6
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE....
Love And scandal💕
Arewabooks@surayyahms
⏯️6️⃣
Da wani irin ƙarfi zuciyar ayaanah ya buga bisaga kallon reaction na zargi dake cikin kwayar idon mutanen da suke zubo musu ido sai taji ta mugun razana da yanayin inayan jikinta atake ya dau rawa itakanta batasan sadda ta zube kasa tariko kafadun addan nata cikin ruɗewa ba...
"Subhanallah… lafiyá de kuwa adda? Méyé sàmèki haka..Mei yé sàmèki a cikin?”
muryanta maicike da tsoro da dumbin rauni yafito da rawa rawa ayayinda harshen buzancin nasu ya dada bayyana cikin kwababben hausarta ta abazata...
wani irin zafi inayah taji agefen acikinta dake tahowa tun daga wajen cibiyatta kamar ana zungurosa da icce irindai kamar ciwon ulcer ko irin ciwon cikin nan da ba asan asalinsa ba.
ganin idon mutane akansu yafara yawa yasaka inayahn tay ta maza tabi ta shanye dumbin zafin datakeji acikinta ta dagokai tana dan ƙoƙarin yin murmushi saidai ji take kamar bazata iya miƙewa tsaye ba..
kallonta ayanaah ta dingayi ganin wani irin sudaɗɗen hucin zufa yadan fansama asaman fuskar addanta me bayyana halin da take ciki na ciwo da tsananin zafi, tsamm inayah tay ganin irin kallon razana da anayahn take mata cikin dauriya tay saurin dauke idonta kasa ahnkli ta danne komi tadauki jakar tadan miƙe tsaye ahankli ahnkli dakyar tana cewa "hai kekam, à handi mboni baki da dauriya sham anyi babban matsoraciya ganin ayaanahn tanata kallonta har yanxu batace komi ba yasa ta kara mikewa
"karki damu Lafiyata lau… wataƙila yunwa ce ko saboda nagaji...
Abunka da yaranta wani irin nannauyar ajiyan zuciya ayanahn ta saki feeling a bit relieved ahnkli cikin sanyin murya tace tohm shikena,sannu da jin yunwa adda am. toh muje ciki ni zanje madafi na kawo mana abinci yau bake ba..ke aizaki huta yau ko??
a daddafe kuma a ɓoye inayah tay still a tsaye da hannunta ɗaya data zamarshi ta cikin hijabi tadan riƙe gefen cikin nata dake mata ciwon sosai sai murmushi kawai takey ma yar uwarta ayanah badon ciwon cikin ya tsaya mata ba sai danta dada kwantar mata da hankli.
not minding ydda ake satar kallonsu da yanayin gulma ahaka har suka saka kai suka karasa cikin gidan nasu atare. saidai dake yamma ne basu tarar da kowa agidan ba, lkcin duk dai ana kasuwa da alama dai izuwa nan bada wani jimawa kowa zaidawo dan ankusa kirar sallan magriba ynxu..
duk da rashin girma da wayon ayanaah yau sosai take saka ido akan yanayin addarta inayah da taga kamar ya dan canza, suna shiga harabar gidan tanema mata wajen zama akan dakalin kofar daki snn ta amshe jakunansu dukka ta kai daki ta ajeshi, aguje tadawo ta same ta tadan jingina da bango tana dan nishi har yanzu da hijabi ajikinta ta damke cikin nata taciki, da gudu gudu sauri sauri ayanah ta je wajen da ake aje musu kwanon abinci ta dauko musu tuwon dawa da jar miyan kubewa har da ruwan sha tazo ta ajeshi agaban addanta duk hanklinta ya tashi ta dauka kawai tsabar yunwace ke neman ya naƙasa mata addanta inayah..
