8
by @surayyahms
ABUNDA KE ƁOYE....
Love And scandal💕
Arewabooks@surayyahms
⏯️8️⃣
juma yana gyara tsayuwarsa yace...
"Dabbobi ne agidan ina tambayarku kuna min shiru?
araunace taawure tace megida dama jikin innari ne babu dadi tunda muka dawo daga tudu yau kwanan mu uku kenan tana zazzabi..
wani irin yatsina fuska yayi cikin katseta da zafin kai yace "toh sai kuma me? akanta aka fara zazzabi ne?yo akan dan wnn ciwon zazzabin shine har zata daka min irin wann ihun jahilcin acikin gidana yo uban waye yasaka mata ciwon inba iskanci da sakacinku ba, nide wallah kar a sake min ihu agidana. ku karata tacan da abun kunyar ku ai da ɗa namiji kika haifa min da bazai zamo rago har haka ba. sai a zauna ana ihu akan zazzabi? Ko waata nyiɗi, ɗum yoɓa wuro.”
yana gama maganar sa still yaja musu tsaki a mugun zafafe ya kuma wucewa ciki lokcin kuka inayah da anayahn sukeyi rungume da junansu abun tausayi...
ayaanah bata taɓa ganin addanta cikin wann yanayin raunin ba sai gabaki daya zuciyanta itama ya fara mata ciwo amma take kkrin daurewa sosai danso take ta koya ma kanta jarumta..
tun bayan faruwar wnn hatsaniyar taawure ta kasa xama dan ko kaɗan bata iya ganin yaranta acikin rauni suna kuka gani take dolenta kawai ta neman musu mafita, acike da jarumta ta miƙe tabi bayan juma cikin turakarsa ta samu har ya gama warware jakansa yaciro kayansa mararsa nauyi daya saba sakawa inzai dan fita majilisansu na dattawa a kofar sarkin buzaye inda kowani gida ake kawo kwanon abinci aci atare. sanin cewa tunda aka haifo ayaanah aka dena cin abincinsa a majalisa ke dada bata mai rai, sabida al'adar kauyen ne inhar duk gidanka mata ne toh andena cin kwaryan gidanka kenan har sai ka haifi namiji ko da guda daya ne. ya dawo daga boda da tsananin fushin sanin kayan abincinsa bai kare ba, gashi yana so ya fita yabar musu gidan yadansha iska acikin mazaje, shikansa inya tuna cewa duk gidansa mata ne sai yaji wani makokon matsanancin bakin ciki ya ƙara rufesa.
taawure tana shigowa tun bata masa magana ba ya bita da wani irin kazamin kallo na tsana, bata damu tadan rusuna agabansa tafara rokonsa koda zai bata izini taje ta nemo ma yarsu innarin maganin zazzabi, cikin magiya tace masa na asibiti yafi ci dan tsabar ta damu batasan ma ta furta masa haka shaf ta mance cewa ya haramta musu ambatar asibiti agidan sa....
shiru yay yana jinta face har saida ta ambace asibiti yaji bazai iya daurewa ba,wani irin harquka yayi Ya sare sanda ya buge bango tare da yin tsalle yace Weehoo…taawure ni kina gayen kalmar asibiti Kangon kafuraye?? Taáwure, anin k’ombon ma yanka....
muryanta na rawa rawa jin ya soma cewa wuyanta yakai na yanka a mugun tsorace" a'a mai gida lafiya nake niman wa innari.. da karfin rauni tace Jikko on wondi sokka, ɗum no feere magani ganya walaa ɗum waɗa. nufinta Jikin yarta ya yi zafi sosai, wannan ciwo ne mai tsanani maganin jeji ba zai iya warkar da shi ba.
wani irin ja idanunsa yay ya ɗada murza sandansa tsabar bacin rai jikinshi na rawa bakinsa har na tara kumfa ya nunata da shi yana cizza labba yace “ Wallahi, miɗo yoɓi maaɓe, on no wala ndiyan...”
