kuma tashi awajen har saiya fito yaganta duk dama tasan bazai taba ce mata uffan ba.

bayan kamar sati da faruwan komi taawure tasha baqar walaknci da baqar magana a hannun juma kafin ya sassauto ya hakura har ya fara shirin tafiya zuwa boaden kasar niger saida sabbin buhunansa na hatsi, yana da akalla buhuhunan kayan noma kala kala yakai buhu dari da ashirin banda yan kananan abubuwa daya tara.

kullum matarsa taawure dake tay karatun allo sosai ita take tayasa lissafin irin uban kudin da zai samu duk dama baiya bata ko asi, dan gani yake tunda ita ta taba yin karatun addini me zurfi hala zata cuceshi

abinci kam kowani iri ne yana sakar musu suci su koshi amma bayan haka sisinsa basa ci. sanadiyar yar lissafin kudin datake tayashi sukeyinsa a kwana biyu yasa hartaci nasarar kawo masa batun yafewa innari, ranar haka ya zage ya gaggaya mata bakaken maganganu masu tsanann zafi da ciwo wanda ko wacce uwa bazataso taji an furta su akan yayanta ba, ya mata gorin tarbiya, yace mata yana ji ajinin jikinsa cewa watsatsstsu karuwai kawai ta haifa masa ba ƴaƴa ba, wanda yake da yaqini cewa sune zasu kawo zubewar duk wani kima da darajarsa a duniya.

sam maganan nan bai ma taawure dadi aranta ba dan bataso yay musu wnn mummunan bakin ba

hakanan tay hakuri sabida ya yafe kuma ta shawo kansa har ya amince akan inayahn zata iya dawowa gida, maganarsan ya mata ciwo aranta amma tanada yaqinin cewa Allah bazai tozarta ta ba tunda har tanata kkrin neman ma yaranta ilimin addini dana boko aɓoye in sha Allah bazasu taba zamowa karuwai watsatssu ba.

duk dama ta aminta da mutanenta na can tudu amma koda juma yay ma yaranta wnn mugun bakin sai kawai tafara jin kamar tafiso ace ita dakanta ne ta tarbiyartan da duka yaranta agabanta kafinsu samu mijin aure basai sunje university ba duk ma babban burinta kenan.

satin nan gabaki daya haka ta tasa ayanah agaba suka hau shirya madara, da kindirmon nono da fura da kwan zabbi masu kyau da yawa, sunata Allah Allah lkci yay juma ya wuce kasuwancinsa a bodar niger dan suma suje nasu kasuwancin a can tudu.

kwanaki basa karya yau kwana sha biyu shaf da gama hidima gangamin jarumai juma da abokanansa duk sun gama shirin tafiyarsu can boadern niger kasuwancinsu da suka sabayi ko wata shekara.

ranar da zasu wuce tun da asubahin fari na farko lkcin waje baigama washewa ba taawuree ta fito daga turakarsa da lullume tare da daurin kirji tanadan murmushi me sanyi tuna irin darensu na jiya.

mijinta juma yana iya walakanta ta akan komi amma daga zarar anzo maganar saduwar aure baya iya boye dumbin soyayyr dayake mata aransa dan bakaramin dadin ta yakeji akan gadon sa ba, albarkan niima da dandano dake kumshe a jikinta yana kawo masa wata iriyar cikakken gamsuwa da nitsuwa a duka sassan jikinsa tareda dadi marar misaltuwa, ruwa me tsafta ta hau zuba masa a babban butan karfe wanda take tsammnin zaiyi wankar tsarki dashi tanay tana murmushi badon komi ba saidan amince mata dayayi akan basai ta zauna anan ba, zai saka musu mai gadi inyaso itama tazauna acan anguwar tudun tay kasuwancinta na saida kwai da nono har saiya gama nashi cinikayyar ya dawo. hakan kusan babban alfarma ya mata.

lissafin wata ukun da zaiyi a boda tay, tasan kafin nan ya dawo ta samu kudi me yawa na kulawa karatun yaranta hala har ayanah tay nisa akaratunta itama.

babu yabo babu fallasa juma ya gama shirinsa komi ya fito, ta rakosa har waje yay kyau sosai yasha baƙar rawani, wanda yau da ace bai kara jadadda mata mugun harsashen dayakeyi gameda da tarbiyan yaransu ba da sai tace cikin dadin rai suka rabu amma inaa saida ya kara jadadda mata cewa yanaji ajikinsa cewa yaransa kaf karuwai ne...

