AGOLA (Behind the palace walls)

Chapter 9

by @hauwajaywrites

Mummy na kallo Daddy sakeke sai kuma ta girgiza kai tace "sai kuma ka kyale shi haka nan?" yace "toh me zan ce masa kuma? yace basu magana ma da yarinyar yanzu" tace "toh zuba masa ido zamu yi haka nan?" yace "Idan lokacin sa yayi za'ayi ba mu'isa mu tsallake ba" ta gyaɗa kai tana kallon Daddy da takaicin sa ya cika ta, ya lalle ta sai kuma yace "Beside ma yace ai akwai wanda yake so" tace "waye ita ɗin, aina take ?" yace "how will I know, Khadija? gani yayi ta mike yace "ina kuma zaki?" tace "ɗakin Rayyan mana" yace "Ni banga dalilin za yasa kika dage sai ansa bikin sa kwanan nan ba, ki bar yaro ya huta, it's already pass 10pm fah, haba ke kuwa". Washe gari, Saturday, Ammi na idar da azkar ɗinta ta ninke prayer mat ɗin ta ajiye ɗakin Leena ta nufa ta shiga cikin ɗakin taga har sannan tana bacci taba ta tayi sai Leena ta buɗe ido Ammi ta mata Murmushi tace "tashi kiyi sallah ko?" gyada mata kai kawai tayi Ammi ta taimaka mata ta tashi tace "ya jikin?" tace "Da sauki" tace "meke Miki ciwo yanzu?" ta girgiza kai tace "yanzu ba inda yake min ciwo kawai dai baki nane har yanzu ɗaci" Ammi ta kai ta toilet tayi wanka sannan tayi alwala suka fito Ammi ta shinfiɗa mata sallaya tace "toh yi sallah kafin nan barin je ɗaura miki breakfast, me zaki ci?" Leena tayi shiru tana nazari sai kuma tace "Zan sha ice cream ɗin da Yaya Rain ya kawo min jiya" tace "Abinci fa?" tace "Sandwich" daga haka Ammi ta mike ta fita. Rayyan yayi sallama a bakin kofar parlorn Hajiya ta amsa masa tace "Riyan shigo mana ya shiga ya zauna ya jira har ta karasa lazimin ta sannan ta karaso cikin parlorn yana kallon ta ya gaishe ta ta amsa masa tana tambayar sa ya aiki ya amsa da Alhamdulillah tana kallon sa kamar wacca ta tuna abu ta fara washe baki tace "ashe za'a je sa ranan bikin ka" da sauri ya kalle ta da kyar ya samu yayi healing daga Abunda yake ji jiya yanzu kuma Hajiya zata fama masa, ya girgiza kai yace "A'a dama Mummy ne tace ya kamata aje sa rana bata san Ni da yarinyar ko magana ba muyi ba" tace "kamar yaya kenan?" yace "kawai dai yanzu ta daina min magana sannan ta siro da wasu dabi'u da ba nata ba" Hajiya tace "Atoh, Ni tunda ka taɓa kawo ta nan bata min ba kwatakwata kar nayi magana ka killaceni" daga haka yayi shiru ta kura masa ido tace "toh yanzu an fasa wannan ɗin kenan" ya gyaɗa mata kai tace "toh yanzu da wa za'ayi?" yace "ba yanzu za'ayi ba Hajiya" tace "tambayar ka fah yarinyar nake yi?" ya ɗan kalle ta sannan ya mayar da kallon sa wani direction yace "yarinyar bata karasa girma ba, amma tana gama secondary school zaku san ta" daga haka ya miƙe Hajiya tace "Toh ai na take?" yace "Hajiya barin fita zan duba jikin Leena daga nan zan wuce gymnasium yau Saturday ne" Hajiya ta tsaya kallon sa tace "zaka zo nan neman kindirmo ai, zanyi maganin ka" ya fice abin sa kamar be ji ta ba. Direct a kofar su Ammi yayi sallama Ammi tazo ta buɗe masa kofar ta koma ciki shiga yayi yana kallon wani direction yace "ina kwana Ammi" ta amsa masa yace "ya jikin Leena ɗin? Hope da sauki yanzu" tace "Eh Alhamdulillah dan yanzu takan ci abinci bata amarwa amma sai dai bata ci daya" yace "zata ji sauki in shaa Allah" ta nuna masa kofar ɗakin tace "toh ka karasa mana" ya karasa ya shiga Leena da jin muryan sa ta kulle ido da sauri ya shiga ɗakin yaga tana bacci Murmushi yayi ya karasa cikin ɗakin ya dauki sauran alluran da ya ajiye jiya a saman walldrope ya haɗa sannan ya karasa inda take still idon ta a kulle ta kasan ido ya kalli bakin kofar ganin Ammi bata nan ya kai hannun sa fuskarta da hankali kaman mai raɗa yace "Leena, don't pretend you're sleeping; I know you too well" bata san sanda tayi murmushi ba ta tashi ta zauna tana kallon sa cikin shagwaba tace "I don't think I need the injection; I'm feeling fine Yaya Rain" hararan ta yayi yace "Haba baby girl, this will be the last injection, and then you'll be all set. Exams are coming up soon, so i want you to be healthy and do well" ta turo masa baki da kyar ya lallaɓa ta ya mata ta fara sheshshekan kuka yace "c'mon, you're not baby anymore fa" ta juya masa baya ya kwashe kwalɓan alluran daya fasa yace "toh ni zan tafi" ta juya tana kallon sa tace "zan bika" yace "gym zan tafi, ki bari da yamma sai mu fita ki kaga layin nan zaki ɗanji dama dama" ta gyada masa kai kawai, daga haka ya fita yayi ma Ammi Sallama. Wajajen karfe takwas Ammi na kwance a ɗakin ta ta rasa me ke mata daɗi haka nan take jin ta ba lafiya amma kuma ta rasa meke damun ta sallaman Hajiya da taji yasa ta amsa ta fito already Hajiya har ta shigo parlorn Ammi ta gaishe ta ta amsa Hajiya tace "ina ita Leena daman faten wake na dafo mata naga bata son komai idan bata da lafiya sai shi" Ammi ta gyaɗa mata kai tace "Sannu Hajiya, tana ma cikin ɗakin nata" dan yanzu Ammi bata wani son surutu, Hajiya ta shiga taga tana bacci ta fito tace "idan ta tashi sai ta sha yanzu naga tana bacci ne" Ammi tace "Toh shikenan, Allah saka Hajiya" daga haka Hajiya ta kama hanya ta fita ita kuma Ammi ta koma ɗakin ta ta kwanta. Wajajen karfe goma sai ga Rayyan ya dawo daga Gym yayi sallama ya shige parlorn ganin Mummy yasa ya tsaya yace "Mummy ɗazu ai na shigo zan gaishe ki naji a kulle nace yau Saturday kila kina hutawa ne" tace "Sure!" yace "ina kwana mummy, kin tashi lafiya" tace "Alhamdulillah, zauna nayi serving ɗinka" yana kallon ta yayi murmushi yace "A haka Mummy? Kalli yadda zufa ke ɗinga daga jiki na barin je nayi wanka sai na dawo" tace "toh before then, Rayyan me yasa ka fasa auren Anisa?" yace "Ohh Mummy, yarinyar ta chanza ba yadda na santa da ba and yanzu kafin na hakura da ita ita ta fara hakura da Ni dan har ce min tayi she's not interested yanzu kuma, so Kinga bani da laifi" tace "toh wa kace wa Daddyn ku kana so?" yace "wata ce, amma ba lalle iyayen ta su yarda su ba Ni ita yanzu ba" tace "saboda me?" yace "because she's still teen, Mummy" Mummy kallon sa take yi bata ko kiftawa kamar me son gano wani abu jin shiru da Rayyan yaji tayi yasa ya ɗaga