7
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE....
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*
⏯️7️⃣
G.R.A..
5;30~AM
kirar sallahn farko ya dira cikin kunnen ibaad dake kwance lumui akan lallausar madaidaicin italian bed dinsa dayaji off white cotton bedsheet me taushi yarufe daga jikin shi har izuwa kan kyaywan fuskansa da bargo me laushi, da adduar farkawa daga bacci abakinsa yadan bude ido cikin kasala bai motsa ba sai after like 5 scnds bayan ya idda adduar snn ya dire kafarsa akasa da bisimillah ya mika hannu ya kunna wuta, tsaftacciyar farar riga ce ta bacci kuma marar nauyi ajikinsa da dogon wando shima marar nauyi, goran ruwan dake gefen gadonsa ya dauka ya sha kurbi kamar biyu sann ya mayar ya ajiye, adan gaggauce ya mike ya shiga bathrum yay alwala ya dawo ya cire rigarsa snn ya dora goggyar bakin jallabiya me tashin kamilallen qamshin kylian love ajikinsa, snn ya saka karamin farin hula, nan take ya saka bedroom sleepers dinsa yabude kofa ya fito just few steps daga inda room dinsa yake ya tsaya jikin wata hadadden kofa ya hau kwankwansata da dan ƙarfi. ahnkli kuma atakaice yace "maheer is time", jin ba amsa shi ba ya kara buga kofar one more time
after like 4 min yaji muryan maheer din faintly yana cewa 2 mins pls. bai kara cewa komi ba yaja ya tsaya yana jiransa can saigashinan ya fito shima agaggauce sanye da riga da wando duk ruwan alwala nabibyar hannunsa suna hade ido ibaad ya balla mai harara dariya yay as alwys yace ok am sorry nasan i am alwys late toh muje mana liman
ibaad yay gaba kmr baiji shi ba yasaka kai suka fara sauka akan stairs
suna daf sauka yace 'kayi ma bappa flashing din kuwa? cikin gyada kai maheer yace eh nama sa zai samesu a masjid dama kuma jiya yace ince maka muna idarda sallan mujira sa yana da magana da mu,
ibaad baice komi ya gyada kai daga haka suka wuce hargate suka bude cikin nitsuwa suka nufi babban masallacin kofar gidan nasu wanda already har mazan anguwa sunfara taruwa, ganin isowar su yasaka wasu kara gaggautawa dan an saba ibaad ne yake jansu sallah kowani lkci dan
farawarsa karatunsa na medicine shiya saka bai samun time yanxu, daga sallan fajr sai na magrib da ishai kawai yake iya jansu maheer ne yafiye yin azhar da asr dake shi law yake karantawa yana ajinsa na biyu..ibaad yana tada kabbara aka daidaita sahu nan saiga bappa zaidun shima ya shigo adan gaggauce. acikin nitsuwa akay sallahn for gud 5 mins ibaad ya jasu aka kammala komi. wani tsohon malami ne ya danyi jan hankali akan yanayin rayuwa da mutuwa snn aka dan watse akabar masu azkhr, lazimi da karatun qur'ani. ganin bappa zaidu yana zaune yana jan carbi bai tashi ba yasaka suka dan jirashi agefe dansu jirashi snn su masa gaisuwar safiya,
bayan ya idar ne suka karaso kusa dashi suka samesa a inda yake zaunen kowannen su ya rusuna kai cikin ladabi yay gaisuwa cikin darajawa da girmamawa, bayan ya musu few question akan karatunsu ya kallesu duka sigar nasiha yace todai kunji abunda malam ya faɗa, mutuwa bata bar kowa ba, tsoho da yaro..kai ana iya haifar jariri ko minti daya baya karawa a duniya zai koma ga mahaliccinsa bare mu da Allah ya bamu dama muna raye dan mu bauta masa, cikin tuna wayar da sukayi da prof jiya yace" ynxu kune manya, kune zaku hade kan dukan yan uwanku kusani hannunku bazai ruɓe ku yanke ku yar ba. shi rayuwar duniya kamar bakonta ne, duk fushinmu da haushin mu da juna wata rana kwasam babu sallama zakuga mutuwa ya dauke wanin mu na har abada. toh dan haka duk a nitsu inaso kuma ku manyan ku daure ku karfafa zumunci a tsakaninku da yan uwanku snn ban cire kowa aciki ba
kai tsaye ya kalli ibaad yace ka dage da karatunka jiya professor ciroma yace nagaya maka cewa zai baka official call acikin group dinsa na young cardiology doctors sabida yaga practical points inka kana da enuf skills for basic medical first aid. unbehalf of you dai nace masa babu damuwa zaka shiga, toh bansan dai ra'ayinka ba. kan ibaad na kallon kasa ahnkli yace badamuwa bappa duk abunda ka yanke min ai shine daidai i will just wait for his call..cikin gyada kai mai cike da apfahari bappa yace toh masha Allah. toh kuje ciki, ni zan gaisa da makwabta kuje ku fara shirin schl kafin na shigo. kai kuma maheer ka tabbata kabi schl dinsu sultana kaji min meyene matsalarta dayasa bata gane lissafi...aladabce maheer yace toh baba
daga haka bappan ya mike ya barsu kafin nan suka taso suma suka kamo hanya izuwa gida.
