GANIN IDO

PAGE 26

by @oumameer2671

GANIN IDO 🥀🥀

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671

FREE-BOOK

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

PAGE 26

"amm! Ina nufin za mu iya yin magana?"

Cike da tsoro na fara matsawa baya a hankali ina mai jin sabon tsoron sa na ƙara dukar mini zuciya.

Ganin irin yanayina sai hakan ya  sanya shi miƙewa tsam ya koma jikin ƙofa ya jingina still muna facing juna da shi in a calm voice ya ce.

" Ki yi haƙuri da abinda ya faru...ni ba haka nake ba, kawai dai abin ya mini wani iri ne a jiyan kin gane....saboda haka kada ki ji tsorona, har abada ba zan iya cutar dake ba. Abun da na sani, shi ne ina sonki sosai, ina matuƙar ƙaunarki....And magana ta gaskiya, I can't wait long, matuƙar dai za ki amince da ni, to bana so a ɓata lokaci. Saboda haka zan baki dama ki yi nazari a kaina amma kada ki ce mini a'a, ina roƙonki. Ina son ki, ina so kuma na aure ki. Sai dai... I won't force you Idan har kika ji cewa you have no feelings on me. Ina fata za ki yafe min da abin da ya faru jiya... Dan Allah!"

Ya ƙarashe maganar yana mai haɗe hannayensa tare da ɗan rusunowa da kansa kaɗan alamar roƙo sannan daga baya ya juya ya fice.

Yana fita ya ci karo da Munira da Haulatu suna tsaye a bakin ƙofar sun yi cirko-cirko fuskar su cike da alamar tsoro.

Kallon su ya yi hankalinsa kwance ya jinjina kai ya ce.

"Ina son Beenafah, kuma zan aure ta in sha Allahu ba da jimawa ba. So please! Don't misunderstood me."

Daga haka ya sa kai ya tafi abinsa hankali kwance, tamkar ba shi ne ya yi maganar ba.

A tare suka shigo ɗakin kowaccen su kuma na rige-rige kawo wa gare ni, cike da tashin hankali Haula ta janyoni tana faɗin.

" Beenafah! Dad...da gaske ne wai Ya Emraan ya faɗa miki son ki yake auren ki zai yi??"

Su ne suke faɗin maganar, amma kuma jin ta a bakin su ya ƙara jefani cikin matsanancin tashin hankali da ruɗani. Wai da gaske abin da ya faɗa musu kenan?

"Beenafah ni fa ina cikin tsananin ruɗani da tashin hankali..."

Ajiyar zuciya Munira ta yi sannan ta kallemu ta ce.

"Naga duk kun wani gigice wai....Ni fa ban ma ga wani abun tashin hankali a nan ba..."

Kallon da na muka jefa mata mai alamar tambaya shi yasa ta jinjina kanta tana mai bamu tabbaci ta ce.

"Eh, saboda shi ne yace yana sonki ba kece kika ce kina son sa ba. Sannan tabbas! Tun da har ya furta to lallai zai cika in dai Ya Emraan ne.... Haula kin manta labarin da Hairi ta bamu yanda akayi wurin zancen auren sa? Ai da farko Aunty Lailah ya so ƙanwar mijin Aunty Labiba, amma tunda suka shiga raina masa hankali ya ba ta baya musamman da ta ce mishi tana ganin kawai su haƙura da juna, tun daga sannan bai sake waiwayarsu ba, bayan ya koma wurin aiki sai ga shi kwatsam watarana ya dawo da labarin Aunty Ziza Hajiya ta so ya auri 'ƴar nan Zamfara amma ya ce tunda har Zizar ta ƙauna ce shi to fa shi bai da wata matar idan ba ita ba. Ƙarshe haka ya tabbata. To in Allahu ko a nan ma hakan ce za ta tabbata muddin dai ba kece kika janye ba..... "

Miƙewa na yi da sauri ina mai girgiza kaina domin abin da ba ma zai yi yu ba kenan, hakan yasa na baro musu ɗakin na koma can ƙarshen flowers ɗinda ke jere a Layin veranda ɗin na zauna ina mai rushewa da kuka. Wannan ɗin ba abu ne mai yiyu wa ba? Na zo da sunan mai aiki sannan in ne mi ruguza farin cikin ma su gidan ai hakan ba zai faru ba, domin nasan har abadan abada ba za su taɓa bari ya aureni ba saboda munyi hannun riga ni da shi a komai na duniya.

Haula kuwa, kallon Munira ta yi jiki a sanyaye ta ce.

"Wai ko Muni kina tunanin cewa wannan maganar da Ya Emraan ya yi da gaske yake? Ni fa wallahi hankalina ya tashi sosai.. Munira kin fa san wa su masu kuɗin nan dangane da masu aiki sai a hankali!!!"