haka ta dinke zafin maganar aranta har sukayi sallama dashi snn ta dawo gidan, bayan kamar kwana daya da tafiyarsa mai musu gadin rugarsu ya taho, ita da ayanah kuma suka shirya suka tattara kayan cinikayyarsu da kayan sawansu suka kama hanyar anguwan tudu ayayinda zuciyar taawure ke cike da tsananin damuwar irin mugun baki da fatar tabarbarewa da juma yake ma yarantan aranta. ayanah kuwa murna takeji anata ran tana Allah Allah taga har su isa anguwar tudu dan ta saka yar uwarta inayah a kwayar idanunta.

Basu da isa cikin anguwar tudu ba sai can can gabanin sallahn magriba sabida biye biyen wasu kananan anguwanni dake bisa ahanya da táawure tay domin saida nono da fura dan ta samu ta cike shauran yan kudaden makaranta na ayanah da ake binsu bashi, suna samun kudaden su suka doso masaukinsu, sun iso kofar gidan goggonta Hajy mairo metuwo lkcin duk sun galabaita sakamakon tafya me nisa da suka sha musmn ma ayanah dake fidda nunfashi sama sama sabida wann ciwon raunin zucya datake fama dashi..

Anguwan tudu kamar bariki ne, is more busy and civil Kamardai wajen kazo nazo ne amma dake yana nesa da garin kano duk kabilu irinsu hausawa, buzaye, katsinawa, kanurai, iyamurai, da fulani asalin irin kauyawan ne ke cin kasuwancinsu anan kowadai yana harkan gabansa .

adaf da gidan sarkin kasuwar tudu gidan goggon taawure yake,

dake shahariiyar Me sana'ar saida Abinci ne agarin, hatta bako inka tare shi a hanya kacemai gidan hajy maituwo zakaje zai iya nuna maka shi kai tsaye dan ta balain shahara wajen iya sarrafa abinci da abun sha kala kala da kuma saidawa, lafyayyar hajiya ce shekarunta ya dan jaa amma tay karatu wayayya ce, tun zuwa makka na naira dari hudu tajeta ta sauke farallinta yakai sau biu zuwa uku, tana da ma'aikata dake aika a rumfar abincinta dayawansu yan mata ne datake daukar nauyin karatun su, sai maza dake mata gadi da sauran abubuwa kmar aika da aikin karfi, itake rufa musu asirinsu kaf ta zame musu tamkar uwa da uba.

Tun a kofar gidanta suka sauke kayansu akansu, taawure na tafiyarta a hnkli cikin tsantsar nitsuwar dake tattare da yanayinta na mace mai kamala wanda babu shakku ko dar dar atattare da ita.

Tun a zauren farko take buga sallama cikin nutsutsaiyar sauti yarta ayanah na biye da ita har suka wuce can ciki ta Inda masaukinsu yake bata fasa sallamar ba, ayanaah kuwa tuni ta bude randa ta hau gwangwadar ruwan sanyi wai koda nunfashinta zai dawo dede, Adaf lokacin inayah ta idarda bitan karatunta kenan tana daga xaune akan wani darduma ta fara jiyo motsi tareda sallamar taawure, da wani irin sauri ta fito tun basu gama hade ido da ummanta ba ayanah ta jefar da kofin ruwan ta daka tsalle da murna ayanayinta ta taho da gudu ta rungume addanta inayah sosai, ahnkli inaya tace "annayo? baki washe ayanah tace naam adda na muma gamu ai munxo tudun. inaya tafara dariya tace" aito shannunku., tun basu gaisa ba ayanah tahau kkrin cikata da surutai musmm ma labarin samun karashin sauran kudin makarantarta da sukayi kan hanya wanda atake yasaka zuciyar inaya yay dadi da sanyi dan tasan tunda har anayah tana cikin tsananin farinciki to hala komi ya daidata ne harma awajen mahaifinsu juma

Tanakan murmushi ta janyota jikinta sosai tana share mata zufa tana cewa"toh ya isa haka anayo, Zo muje can wajen ki wanke sawunki kikalle yadda kikay futu futu da kura kamar delu me wasan kasa..anayah da bata wani damu ba sai washe baki takey yanayinta me cike da xumudin ganin addanta ga kuma batun komawrta karatu dan bakaramin son karatun boko takeyi ba.

