AGOLA (Behind the palace walls)

Chapter 6

by @hauwajaywrites

Suna cikin tafiya duk sunyi shiru Leena pouted, "Daddy , why did I even come to pick Mummy up? She didn't even tell me she was going and she didn't care to know how I was doing?" Daddy yayi murmushi while driving yace "Sorry dear, she used to call me and ask me how you're doing, but mostly I'm in the office and you're in school too, so Kinga laifi nane da bana isar miki" ta girgiza kai tana kallon bishiyoyin kan hanya can tace "Daddy! But what about her traveling without telling me baka ce komai a kai ba? At least she should have told me. I was really upset when I found out, I even cried" yace "Leena rasuwa aka yi shiyasa kuma su Mamin ki zasu tafi a ranan bayan wannan jirgin ne kawai available bayan shi sai na washe gari so nace tabi wannan din su tafi tare da su Mami kawai" ta gyaɗa kai kawai har suka karasa airport ba wanda ya sake cewa komai

As Sirbajo emerged from the arrivals area, she spotted her loved ones waiting for her. Her love of her life Leena's face lit up with a bright smile, and the little girl exclaimed, "Ammiiiii!" before rushing towards her Ammi. Sirbajo ta ɗurku sa opened her arms, and Leena launched herself into a tight hug, hawaye ne taji suna sauka a fuskar ta Ammin ma taji kamar hawayen nason saukowa amma sai ta rike Leena ta ciro fuskar ta ajikin Ammi tana kallon idon Ammin tace "I'm so happy to see you, Ammi!" holding her mother back tightly. Daddy smiled, watching the reunion. Shima ya karasa yace "Welcome home, Sirbajo," he said, his voice filled with warmth. Leena let go of her mother and stepped aside as Daddy wrapped his arms around Sirbajo, holding her close. Ammi ta fara kalle kalle ganin ba wanda yake kallon su ta ga kowa ta kansa ya ke hakan yasa ta ɗan sake jiki Daddy yayi murmushi ganin reaction ɗinta yace "I really miss you, dear. Welcome back, my peace of mind" Murmushi tayi tace "thank you, yaya na" daga haka suka kama hanyar inda motar Daddy yake, suka kama hanyar Gida Leena sai bawa Ammin labarin take Daddy yana addu'an kar ta bata labarin ɓatan ta ga Leena kuma idan kace mata karki faɗa kaza ma wane Toh ita kuma nan kake jawo hankalin ta sai ta faɗa kawai dai yana hoping Allah ya mantar da ita ko da zata faɗa ya kasan ce not now. Kusan tare motar Daddy da na Mummy suka kusa kan su cikin layin yau ma, Daddy ne ya fara shiga da motar yayi parking Ammi na sauka mai gadi da drivern yara suka zo kara ma Ammi ta'aziyya Mummy na parking ko kallon idan su Ammi su ke ba tayi ba tayi wucewar ta ciki, Daddy ya bita da kallon, da kansa ya dauki jakkar Mummy ya wuce da shi su kuma suna biye da shi a baya a bedroom ɗinta ya ajiye ita kuma nan sofan dake parlorn ta zauna Daddy ya fito nan suka sake sabon gaisawa yana sake mata ta'aziyya kallon Leena tayi tana murmushi tace "Me haka kuma Leena?" tace "ai Ammi na manta ne na miki oyoyo a airport" Ammi tace "na san kina fushi da ni Toh kiyi hakuri, kuma naga ai ga Hajiya kuma Ya Rayyan yana nan" taki kallon direction din Ammi ita sai yanzu ma take jin zafin abinda Ammi ta mata because she never expect, Ammi ta mike tana kallon Daddy tace "barin watsa ruwa sai na chanza kaya" tana kallon Leena sai kuma ta ja mata kumatu tace "shikenan zan koma gidan mu ai idan kika ci-gaba da fushin" tana gama faɗar haka ta wuce ciki, kallon ɗakin tayi ɗan 3 days da tayi bata nan kalli wajan har ya soma kura dole ita zata gyara kafin mai aiki su zo gobe. Ana idar da Magrib Daddy direct part ɗin Ammi ya wuce da sallama ya shiga Leena na zaune tana