Cike da ɗan shakku Munira ta ce.

"To Haula! Duk da cewa bana shaidar Ya Emraan ɗin amma kuma bana tunanin ya aikata wani mummunan abu akan Beenafah. Ina kyautata masa za to, domin duk tsayin zamana a gidan nan ko alamun maganar banza ko kallon iskanci bai taɓa yi mini ba, kema kuma na san haka, sauran masu aikin su da suka gabata kafin mu ma haka. Saboda haka, tunda har hakan ta faru, ina ji a jikina da gaske yake kuma in sha Allahu alheri zai faru."

"Touhh! Allah ubangiji ya ƙaddara ya kuma zaɓa muna mafi alheri baki ɗaya."

"Amin, shi kaɗai zamu ce."

Haɓa Haulatu ta kama tana jinjina kai alamar al'ajabi ta ce.

"Uh uhm! Ko ya za ta kaya idan Aunty Ziza da Hajiya suka dawo?"

Dariya Munira ta sheƙe da ita tana gyaɗa kanta ta ce.

"Akwai kallo ko... Tabbas akwai ɗanɓarwa...to wai ke Haula ko dai daman Aunty Ziza ta gano cewa mijin nata ya kamu da son Beenafahr ne? Ki duba irin abubuwan da ta dinga yi mata ɗin nan komai cike da wulaƙanci..."

Cikin yarda da zancen na Munira ta gyaɗa kanta ta ce.

" Tabbas kuwa, biri ya yi kama da mutum. Haba! Ashe ba a banza Aunty Ziza ta dinga gallazawa rayuwar Beenafah ba. "

" Wallahi kuwa! Yanzu dai mu bata lokaci ta yi nazari tukun. Amma dai gaskiya ni ina bayan wannan maganar ɗari bisa ɗari muddin dai shi ɗin da gaske yake."

******

Misalin ƙarfe uku na rana, Ashiru ne da 'ƴan uwansa zaune a kan tabarma yayin da Ammie ke zaune a wurin ƙofar ɗakin ta, sai Babansu Jafaru shima zaune a gefe ɗaya.

Bayan sun gama gabatar da maganar da ta kawo su ne Babansu ya Jafaru ya yi gyaran murya a hankali ya fara yi musu bayani da cewa.

"To! Alhamdulillah! Mun ji dukkan abun da kuke tafe da shi, amma kuma kamar yanda muka yi muku bayani tun farko, cewa ni ɗin maƙoci ne kawai, zama na mutunci ne ya haɗa mu da su tsawon shekaru uku, kuma tun da muke dasu a unguwar nan babu wanda ya taɓa samun su da wani abun ashsha, sai dai kuma, har yau babu ko mutum guda da ya taɓa zuwa nan da sunan dangin su...."

Ɗan ƙara gyara zamansa ya yi sannan yaci gaba da cewa.

"Abin da har yasa na yi wannan maganar kuwa shi ne; shi aure, ana gina shi ne akan turba ta gaskiya da kuma amana, wanda duk wani abin da zai je ya dawo duk rintsi zumuncin iyaye na nan har abada ba zai rushe ba, sanadiyyar komai an kafa shi akan gaskiya. To magana ta gaskiya bamu san wasu dangi nasu ba kamar yan da kukaji, sannan ni ba zan iya shiga gaban wannan al'amari ba amma dai akwai Wan mahaifinta wanda suke Uwa ɗaya Uba ɗaya wanda a yanzu haka yana Abuja. To In Sha Allahu zamu tuntuɓa daga gareshi daga nan sai ku shirya ku tafi can wurin sa idan har hakan ya yi muku, kunga duk yanda kuka yi da shi, magana ta ƙare,ko ba haka ba?"

Jinjina kai suka yi dukkan su na gamsuwa da bayanin sa yayin da wa su daga cikinsu suka cika da shakku na wannan rayuwar da su Beenafahr suke kai. Bayan ya ɗan tsahirta na ɗan lokaci sannan baya ɗai daga cikin yayyun Ashirun ya ce.

" Ba matsala In Sha Allahu, zamuje kuma zamu jira daga gare ku, idan ma Abujar zamu je mu same shi, wannan duk ba matsala In Sha Allahu. Allah Ubangiji ya tabbatar mana da alherinsa amin. Mun gode sosai."

Shima Yaya Nura ya ce.

"Alhamdulillah! Kuma munji daɗin faɗa mana gaskiya da kuka yi, domin ita gaskiya ita ce mutuncin ɗan adam, hakan kuma shi ne daidai....mun gode Hajiya, sai munji daga gareku."