da mamakin jin yace zai ci ubanta ta budi baki kenan zata amsashi ya rufeta da wata harzukakn duka
yanayi taawure ta saka ihu tana neman tsira amma yabi ya shaƙeta kamr zai kasheta ayayinda yaransun suke jin abunda ke faruwa duk jikinsu ya dau rawa anayah tafara kuka me ƙara.
wani irin kukan tsoro sukeyi suka rungume junansu suna kiran umma umma umma
duk da acikin zafin ciwo inayah take amma wani irin ɓari jikinta ykey tamkar mazari yanayinta me cike da zafin rai da zuciya sai cixgewa take tana Allah Allah ta iya koda miƙewa ne tsaye koda da ja da gindi ne jitake za taje takarbe uwarta, saidai ganin ciwon ya hanata koda motsawa na da can yasa tayi ihu me karfi lkcin numfashin ta sama yayi kamr zai dauke jin irin dukan da ubansu yakey wa taawure aciki kamar ba mutum ya samu ba, kuka suke suna kirar taawuren gashi basuda makwabta sune karshen gari daga dabbobinsu sai gonayen su
kamar daga sama ayanah tasake kirjinta data damqeshi tamiƙe tsaye arikice kuma a zuciye kusan idanunwanta a rufe tana kiran sunan ummanta da wani irin zafin zuciya me radadi abunda bata taɓayi arayuwarta ba sabida kowa yasan ayaana da rauni.
yauda dan uban gudu ta tsallake inayahn dake kwance tana nishi ba acikin hayyacinta ba takai zuwa kofar batajira ba kawai ta fanjama cikin dakin baban nasu da dama bata taɓa shiga ciki ba
tana shiga ta faɗo kan jikin taawure ta riƙeta dam dam tana wani irin razanannen kuka tana cewa...
"Baba no ɗuka umma maa! No waɗa umma maa. babaaa.. babaaaa no ɗuka umma..
sanadiyar kanannede taawuren da ayaanah tayi tana kukan cikin firgici yasaka juma ya hakura da dukan ransa a matuƙar bace ya dau rawaninsa ya dora bisa kansa jikin shi harna kyarma muryansa tamkar tsawa ya dube su duka yace falmata Wann ma kadan kikakga gani tunda rainin ki har yakai in saka doka agidan nan ki taka. dama can ana gaya min cewa na sake miki dayawa bansani ba saiyau dakike neman ki nuna min kuskure ne toh wallh baki isa ba. in kuma kika kara ambatar wani asibitina kafuraye agidana saina hallakaki daga ke har yayan naki dama ba amfanin komi kuke min ba banda kuci kuyi kashi. kai bari ma ingaya miki,' daga yau sai yau idan kika kara ficewa agidan nan abakin aurenki..shashasha mutuniyar banza mutuniyar wofi
daga haka ya saka kai ya fice baiko lura da inayah dake kwance awajen cikin tsananin murkususun ciwo kukan zuci da gushewr hankali ba.
ranar taawure tay kuka ranar bana kadan ba har sai bayan da abun ya lafa musu snn ta daure ta aike aayanaah jeji ta dan debo musu wasu ganyen ta aje kurkusa duk baqin cikin dake ranta haka tazauna tayita hadin maganin gargajiya ma inayah tana bata tanasha tana amai har dai zafin jikin ya sauƙa.
kwana daya bayan haka yasakance Yaune bappa zaidu sukay da ibaad akan zai kai ziyara da yammaci izuwa gidan su zainab Arifah, abun ya mugun tsaya ma ammi babba a wuyanta anma shi sam abun be wani ɗarashi ba, shide aransa yasan umarnin bappa zaidu kawai yake bi .