ita kuwa inayah gashi dai ciwon cikin na mata kamar na yunwa yunwa amma koda ayaananh ta zubo musu abincin sai taji abincin kamar yana daga mata zuciya tana jin ɓacin rai sai tanaji kamar ta washe abincin aranta, saidai dake batason ta dagawa yar uwarta hankli yasaka ta daure taci abincin kadan baifi loma biyu ba snn ta sha ruwa sai tace mata zataje ciki ta cire uniform ta dawo tunda ta taɓa abincin kadan. tafiya ahnkli ahnkli tayi har ta shiga dakin ta cire kayanta ta saka riga da zani jin ciwon cikin gabaki daya yane neman ya hanata tsayuwa da kyau, kawai sai ta nemi waje ta kwanta atake kuwa wani bacci me nauyi ya kwasheta abazata
wanda kusan abun al'ajabi ne kaga inayah tana bacci gabanin magriba sabida bata kaunar abunda zai saka tay lattin sallah a rayuwarta dan in batay sallahnta akan lokaci ba har kuka takeyi.. jim kadan koda su taawure suka dawo gidan gabanin magrin suka tarar da Ayaanah ita daya a haraba ta saka tuwon agabanta ta tsaya cak bata cigaba da ci ba, ta kuma rabza uban tagumi hawaye sun ciko acikin kwayar idanunta sosai abun yadaga musu hankli.
hajya mairo ce ta fara rufeta da tambaya toh ita bata gane komi ba, sai tahau gaya musu iya abunda ya faru, cewa takewa addanta tana jin yunwa amma taqi cin abinci dayawa kuma gashi nan bata baccin yamma sai yau taga tanayi, yadda ayanah ta daga musu hankli babu shiri taawure ta shiga dakin tahau tattaɓa jikin inayah ta na duddubata sai kuma taganta kalau, kaidai dakyar suka wanye maganan aka bari akan cewa ko yunwa ne ya haɗu mata da gajiya. hajy mai tuwo har da cewa kar asaka inayan aikin gida gobe da sassafe abarta tana dan samun isasshen bacci...
Bayan awanni biyu ana daf da ishai snn inayah ta farka lkcin zafin ciwon cikin nata yaƙara matsawa izuwa gefen dama kusa da kasan cikinta. but the pain is bit bearable, duk sai ta farka a ruɗe, ga kuma anxietyn rashin yin sallah akan lokaci kawai saita daure ta waske ta miƙe garau ta yi sallolinta har ta dan saki jiki ta zage ta koyawa ma anayah karatun sukayi basic phytogoras theorem dan kawai hanklinsu taawure ya kwanta sosai.
washe gari basu barta tay aiki mai yawa ba duk dama ta nace saida tay yar shara da wanke wanke snn suka ci abinci nan ma sama sama taci snn suka wuce makaranta
yau suke cike wata daya da sati biyu a tudu, ana saura sati guda kenan ayi ma inayan saukar qur'ani, ga kuma tests na boko shima sun farashi dan anata tsammanin exams dinsu na zuwa ajin gaba yazoshi akan lokaci
sosai yaran suka kara zage damtse wajen karatu, saidai ata fannin inayah kmr kusan kominta ne takejin yana canzawa acikin jikinta, tun data fara ciwon ciki sai taji takasa gane ma jikinta gabaki daya amma dake tanada taurin zuciya sai ta matse komiii tana kaucewa duk wani abunda zai jawota baya a karatu dan batason tay wasting wann dumbin Risks da effort da kuma uban kudaden da mahaifiyasu take zubawa akan batun ilimin datake basu.
kasancewarta ƴar fari, al'adar kunya da dumbin kawaici dake tsakanin uwa da ƴar fari bai ɓari sun shaƙu sosai da taawure ba, saidai fiye da kowa a duniya inayah ce take mugun mugun tausayawa ma mahaifyarta aranta, duba da tsauraran dokoki na al'ada da sukebi a kauyensu, da kuma irin jahilci, taurin kai da tsaurin ra'ayin irinna mahaifin su malam juma.
tasan bakaramin jarumta da soyayya me yawa taawure take musu aranta ba musmn data iya daukar wann babban Risk na rintse ido akan batun al'ada tare da saɓawa ra'ayin mijinta nazama acikin jahilci har tay burus tasakasu a makaranta a ɓoye donta ilimantar dasu addininsu da zamani duk dama abune wanda tasan zai iya ƙarar mata danata rayuwar, zai jawo mata mutuwar aurenta da juma, da kuma tsangwamar mutane duk sanda aka kamasu suna aikatawa.
shiyasa koda wann ciwon ciki ya fara mata taki sam tana nunawa a fili, babban burinta shine taga ta karfafawa taawure gwiwa, sun zamo silar farincikinta ita da yar uwarta ayanah, duniya da lahira. dan taawure jajirtacciyar uwace data musu dumbin sadaukarwan da bakowacce uwa bace zata iyashi.