kansa ya kalle ta tace "kuma dole sai ita zaka aura? Ina Husna kanwar abokin ka da ta nace maka why not ita akan yarinyar da kake magane, wato sa'an su Niswa fah" yace "Mummy bana son Husna, bata da kamun kai, baki ga yadda take exposing kanta a social media ba" tace "Ga ƴaƴan aminiyarta dukkan su uku mata ne sai wanda ka zaɓa aciki bari zan mata magana" da sauri ya ɗaga kai yana kallon ta matar da ya tsana alakarta da Naman sa ace ya auri ƴarta God forbid yace "Mummy kinsan ba zan iya auren ɗaya daga cikin ƴaƴan ta ba, kiyi hakuri kawai" tayi shiru tana kallon sa yace "but Mummy me yasa kike so kiga nayi aure ne all of a sudden" tace "Mate ɗinka nawa suke yi, shiyasa" yayi shiru yace "barin shiga zan yi wanka kafin na fito" tace "Okay, but ka sani Maganan be mutu ba Rayyan dole zaka fitar da mata ko na fitar ma". Ya shiga ciki da tunani iri da kala suna yawo a ransa. Jidda tace "Ya Sadeeq na jira ka idan zaka fita sai kayi dropping ɗina a gidan su Leena" yace "waye haka?" ta kalli Sultan da yake murmushi sai kuma ta sake kallon sa tace "wannan little baby da tazo gidan nan mana few days back?" Sai sannan ya ɗa ga kansa ya kalle ta yace "dama akwai wacca tazo gidan nan ne few days back ban sani ba? ta juya ta kalli Sultan sai taga Mummy da yanzu fitowar ta a ɗakin ta da sakon da zata ba Leena, Mummy ta harare sa tace "ki ta ɓata bakin ki ma Sadeeq" ta karba turaren tace "ta gode Mummy" daga haka Sadeeq ya mike ya haura sama Jidda tace "ɗan rainin hankali ne wallahi ya Sadeeq din nan" sai yanzu Sultan ya fashe da dariyar daya ke kunshewa Tun tuni yace "Kin san I caught him watching her videos countless times" Jidda ta zara ido tace "When? bayan na goge a wayan sa" Sultan na dariya yace "harda recycle bin kika goge?" tace "No" yace "definitely ya dawo da su ne" tace "kasan ranan da muka kai ta ina zuwa a lectures nace ya ban wayan sa zan tura videos ɗinta saboda idan na koma zan turawa maman ta sai ya fara masifa ashe be shiga ya gansu ba da kyar na bashi hakuri ya yarda na tura sai na goge, kai amma da mamakin ya Sadeeq zan kwana, imagine fah wai waye ita?" Sultan yace "Kaɗan daga aikin sa kenan" Mummy ta tashi ta wuce ciki abunta sai ga Sadeeq ya kuma shan wanka ya fito jidda ta ɗauke kai Sultan yace "wajan ɗaura aure zaka ne? naga ka kuma wani wankan gashi yau dama Saturday ne" ko kallon Sultan be yi ba balle Sultan yasa ran zai basa amsa, ɗaukan Apple ɗaya yayi dake kan Centre table yayi hanyar kofa ya fice Jiddah na kallon Sultan tace "duk kai ka jamin Ya Sultan wai na bisa ya rage min hanya" sai da Sadeeq ya shiga motar sa sannan ya danna mata horn, Sultan yace "yana kiran ki fa" tace "kyale sa Ni ba inda zanje na fasa zuwa da shi ɗin" sai gashi tun kan ta rufe baki ya kira ta a waya ɗaukawa tayi tasa a handsfree tace "ina ji" yace "ke dalla Ni sa'an ki ne da zaki bari ina jiran ki?" ta kalli Sultan jin abin da yayan nata yace tace "toh ai baka ce zaka kaini ɗin ba" daga haka ya katse kiran ta tashi tana kallon Sultan tace "ya Sultan na