Daga haka suka kakkaɓe suka tashi suka fice tare da Babansu Jafaru wanda daga nan ya koma gida.

A mota Yaya Kamal ya kalli Ashiru ya ce.

" Ashiru ka tabbata kaga gidan aure a wurin nan? Kada fa kaje ka jefa kanka a matsala ka dawo da ka sani watarana..."

Cike da confidence ya ce.

"Yaya Kamal In Sha Allahu babu abin da zai faru, daman ai ni nasan asalin su waye su...."

Jinjina kai Yaya Kamal ya yi ya ce.

"Auuu! Da gaske kasan asalin su? To faɗa mana muna ji."

"Yaya ka gane, ni dai nasan can inda suka fara zama wanda shi ne gidan Wan mahaifinta daga baya suka dawo nan ɗin...."

Tsaki ya ja sannan ya ce.

"Hakan shi ne kake cewa kasan asalin su?"

Cike da magiya ya ce.

"Ni dai dan Allah ka yi haƙuri, ina sonta a haka, Beenafah yarinya ce mai hankali da natsuwa, sannan ko mahaifiyarta ba ta da matsala."

Girgiza kai ƙanin mahaifin su ya yi Alhaji Bala ya ce.

"Ka ƙyale shi Kamalu, tun da har ya kafe yace ya ji ya gani. Ai wannan mai sauƙi ne, mu dai zamu fitar masa da haƙƙinsa. Allah ya zaɓa masa mafi alheri amin."

Da amin suka amsa yayin da motar ta ɗauki shiru suka ci gaba da tafiya.

Ammie kuwa, suna wucewa ta fito ta shiga gidan Maman Fakiha inda ta tarar da su zaune a tsakar gida Baba yana bata bahasi. Wuri itama ta samu ta zauna hankalinta a tashe ta ce.

" To, kin ji dai yanda muka yi da su ko Maman Fakiha?"

Jinjina kai Mama ta yi ta ce.

"Na ji komai Hajiya, yanzu mi kika yanke a kai?"

Baba ne ya ce.

"Ni ina ga, yanzu ki kawo lambar wayar shi Alhaji Mudassiru ɗin sai in saka a wayata in kira shi in mishi bayani..."

Girgiza kanta ta yi ta ce.

"Idan har kai ne za ka kira shi tabbas ba za ku kwashe lafiya ba, amma zamu shirya zuwa an jima da yamma sai muje can ainahin gidan nasa mu samu Isma'ila Ƙanin matarsa sai muyi masa bayani daga nan sai ya faɗa masa in yaso duk yanda suka yi sai ya sanar mana."

"To shikenan, Allah ya kai mu anjima lafiya."

Kallonta Mama ta yi ta ce.

"Yanzu idan har ya amince kenan za ki aurawa Ashirun ita??"

Jinjina kanta ta yi ta ce.

"ƙwarai kuwa Maman Fakiha. Ashiru mutumin kirki ne, kuma ya taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarmu, sannan akwai wani mummunan abin da ya faru jiya wanda har ya hana mini bacci, da shi na kwana a raina yayin da zuciyata ta cika da tsoro da fargaba, saboda haka auradda ita a wannan gaɓar, shi ne kwanciyar hankalina. Kuma aurawa Ashiru Beenafah da zan yi, har abada ba zan yi danasani ba."

"Allah yasa shi ne mafi alheri."

"Amin, na gode muku sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Bari in je nasan yanzu tana can ta dawo."

Koda ta shigo gidan ta tarar dani kwance akan tabarma na yi shiru tare da lumshe idanuwana.

Kallona ta yi ta ce.

"A'a, Beenafah. Kin dawo?"

Tashi na yi na zauna ina mai yin ƙasa da idona na ce.

"Na dawo Ammie, ina nan ma Bahrain ya wuce islamiyya.."

Matsowa ta yi inda nake zaune ta janyo hannuna a hankali tana mai zuba mini ido ta ce.

"Wai miye yake damun ki kwana biyun nan? Gabaɗaya kin yi wata iri. Kar ki manta ni ɗin fa nice mahaifiyar ki, ba ki da wata wadda ta fini, ni ce nan ƙawarki abokiyar shawarar ki, tabbas ba zazzaɓi ne yake damun ki ba, akwai wani abu na daban,miye shi?"

Ban san lokacin da na fashe da wani irin sabon kukan ba ina mai jin wani irin sanyi na saukar mini a hankali jin yanda take neman ta ji matsala ta. Tabbas dole yau zan buɗe zuciyata in faɗa mata abin da yake damuna, ko Allah zai sa ta sama mini mafita...