tafiyar kurmaye suke sai can suna cikin tafiyar snn maheer ya tsinke silence din dacewa ohh i hate going to dat schl. ibaad dake kallon gabansa yace kabari saida muka bar gabansa snn zaka fada min? maheer yace "hmm kai bazaka gane bane innaje they will waste my time ne so why not kai kaje min, kaga dama sunfi tsoronka, da sauri ibaad yace 'no please kawai kaje din ni yanzu haka ma inada 7:40am practicals a lab kuma nagaya maka na shiga wani reading group i need to be der on time. sai dai shawara inkaje ka fara lura shin matsalar daga itace ko na duka yaran ne dan kasan sumtimes gane karatun maths depends totally in the method of the teacher..maheer yace alryt good idea. inde kuwa daga wajen malamin ne kaga dole ne anema mata lesson teacher agida...bt do u have any idea why baba yake mana magana akan zumunci? atakaice ibaad yace "i dont knw..nd i dont care to know..kawai de nasiha ce me kyau.
maheer yace hmm jikina yana bani akan kawu babba ne, can you believe dat jiya ya kirasa da daddare bayan mun gama kallon ball?
adan miskilance ibaad yace and how is dat an issure..
baki bude maheer ya kallesa yace "a sudden call from prof after 7yrs of snubbing him kace how is dat an issure? hmm duk uban abunda ke faruwa wallah bai taɓa daukar wayarsa ya kira baba ba sai dai inzai bada sako kaga ya kira uncle moh kai tsaye amma jiya kawai wai saigashi ya kira.
.."dan shiru ibaad yay snn yace ohryt maybe ure ryt, akwai dalili, amma kuma dama ai shine baison ayi zumuncin dashi, maybe ya dawo hayyacinsa kenan. cikin kyabe baki maheer yace oho, but i dont think so, naji de ance yarsa ba lafiya. bansan masa ba but anyway sha mu aidama bama fushi dashi..ibaad ya saki umm sai baice komi ba har suka bude gate din gidansun suka shiga ciki daga nan kuma kowa ya wuce dakin sa domin shiryawa..
ibaad yana shiga room dinsa ya ciro wayarsa ya kira mahaifyarsa suka dan gaisa snn ya mike ya gyara koina a dakinsa, he rake care if his room kamar ƴa mace, kominsa sai ya kal kale ya gyara tsaf ya share tass, he is a very very neat guy. within few minutes wajen yay fess kafin nan ya wuce wajen wanka within 20 min shima ya gama shirinsa cikin sky blue fitted long sleeve shirt, da wandonsa baki sai gogaggen labcoat dinsa da system dinsa daya zubasu a jakar baya.
as usual he look mr neat and breath taking dake komi ya saka ajikinsa tana masa kyau dake Allah ya bashi kyau ne me daukar ido da hankali, 6:49am ya nufi kofa yana baza ssnyar qamshin turarensa na original dior souvage mixed with creed aventus na smart collection wanda inya wuceka dole ne zakaji kamar kabishi ka lasheshi..
yana kammala daura agogonsa ya bude kofar room dinsan zaii fito kenan yaci karo da cousin dinsa sultana, she is fair and slender a shekaru ita kusan sa'a ce da inayah, da plate din abinci a hannu ta taho suna haɗe ido jikinta yadan fara rawa, cikin rike nunfashinta a mugun tsoroce tace "ina kwana yaa ibaad, .kallo daya ya mata snn yace "ke lafiya? muryanta na rawa rawa tace uhmmm dama mummy ne tace inkawo maka abincinka daki
saidai tay 2 mun yana kallonta har saida jikinta ya tsananta ɓarin sai baice mata komi ba anitse ya saka hannu ya karbi abincin baiko damu ya bude ba cikin sauri yaga zata juya yace "sultana..da sauri tace na'am. daga ido yay ya kalleta yace next time aka baki abinci ki kawomin just use d landline nd calll me zanzo na dauka dakaina..da sauri sauri tace toh yaa
..tana juya kusan cin karo da maheer tay duk basu san ma yaushe ya iso ba a mugun tsorace ta kalleshi shima tace "sorry yaa, gud morning, da kallo maheer yabita yace morning, uban mikekyi anan .
cikin nunfashi tace ai mummy ne tace na kawowa yaa ibaad breakfast dinsa nayau anan..
cikin katseta yace 'what?..nikuma ina nawa abincin..
tace ya na kan dinning ai tacema ince maka ka sauko kasa yanzun nn zamuci abincu.. yace its alryt, jeki ina zuwa..tana barin wajen ya karaso wajen da ibaad yake tsaye da plate ahnnunsa looking confuse yace dude did you tell her dat u want to eat alone??