tafi, i wish tare zamu tafi" yace "zan zo ɗaukan ki sai mu gaisa da ita" ta wuce ɗakin Mami ta mata sallama sannan ta wuce ta fita buɗe gaban motar tayi ta shiga bai ko kalle ta ba yace "Ina ne gidan nasu ya ke?" tace "ita wa ɗin?" ya juya ya mata wani kallo yace "if you're not ready, get out" ta kusan fashewa da dariya da kyar ta kunshe tace masa "Sorry big bro, na dauka tambaya ta za kayi ina zaka yi dropping ɗina" kai hannun yayi zai buɗe mata kofa ta fita masa da kyar ta basa hakuri tace street F suke bai sake tanka mata ba suna shiga layi tace masa "Ya sadeeq daidai wancan gidan zan sauka parking yayi without looking at her, wani direction daban yake kallo ta sauka tace "thank you Y Sadeeq" ta buɗe motar zata fita to her own surprised taji yace "yaushe zaki fito? Or just call me idan kin gama" ta juya tana kallon sa sakake saboda shi baya kai mutun waje kuma ya dawo da kai gida balle yadda ta riga masa hauka yace "Ke zaki sauka ne ko sai na saukar da ke" da sauri ta sauka tana kallon sa tace "thank you" yaja motar sa yayi gaba ta karasa bakin gate ɗin ta konkwasa gatekeeper ya buɗe gate ɗin ta gaishe sa ya amsa yace "wa kika ko nema?" tace "wajan Leena na zo" yace "Okay, tho ki shigo" ya karasa buɗe gate ɗin ta shiga tana kallon sa tace "dan Allah ina ne part ɗin su?" yace "wancan na hannun hagun ki shi zaki shiga" tana kallon sa tace "Nagode" ta karasa kofar parlorn tayi sallama Ammi da ta fito daga kitchen ta karaso kofar parlorn tana amsa sallaman ta buɗe tana kallon ta sai kuma ta masa mata tace "shigo mana" ta karasa cikin parlorn tana gaishe ta Ammi ta amsa da fara'a tace "Sai dai ban gane ki ba" tana murmushi tace "Eh baki sanni ba, wajan Leena na zo" Amma tace "Lafiya dai ina? tace "Eh lafiya klau, dama tace zata zo min a weekend ne toh na san ba lalle ta zo ba shine na zo mata yanzu" Ammi da ta kasa gane maganar tace "Muje tana ɗakin ta, dake ba lafiya dake da shi ba" Ammi na gaba Jidda na baya suka shiga Leena dake kwance tace "Laaa Anty Jidda" Jidda na murmushi ta karasa tayi hugging ɗinta tace "Me yake damun ki Leena?" Ammi tace "Ayyah, ai sai kice min ke malamar su ne" Jidda ta kalli Ammi da rashin fahimta Leena tace "A'a fah Ammi ba malaman mu bane" at this point kan Ammi ya kulle ta koma parlorn ta barsu a ciki bayan sun gaisa Leena tace "Ina Nice Uncle da wicked Uncle" Jidda na dariya. Jidda bata wani daɗe ba tace "zata tafi" Leena suka fito parlorn tare kamar zata yi kuka tace "Ammi bani wayan ki Anty jidda tasa min numbern ta" Ammi ta mika mata ta sa sannan tayi dialing ya shiga sai ta kashe, tana kallon Ammi tace "Ammi da zaki yarda ki bamu Leena da munji daɗi" Ammi kawai tayi murmushi, tayi kissing forehead ɗinta tace "zan yi missing ɗinki Leena Allah baki lafiya" tace "Amin ki gaishe min da Mami da Uncle ɗin na tace "wanne kenan?" tace "O'o ban son wannan arrogant ɗin" Jidda sai dariya take zata fita Ammi tace "Leena raka ta mana" Leena zata bi ta haka Ammi tace "bana ce Miki kina sa hijabi idan zaki na fita ba ta koma