suna kkrin barin wajen taawure tabisu da sanyi kallo tana dan murmushi har ta kusa cikin falon goggontan cikin nitsuwa

Hjy mai tuwo dake kwance bisa kujera da jikin tsufa tadan miko kanta cikin sauri tana amsa sallaman taawure adan rikice amma dake tanada shegen mita yasa bata gane muryanta bugu daya ba, Wani Caraf ta yatsina fuska tace 'ohni yau naga takaina waye kuma haka da yammaci tun bamu ci na dare ba? Kode sabbin masu saida abincin nan ne suka dawo zasu sakani agaba da mita akan kudi...ohh ni Yau mairo naga takaina Waye ne kam... shigo daga ciki mana..ke innari zoki dubamin

Gyara zamanta tayi akan kujerar tana dada gyara mayafinta akafadunta, sashenta Babban self contain ne amma na ginin laka me karfi da aka bi jikinsa da siminti yay fess fess duk da ba a fentashi ba, ciki da falo ne me dakuna biyu, ta kakkale koina da brown leda carpet da kujeru kananan seti da tv dan madaidaici da wooden center table iri daya da brown cupboard dinta datay wani irin jeren kwanukwanta akai.

Jim kadan saiga bullowar taawure cikin falon, gabanta gadi fuskarta dauke da Wani dattijuwar Murmushi wanda tun daga yanayin shigar ta Kamala yasa hjya mairo kara bada hankulanta akanta da sakin fuska tahau mata maraba har idonta na tara ruwa.

kullum taga taawure sai taji wani irin tausayinta aranta sabida asalinta yar gata ce da rayuwar maraici ya juyata ta dawo abar tausayi.

"ooo taawure? ai sekice min kece kika lankayo sawun kafafunki kikazo, toh sannu da da zuwa lale maraba da xuwa.

taawaure nata sakin murmushi har ta nemi Waje ta zauna Adan dofane feeling so uncomfortable da irin kallon kurilla da hajy mai tuwo ta ke jefa mata. zuciyarta ne ya shiga mata Wani irin zafi ganin yadda taawure take kkrin dawowa kamar wata sokuwa kamar batay ilimi da take gidan ubanta ba..

Gaisuwa suka somayi

Irin gaisuwan Nan na darajawa da kuma kimantawa gwanin burgewa, hajya mairo tana tambayarta lpyarta tanayi tana hada mata da addua masu karama Inda basai angaya kasan tamkar uwa taawure take kallon hajy mairo

bawani alakar jini me yawa bane atsakanin su,saidai kuma kawun taawure wato alhj mamman me gareji daya rasu da jimawa wanda anan anguwar tudu yake zama shine mijin hajy mairo na biyu, mijinta na farko a kano yake, suna da yara maza har hudu shima din rasuwa yay, aurenta na biyun kuma bata haihu dashi ba sabida shekaru yaja kuma dake auren nata dashi bai jima ba ya rasu da ciwon cancer, toh a ahannunta taawure tazauna harsaida tay aure, duk wani abu dake tafe a rayuwar taawuren ta sani duk dama batawani shiri da juma, ko kodan jininsu bai hadu ba anma bashi yahana

take rikeda lamarin taawure da yaranta a tsakani da Allah ba.

hira sukayi na yaushe rabo da kuma abunda ya faru awajen wasan gasa, kmr kullum yauma juma yasha caccaka awajen hajy mai tuwo dan tsani irin zafafa al'adar jahilci dayakei akan iyalansa, can dai data gaji da mitan sai kuma tahau kara ma taawuren karfin gwiwa akan batun karatun yaranta sabida malaman nasu nayawan cewa dukansu suna da baiwa na musmn.

hira me tsayi sukayi akan yadda inayar tafi kwarewa akan karatun addini harma ana kwatance da ita a tudu, ayanaah kuma daga dukkan alamu bokon nan dai yafi dauke mata hankali, har dare yay nisa suna hira salla ne kawai ke tadasu, nan ma taawure ta sanar da ita cewa har tsawon wata uku suna nan tudu kafin nan juma ya dawo. da kyar suka rabu taawure ta koma dakin kusa da zaure da ake ware mata intazo da yaranta, ta samu anayah tay bacci akan cinyar addanta inayah wace ke zaune akan dadduma tana kkrin shafe mata nasi da falaki da ayatul kursiyu ajiki dan ta samu kariya. sabida kunyar haihuwar fari dake tsakaninsu hira kadan sukay da taawure kafin suka kwanta da niyyar washe gari sassafe duk zasu fada cikin harkokin gabansu na kasauwanci da kuma karatu.