bayan kwana biyu rayuwarsu ya cigaba ahaka, alamomin ciwo sunata zuwa ma inayah suna tafiya, wani lokaci ta ji sauƙi, wani lokaci zafin cikin nata sai ya dawo, musamman bayan cin abinci ko wani aikin wahala. wata rana koda ayaanah tayi kmr ta ganota sai ta ce mata gajiya ko ulcer ne.
satin sauƙar qur'ani na zagowa aka qaddamar, wanda kusan babban hidima hjy mairo me tuwo tay domin jikarta inayah
nan akayi mata gagarumin murna na zamowa gwarzuwan karatun qur'ani na gabaki daya yankin tudu, anyi abinci hilimi guda akay sadaka aka ciyar da almajirai sosai, kai dai tamkar bikin auren inayah haka hajy mairo ta daukaka abun har anko na kaya saida tay musu shadda me kyau. ayaanah duk tafi murna da cigaban da addanta ta samu na zamowa gwarzuwa kuma mahaddaciyar littafi me tsarki, ranar Taawure bakaramin dadi tare da alfahari da yarta inaya tay ba.
basu taɓa magana cikin nuna soyayya ta uwa da ƴa me tsayi ba ma sai aranar. bayan hidiman ne ciwon cikin ya fara taɓa inayah acikin dare sosai, wani bin da dadderen zata ji ciwon ciki da ba ta taɓa jin irinsa ba.
Cikin nata kamar ana murɗa shi da icce mai kaifi, haka zata kasa bacci tayita juyi tana huci, Ayanah takan ji tsoron duk abunda ke faruwa da yar uwarta inayah da kuma mugun tausayinta amma hakanan inayan take hanata gayawa kowa halin da suke ciki dake kuma suna farkawa da safe sai taganta garau har suje makaranta.
tunda aka ma inayah sauƙa sai ta dan bude karamin islamiyatta na dare, bayan isha sai ta jawo ayaanah zuwa zauren gidan ko gindin bishiya inda take koyawa sauran yaran anguwar wanda iyayensu basuda halin sakasu a makarnta karatun qur'ani dana bokon sama sama ayaanah tana tayata.
hajy mairo mai tuwo ce ta dada daure mata gindi, dan ita macece me kaunar taga yaro karami mai dumbin kwazo tare da son kawo babban cigaba musmn ma ga dumbin al'umma, riƙe ƴayan taawure kusan abun alfahari ne agareta duk dama riketa kawai tay basu haɗa jini ba, duk safiyar Allah sai sun sakama inayah Albarka a rayuwrta.
kwanaki basu karya suna cika wata biyu sharp a tudu aka fara batun exams dinsu ayayinda shaƙuwar ayaanah da inayah yake cigaba da burge kowa dan babu wanda yasan halin ciwo da inayah take ciki kamar ayaanah, duk hanklin taawure yafi ta allaka ne ga shirin komawar su gida can kauye majiya sabida nan da sati uku taji labari cewa mijinta juma zwi dawo, at same time tanata kkri wajen kare sirrin ƴayanta, ko kadan bataso ace ankai gulman yaranta garin majiya musmmn ma da inayah tay kaurin suna kwana biyun nan, duk inda taje zakaji ana kiranta gwarzuwan tudu, sabida aikin koyarwa datakey wa ƴaƴan marasa karfi wanda ya jawo kusan babu wanda baisan sunan inayah a tudu ba.
babu irin addua da fatan alheri da bata samu daga bakin mutane. matsalarta daya ne wann ciwon ciki me tsanani dayake cinyeta ahankli ahankli, an shiga satin jarabawa ne amma bata samun isashen bacci sabida zazzabi, gefen cikinta yafara kumburi yana tauri tauri taciki, wanda ko tsugunawa tay ko mistakely ta taɓa tawajen kumburin cikin bakaramin zafi takeji ba. ahaka kuma ta dinga dauriya har suka fara rubuta jarabawa, hanklin ayaanah bai fara tashi ba saida taga kasala, rauni da rashin ƙarfi ya fara nunawa sosai ajikin addanta. ranar tana kuka tace addah bazan iya ba kawai zan gayawa ummah inyaso akaiki asibiti, amma inaaa, haka inayahn taki barinta tace tabari sugama jarabawa, tay mata alkwari ita dakanta zata faɗa musu komi.
