AGOLA (Behind the palace walls)
Chapter 12
Thank you so much, my dear readers, for reading my book🫂🫧! I'm grateful to those who've added my novel to their reading list📖💕. May Allah bless you abundantly and provide for your needs, so you can keep enjoying my stories without any distractions (like running out of data 😊)! 🙏📚❤️
Gudun hauka yake kamar wanda ya ke son kashe su, ga shi Leena abinda ta tsana a rayuwar ta kenan hakan yasa ta tsorata matuka, a quarters ɗin su yayi parking kusa da block 1 yace "Get out" Leena jiki na bari ta buɗe kofar motar ta sauka ta karasa gidan da yake kallon inda yayi parking tayi knocking sau biyu sannan taji muryan wani yace "Who is it?" tace "It's Leena" wani saurayi ne ya karaso kofar ya buɗe yana kallon ta sai sannan ya matsa mata gefe yace "Come on through" ita duk tunanin ta may be wani ɗan uwan su Jidda ne ta fara shiga taji mutumin yace "thanks for coming to check on him. He's feeling a bit better now. The doctor even gave him an injection, and he's actually sleeping right now" sai sannan Leena ta ɗaga kai da sauri tana kallon sa sannan tabi cikin parlorn da kallo ganin ba na Jiddah bane za tayi magana taji yace " If you can wait for him, you're welcome to. I need to head back home for something important, so if he wakes up, please call me and I'll come back" ya karasa maganar yana mika mata hannu alamar ta basa wayan ta ya sa mata numbern sa da sauri tana girgiza masa kai tace "I'm so sorry, I think I'm mistaking. This isn't my sister's house. I think it's the next block" bata jira cewar sa ba ta buɗe kofar parlorn ta fita da sauri Mutumin ya tsaya kallon ta da mamaki and her face looks familiar to him, ko da ta fita bata ga motar sadeeq ba next block ta bi duk da taga mota kusa da shi amma still tana hoping shine tayi knocking Fortunately ashe gidan ne, Jidda tazo ta buɗe Leena na shiga ta fashe da kuka Jidda da take kan kallon Videon Leena da aka gama watsa wa a media tana murmushi ganin yadda Leena ke performing well shine taji anyi knocking kuma ta buɗe taga Leena to her surprise tho me ma yasa Leena kuka kuma tana tsaye bakin kofar har Leena ta karasa cikin parlorn sai kuma da sauri ta kulle kofar tabi Leena hankali tashe tace "Meya faru Leena? Kuma lafiya kuma?, ki daina kuka kimin bayani" Leena tana share hawayen ta tace "Amty Jidda, it's uncle sadeeq" Jidda tace "Uncle sadeeq? wani uncle sadeeq ɗin? Me yayi Miki toh?" Jidda na sheshshekan kuka tace "He went to where I was performing my poem and grabbed my hand, pulled me out of the hall, and forced me into his car. I didn't even get to say goodbye to the people who invited me, and the governor even wanted to take a picture with me, but he just dragged me away. He drove so fast, I was scared. I kept apologizing, but he wouldn't listen, just shouting at me. He brought me here and dropped me off" Jidda ta sake baki tana kallon Leena da mamaki Leena na sheshshekan saboda tsorata da tayi ta ci-gaba "I'm still shaken, Anty Jidda, I'm worried about how those people will feel, especially since I didn't even get to thank them or say goodbye" Jidda bata fasa kallon Leena ba sai kuma ta fashe da dariya Leena ta tsaya tana kallon ta sai kuma ta tashi ta wuce ɗakin da ta sauka aranta tana mamakin what was funny here, sai