washe garin ana kkrin zaa kiran sallan asubahi sassanyar sautin bitan karatun qur'ani da inayah take zubawa acikin yanayin kwarewa ne ya farkan dasu daga bacci. zaune take agaban fitila ta rufe kanta da zani, da wani irin farin ciki da zumudi ayanah ta diro daga gadon baccinta itama taje tay tsarki da alwala awaje snn tazo ta zauna daf daf kusa da addanta tana karanta musu suratul Duha itama nan ta jonata sunayinsa tare.

tsabar sanyi da dadin muryansu d ayadda suke karatun fuskokin su cike da murmushi da dumbin son da suke ma juna atake atake kwayar idanun taawure ya cuko da ruwan hawaye mai tattare da rauni da kuma tsantsan alfahari tareda farin ciki mai sanyaya zcyar kowata uwa.

saida suka kai har suratul mutattafifin snn aka kira sallah, nan suka mike duka sukayi ibadar su, suna gama azhkar na safe sukayi gaisuwa, tuni inayah dake ita tana da zafin nama tayo waje tafara shara tana kimtsa tsakar gidan.

ayanah kuma dake tana da rauni da tsoron sanyi ta tsaya tana gyara cikin dakinsun, bayan ta gama ne ta zauna bisa tabarma tanadan bitan dan gyarrarkin da inaya ta mata akan sallah. taawure kuwa tuni ta kwashe toka a murhu ta fara daura kunu da dumame, kafin kace wani abu gidan yayi fess, ya kuma dauka da qamshin kunu da dumame. da tsananin farinciki ganin sun gama komi hajy mai tuwo ta fito duk aka gaisa cikin raha, aka ci abinci akayi dam kowa yay wanka kafin ma'aikatan hjy me tuwo suka fara zuwa ana shirin wucewa shago, taawure bataje

kasuwa ba, yaranta biyu suna kammala saka uniform dinsu ta saka su agaba sukeje har makarantarsun ta biya sauran basuka da ake binsu na karatun ayanaah both islamiya da bokon duka snn ta musu sallama ta dawo gidan ta samu duk su hjy mero me tuwo har an wuce wajen sana'a, itama tattara nata kwaryan nonon tay ta wuce cikin gari saidai daga tadanyi shiru sai taji zcyarta baya mata dadi, dan har ynxu gani take kamar fa mugun bakin da juma yay ma yayanta akan karuwanci hala zai iya kamasu. dakyar da addua snn abun ya lafa mata. rayuwar su mai tsafta sukeyi a tudu, ayayinda kowa cikinsu yake cigaba da sanaarsa yaynta kuma sun balain jajircewa wajen karatu. inayah dake da 12yrs tana aji biyar na firamare dake a aji biyar din zata tsaya, qur'ani kuma saura mata shafuka shida ta hade haddar izu sittin, fiqhu, sira, hadisai, da tauhidi, duk saida ta kwarance sosai, asali ita bata da wani aibu face zuciya da taurin kai da Allah ya zuba mata. ita kuma ayanaah yanxu ne ma take kkrin kaiwa izu talatin a qur'anidake tafi saka ilimin bokon aranta, babban burinta shine ta dawo me ilimin bokon sosai dan tay kudi takai addanta da mamanta makka, she is soo frail nd innocent, duk dama mutanen tudu suna yawan nuna mata favouritism da fifiko sabida tafi addanta kyaun fuska amma hakan bai taba raba kansu ba, they love each oda deeply and immensely dan ko tafiya suke ahanya haka zakaga suna hira sosai suma alkwaru ma juna kullum kuma hannunsu makale da juna. inayah ke yawan koya ma ayaanar ilimin lissafi (mathematics) da bitan islmiya dake tay nisa. mahaifiyarsu taawure kuwa sosai take kara saka ido akan duk wani motsin su da kuma tarbiyansu, hakanan rayuwarsu ta kasance yau da gobe komi ya lafa suna zamansu anan acikin tsananin kwanciyar hankali da nishadi a anguwar tudu....

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 👇🏻

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025