soyayya da kulawa na musmmn ayaanah take nunawa addanta dan duk tafi kowa sanin halin ciwo datake ciki, ayan kwanakin nan daga sun zauna zakaji inayah tana mata nasihohi masu shiga jiki......
kano..9.30pm
wajajen ƙarfe tara na dare Rahma exclusive private Hospital Kano.
karamin asibiti me zaman kansa da akayishi domin ƙrban emergency na masu hannu da shuni dan yawanci turawa ne da indiyawa suke aiki anan asibitin wanda acikin masu kudin ma bakowa ne yake da arzikin kawo jinyarsa anan ba.
security ne kusan guda hudu sunsha uniform agaban wata kofa nan cikin special ward na private consultation dake nan ne kusan ƙebetaccen waje ne na manya.
babu wani hayaniya bare wulgawar wani mutum, koina tass yake da kayan alatu da naurorin kiwon lafiya na zamani kamar ba a nigeria kake ba.
Daga cikin Room 7 iyaka Sautin ƙarar “oxygen machine” da ƙamshin magani shine ya cika ɗakin ayayinda Zainab Arifah take kwance shame shame akan gado an lankaya mata na'urar taya nunfashi da kuma drip a hannunta na hagu.
idanuwanta a lumshe suke tamkar wacce take cikin nisan bacci saidai ahakikanin gaskiya babu abunda yake yawo acikin zcyrta da kwakwalrta face tunanin yadda dan uwanta ibaad zai zamo nata har abada
wanda tun bayan zaneta dayai basu kara samun wani ganawa dashi ba intaje gidan ta gaishe sa zai amsata normal saidai tunda yafara karatun jamia rashin yawan ganinsa da kuma samun sakin fuskansa sosai agareta shine yafi komi daga mata hanki yanzu. tsakaninta da ibaad a shekaru baifi ace 4-5yrs ba, tunda mujaheed dake sa'an ta agidan dai 4yrs 11 month yabata baima cika full year ba kuma tasan akalla dai shekara hudu ne cass tsakanin ibaad da mujaheed. ita bata ga wani dalilin mugun jan aji da miskilincin da ibaad yake mata ba shiyasa ma haryau take ji kamar bazata taba iya kiransa da inkiyar yaya ba.
gani take tana da komi na duniya kama daga kyau, ilimi, gata, da kudi to menene kuma zai saka wani ɗa namiji ja mata aji?
takaici take jin ita tuna kamar ibaad bai wani girmeta cancan ba nd she want noting frm him face for him to be free with her, tanaso taga tana iya masa magana a duk sanda taga dama, intace mai yayi mata abu shima marmaza yay, kamar yadda kowa yake haba haba da ita saidai amma duk ta tuna cewa yataɓa dukanta last time data gwada jan hanklinsa da maganan soyayya sai taji duk takara shiga damuwa sosai
gashi har ilayau tana mutuwar sonsa aranta wani bin inta zauna tana tunanin rasashi sai dai kawai aga numfashinta yana sarkafewa...
yauma kusan abunda ya afku kenan wanda har yajawo akayi rushing inta izuwa emergency, iyayenta duka biyu suna tsaye agefenta idonsu cike da damuwa gashi sam taki tabude idanunta barema har susamu dama su tuhumeta abunda yake damunta dake yanxun tadany wayo tamugun kwarencewa wajen boye feelings inta acikin zuciya..
jim kadan wani babban Likita sanye da farin labcoat da green file a hannunsa yashigo dakin, jikin rank tag dinsa an rubuta Dr. Yusef suleim ajiki, wanda daga ganin yanayin dattakonsa kasan tabbas kwararren likita ne, yana musu sallama kai tsaye ya ƙarasa kusa da gadon zainab din yay yan dube dubensa snn ya bude file din ya fito da dawata takardar sakamakon gwajin numfashi ya dudduba kadan yana rufewa ya juyo kan prof zayyanu da matarsa da suka kafesa da wata iriyar idanu
cikin gyaran murya yace ranka shi dade Alhaji, Hajiya. ina so mu je ofis ɗina mu dan tattauna daku kadan game da lafiyar Zainab Arifah if you dont mind please.
kafin su amsashi saida Suka kalli juna sannan hjy hamidar tacemai "sure" daga nan suka bi shi har izuwa ofishinsa. ofis ne mai girman gaske ga tsafta yasha set na pure white L shape cushions dan tamkr wani palorn haka zaka gansa.