cikin kyabe baki ibaad yace 'nop, but its fine..
maybe she have a reason
.. maheer yace wani reason? bayan baba ya sha hanata saka maka abincinka daban, we are all suppose to eat on the table..kawai kazo muje
a dan shashance ibaad yace "maheer, let it go, i am not even hungry sauri nake zan fita. cikin share sa maheer yace "kajika kuma amma ai zaka taɓa abincin koda kadan ne, ban plate din bari inga meye ne ma aka dafa mana, kafin ibaad ya hankara maheer har ya saka hannu ya kwace plate din yana budewa yabi ya fidda idonsa waje in shock ganin walakntcen dumame ne na miyan busashen kubewa daya kwana a fridge ya fara sakewa bama agidansun akai ba, wanda ta aika ne jiya aka bata daga gidan matar me gadinsu maman ummi
..atake maheer ya dago kai cikin yatsina fuska yace "what d hell is this ibaad??
ibaad yay rolling idanunsa a mugun miskile yace "tuwo, dumame." maheer yace oh fuck it..am not eating this, this shit is smelling awful..anya ma an dumasa da kyau kuwa
amma ai dazu naji ana soya irish ko ce musu kay bakaci??..ibaad ya masa wani irin kallo da alaman baison yama amsa wann maganan ahnkli cikin nemn wakansa nitsuwa yace "guy pls i need to take my leave, inada practicals karnay latti, kawai bani abincina ka kara gaba, zan kai na aje inna dawo inci. da wani irin ƙarfi maheer yace noo you cant eat dis
..baridai naje na nuna ma mummyn hala kuskure akayi kode abincin me gadin ne sultana ta dauko ta kawo maka" ibaada yace "ohh toh inme gadi zaici ainima zan iya ci kenan, just give me."cikin zare ido maheer yace "no, i wont,this isnt ur food". yana gama rufe baki sai ganan bappa zaidu ya iskesu tareda binsu da kallo yace what is going on here..da sauri ibaad yace babu komi bappa, da sauri still maheer yace baaba abincin me gadi fa aka kawo mai as breafst shine nace ko mummy tay mistake ne ta aiko nan
da mamaki bappa zaidun yace "abincin me gadi kuma? let me see it,
maheer baiyi kasa agwiwa ba ya mika masa yana satar kallon ibaad dake harararsa da gefen ido, bude abincin bappa zaidu wanda atake yaji ransa ya mugun baci ya dgo ya kallesu duka yace waye aka aiko da abincin nan?nd why did ur mother sent the food here? dama ana kawo maka abinci..kai ibaad banace maka kowa yanacin abinci a table ba"
ibaad ya sauke kai kasa ahankli yace "kafada, a mugun dake bappa zaidu yace "so, what is this nonsense then? ahnkli maheer yace baa dama sultana tace mummy ne ta aikota ta kawo masa nd she had been.. ransa a bace cikin katseshi. yace enuf, just go nd call sultana here my friend.. da sauri maheer yace yess, snn ya sauka kasa bappa ya kalli ibaad yace kai kuma ka wuce dinning table yanxun nan bana son naji wani magana, cikin ladabi ibaad ya amsa da toh snn ya sauka kasa. bappa zaidu baijira ba kawai yabiyosa kasan da plate din abincin a hannunsa, kusan lokci guda suka isa dinning da ibaad suna kkrin zama saiga ammi babban ta fito jikinta sanye da wata doguwar riga A shape ta atamfa a hujajan ta doso falon sultana nabin bayanta adan tsorace
wanu dan uban hade rai tay tana cewa uban waye yake neman sultana, toh nina aiketa gani nan sai agayamin lefi na. ina shi ibaad din dayake neman ta in dukanta ma zaiyi gani nan saiya fara dani..
tagama furta hakan kenan zata sharo kwana caraf suka hade ido da bappa zaidu wani rasss taji gabanta ya tsinke ganin irin kallon dayake mata gabaki daya sai taji ta mugun tsorata da tarin kwarjinin dake cikin kwayar idanunsa sosai...
atake ta sauya murya kmr ba itace ke zuba masifa ba amakirce tace sallam alaikum, ibaad dakansa ke kallon kasa ne kawai ya amsa bappa zaidu baiko amsa taba, ta taho da rawar jiki yaa zaidu ashe har kafito, jikinta na rawa rawa ta dau serving spoon tafara bude warmers tana murmushi" abbansu, ai bansan kai ka aika a kira sultana ba toh baridai na xuba maka abinci..
wani irin shareta yay fuskarsa a mugun dake cikin hakimcewa
yace ke sultana zo nan..
kafafun sultana harna hardewa tazo gabansa ta dan rusuna tace gani nan baaa.. yace daga yau sai yau..karda ki kara kaiwa yayanki ibaad abinci a daki saidai in shine yace akai masa can bare ma na soke dokar cin abinci a daki, once is family time for breakfast lunch or dinner dolene kowannenku ya fito aci abinci atare
duk randa na sake jin an aikeki kin kai ma wani abinci during family time saina miki shegen duka..
hawaye na zubo mata tace toh baba kay hakuri dama mummy ne tace saina kai masa,..baice mata komi ba yace kindai ji abinda nace miki ko??? tace eh baba. tashi ki zauna kici abinci karki lattin schll. jikinta a sanyaye ta miƙe tazauna kusa da yaa maheer dinta tana share hawayenta sabida tana mugun tsoron fushin babanta..
basu kara cewa komi a table din ba suka fara cin abinci kowa ya share ammi babba.