"Ko kuma don Ashiru ya faɗa miki yana son ki ne yasa duk kika rikice haka Beenafah.??"

Lokaci ɗaya na ji zuciyata ta yi wani irin Dum-dum ta buga jin tambayarta ta da ta zo mini a ba zata. Wani irin rarraunan kallo na jefa mata wanda yasa ta jinjina mini kanta ta ce.

" Ƙwarai, nasan komai, kada hakan ya ɗaga miki hankali. Domin kuwa har sun zo nan yanzu ba su jima da tafiya ba da shi da en uwansa wurin neman auren ki...."

"Ammie Kuma kin amince?"

"Eh mana."

"To amma miyasa? Ammie idan kika aurar dani wanene zai ci gaba da kulawa da ke?"

"Allah! Allah shi ne wanda zai ci gaba da kulawa da ni da dukkan al'amurana. Shi ne wanda ya hallice ni, kuma shi ne wanda ya fi ni sanin abin da yafi dacewa da ni..."

Kwantowa na yi jikinta ina mai girgiza kaina na ce.

"Ni dai Amm..."

"Shihhh! Ya isa Beenafah, akwai abubuwa da yawa da nake hangowa da hasashe, saboda haka aurenki da Ashiru shi ne kwanciyar hankalina. Duk mutumin da ya taimake ki a rayuwa a lokacin da kike cikin tsananin buƙata, muddin ya zo neman wani abu gareki, idan har abun nan bai zama cutar wa ba to ya kamata ki taimaka masa, sannan kuma idan kika ga wani abu yana ƙoƙarin cutar da rayuwar shi, shi ma tabbas sai inda ƙarfin ya ƙare wurin ganin kin bashi kariya. Saboda haka, ki kwantar da hankalinki, In Sha Allahu za ki yi farin ciki da wannan auren."

Ta shi na yi na shige ɗaki na faɗa kan katifa na sake fashewa da wani irin kuka. Na shiga cikin tsananin ruɗani da tashin hankali. Kafin in baro gidan Hajiya sai da su Munira suka sake bani maganganu akan Emraan har da cewa idan na aure shi Aunty Labiba za ta yi matuƙar farin ciki, kuma shi ne tukuicin da zan bata na amsa soyayyar ƙaninta akan duk irin alherin da ta yi mini. Sannan yanzu ga shi Ammie ta maimaita mini, to kenan idan har haka ne ya tabbata dukkan su suna neman saudaukarwa ta. To ta ya ya? Ga shi wai har Yaya Ashiru da iyayensa sun zo nan. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ya Allah ka ka shiga al'amarina, idan cikin tsananin duhu da ruɗani, Allah ka haskaka mini ka cireni daga cikin wannan ruɗanin.

*******

Tun da suka zo ƙofar gidan Daddy ba su tarar da Uncle Isma'ilan ba kamar yanda mai gadin ya faɗa musu cewa baya nan. Da magiya da komai suka samu ya kira musu shi yace yana kasuwa amma yana hanyar zuwa.

Sun kusa shafe hour biyu a ƙofar gidan suna jiran sa sannan ya dawo. Ga mamakin Ammie sai gashi ya yi musu iso har cikin gidan nasa ya ce su shigo ciki.

Bayan sun shiga sun gaisa, Ammie ta yi masa bayani sannan daga baya shima Babansu Jafarun ya ɗora da nashi bayanin dalla-dalla.

Jinjina kai Uncle Isma'ila ya yi sannan ya ce.

"To! Na ji dukkan bayanin ku, sai dai bani da wata magana da ta wuce in kira miki shi a waya nan a gabanku ku ji yanda za'a yi."

Wayar ya ɗauko ya kira Daddyn. Bayan sun gaisa ya yi masa bayani tiryan-tiryan kamar yanda suka masa.

Bayan ya kambala daga can ɓangaren Daddyn ya ce.

"Hmm! Wai Yanzu Mulaifa ce har ta yi tunanin aurar da Beenafah? Wato ma bata tashi neman izinina ba sai yanzu da ta gama hore mata kunne ta gama yawon ta wanda take na banza sannan za ta tunkaro ni ta ce ni ne ubanta. In banda lalaci Beenafahr gabaɗayanta ƙwaya nawa ce..... "

Cikin wasu zafafan hawaye ta ɗaga muryar ta ta ce.

" Ka ji tsoron Allah Alhaji Mudassir! Yarinyar nan ta isa aure kuma ina so in aurar da ita, dan Allah ina roƙonka da ka yi mini alfarma koda ita ce ta ƙarshe a rayuwata, kada ka ƙeta ce ni a wannan. Ka tsaya mini in aurar da ita."