Dr yusef ya zauna yana dan kallonsu har saida suka samu nitsuwa snn ya bude file din da calm voice dinsa yace Alhamdullhi ga sakamakon gwajin da muka mata ya samu fitowa saidai kamar yadda kuka tsara mana ne babu inda bamu duba ajikinta ba cikin gyaran murya yace toh agaskiya dai alhji, bazan boye muku ba Zainab Arifah tana fama ne da provocked asthma wato tasowar ciwon numfashi da bai riga ya haɓaka ba, saidai da akwai wani abu nadaban da nalura cewa shinei ya jawo mata wnn ciwon wanda gwaje gwajen mu ya tabbatar mana da cewa ciwon Damuwa ce.
cikin katsetsa prof yace ciwon damuwa kuma kai kasan me kake cewa kuwa?
da calm voice Likita yace " yes sir, ayi hqri. ciwon Damuwa mai tsanani ne wanda yaketa kokarin ya jawo mata matsalar wahalar fitar da numfashi.”
dede nan Ya dan ja numfashi kafin na ya ci gaba cikin nutsuwa “shawarar da zan bayar shine a samu a kula da bangaren damuwartata cikin gaggawa tun yanxu inba haka ba zai iya rikidewa nan bada jimawa ba za zamo mata matsalar raunin zuciya ko kuma jikin nata ya gaji gaba ɗaya. in har ana son zainab arifah tay tsawon rai sai anjuri kwantar mata da hankali snn aguji komai da zai rinka shigewa cikin tunaninta.
kafin ya dora kalma na gaba gabaki daya idon hajy hamida ya cika da hawaye. prof dai ya yi shiru yanata kallon likita kamar baisan ma meyake cewa ba.
fuskarsa ba awani sake ba yace "toh shikenan likita munji bayananka amma ynxu meyene mafita?
doc yace eh to alhaj mafitar kenan she has to use a terminal inhaler for now, snn Zan rubuta mata wani magani, to be taken once daily ko wani rana sabida ya rage mata tunani. amma fa lallaine ta sha, snn ta zauna a gida na wasu kwanaki tadan huta a kuma tabbatar during dis time bata shiga wata damuwa ba..
hajy hamida dai batace komi ba dan sosai zuciyarta yake tafarfasa taciki dan haka kawai jikinta yake bata kamr duk akan lamarin yaron nan ibaad ne yasa har yarta kwalli daya take kan azabtuwa..
Likita yace inba wata tambaya inaga we can call it a day, i will make an arngemt so dat you can take her home with you within few minutes. prof ya gyada mai kai baice komi ba, dake manyan mutane ne shi likitan ne ya miƙe ya basu waje, yana ficewa kuwa prof ya miƙe tsaye yana kallon sama cikin tashin hankali tareda lumshe ido da budewa yace "ya salam, what is all this? mutanen nan ashe bazasu barni in cigaba arayuwata ba, ƴata kenan mini tall a duniya amma sukeso sai sun kashemin ita hmm hamida did u have any idea why my only doter is behving like this? damuwan uban waye tasaka aranta? kece nake barin miki amanar zainab arifah agida, babu abunda kuka taba cemin kuna buƙatarsa wanda ba baku ba, but why dint even the god damn family doc say anything to me..wallh inhar ƴata ta mutu toh duk duniya sai ansan antaɓoni.
daga jajayen idanunta da sukaji kwalliya tay ta kallesa muryanta a raunace abunka da farin fata har fuskanta yayi jaaa, hawaye na zuba mata tace alhaj ni ina zan san maka meke kumshe acikin ran yarka? bayan kaima kasan zainab tagama raina uban kowa, batajin maganan kowa sai naka, nima i just found out abt her health frm elizabeth daya daga cikin maids dinta dake shirya mata daki, wai each time home doc yazo dubata ashe wai ita takece mishi karya sake yana gaya mana halin datake ciki...our doter is clearly trying to kill herself bcos of one stupid local boy
..wallah ba haka ƴata take ba, Arifa tana da wayo da ilimi, saidan in sihiri aka mata tabi ta dora walakntaccen yaron nwankaan aranta, kaima dai kasan zainab arifa ba matar karamin mutum bace, nide wallah wallahi bazan bada ƴata ma wann yaron ba, tafi karfinshi har abada, saidai in zasu kasheta su kasheta..