..wani irin borin kunya ne yabi ya rufe kwayar idanunta taja wani irin tsaki zata bar wajen a fusace...wayar ibaad ne yay kara ya dan duba yace
uhmm bappa, ana jira na wajen practicals its urgent.
bappa zaidu yace its okay
..amma kaci abincin kadan. yana furta hakan ya juya ta kalle ammi babban kamar bada ita yake magana ba yace "ke raihanatu saiki gaggauta kiyi packaging masa breakfast dinsa a wani abu dazai wuce dashi school dan suna da important practicals da safen nan.
juyowa tay ta kallesa jin datay kamar zuciyarta zai tarwatse dan zafi, kasa motsi tay har saida shima ya juyo ya mata wani irin kallon sama da kasa snn ta kama kanta ta wuce kitchen ta dauko karamin food flask, abincin gaban ibaad din ta saka hannu zata dauke awalaknce ta juye masa aciki, bayabo ba fallasa cikin katsetsa bappa zaidu yace "wai meye haka ne kam da Allah. karkisa masa wnn da alredy ya fara ci yayo sanyi, just get him fresh ones daga warmers.
ranta a mugun dagule ta jawo warmer din ta bude tana deban irish da fried egg din rabi yana zuba akan table dama kuma gashi iya su familynta kawai ta dafa musu breakfast yau banda ibaad a budget dinta shisa ma ta duma masa tuwonsa daban..wanda ya ragen zataci shi ta zuba ma ibaad din dan kadan a cooler tana ajewa kuwa bappa zaidu yaja tsaki ya dauki sauran irish din dakansa ya juye masa duka saida coolern yacika tam snn ya mika wa ibaad baiko kula kumburin data keyi ba, cikin gyaran muryan yace ibaad maza tashi ka amshi dayan key dina na camry a wajen adamu driver kaje makarntar.
ibaad yamiƙe tsaye jikinsa a sanyaye yace nagode bappa..toh sai na dawo.. bappa ya gyada masa kai..ya juya ya kalli maheer sai yaga yana masa murmushi, jakar sa ya saba abaya zai dau food flask din yafice
ammi babba ta wani irin bangajeshi ta wuce kamr zata haura sama can kuma sai taji bappa zaidun nacewa yawwa ibaad namanta ma nagaya maka ka shirya zuwa jibi da yamma kaje can nasarawa extension ka same kawunka yana nemanka agidansa..just you.
wani irin faduwa gabansa yay amma bai nuna a fili ba yace toh in sha Allah zanje, saina dawodaga haka ya fice...
da wani irin gingimammen feeling na rawan jiki me cike da son jin gulma ammi babba tay maza ta dawo kan dinning table din tafara bambamin karya murya kasa kasa tana cewa abbansu to ni me zanci kabi ka dauka abincin duka ka bawa danka ya tafi dashi..
da kamar bazai kulata ba can ya mata kallo daya fuskarsa ba asake ba yace ga can dumamenki ai sai kici.
cikin yatsuna fuska tace Allah ya kiyaye Duk salon anuna min bani da gata ne zaa ce min ga dumame..ai dake masu gata ne agidan har kira na musmnn suke samu daga kawu babba..
a dake ya kalleta yace
"duk dai babu ruwanki da wann. ashe dama dan kinuna masa baida gata kenan kika aika masa dumame not after i specifically told you banason ana rabamin kan yara na...
wani irin bori ta tayar toh ni faɗa zakamin agaban yara its seems like nobody respect me in dis house... cikin katseta yace dont talk abt respect
bayan idan na fadi abu jira kawai kike na bada baya ki canza shi. kina hauka ne zaki raba mana abinci shikadai ki aika masa wani walaknccen dumame da ko karen gidan nan bazai iyaci ba..how will u feel in danki ko yarki ake ma haka?
ransa a mugun bace yace maheer how long has this been going on karka ka sake kamin karya
adan tsorace maheer yace baba wallah ban taɓa lura ba saiyau saidan in sultana dake ita ake aikawa
tun kan ya juya ya kalle sultanan ta fashe da kuka "baba infa baka nan ne suke abunsu da mai aiki ni wallah bantaba kaima yaa ibaad abincinshi daban a daki ba saidai atambaye sadika me mana aiki ai ita tasani.