ɗakin ta ta ɗauko hijab har bakin gate ta raka ta Jiddah tace "ba zaki gaisa da Uncle ɗin ki ba" Leena tana karasa jikin motan suka haɗa ido da Sadeeq ta sauke idon ta kasa tana wasa da bakin hijab ɗinta sai kallon ta yake ko kiftawa be yi ba tace "Ina wuni" ya ɗauke kan sa ta kalli Jidda da ke bayan ta tana kallon su tana dariya ta sake mayar da dubanta kanshi ta murguɗa masa baki karaf a idon Sadeeq daya sake jiyowa da sauri ta juya ta koma baya tana kallon Jiddah ta mata bye bye ta shige gidan su Jidda zata buɗe motar taga Sadeeq na Murmushi ta taɓe baki sai kuma tace "toh Ya Sadeeq ka gane ta ko?" ya ɗaure fuska yace "ita wa ɗin?" daga haka bata sake ce masa komai ba ya taɗa motar suka tafi. Leena na komawa parlor Ammi tace "zo Leena" ta karasa ta zauna gefen Ammi tace"gani Ammi" Ammi tace "Aina kika san wannan kuma?" tace "lokacin da na ɓata ai sune suka ɗauke Ni a gidan su na kwana" Ammi with shock take kallon Leena tace "ban gane ba yaushe ne kika ɓata? Ai na kuma" Ammi ta jera ma Leena duk waɗan nan tambayoyin Leena ta fara "Lokacin da kika yi tafiya kika barni......" Ba abinda Leena ta mance bata faɗa ma Ammi ba, Ammi ta rungume Leena ta fara kuka. Wajajen karfe 3pm Rayyan yayi sallama Leena ta leko da gudu tana masa murmushi yace "Eh Lalle lafiya ta samu" tace "yanzu zamu tafi?" yace "go and wear your hijab" daga haka ta koma ciki sai gashi ta fito, tun da suka fito suka fara tafiya suna taɗi Leena na dariya yana bata labari ya gaji yayi shiru ta cigaba da basa Labari suna dariya tsintan kansu sukayi a street C Leena tace Laaaa ya Rain ga can gidan dana kwana ranan" kallon gidan yayi sai kuma yace "wai haka kike son yawo? Baki gaji bane?" Dariya take yi, kallon motar da tayi a parking a kofar gidan su Jiddah yasa take kallon ciki ganin kamar da mutum suna zuwa daidai wajan kawai taga Sadeeq ne kallon ta yake kuma be fasa ba har suka yi gaba be fasa kallon Rayyan da yake yi ba, Rayyan na kallon ta ya e "ke mu koma gida, ganan short code mubi ni na gaji" suna cikin tafiya yace "Leena" tace "Na'am" yace "Hope zakiyi jumping a school ɗin ba? Ba za kuyi jss3 and Ss3 ba ko?" tace "sai dai kama Ammi na magana wai ita nayi karama" yace "zan mata magana" duk sukayi shiru sai kuma yace "Leena" ta kalle sa tace "baka da Lafiya ne" sai ya girgiza kai ba wanda ya sake magana har suka isa gate din giɗan su Leena ta rike cikin ta tace "Ashh" yana kallon ta yace "what?" tace "ciki na" ta fara yarfe hannu ta ɗurku sa nan kasa ya ɗaga ta, har wani mota ya zo yayi parking a bayan su Amma shi bata motar ya ke ba, wani murɗa wan da cikin ta yayi bata san sanda ta kankame sa gamgam ba,nan yayi noticing blood daya gani a jikin hijab ɗinta yana kokarin gyara mata hijab ɗin still tana manne a jikin sa tana kuka aka buɗe gate ɗin za'a fito nan yayi ido hudu da Mummy da Aminiyar ta duk suka tsaya with shock suna kallon sa.


ayi following acc dina pls, a danna min gifts ko likes, sannan ayi sharhi mutanen arziki

Za’a same ni a duk social media @ Hauwajay writes