tana fadin haka dede nan ta rushe mishi da wani irin kuka..
yay sauri ya dafa kafadarta yana cewa ohh nooo hamida kinjiki ke kuma,toh meye haka?
a mugun harzuke tace alhaji kaima fa kanajin abunda likta yake cewa yarmu zqta iya mutuwa da ciwon damuwa ko zuciyarta ya buga anan gaba, shikenan sai ninasha wahala na haifi zainab dakyar bata taɓa saba maka ba amma sai gashi wai yau zainab tana boye mana halin datake ciki akan yaron nan? this is insane.. toh bagashi ance ma ciwon zuciya zai iya kamata ta mutu ba shikenan yan uwanka sunji dadi sun hadakai zasu kashe mana yarmu kwalli daya wanda da kyar muka sameta wayyo Allah na
shima sosai abun yake kuntata masa aransa amma yayita maza yace 'shushhh hamida calm down kefa ba yarinya bace kuma ban mutu ba tukuna..kidena kukan nan mana ehh. cmon darling its okay ninasan me zanyi i know what to do zainab arifa bazata taɓa mutuwa ba, i know she hides it sabida bata sone inhanata bare ta saɓamin, i knw my doter, abun kawai yafi karfinta ne shiyasa take boyewa..so, dole ne mubi abun ahankli cos is getting pretty serious with her health, ynxu haka rayuwar yarmu ne on the line. get urself together idan munje gida we will make some key decisions to save her life bazata iyayi iya kadai ba.
cikin gyada mai kai ta share hawayenta da wani hadadden farin hanky data fiddashi daga cikin jakarta mai matsanancin tsada ta maida hankun jaka kenan securitynsu yazo ya kirawo su akan angama komi..
dauƙar jakarta tay ta dada gyara zaman mayafinta dayaji original silver stones babbane sosai rare design daga mum ramlat collections, ya bi yarufe mata duma duman jikinta na manyan mata isasshu koinanta acike yake tamm bata da ko ƙashin wuya bare alaman rama, wani shegen abun wuyar gwal ne kwance a wuyartata, gata da farin fata koinanta yayi soll tana sheqi gata doguwa, tsabar iya daukar zakace ko balarabiya ce dan bakaramin cika babban mace tayi ba.
tana gama yafe gyalen tabi bayan mijinta suka samu har an gama shirya musu komi, nan suma sako yarsu zainab arifahn atsakiya suna mata sannu sannu tun anan ta sharesu batace musu uffan ba har suka kama hanyar gida, tun a mota tay bacci dukunkune ajikin mahaifinta dake likita yagaya masa cewa ya mata allurar bacci dan ta samu isasshen hutu sai bai damu ba, suna isowa gida kai tsaye prof ya wuce da ita purple colour princess theme bedroom inta na yar gata ahnkli cikin kulawa ya shimfidata akan makaken italian gadonta me tuff board double spring saida ya fita kafin nan masu aikinta kusan su biyar suka karasa sauran gyara mata jiki da kwanciyar me gabaki daya..
fitowarsa falo tun daga saman stairs ya fara jiyo muryan matarsa tana kan amsa waya dagaji kasan kanwarta ne hajy hajara shettima
duk sanda kaji ta nemi wann matar to da akwai babban matsala itadai sam taki ta amince aranta cewa har yarta zainab arifah zata saka wani soko matsiyacin yaro aranta da sunan soyayya tunma bataje koina a shekaru ba gani take kamar kawai asiri ne akama yarta
jin motsin saukowar mijinta cikin falon yasaka ta karkare wayar tare da cewa hajiya hajjara dan Allah ace ma malamin nan its very urgent, inde sihiri aka ma ƴata kawai agaya min insan nayi kafin su kashe min ita..pls i will wait for ur call
..daga haka ga katse wayar tana sauke ajiyan zuciya me nauyi....