a mugun hatsle ammi tace ke wallah zanci ubanki
kikamin sharri agaban babanki, ashe baki da kunya sultana?
rai ahade bappa zaidu yace raihanatu dont provock me, snn karki ma yarinyata tsawa agabana dan ta fadi gaskiya
cikin kukkuni me zafi tace ni fa yaya biyu kawai na haifa, kaga kuwa dan na manta dan wata acikin budget ina dole ne insaka masa nasa daban daga abunda ya sawwaka, yaron nan fa yana da uwarsa acan toh yakoma gabanta ya zauna mana inyaso sai tadafamai duniya a bashi yanaci nide bazan kashe kaina akansa ba, in de dan dumamen ne danayi kkri na taimaka nabashi ya baka haushi to Allah ya huche zuciyarka.. ai kasan abunda kakeyi sarai, haka kawai dai bazaka fifita dan wata banziya akaina ba.
tana fadin hakan ta mike da sauri ta wuce sama ranta a mugun bace
bappa zaidu yabita da kallo..cikin lumshe ido da budewa yace Allah ya kyauta. the tablw was quite for a moment sai can snn yy karamin nasiha ma yayansa akan karda su biye ma uwarsu suki zumunci, saida duk suka nuna sun fahimceshi snn ya sallamesu suka wuce makaranta..
wani irin makokon baqin ciki da haushi mai tsanani ne ya turnuke ammi babba kasama zama tay a dakin sai safa da marwa take tsakanin corridor da corridor tanaji tsanar ibaad din na kara ninkuwa aranta bana kadan babu kalar abunda bata raya aranta ba, can sai ta wuce daki da sauri ta dau wayarta kusan bugu ma uku sai aka dauka
atake take ta sauya murya izuwa na makirce tana maganan tana dan jan girma "wa alaikis salam safeera, Allah sarki na katse miki baccin safenki ko?
dagata dayan bangaren anty safeera tace bakomi ammi babba ynxun nan na dawo daga raka mijina zaije aiki
"Allah sarki..toh ya gidan naku..ya mijinki ya yaranku.. anty safeera tace duk lafya muke dama ammi karamace kawai bataji dadin jikinta ba..
yi tay kmr bataji hakan ba cikin sharewa tace "uhum kinajin labarin antynki kuwa? ina nufin hajy hamida shettima ..anty safeera tace a'a, amma dai naji ance yarta zainab arifah bataji dadin jikinta ba so bana tsammanin ma zatazo wnn wkends anjima dai nake so na kirata inji ya jikin.
tace ohhh ayyah hala ko shine dalilin dayasa kawu babba yace suna neman ibaad agidan, did she say sumtin abt him to them? ko har sun amince zasu bari ta kulla soyayyan ne dashi, hmm amma da abun baiyi ba..
adan mamakance anty safeera tace ahh toh gaskiya nide bansani ba amma kinsan abu me wuya ne dama su hanata abunda takeso..
wani irin zafin tsana da kishi me tsanani ammi babba taji na tsagawa aranta, tay shiruuu, san can sann taja nunfashi adan dakile tace hmm toh Allah ya kyauta..nidai nake xaune da yaron nan nine kuma nasan halinsa, inda ace zaku nemeni shawara ta danace muku karda a sake abar zainab arifah tay wannan mummunn zabin makanta..wallah yaron nan baida mutunci kigadai mugun bugun daya ma zainaba ranar gashi da girman kai sam baida kunya ko kadan
anty safeerah tay shiruu batace komi ba sai can tace yanxu dai bani da tacewa ammi babba kisan dai kawu babba ne keda ikon yanke duk wani hukuci akan yarsa amma in har anty hamuda ta neme shawarata i will try nd talk to them
cikin washe baki ammi babba tace toh ai shikenan bakomi, pls inkin kira kinji jikinta saiki gaya min snn ki gaida min hajy kice ina mata fatan alheri.
anty safeerah tace toh ammi mungode da gaisuwa duk dai abunda ake ciki zan taɓaki
...murmushi tay tace toh kardai ki manta nagode safeerah agaida yara insun dawo.
daga haka suka katse wayar..anty safeera bata kawo komi aranta ba duk dama tasan da cewa abun ammi babban harda zafim kishi da tsanar datakewa ammi karama aciki, deep in her heart tasan a nitsuwa da hankali da kyau da komi ibaad yafi karfin ya aure zainab arifah nesa ba kusa ba. infact banda gata da arzikin da ubanta yake dashi da ko kusa da ibaad akace tazo bazatazo ba. saidai bataga lefin ammi babba datake zafin kishi da ammi karama ba, ammi karama is almost perfect ga kyau, ga kamala, nitsuwa, ga kuma ilimi, itama kanta safeeran bata kaunar kalmar kishiya bare ƴayanta. kai kaf duniyan nan ma babu wani abunda ta tsanaji kamar batun kishiya. ji take ranar da uncle moh ya ce zai mata kishiya toh ranar zata iya kashe kanta kota kona gidan gabaki daya.