"To na ji. Sai ki jira idan na yi shawara sai ki kirawo ni daga baya idan na ji zan iya amincewa to, idan kuma ba zan iya ba shikenan dole ki ƙyale mini yarinya ta muddin dai ina da iko da ita."

Daga ita har Maman Fakiha da kuma Baba, babu wanda ya sake cewa komai har suka tattara suka koma gida.

******

Daddy kuma, tun da suka kira shi ya ji cewa gabaɗaya ma babu abin da yake muradi idan ba gida ba, hakan yasa ya tattara ya koma gida.

Yana shiga ko hutawa bai yi ba ya zayyanewa Mummy buƙatar Ammie da ta zo mishi da ita.

Wata irin zabura ta yi ta miƙe tsaye ta ce.

"Wace ma shawara za ka tsaya nema Alhaji?...."

Daga haka ta janyo wayar ta a zafafe ta kira Isma'il, yana ɗagawa ta ce.

"Isma'il wace maganar banza ce wannan nake ji a yanxu? Ba kai ne ka faɗa mini cewa wani lalataccen mashiririci ne marar aikin yi ke neman Beenafahr ba?"

Daga can ɓangaren Ismaila ya jinjina kansa tamkar yana gabanta ya ce.

"Ƙwarai kuwa, ni dai yaron da na sha ganinta da shi gaskiya ba kowan kowa ba ne,..."

"To ya akayi Alhaji yazo mini da wani zancen banza na cewa wai wani ne ɗan kasuwa yake sonta daga Kano?"

"To, nima dai ban san yanda wannan abun yake ba, to amma ke miye naki a cikin rayuwarsu ne wai? Kina can kina rayuwar ki suma suna nan suna ta su, miye ruwan ki da koma waye zai aureta..."

Wata irin razananninyar tsawa ce ta doka masa wacce ta yi kama da dirar aradu cikin tsananin ɓacin rai ta ce.

" Ina ruwanka Isma'il! Wane ne kai da har za ka tsare ni kana tambayata? Ka kiyayeni sannan ka tsaya matsayinka... A na nan ana gyaran gidan ko kuwa??"

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Eh, ana nan ana yi, Allah ya baki haƙur...."

Ƙitt! Ta gimtse kiran sannan ta waigo ga Daddy ta ce.

"Wani lokacin Alhaji Mudassir sai Inga kamar baka da tunani da sanin ya kamata! Idan har ka bari Hajiya Mulaifa ta aurar da Beenafah ga wanda suke so to tabbas ta nuna cewa ba kada wani amfani kenan, sannan duk wani abun ashsha ya taso to fa ba za'a kira sunan uwarta ba kai ne za'a kira. amma kuma idan kai ne ka zaɓo mata miji ka aura mata, hakan shi zai nuna mata cewa kai ne ubanta kuma wanda yake da iko da ita. Tun da har take so ta aurar da ita, to ka aurata ga drivern Humaida Ilyasu, daman na ji yana zancen ƙara mata ta biyu ranar, sai ka aura masa ita. Kaga dai kasan shi kuma kasan wanene shi da kuma inda yake zaune.... "

Miƙewa ya yi yana jinjina kansa da murmushi a fuskarsa ya ce.

" Tabbas! Kin kawo shawarar ƙwarai, haka kuwa za'a yi... "

"Yauwa, Kaga idan har ka yi haka! Har abada za ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar ka kuma za ta san cewa ka kare mata mutuncinta da kuma tsayawa a matsayin uba a gareta. Ana kambala auren en biyu da sati ɗaya tunda muna can gida sai a yi nata a huta kawai, a kai ta can ƙauyen su idan ya gama cin amarcinsa ya dawo bakin aiki."

******

Washe gari tun ƙarfe Shida ina waje ina haɗa abin kari na ji ana ta dukan ƙofar gidanmu tamkar za'a ɓallata.

Cike da wani tsoro da mamaki na zo ina tambayar waye ne.

" Uncle Isma'il ne... "

Ina jin haka na yi saurin zare sakata ɗin ina mai ce mishi ina kwana.

Cikin gidan ya shigo kai tsaye bayan ya amsa ya tsaya a tsakar gidan ya ce mini in shiga in kira mishi Ammie.

Kafin ma na kai ga saka ƙafata a ɗakin sai ga ta ta fito hankalinta a tashe ta ce.

"Isma'il lafiya kuwa?"

"Lafiya lau, ina kwana?"

A darare ta amsa masa gaisuwarsa domin ba ƙaramin shayarda ita ruwan mamaki ya yi ba na gaishe ta da ya yi.

Wayar shi ya ciro a aljihu ya kira mata Daddy ya miƙa mata yana faɗin.

"Alhaji Mudassir ne ke son magana dake."