cikin tafiyar takama tareda nitsuwa prof ya karaso cikin palon wanda komi cikinsa golden colour ne, anitse ya nemi waje zauna yanamia dafe kai Hajiya hamida tay sauri ta ƙaraso kusa da shi a hankali ta dora hannunta dayaji jan kumshi akan gadon bayansa tana cewa Alhaji Idan muka ci gaba da barin zainab Arifah ahaka wannan ciwon numfashi nata ba zai taɓa warkewa ba honey pls we have to do sumtin fast. kasan bata saɓa ma umarninka why not ka rabata dashi ko kawai gobe gobe taɓar kasar nan taje tay karatunta gabaki daya akasar waje..
laushin hannunta dake yawo gadon bayansa yasa ya lunshe idonsa tare da kara relaxing yanamai cewa "Na san da hakan hamida amma fa duk wnn matakan naki bazasu saka ta daina tunaninsa ba inhar kuma bawai tunaninsa zamu cire a ranta tabbas abunda muke gudun shine zai faru damu duk inda zamu kaita a duniya hakanan zata cigaba da lalacewa.
Shiru ne ya dan ratsa falon kafin can hjy hamida ta kallesa tace toh me kake ganin zamu iyayi mu ciresa a tunaninta.
hannunta ya kamo yana kallom kwayar idanunta yace leave that part to me..
zainab Arifa yarinyace yanxu tabbas idan muka matsa mata ta rabu da yaron nan toh tabbas zamu rasa ta. so, i am going to have to use a reverse psychology here, mu jawo yaron jikinmu mu bata abunda take so ynxu, nan gaba zamu zo matsayinda inhar nasaka mata doka akan yaron ma bazata iya tsallakewa ba, but for now dolene mu saka rayuwarta da lafiyarta as our main priority.
shafa fuskarsa takey ahankli cikin sauke ajiyan zuciya tace honey, are you suggesting we just let her be with him for now?
amugun kasale yace yes my love..inason zainab ta samu nitsuwa ne kawai tay karatunta me zurfi ta cimma burikanta dana tsara mata tukuna
..just trust me..i will handle her personally inta girma ta mallake hanklin kanta Inhar kinga wani a dangi na ya aure min yata sai inbayan na mutu...
kiss kawai ta dora mai agefen kunci ahnkli da alaman taji dadin furucin nasa ahnkli tace "your wish is my comand my love. amma kuma nasaka hajiya hajara ta duba min lamarin awajen malamai
yace hakan ma yayi..
daga haka ya miƙe, ya ɗauki wayarsa "kije ciki ki shiryamin kanki da kyau zanzo gadon naki na sameki.
wani murmushi tay irin wanda tun dazu baigani tay ba face sai yanzu daya furta mata hakan, cike da kasaita mai haɗe da rangwadi irinna manyan mata ta miƙe tsaye tanamai cewa "okay love..Dont keep ur queen waiting.
gyada kai yay yace sure. tana wucewa ciki ya ciro wata sim a wallet dinsa ya saka awata yar karamar waya snn yay dialing lambar dan uwansa bappa zaidu tun wayar baiy ringing ba ya wani hade rai yafara jan tsaki.
wayar yana fara ringing ya fice waje dashi a kunne after like 30 min ya dawo ya same matarsa har ta gama shiri jikinta sanye da wata arniyar nite gown ta bude tuma tuman fararen cinyoyinta akan gado tana jiransa, yan kwabe garensa wani dira yay kan gadon ya dora mata kiss me zafi snn ya kalli cikin kwayar idonta yace "
"jibi yaron nan ibaad zaizo gidan nan zanyi magana dashi nd i need you to be cool with him too..
wani chak annurin dake fuskarta ya dauke a mugun hargitse tace alhaj bangane ba, akan me zaizo mana gida kuma?
atake ya dan haɗe rai yace "kin manta ne, is All part of my plan hamida. kedai kawai kiyi abunda nace miki..
tun bata kai ga budan baki ba yawani irin wawushota jikinsa yanamai susuta da kisses daga haka har suka fada kan gado...
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
AREWABOOKS
@SURAYYAHMS
WATTAPAD @SURAYYAHMS
WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025