fannin su inayah kuwa yauma suna idar da Alwala a bore-hole din makaranta tadan miƙo tattausan hannunta tariko kyakkwan fuskar ayanah tanamai sakin sassanya kuma nakasshiyar mrmushi mecike da tsumayi wanda yake saurin fallasa wann dumbin kaunar datake yima yar uwantan aranta.
ahnkli tahau gyara mata zaman dark green hijabinta dakema ayanahn tana da yololon ɓakin suman gaban goshin mai hade irin wani kwantaccen shatin saje mai daukar hankali wanda yake yawan nunawa a fili sosai, idanuwanta masu cike da nuna kaunar da take mata ahnkli take fmr cusa suman ciki tana cewa "Ayaana am, Idan wata rana kikaji sanyin ruwa ko iska me sanyi tana busawa, har kuma tashafi gashin kanki, ki sani ina nan kusa da ke."koda ace ranar bana numfashi soyayyata zataci gaba da zagaye ki, "koda ace bani da murya,
addu’ata zata rika zuwa gareki tamkr yadda iska yake riskan ramin hancinki ayanzu, inaso koda bana nan a duniya kicigaba da kulamin dakanki, ina sonki sosai anayo am kinji ko??.
..ayaanah data zuba mata ido ta dan kyalyale da dariyar yaranta "addana ina sonki nima sosai ai bazamu taɓa rabuwa ba har abadan abada ko mutuwa zamuyi tare zamu mutu..bakiga duk kika tashi a bacci cikin dare kina ciwo nima sai natashi sai naji zuciya na yanamin ciwo ba?yo duk inaa kikaje aduniyan nan saina biki shiyasa ma Allah yayimu mu biyunmu awajen ummanko ko??
ahnkli inayah tay mata dariya me sanyi ta gyada kai sai batace komi ba..
..kusan duk rana sukan yi ire iren wnn maganan shirmen atsakaninsu amma dukansu basu taɓa daukarsa akomi ba inayah ne kawai takeji ajikinta da xuciyarta kamar dai wani abu nadaban xai faru da ita.
washe gari shine ranar da zasuyi papernsu na karshe sassafe tun kan akira sallahn fajr inayah tafarka jin jikinta ya dau zafi sai kuma taji cikinta na kugi kusan aguje tawuce bayi tayi zawo sosai sai snn taji dan dama dama
saidai tunda ta fito wani dan uban kasala ya sake rufeta, ko yar dauriyan nan yau takasa yi sabida tunda tay zawon kasalan yabi ya dameta ta zama bata jin karfi ajikinta ko kadan. yau ko abincin safen ma bata ji sha'awar ci ba, haka hanklin taawure yatashi sai kawai ta ɗeba mata fura da nono a gora akan idan tay jarabawar sai ta zauna tasha tunda jarabawar karshe ne anatashinsu da wuri..
tace daga antashesu yau suje kasuwa su zauna a shagon hajy mairo har saita dawo daga saida nono ne zasuje chemist abawa inayan maganin zawon daya jawo mata wann kasalan yau da safe
ahaka suka rabu kowa ya fita sana'arsa amma hanklinsu nakan inayar, dake gabaki daya yau ciwon yaki sam ya ɓoye kansa, kusan a daddafe ma tay jarabawa dama kuma shine mata na karshe, tagama firamare kenan, ba a wani bada wani kyauta a schl din amma ita sosai ta samu kyautar jinjina daga wasu malamai musmmn ma na lissafi, wasu suka bata kudi naira dubu biyar, wasu suka bata littafai da jakan baya, wani dan nysc har na tunanin biya mata kudin zuwa private scndry schl a cikin garin kano sabida aganinsa bai dace dumbin ilimin inayahn ya tafi a banza acikin kauye ba.
duk da ciwo na cinta aciki haka ta matse tay musu godiya, ta kuma nemi yafiyar kowa aka rabu cikin lumana da ita, ayanah na rike da ita duk inda zataje sabida wnn dan uban kasala da zafin datakeji ajikinta har yanxu.
ahnkli ahnkli suke tafiya manne da juna, but is like every few mins jikin inayahn ke dada sacewa karshe ayaanah ta nema musu wani gindin bishiya ahanya suka zauna dan ta samu hutu tay catching breath inta, suna zama ayaanah ta ciro goran nonon ta girgiza ta bude mata hankli a matukar tashe tace "tashi kisha wann adda koda zakiji karfi..tana faɗa tana kai mata baki.. idanunta duk yay jazir da damuwa aciki.