yau tun bayan sallahn asubahi ibaad ya dawo dakinsa yana ta rera karatun qur'ani for almost 50 mins ya dauko tundaga kan suratul ma'ida izuwa suratul taubah cikin hadda, bayan yagama ne ya dau lokaci sosai yanaima mahaifinsa adduar samun rahma a kabarinsa,snn yay ma mahaifyarsa adduar samun lafya da miji nagari, yayima da shikansa kafin yay ma sauran ahalinsa gabaki daya bai rage kowa ba, baitashi a wajen dayay karatun ba har saida zuciyarsa tay masa sanyi cos there’s always smthing heartbreakingly disciplined about him, shi namiji me dauke da wata inner wounds aransa na kalubalen maraicin uba ata young age that made him sharper nd not bitter nd hot tempered kamar yadda wasu suke fassarashi
bayan yagama karatun ne ya dan samu dama ya runtsa idonsa just for few min kafin ya tashi ya kimtsa dakinsa sosai, snn yayaje shi club na medical first aids and emergency practicals na Dr prof ciroma babban abokin bappa zaidu, inda anan kadai ne ake koyarda wasu additional medical skills. is not a schll routine, kawai de babban club ne na yaran masu hannu da shushi da ake budewa a killace dan kawai su kwarance sufi kowa ilmin sanin makamin aiki tun basuyi nisa a karatu ba.
kusan ma ibaad ne kaɗai awajen ba asan asalin miye matsayin ubansa ba andai san daga familyn almansur ne, daga yaran powerful govrs ne saina ministers sai na sarakuna da manyan yan kasuwa, duka duka basufi 30 a killatacen medical club dinsun ba amma dake ibaad yana amfanine da family name dinsu na al- mansur ne kusan koina suka shiga saikaga anata respa masa dan duk ansan tashen sunan gidansu na masu dumbin dukiya ne da power sosai..
tunda ya kwanta bacci bai farka ba sai can around 8:30am, yana lullube acikin bargo bai bude idanunshi ba tukuna, karamin motsin bude kofar da maheer yay yadada tadashi a bacci yanaji maheer din yashigo yana cewa"Dude kati na ya kare pls can i use ur phone? baima jira amsar ba ya dau wayar ibaad din akan table yakira uncle moh ya zauna akan chair nan suka cigaba da magana akan wata yar project da uncle moh din ya samu ta hannun wani dan siyasa toh dama shi babban dansa abokin maheer ne, ana ce masa Abdul gaffar tafida shine ma yake dan kkrin taimaka ma uncle moh din tawasu bangarori.
surutunsu yasaka ibaad ya miƙe ya nufi bathrum, white towel ya dauka ya Dora a kugunsa sannan ya tsaya agaban sink yy brush, ruwa yahada mai dan uban dumi a tsaftaccen bathtube dinsa da kyar sabida kasala yadan zuba shower gel nanda nan bayin ya cika dawani irin mugun kamshi ya shiga cikin ruwan ya lumshe ido yanadan tunani, yakai kusan 10min ahaka maheer yai knocking kofar rike da wayarshi dake ta haske murya chan kasa kasa yace bad your phone is ringing..dan yatsine fuska yayi yana dada karasa rufe tsaraicinsa da kumfa cikin kasalalliyar murya yace"who is calling?" kallon screen din maheer yayi ganin "m" da emojin heart ajiki,a hnkli yace "Ammi ne..ibaad yace ohhh ok talk to her first dan Allah duk hirar da zakuyi katabbata kace ce mata my schedule are soo tight, yanzu zan fito, daga can kofa maheer yadany kwafa ya hararesa yana ficewa ya saki ajiyan zuciya me dan nauyi dan he knows his mum is kindof desperate to see him today yasan inyaje kuma basa rabuwa da wuri toh gashi ya riga yay alkwarin zuwa gidansu zainab arifah ma bappa yaudarar mum dinsan ne kawai banson yi.
wayar na daf da tsinkewa maheer ya dauka yasaka a handsfree "salam alaikum gud morning Ammi. kin tashi lafya? Daga Jin yankewar sautin muryan tan yasan mamkin Jin muryansa taji dan tasan batare suke kawana da ibaad din ba, ahnkli cikin nitsuwa"..tace wasalam ikon Allah maheer Babban Mutum, ka tashi lpya?inashi rayyan din yau naga baiko neme ni ba.
dan murmushi yay yace ammi muna tare ne dashi karatu ne yadan masa yawa amma anjima da dare namiki alkawari insha Allh zamu taho gidan tare mu dubaki..