kuma taji haushin Jidda toilet ta wuce tayi Alwala sannan ta fito ta shinfiɗa sallaya, Jidda ita kadai ta ringa dariya a parlorn ta jawo wayan ta ta kira Sadeeq har ya katse be ɗauka ba ta kuma kira ya ɗauka a tsawa ce yace "Why are you calling me? Are you owing me? Stop calling me with this nonsense! It's all your fault for letting her go there alone to perform that so-called poem. Do you want her to be exposed to all those men? Can't you see most of the people there are males? What kind of aunt are you?" Duk maganganun nan be bata damar magana ba, tana ta kunshe dariyan da take ji yana gama magana ya kashe wayar sannan Jiddah ta fashe da dariya ita duk abinda taji a muryan sa tsantsan kishi ne bayan ga haka bata ga komai ba, tashi tayi ta koma ɗakin da Leena take ciki taga Leena ta idar da Sallah amma bata tashi akan dadduma ba ta zauna gefen ta ta kama hannayen ta tace "I'm sorry Leena! Ba wai dariya nake Miki ba, but to be sincere wallahi abinda na gane a cikin wannan lamarin Ya Sadeeq yana matukar kaunar ki Leena" da sauri Leena ta ɗaga kanta tana kallon Jidda, Jidda ta gyaɗa mata kai tace "Dagaske nake Leena, ko ƙaffara bazan yi ba Ya Sadeeq yana so ki, idan har ba haka bane ba yadda zaiyi wannan abun da yayi, na san Ya Sadeeq fiye da kowa bayi shiga harkan da be shafe shi ba, toh ki sani son da yake miki ne yasa ya Miki wannan Abunda yayi" har ta gama magana Jiddah girgiza mata kai take yi tace "Dan Allah ki daina faɗin haka Anty Jidda and I don't want to believe it" Jidda tayi dariya tace "ajuri zuwa rafi" Leena tace "in shaa Allah hakan ma bazai taɓa yiwa ba, he is so wicked" Jiddah tace "Wallahi Leena kin ma Sadeeq mummunar fassara, he is so nice yadda baki tunani kawai dai saboda baku saba bane" Leena ta ɗauke kanta tana kallon wani wajan Jidda ta mike tace "barin barki ki huta daga haka ta fice "Leena ta jawo wayan ta Mutumin da ya shiga da ita cikin hall ɗazu ta tura masa voice note da ya tura mata da videos ɗin da aka ɗauka. Rayyan har wani dishi dishi yake gani da kyar ya samu yayi parking, yana sauka part ɗin Hajiya ya wuce ya same ta tana shan fura da nono ya zauna yace "yanzu Hajiya idan har Daddy da ita Ammin basu hana Leena zuwa Abujan nan ba ke ba zakiyi magana ba?" Hajiya tace "Yo Ni nawa a me? ɗazu ma yaron nan Ayaan yana ta murna wai yaga Yayar sa a Tv ni na ɗauka ma karya ne can kuwa ina cikin kallon labarai naga an saka ta sai turancin nan take yi kamar baturiya" Rayyan yace "Hajiya dan Allah na roke ki, kiyi ma Daddy magana kar ya sake yarda Leena ta cigaba da wannan abun" Hajiya ta kwalo ido tace "A'a wallahi ba ruwana Nikam, so kake mu taru mu tsana yarinya diflashon ya kama ta? Da acikin gidan nan kai kaɗai kake mata magana toh kai ma yanzu ka tsane ta, a tunanin ka ban san abinda yake faruwa bane dan kawai na zuba ido, toh Abunda yake sata farin ciki bazan zama sillar ruguza mata ba" Rayyan ya dafa kansa dake sara masa yayi kusan 2minutes a haka Hajiya ta harare sa sannan ta cigaba da shan furan ta, ya ɗanga jajayen idon sa ya kalli Hajiya da su wanda hakan sai da ya ba ma Hajiya tsoro tace "Lafiya Rayyan?" Ga Mamakin ta hawaye ta gani a idon sa tashi yayi ya fice a parlorn nata tana kiran sa amma ko tsayawa be yi ba, yana shiga parlorn su yaga Mummy da Hajiya Fatima suna magana