rubutun da ta saba yace "Leena kinyi sallah kuwa?" ta girgiza masa kai yace "Toh tashi kije kiyi idan kika fito sai ki ci gaba" ta gyada masa kai sannan ta wuce ɗakin ta, Zama yayi akan sofa ya ɗauki littafin Leena yana ganin Abunda take rubuta wa mamakin yadda rubutun Leena yake da kyau yake yi ga ilimi sannan ga baiwa Ammi ne ta fito a ɗakin ta ta tsaya bakin kofar tana kallon sa tace "ya ka tsaya a can kuma" yace "Naga ba hakura zakiyi da share share da kike yi bane, ki bari gobe masu aiki su gyara miki sai ki kwana a part ɗina ba sai kin wahalar min da kanki ba" Ammi ta ɗauke kanta tace "ai harna gama ma kuwa" daga haka ta karaso cikin parlorn tana kallon sa tace "me wannan kuma?" yace "talent ɗin Leena nake karantawa" Sallama akayi Ammi ta ɗaga kanta tana kallon kofar ta amsa tace "Shigo mana ya Rayyan" karaso wa cikin parlorn yayi zai zauna a kasa tace "haba ya Rayyan dan Allah karka zauna a kasa na sha faɗa maka haka" Murmushi yayi ya gaida ta ya kara mata ta'aziyya sannan ya kalli Daddy yace "Sannu da zuwa Daddy" Daddy yace "yauwa, amma ba anan kayi magrib ba ko?" ya gyaɗa masa kai yace "eh a hanya nayi" Leena ta fito da gudu "Ammi tace "Amma Leena ban hanaki wannan gudun ba ko?" tace "toh Ammi ai kar ya Rain ya tafi ne" ta maida dubanta kansa tace "Ya Rain na rubuta wani abu ina zaka ban wayan ka nayi video ko?" ya gƴada mata kai ta kuma cewa kasan me za ayi inter school debate kuma an sani" yace "Ma Shaa Allah, dear. Haka nake son ji kullum " ta gyada masa kai sai kuma ta juya tana kallon Daddy tace "Daddy ina kace idan na cigaba da kokari ina ba zanyi Jss 3 ba ko?" yace "Eh ba zakiyi ba" tana kallon Ammi tace "Toh Ammi kinji ko? Kuma a school ɗin mu ko baka cika ba idan kana kokari su suke maka tsallake" Ammi tace "Haba, ai dole zata ma yi Leena fah kawai sawon kafa ne gare ta kuma fah haka aka mata tsallaken primary 6 yanzu kuma kuce zata kuma yi" Rayyan yace "Toh ai Anty what matters shine ace tana da kokarin balle Leena kuma sai dai ace Alhamdulillah" Daddy yace "bar yarinya tunda bata so karki cuce ta" Leena tace "Wallahi ya Rain ina so naga na gama secondary da sauri" Ammi tace "ke bana son Manyan ce" Sallama aka rafka a bakin Kofa Ammi ta tashi daga kujeran da take ta koma gefe ta zauna Hajiya ta shigo Ammi tace "Dan Allah Hajiya kiyi hakuri yanzu fah nake son shigowa na gaishe ki sai gashi kin shigo kuma" Hajiya tace "A'a, ke kuwa banda abun ki ai mune ya kamata mu shigo mu muki sannu da hanya da kuma ta'aziyya" Ammi na Murmushi ta gaishe ta ta amsa nan Hajiya ta mata kara mata ta'aziyya Hajiya na kallon Leena tace "ba shakka yau Kinga Ammin ki shine ba zaki kulani ba ko" Daddy yayi dariya yace "yanzu kar a shiga tsakanin ku mutun yaji kunya kuma" Leena tace "Dama fa ina jira ki gama magana da Ammi nane fa" Hajiya tace "kiyi ta kanki ke kika sani kuma" Leena ta fara dariya daga haka ta tashi ta fita Rayyan ma ya mike Ledan hannun sa ya mika ma Leena yace "Ki kaiwa Ammi" Ammi tace "Me haka kuma ya Rayyan" yace "Ammi naga yau kika dawo Toh yaushe kuma kikayi girki shine nace barin tsaya na siyan miki kawai" tace "Toh na gode, Allah an fana" yayi ma Daddy sallama sannan ya fita. Washe gari da safe bayan Ammi ta gama shirya Leena tasa mata abinci a lunch box ɗinta sai ta ɗago tana kallon Leena tace "Amma nikam Leena baki cin abinci ne da na tafi naga kina rame min?" "toh bayan kin tafi kin barni Kuma kinsan Mummy ba zata bani ba, Hajiya kuma kullum sai munyi faɗa sometimes I prefer na sha Golden morn, sometimes kuma ya Rain ke siyamin abu" Ammi ta karasa saka