Tace toh bakomi Allah ya kaimu lkcin Allah ya maka albarka maheer ,yace Ameen ammi. daf zai katse wayar tace nd wen he comes around kace yanemi ni..tell him I have a surprise for him tonite he shudnt miss it.
Maheer yanadan murmushi yace copy dat ma..,baijira jin mezata karacewa ya dan katse wayar...yazo daf kofar bayin yace Kaikuma Saikayi sauri ka fito ka saukeni agidansu abdul gaffar cos I hate to be late.
Ibaad dake kkrin dauraye kansa da ruwan dumi baiko amsa ba saida ya gama gyara kansa da toilet dinsan tsaf snn ya fito...
A gurguje ya kimtsa kansa cikon kananan kaya suka fito haraban mansion din bappa zaidun kusan atare kai tsaye Suke baza takunsu a hnkli Mai tafe da tsantsar nitsuwa da kasaita irinna zaratan maza masu ilimi da aji Inka gansu tare gwanin sha'awa dake ma yanayin dirin jikin su kusan iri daya ne, banbaci baifi kadan ba, dake shi ibaad yariga yafara zuwa gym yana training sai yadan fi maheer din fasalin kyaun dirin jiki harda Dan tsayi shikuma maheer yanada wani irin tsiririn fuska ne mai mugun dauke hankli dirin nashi jikin Bai Kai na ibaad ba dake shima yana buga kwallo sosai..
key din babban baqar mercedez din bappa zaidu maheer ya miƙawa ibaad, ministrs qtrs suka wuce kai tsaye anguwan su abdlgaffar wanda yakasance ma maheer din tamkar babban abokinsa tun suna secndry suna tare. ibaad yana sauke sa agaban gate dinsu ya juya abunsa. saida har ya isa club dinsu snn yaga text dinsa akan ya riga yacewa ammi karama akan zasuje gidanta su dubata anjima da dare"..karamin scoff ibaad ya saki, kafin nan ya jefa wayar a silent ya tsunduma
aikin practicals dinsa dakema
introductory lessons ake ta koya musu akan field din su, dake shi likitan zuciya ne burinsa anfi jefasa wajen trial robot patients masu matsalar ciwon numfashi da basic first aid help da ake bawa masu ciwon zuciya. dake baida aboki awajen he had been more nd more focused than his seniors dake wajen shine yanxu yafara karatun nasa., hakan yasaka mutane dayawa suka fara jansa ajiki, wasu suyi challenging dinsa wasu kuma su dada zurfafa masa kaifin tunani.
dake yau baida lecture da wuri sosai ya jima anan, break da sallah ne kadai yake fitar dashi, arnd 2:40pm lkcin kusan kowa ya gaji aka farawucewa gida amma shibai gama ba sai da karfe uku da rabi yay snn yay hamdala ya tattara reports dinsa yasakasu ajaka kafin ya wuce masallaci...
yana idar da sallahn ya buɗe jakarsa ya ciro wayarsa da tun safe ya sakata a DND,missd calls takwas hudu aciki duk na bappa zaidu ne saida da sakonni guda biyu, dialing lambar bappan yafarayi dayaji lambar akashe sai ya duba sakonin ya karanta daya kudi ne me yawa da bappa ya turo masa, dayan kuma sakon mamansa ne sai yay mata reply, snn ya miƙe ya nufo waje ya bude motar dayazo dashi ya shiga, ahnkli ya dinga tuki har ya kai kansa gaban wata mayyar "velour palor" irin vintage boutique din nan ne dayake da wajen sayan kaya ,da fitting room da babbn refreshment palor da kuma luxury changing rooms. yana gaba parking benz dunsa ya dau iya wallet dinsa da wayarsa ajakarsa snn ya shiga wajen kai tsaye, bai kula kowa ba ya mule cikin sashen maza yafara duba kayan da zai saka dan shi mutum ne me mugun son tsafta ji yake kmr bazai iya zuwa gidan mutane da kayan da suka wuni ajikinsa ba.