Tana jinginata a kunnenta ko sallama bai yi ba ya ce.

"Mulaifa ina fatan kina ji na? Maganar wannan yaron da Beenafah wallahi tallahi ban amince ba ban yarda ba. Haka kawai ki je ki samo yaro from no where ki ce wai in aura masa 'ƴata to hauka ake? Duk abin da zai je ya dawo dole watarana dani za ku yi kuka saboda haka ban amince ba. Kuma ma in faɗa miki zancen gaskiya na yi mata Miji... Eh! Ilyasu shi ne wanda zan aura mata, domin shi na san shi na san asalin shi, kuma zai riƙe ta amana. Saboda haka ki shirya nan da wasu satuttuka za'a yi, ban ce ko gishirin ki ki kawo mini ba, ni ne nan ubanta, ni zan yi komai da komai."

Yana yanke wayar ta faɗi a ƙasa dirshan tana maimaimata.

" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Faɗawa na yi jikinta ina wani ƙirƙirar murmushin ƙarfin hankali don kawai in samu ta kwantar da hankalinta na ce.

" Haba Ammie! Dan Allah ki kwantar da hankalinki wannan ba komai ba ne, ki ɗauka yana daga cikin ƙaddarar da Allah ya rubuta mini....Shin ba kece ranar kike faɗa mini cewa Allah ne gaba ga dukkan al'amarinki ba? shi ne wanda ya halliceki sannan komai na ki a hannun sa yake? To nima haka ai! Shi ne wanda ya tsara mini komai na rayuwata, tundaga haihuwata da abinda zai faru dani a cikin duniya har zuwa mutuwata. Saboda haka ki daina ɗaga hankalin ki akan wannan, ki ɗauka ba Daddy ne ya zaɓa mini hakan ba Allah ne..... "

Rungume ni tayi gam a jikinta tana mai fashewa da wani irin kuka tana girgiza kai tana faɗin.

"Na yarda da maganar ki Beenafah...Amma dai abin ya yi mini wani iri a zuciyata ace wai Beenafah ke ce za ki auri driver... Drivern ma Ilyasu! Lallai duniya, aka ce juyi-juyi. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah na gode maka da wannan rayuwar da ka zaɓa mana, yah Allahu kasa hakan ya zamto alheri a gare mu."

Cikin nuna tausayawa a garemu na Uncle Isma'il ya ciro kuɗi masu yawa daga aljihunsa, abin da bai taɓa yi ba, ya ajiye a gefen Ammie yana mai bata kalmomin haƙuri sannan ya juya ya wuce.

Lafiya ƙalau na ƙarasa duk wasu aikace-aikace na, na shiryawa Bahrain ya wuce sannan ni ma na shirya na na zo inda take zaune a ɗaki na sameta ina mai zaunawa a gefenta na kamo hannunta na ce.

"Ammie! Ki yi mini alƙawarin ba za ki shiga damuwa ba akan wannan maganar..."

Girgiza kanta ta yi a hankali tana mai share hawayenta ta kalleni ta ce.

"Beenafah hakan ba zai faru! Idan na ce miki ba zan damu ba a gaskiya na yi miki Ƙarya...."

Ina murmushi na ce.

"Na sani Ammie,dole akwai damuwa, amma kuma kada ki yi ta takai ƙololuwa da har za ta kai ga taɓa mini lafiyar ki. Ki yi sallah, ki ɗauki alƙur'ani ki karanta idan har kika ji ƙunci mai yawa."

Bayan na fito, gidan Maman Fakiha na shiga na faɗa mata cewa dan Allah ta duba mini Ammie domin na barta ba ta jin daɗi. Daga nan na fito na wuce.

Na share kusan kwanaki biyar ba tare da na sanya Ya Emraan a idona ba, Yaya Ashiru ma tun da suka dawo suka ji irin amsar da Daddy ya ba su ban sake sanin a wanne hali yake ciki ba kuma.

*******

A ranar da Hajiya ta iso daga tafiya, da dare bayan Emraan ya dawo Masallaci ya tarar da Hajiya a parlour tana zaune ya gaisheta sannan ya ja baki ya yi shiru.

Kallon shi Hajiyar ta yi ta ce.

"Emraan! Lafiya kuwa?"

Ɗan ƙara muskutowa ya yi zuwa gaba kaɗan yana kallonta a nutse, ya ce.

"Hajiya Beenafah na ke so! Da gaske nake, so nake na aureta."

Cikin jin tsananin mamaki Hajiya ta kalle shi ta ce.

"Emraan! Kasan kuwa mi kake faɗa? Beenafar ce kake so?"

Hankalinsa kwance ya kalle ta ya ce.