ko kallon inda Hajiya Fatima take beyi ba balle ya gaishe ta ya wuce ɗakin sa Fatima ta sake baki tana kallon sa har ya shige sai sannan ta mayar da duban ta gun Mummy tace "iyyee, shi kuma yaushe Rayyan ɗin ya zama haka?" Mummy tace "is like akwai Abunda yake damun sa" daga haka ta tashe ta bishi har ɗakin sa to her surprise ta burɗa handle ɗin kofar taji shi a rufe, ta bubbuga tayi magana still Rayyan be amsa ba ta koma ta zauna a parlorn amma hankalin ta ya tashi Fatima ta taɓe tace "kila yaga yadda yau ake ta posting Agolan nan ne shine zai wani shigo kan mutane haka?" Mummy ta girgiza kai tace "bana tunanin haka ne" tayi shiru tace "Nikam anya shegiyar matan nan bata asirce min ɗa ba yaro fah yanzu shekara da shekaru ya gagara zama yadda yake da ko fah walwala bayi da shi, Abunda yafi damu na yanzu shine ko maganar aure baya so a mishi" Fatima tace "Tabbacin da baki ɗauki wannan shawaran raba su ɗin ba da yanzu kila har ya aure ta" Mummy tace "ai wallahi ko bayan raina Rayyan ya auri ƴar nan ban yafe masa ba". Leena da ke video call da Ayaan, Ammi na sa musu baki lokaci zuwa lokaci tace "see you later" daga haka ta kashe wayan, Maganganun Jidda ne yake ta yawo mata a kai ita kaɗai ta fara Magana tace "How?" Sai kuma ta kyabe baki, ɗaukan hijab tayi ta saka sannan ta fito parlor ta tarar da Jiddah dake jiran ta har ta gaji ta fara game tana kallon ta tace "Anty Jidda gani" fita su kayi. Bayan sun gama sayyayan su, bolt yayi dropping ɗinsu a bakin Quarters ɗin, suka sauka su ka fara taka wa zasu karasa block ɗin Jidda wani mota ne ya shige su Leena na bawa Jidda labarin ɗazu ai ta shiga wani gida daidai inda ɗazu akayi parking nan yanzu ma mutumin yayi parking ya sauka ganin su Leena yasa ya tsaya be shiga cikin gidan ba ya jingina da motar sa Leena nata kallon sa ganin kamar ta san fuskar sa sai sannan ta tuna shine mutumin da ɗazu tayi mistake ta shiga gidan da yake ta ɗauke kanta suka cigaba da labari sai da suka iso daff sannan ya karasa inda suke yayi sallama Jiddah kaɗai ta amsa yace "Excuse me Ma'am, idan ba damuwa ina son zanyi magana da sistern ki" Jidda murmushi tace "It's Okayy" Leena ta girgiza mata kai ita ba zata tsaya ba Jidda a hankali ta mata magana me haka Leena zaki sa ya raina mu" Leena ta kamata gam idan Jiddah ta fara tafiya itama sai ta bita idan ta tsaya itama sai ta tsaya, Jiddah tace "ke me haka? Ki tsaya kiji me zai ce Miki" daga haka ta karɓe Ledan hannun Leena tayi gaba da sauri shi kuma ya samu daman shan gaban Leena, Leena ta ɓata fuska kamar zata yi kuka amma hakan bata bari ya nuna a fuskar ta ba yace "Leena right?" Bata ce masa komai ba ji take kamar ta kwashe a guje ta shige gida yace "I'm sorry na tsayar da ke kuma kamar you're not comfortable" to her surprise ya karɓe watan hannun ta ta saya sakeke tana kallon sa yace "Your passcode?" ji tayi kawai ta faɗa sannan tayi realizing ashe faɗa masa tayi, sakake tana kallon sa ya gama sa numbern sa sannan yayi dialing tana ji wayan sa yayi ringing a aljihun sa sai ya kashe sannan ya mika mata wayan yana murmushi yace "Thank you so much" ta karɓa watan tana jin haushin Jidda ta wuce sa, tana shiga Jiddah ta kwashe da dariya tace "Leena me kike yi kamar wata gwaɓuwa? Kinga reaction ɗinki kuwa? Haba zaki sa maza su raina ki