kurɓi biyu zuwa uku inayah tay sai taji gabaki daya taste din nonon yana ɓata mata rai sosai dan haka kawai ciwon yake sawa taji ta washi cin abinci ko shan wani abu gashi kuma matsanancin yunwa takeji. magiya ayaanah ta dingayi mata amma taqi sam takara kurɓa, can sai ga wani dan yaro almajiri yayi futu futu rigarsa duk ta yi dukunkun baida takalmi ga mtsnancin yunwa ya galabaitasa tsabar layi agigice ya zauna akasa snn ya riƙe cikinsa yana nishi daga ganinsa kasan yunwa yakeji bana kadan ba. ganin wann almajirin ne yasaka inayah ta mance da nata yunwa ta kuma dawowa cikin hayyacinta babu shiri cikin dauriya ta miƙe tsaye ta isa gareshi da gorar furan ta miƙa masa tace mai yasha kusan a gigice yaron ya karba muryansa da jikinsa na rawa rawa yana mata godiya yakai baki ƙwad ƙwad yafara gwankwadar lafiyayyen nonon like his life depend on it har saida ya shanye tass, ya daga ido ya kalli inaya yace "Allah ya saka miki da gidan Aljannah
ayaanah na kkrin yin mgn ta tsareta da ido tana murmushi ahnkli tace ameen, yaron ya tafi,suna wuceshi tace ma ayanah suje can kasuwan kawai sujira taawure inyaso awajen hjy mairo zata nemi wani abunda zataci. hakan yasaka ayanah jin dama dama aranta sabida tasan yunwa na damun addanta sosai amma kuma sau taga bata iyacin abinci
suka rike juna suna tafiya ahnkli ahnkli har suka kai cikin kasuwa, as usual babban shagon hajy mairo me tuwon acike yake tammm da customers ana shige da fice ga qamshin abinci kala kala yana tashi takoina, ta kofar baya suka shiga suka sameta a inda take yawan zama, dake kamar kaka take awajensu suna gama gaisheta maza tasaka aka kawo musu lafiyayyen abinci shinkafa da miya da ganye akai wanda sun fara ci kenan still inayah ta dau rabin nata ta fita waje taje ta bawa wani mai daƙo da yunwa ya mugun galabaitashi ya daure cikinsa da tsumma ya jingina akan wheel barron sa awaje har ya kasa motsi.
anan ma koda ayanah tamata magana akan meyasa ita bataci abincin ba tabashi, saidai tay murmushi tace mata sudin sunfita bukata ne shiyasa take basu. bare ma awajenta ai ciyar da wanda bai dashi yana ɗaya daga cikin manyan ayyuka mafi soyuwa awajen Allah ta gwammaci hakan akan komi.
bayan sun tattauna kaɗan akan hadisai da kissoshi tareda ayanah wani irin bacci ne ya dauke inayan batare da taci wani abincin kirki acikinta ba duk da uban yunwa dake damunta aranta, ayaanah kuwa tuni tamiƙe tawuce wajen hjy mairo mai tuwo ta zauna tanata kallon yadda ake shige da fice tareda hada- hadan abinci dakema sunfi shaƙuwa sosai tafiyeson balbale hjya me tuwo da surutai na yaranta....
sallah ne kawai ya taɗa inayah wajen yin tsarki hakanan ta amayo da duk wani abu data saka acikinta batare da kowa yasani ba, gashi dakyar take tsugunawa kasa tsabar ciwo da zafin da cikinta yake mata, koda ta fito sallahn ma yau addafe tayishi can da yamma liss sai ga taawure ta dawo shagon hajya mairo ta debesu suka wuce chemist direct akay ma inaya gwaje gwaje akace musu wai typhoid ne, haka aka siya ma inayan wasu magani tana sha kuwa tadan samu relieve har kamar ta warware, a kwana na ukun da yamma suka shirya tsaf sukay sallama da hajiya mairo me tuwo da sauran mutanenta, taawure ta debi fiye da rabin tarun kudin cinikinta ta zuba a asusun hajya mai tuwo akan idan hutu yakare daga sun dawo za'a nemawa inayah makrntar sekandari tadan fara kafin mijin aure ya fito amata aure. bayan hakan ya kammalu wajajen 4:30pm na yamma suka kama hanyar komawa gidansu acan kauyen majiya da zimman sai hutu yakare snn zasu dawo.
ba su da isa garin su ba sai wajajen karfe 6:30pm dake akafa suka taƙa, kafin sukai gidan nasu gabaki daya inayah ta zama wani iri tafiyar da suka kwasa sosai ya motsa mata da ciwon cikinta,still maganin dasuka amsa a can chemist taawure ta kara bata hardai ta samu tay sallolinta yauma ko abincin arzkii bataci ba ta kama bacci, can cikin dare kwasam ta farka da amai, da zazzabi me tsanani kumburi da taurin cikin nata kuwa sai karuwa dayayi, duk sanda tay numfashi ko tari zafin datakeji acikinta ya tsananta sosai da sosai.
kafin kace wani abu inayah tafara ficewa ahayyacinta tun abu na wasa wasa har maganin chemist ya ƙare amma basuga alaman sauƙi ba gashi sunriga sunbar tudu bare ma su je asibiti.