"Ƙwarai Hajiya, sonta nake, kuma na san cewa da nayi ina sonta don tana mai aiki ban aikata wani zunubi ba. Sannan ke kanki yarinyar nan dai kin santa tsawon lokaci Kinga irin tarbiyyarta..."

Jinjina kai ta yi sannan ta ce.

"Ka sanarwa Labiba ne?"

Girgiza kansa ya yi ya ce.

"A'a"

"To ka fara neman so ga ita Beenafahr, sannan ka shawo kan matarka, daga nan sai ka sanarwa ita Labibar, idan har matarka ta amince itama yarinyar ta amince to nasan ba za ka samu matsala ba, Allah ya taimaka ya bada sa'a ya zaɓa mafi alheri."

"Amin amin hajiya, na gode sosai Allah ya saka da alheri, Allah ya ƙara tsawon rai da lafiya mai amfani."

Daga haka ya miƙe ya fito cike da farin ciki yana mai hamdala ga ubangiji domin haƙar sa ta kusa ta cim ma ruwa.

*******

Aunty Aysha ce zaune ita da su en biyu, yau kwananta huɗu da isowa ƙasar wurin hidimar auren ƙannen na ta dake ƙaratowa a yanxu.

Tun misalin ƙarfe tara na dare suke abu ɗaya da Hassana akan Ita fa har yanzu tana kan bakarta domin wallahi ba za ta auri Ameer ba.

Kuka take ta yi ba ƙaƙƙautawa yayin da Aunty Aysha ke ta aikin rarrashinta da cewa.

"Ya kamata fa ki sassautawa kan ki hakanan Hassy...ki duba tun kafin in zo ƙasar nan ake ta wannan badaƙalar kuma Mummy ko sau ɗaya bata taɓa nuna alamun tausayawa a gare ki ba ballantana ma ki yi tunanin za ta iya canja ra'ayinta akan wannan maganar..... Ki tausayawa kan ki hakanan dan Allah, ki yi hak'uri ki karɓi wannan auren na Amee..."

"Wallahi tallahi na fi so in mutu da in aure shi,kuma tun da har hangen dukiya yasa sun yi biris da neman farin ciki na nima gwanda in mutu in ɗanɗana musu, sai su je su ci dukiyar in gani..."

Da sauri Husaina ta girgiza kanta idanunta cike da hawaye ta ce.

" Dan Allah Hassana ki daina zancen mutuwar nan dan Allah na roƙe ki, wallahi hankalina tashi yake, idan kika mutu kika barni to ni in rayu da wa kenan?"

Miƙewa ta yi cike da hargagi tana wani irin kuka mai ban tausayi ta ce.

"To ku nema min mafita mana! Idan har bakwa son in mutu kuma kun tabbatar ni ɗin 'ƴar uwar ku ce ku sa a bani Salman ɗinda na ke so.. Idan kuwa ba haka ba wallahi tallahi sai na kashe kai na..."

Jinjina kai Aunty Aysha ta yi tana mai share hawayenta ta ce.

" Mafita muna nan muna ta kai kukanmu a wurin Allah, In Sha Allahu shi ne zai yi mana mafita. Ke ma ki yi hak'uri ki yi ta gayawa Allah in sha Allahu za ki samu abin da kike so idan kika yi haƙuri, idan ma kuma baki samu Salman ɗin ba ki yi hak'uri Hassana mai yiyuwa ƙila ba shi ne alheri a gare ki ba."

A tare suka rungume Aunty Ayshar suna ta kuka gwanin tausayi. Yayin da Aunty Aysha ta yi ta ba su kalamai ma su sanyaya zuciya.

Daga wannan ranar shikenan ta saki jikinta ta dawo yin abubuwan ta yanda take tare da ɗora dogaronta da yarda ta ga Allah da kuma Aunty Aysha.

Haka suka ci gaba da tafiya, ana ta mashahurin shirye-shirye na musamman.

Yau suna zaune a parlour suna lissafin abubuwa. Husaina ta kalli Mummy ta ce.

"Mummy yau fa saura kwana takwas cif mu tafi, ga shi har yanzu ni banga jikin mu ya yi irin canjawar nan ba da ake ta zuzuta wurin gyaran jikin da shi, ki duba irin kuɗin da ake ta kashewa."

Jinjina kai Mummy ta yi ta ce.

"Ni ma fa na lura da hakan. Tashi ki kira mini Hassana ta haɗamu da wannan matar da tace mu juya zuwa gareta mu gani kafin nan da kwana takwas ɗin."

Nan suka ci gaba da tattaunawa da Aunty Aysha tsawon lokaci, sai ga Husaina ta dawo a ruɗe ta ce.