wallahi" Leena tayi shiru tana kallon Jidda ita yau gaɓa ɗaya ta rasa me yasa ta zama wani iri ne ko dan Abunda Sadeeq ya mata ne Oho, ita dakyar ta bari aga hawayen ta balle aga gazawan ta tana cikin wannan tunanin taji Muryan Sadeeq na sallama da sauri ta ɗaga kai ta kalli jidda kan kace me ta tashi da gudu ta wuce cikin dakin. Strickly yana kallon Jiddah yace "yaushe zata koma?" tace "Dama kwana uku zata yi, jibi kenan zata koma" yace "tell her ta shirya kayan ta gobe zata koma" Jidda ta wani kalle sa tace "akan me Ya Sadeeq?" yace "saboda gobe zan koma itama dole ta koma gobe" Jiddah tace "toh dan zaka koma gobe sai ya zama na lalle itama goben zata goma? Toh tare ma kuka zo ne?" yace "wannan kuma ku kuka sani, dan na gama magana" Jiddah na masa wani kallo tace "Ni ban gane takuratan nan da kake yi ba, idan ma wani abun ne a ran ka gwara ka faɗa dan wannan ba solution bane" ya watsa mata wani kallo ta ɗauke kanta tana kunshe dariyar da ya taso mata. Sai bayan Magrib Sadeeq ya bar gidan kuma har ya koma be haɗu da Leena ba da gangan taki fitowa sai da taji tafiyar sa sannan ta fito ta ɗauki some snacks ɗin da suka tsaya ɗazu ta haɗa tea tana sha ta kalli wayan ta jin yana ringing taga numbern wannan mutumin ɗazun ne toh ita me zata ce Idan ta ɗauka, stranger ne fah a haka har ya katse kuma tun ɗazu yake addaban ta da kira, Jidda ta shigo da sallama Leena ta amsa ta karasa ta zauna kusa da Leena tana kallon ta tace "Leena meyasa baki fito kun gaisa da Ya Sadeeq ba?" Leena ta turo baki taki cewa komai tace "Har yanzu kina nan a Leenan ki na baya sai dai wancan ba ta da saurin kuka ita ɗin jarumai ce" Leena tayi murmushi bata ce komai ba duk sukayi shiru sai can Jiddarh tace "Leena Uncle ɗinki fa ɗazu da yazo fah yayi booking muku flight Leena ta kalle ta sai kuma ta tsunkuyar da kai kasa tace "I'm sorry Leena haka yayi requesting toh ba zai saurare Ni ba sai sa kawai na basa info" Leena that was speechless kawai wani wajan take kallo Jiddah ta kamo hannaun ta tace "I'm sorry dear, beside yana son ki samu enough time ɗin rubuta WAEC ɗinki ne" Leena tace "Allah sa hakan shi ya fi alkhairi". Leena ta kwanta amma kwata kwata bacci yaki ɗaukan ta, ta jawo wayan ta Whatsapp ta shiga nan taga messages ɗin wannan mutumin har guda 10 kamar tayi skipping sai kuma ta buɗe ta shiga tana ta kallon message ɗin da ya mata kamar haka "Hello Leena, you're my long-time crush! I've been watching your videos on Instagram. My name is Muhammad Faisal Arab, I'm 35 years old, living in Maitama, Plot 12, Street 5. I work with NNPC. I graduated from the University of California, Los Angeles (UCLA) with a degree in Petroleum Engineering. I did my master's degree in Energy Policy from Stanford University. And, I completed my PhD in Renewable Energy from the Indian Institute of Technology (IIT) Delhi.
I want to be honest with you; I'm not here to play games with your heart. Sincerely, I love you so much and I want to marry you. I'd love the opportunity to get to know you better and show you my feelings. If you're willing, could you tell me a little about yourself, where you live, and a bit more about your life?" Tayi ta kallon hoton sa kamar tana son gano wani abu, kawai ganin kiran sa tayi ya shigo tayi picking takai kunnen ta.....