ganin basuda mafita da safe taawure tafito tasame su awaje akan tabarma, ayaanah tana fifita ma inayah dake kwance riƙe da cikinta cikin azaban ciwo da murkususu wanda ruwama ynxu da kyar take iya shansa sai nishi kawai take da juye juye.
cikin ran taawure cike da fargaban yuwar dawowar mijinta any moment saidai duba da jikin inayah yasa kawai ta runtse ido ta saɓi mayafinta da karfin zuciya tana fitowa tadube yaranta dukansu abun tausayi muryanta kasa kasa ahnkli tace shannu innari dakyar inayan ta dan dago ta kalleta
..zuciyarta sosai yay rauni sosai dataga inaya bata ko iya amsa magana saidai ta dan dago idanu, cikin jan ajiyan zuciya tace "ayaana ki kula da yar uwarki ni zan gudu gudu inje tudu na sake karbo maganin ciwon innari wajen likitan nan na tudu tunda jikintan yaƙi yin sauki..
ayanah ta share guntun hawayenta ahnkli tace "toh saikin dawo ummah addana batako iya magana kiyi sauri jikin nata yana kara zafi.
ko gama amsata taawure batay ba sukaji kakkausar sallama akansu wanda saida yasaka zuciyar taàwure ya tsinke sabida jiyo muryan mijinta juma datayi, ayanaah kuwa tuni taji hanjin cikinta yana kaɗawa sabida balain tsoronsa data keji, inayahr ce kadai bata bude idanunta ba dan banda nishi bata iyayin komi..
fuskarsa ba a sake ba ya shigo cikin gidan ganinsu cirko cirko a tsakar gida ga innari akwance akasa akan tabarama kamar ruwa ya kwasota yasaka ya mugun hade ransa kamar ma ɓe taba murmushi a duniyar nan ba..
taàwure ta kalleshi da karyayyen zuciya ganin ya zuba musu idanu mecike da tuhuma sai tay sauri ta taho gabansa domin ta amshi jakar dake hannunsa wanda tunkan ta karaso ya tsime tare da daka mata tsawa yanamai cewa "Ke da Allah. Dakata min awajen. ya dada haɗerai yanamai kare musu kallo"wai meke faruwa ne na ganku haka a tsakar gida cirko cirko? kuma ina kike nufin zakije da mayafi ajikin ki batare da izini na ba. kafin ta bude baki cikin masifa yace "ikon Allah wato abunda ake yawan gayamin akanki gaskiyane, dake da yaranki duka baku da tarbiya daga nasaka kafa nabar garin nan dandalin bushasharku kawai kuke buɗewa kina yawo kamar wacce bata da aure su kuma kmr wanda basuda uba, duk kinbi kina zubar min da mutuncina a garin nan ana gulma na akanki keda ƴaƴanki, toh wallh taawure nafi karfinki, karyanku yakare tunda na dawo gidana kuma da cikinki na dawo, zan nuna muku cewa ni juma, tsayyayen namiji nake agidana kowa cikinku sai ya gane kurensa agidan nan.. mtss yaja tsaki daga fadin hakan ya kama hanya yawuce turakarsa fuuuu ransa a mugun zafafe.
kallon bayansa taawure ta dingayi cikin rasa nacewa
jikinta a matukar sanyaye ta dawo jikin yaranta da suke zaune akan tabarma itama tazauna tay wani irin tagumi shiru ne ya ratsa wajen banda nishi nishin inayah babu abunda ke wulgawa, can cikin tunani taawure ta miƙa hannu tajawo sauran ruwan maganin zazzabi data jikashi acikin kwarya ganyen rai ɗore ne aciki tana kokarin bawa inayar abaki sai kuma taji jikin inayar yay mugun zafi harma fiye da kima.
hankali atashe ta tallabota ayayinda taji jikin inayar yafara mild convulsing kusan koinanta yana rawan ɗari, zanin inayar atake yadan subuce gefen cikinta na dama inda ya kumburo sai yay kamr wani babban kurji ne acikin nata.
a mugun tsorace taawure ta kai hannu kan kumburi zata taɓa taji meyene tana tabawa kawai inayah tay wani irin gigitacen ihuuu saida dukan su suka rude sukaja baya suna salati me ƙarfi
rawanin juma a hannu ya fito daga turakarsa a mugun razane shima kusan arude yana cewa wacce yar kafurar ce take mana ihu acikin gidan nan waye..waye waye me ihun nan...yan iska kawai marasa tarbiya da imani mutum ya dawo gidansa bazai huta ba kenan wata shegiyar yarinyace tay ihun nan inci ubanta.
da gudu ayanaah taje ta kara rungumar inayah tareda fashewa da kuka me tsananin rauni wanda kukan ayaanahn ne ya dan katseshi,taawure tay sauri tarufe kumburin cikin inayan da zani dan karma juman ya gani yayi musu wani fassara na daban dan talura kamar ransa a mugun baçe ya dawo daga boda.
#surayyahms
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
AREWABOOKS
*@SURAYYAHMS*
WATTAPAD @SURAYYAHMS
WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025