"Mummy Hassana fa bata nan! Sannan kalla kiga takardar da ta ajiye akan gadonta...."

Wani irin fisge takardar Mummy ta yi da ƙarfi ta fara karantawa kamar haka.

"Mummy... Daddy... Aunty Aysha...er uwata...Yaya Hafiz da ma duk wani wanda yake da haƙƙi akaina... Ina mai neman gafararku, na tafi wurin da zan samu farin ciki, tunda har baku damu da damuwata ba, ku dukiya kuke so ni kuma farin ciki nake nema,saboda haka ni na nemawa kaina mafita,kuma kada ku ce za ku  wahalar da kanku wurin nemana domin har abada ba za ku sameni ba. Na bar ku lafiya...Hassana Mudassir Wazeer."

Wani irin gigitaccen ihu Mummy ta buga lokaci ɗaya tare da zubewa zuwa ƙasa somammiya. Cike da tashin hankali Su Aunty Aysha suka kwasheta sai asibiti.

*********

Ina cikin Kitchen ina haɗawa Hajiya kwaɗon zogale! Na ji muryar Ya Emraan a bayana a hankali ya ce.

"Lady B..."

Waigowa na yi muka haɗa ido da shi cikin sauri na sauke nawa idon a ƙasa a darare na ce.

"Ina wuni!"

"are you sure cewa wuni ne yanzu Lady B..."

Ya ƙarashe maganar yana mai duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa sannan ya sake Kallona ya ce.

"11am ce fa yanzu.."

"Ina kwana.."

Murmushi yayi mini har ina iya jiyo sautinsa duk da cewa ban kalle sa ba ya ce.

"Zamu iya fita waje muyi magana?"

Jinjina kaina na yi ba tare da sanin wace wajen yake nufi ba. Ban gama digesting maganar tasa da kyau ba sai gashi ya ƙara so kitchen ɗin ya zura hannunshi ya ɗeba kaɗan ya kai bakin shi ya tattauna a hankali ya haɗiye sannan ya ce.

" It taste good....i will wait outside."

Ɗauka na yi bayan ya fice na kaiwa Hajiya zuciyata cike da fargaba ina gudun kada ta ji ya zo inda nake ta yi mini faɗa.

Bayan na ajiye mata na tashi na koma na ci gaba da aikina kawai na share shi.

Ina nan ina aikin sai ga Haulatu ta shigo tana faɗin.

"Dan Allah wai miyasa kike haka Beenafah? Ya Emraan ya ce mini yazo nemanki..."

Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalle ta na ce.

"Wai dan Allah Haulatu sau nawa zan faɗa muku cewa an yi mini miji a gida..."

"And so! Tun da har ba'a ɗaura ba ai ba za ki hana shi gwada sa'arsa ba..."

Hannuna ta janyo ta kaini wani kyakkyawan lambun da yake zaune a ciki wanda ban taɓa sanin da shi ba a gidan. Wuri ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali.

Jikin wata flower na ɗan jingina kaɗan tare da kama ganyenta ina murzawa a hankali.

" A tsaye kike so muyi maganar?... To ba damuwa..."

Daga haka ya miƙe tsaye ya matso inda nake wanda har ina iya shaƙo daddaɗan ƙamshinsa, a hankali na ji bugun zuciyata ya fara sauyawa wanda har sai da na ja baya kaɗan ina mai ɗago idona na kalle sa.

Kwalin waya ya miƙo mini yana faɗin.

" Ga wayar ki da na fasa...ina fata za ki yafe min?"

Girgiza kaina na yi na ce.

"A'a kabar shi..."

"Ki karɓa mana. Rashin karɓar wayar nan zai sa na ji ba daɗi a raina."

Jin hakan yasa na amsa kawai amma ba da nufin amfani da ita ba.

"Yaushe kike so na zo gida wurin maganarmu? Yau?... Gobe..jibi??"

Shiru na yi ina jin tambayarsa mai kama da tatsuniya domin babu abu guda ɗaya da zai samu daga gare ni.

"Lady B...lokuta da dama a rayuwa, shiru ya kan zama amsar da ba'a buƙatar ƙarin bayani a cikinta. In Sha Allahu ranar Juma'a mai zuwa, za a je nema mini auren ki. Ina son ki sosai, na yi alƙawarin kare ki da dukkan ƙarfina, na yi miki alƙawarin farin ciki iya yanda zan iya..... "

Cike da wani iri a raina na girgiza masa kaina tare da motsa laɓɓana tamkar ana mini dole na ce.

" Kada ka bari hakan ya girmama a ranka, domin an riƙa an zaɓa mini mijin da za'a aura mini nan da wasu kwanaki..... "

✍️ OUM-AMEER ✍️