mata jakkan ta a baya tace "it's okay Leena, yi sauri ke tafi kafin su riga ki fita su fara mita" daga haka tayi wa Ammi bye ta wuce parking space tana zuwa ta gaishe da driver ya amsa mata da fara'a tana zaune sai gai su Nisreen sun fito suna zuwa suka shige motar. Nisreen na kallon abincin ta daya zuɓe a kasa tana ɗaga kai sai suka haɗa ido da Leena, Leena ta buɗe lunch box ɗinta ta raba abincin into 2 ta bar ɗayan akan desk ɗinta dayan kuma ta tashi ta karasa inda Nisreen take ta mika mata tace "take this, Nisreen"  Nisreen da hawaye ke zuba a fuskan ta ta wanke Leena da mari tace "shine kika zuɓar min da abinci na?" Kowa ya buɗe baki yana kallon Nisreen da mamaki wani teacher ne yazo wuce wa ya tsaya yana kallon su yace "Hey, girls, what's happening here" Nisreen tace "She poured my food on the ground" ta karasa maganar tana pointing ɗin Leena duk matan class ɗinsu suka buɗe baki suna kallon ta da mamaki teacher ɗin su ya buɗe baki zai yi magana sai One of the students said "Uncle, Nisreen is lying. She fell down with food in her hand, and it spilled on the ground" ya juya yana kallon Nisreen da mamaki Basma said, 'And uncle, you know what? Leena was just trying to help Nisreen. She divided her food into two and gave her half, but Nisreen just slapped her and said it was Leena who poured her food" wata tace "this is bad Nisreen" Uncle scolded Nisreen, saying, 'You're lying. What you did was wrong. The food spilled from your hand, not because someone poured it. You should stop behaving like this, okay?" daga haka ya fice a class ɗin Nisreen started crying Leena ta juya tana kallon Basma, All the students started shouting, 'Nisreen, stop lying! Nisreen, stop hating your sister! Nisreen, you're bad!" Leena ta haɗa hannayen biyu tana rokon su tace, it's okay, please stop shouting at my sister. She's good enough." Nisreen ta maso daf da Leena tana kallon cikin idon ta tace "I hate you, Leena" daga haka ta fice ta bar class ɗinsu Basma na kallon Leena tace "Toh me na damuwa?" Leena ta girgiza kanta kawai ta koma kan desk ɗinta ta zuba abincin ta fara ci, can sai ga Nisreen da Niswa sun shigo class ɗin tare Leena kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta Basma tace "Look at her, she called her sister, and she wants to cause trouble" daga haka Basma ta fice da gudu taje kiran teacher ɗin ɗazu Niswa tace "ke Leena uwar me ta Miki zaki kai karanta wajan malamin ku har kisa ƴan ajin ku su fara mata waka" Leena ko ɗago kai bata yi ba cin abincin ta take hankali kwance wata tace "Sister ba haka abun ya faru ba, sistern kice bata da gaskiya at all so don't just judge her" ta harari yarinyar ta mayar da dubanta kan Leena tace "ke dan uwar ki ba zaki kulani ba ina Miki magana kina jina" Leena tace "Excuse me, please. If you're not comfortable speaking English, I'd like to clarify that we're in a school setting, where English is preferred. At home, I can communicate with you in Hausa, but here, let's try to use English, okay? Ƴan ajin suka kwashe da dariya Suna ihu Niswa tace "bura uba!! Har Ni zakiwa rashin kunya?" ta daga hannun ta wanke Leena da mari daidai lokacin da Uncle ɗin yake shigowa class ɗin tare da Basma, zane niswa yayi sannan yayi warning Nisreen, Niswa taci alwashin sai ta rama dukan da aka mata akan Leena da kuma rashin kunya da ta mata har tasa ana mata dariya,

Hey, sis! Please hint the star at the corner.

ayi following acc dina pls, a danna min gifts ko likes, sannan ayi sharhi mutanen arziki

Za’a same ni a duk social media @ Hauwajay writes

***