sashen kananan kaya ya nufa cos he wants to look low tone and high standard, ko kadan kuwa bai kawo batun zainab arifah aransa ba kawai de yay tunanin cewa dole ne akwai babban dalilin da kawu babba nasu yake son ganin sa agidansa. within few minutes ya zaro wata maroon polo shirt irin fitted hugo boss din nan, da dark chinos, sai simple maroon colour designer loafers, yabi ya hada da agogon fata ɓaka me silver face na raymond weil,
da dior souvage perfume, kai tsaye ya wuce fitting. snn ya fito yaje ya bada katin sa ya biya kudin duk abunda ya suka mqsa acikin wanda ya dauka, daga nan refreshing lounge ya shiga sashen maza yasakar ma kansa shower yacire zufar dake jikinsa tass yana fitowa ya shafe jikinsa da disposable lotion yay fess, snn ya wuce private changin room, ya saka clean new boxers da sabbin kayan daya dauka kafin kace wani abu ya fito rass kamar bashi ba. he look plain nd simple but with high standard vibes irin nasu na masu shi...
duka duka minti kusan
ar'abin shirin ya dauke sa, kayansa daya cire ya zuba a jaka snn jefa a seat din baya
ya kunna karatun qur'ani all the way yanayi yana duba adress din da bappa zaidu ya basa har Allah yasa ya gane anguwar..
A bangaren zainab Arifah kuwa tun bayau ba dama babu wani mahalukin daya isa ya tasheta a barci,komi ma jiranta yake komin muhimmancin sa.
At half past 8am ta farka shima da kyar sabida yau tariga tasaka aranta bazata leƙo koda kofa dan taga menene yake gudana agidan ba sanin cewa duka iyayentan zasu iya tutsiyeta da maganan ciwon tan nan. tana cikin wnn tunanin iphone inta da yasha tsadadden purple phone case yay ringing as usual tay banza dashi tanakan jira ya yanke kafin ta sauka taga ko zata iyayin alwala,ganin ba'a dena kirar ba yasa ta dan leƙa saman screen din tana dubawa kuwa taga sunan Dad dinta ne akai, kasallen mikewa zaune tayi kafin ta dauki wayar takara a kunnenta dan batay tsammanin shi bane duk ta dauka mahaifiyarta ce take kirarta akan maganan ciwon nan, cike da shagwaba tace good morning daddy, Daga ta dayan bangaren prof yay murmushi yace "morning princess, kin tashi lafya, how are u feeling now? Tayi rau da ido tare da ƙarewa dakintan kallo snn tace "not bad" yace inde bakijin dadin jikinki ki gayamin..cikin katsesa tace noo dad pls krmuyi wnn maganan i am fine. yace uhum haka kike yawan cemin even if ure not, but anyway, abar maganan tunda baki so..cikin turo baki tace 'And don't ask me to come down and eat cos i am not hungry yet
..cikin nuna mata soyayya da gata yay murmushi ya ce no problem princess bamai takura miki i jst want to let u know dat i have invited ur brother ibaad over for dinner, this evening, lkcin ai zaki sauko ki kulani ko?
cikin kwalo ido waje ta miƙe tsaye buttt ta tsaya jikinta har na rawa rawa tace "what??dady kace ibaad zaizo gidan nan?
karamin murmushi yay yace "yess" and is just for ur sake..
wani irin ihun murna na bazata tamasa a kunne kamr ba ita ba tafara tsalle ohhh my god i love u i love love u super daddy..i love this surprise .
..saida har ya barta ta gama murnan ta snn ya dan tsime yace 'okay listen, kema kinsan There will be rules my princess.
rungume pillonta tay ta koma ta zauna akan gado tace i am all ears.
muryan sa cikeda yaudarraen salo yace zainab, kinsan babu wani abu a duniya dazai kawo miki farinciki wanda bazan iya nemo miki shi a duniyan ba, so pls i want u to behave arnd him my doter.. whos doter did i tell u you are???
cikin sauke ajyan zuciya tace " i am her fathers doter, born of strength and love, i am the storm i dont break, i always rise...dariya me sanyi yay yace now thats my girl...i have to make this work for ur sake, amma saikin min alkwarin zaki nitsu mubi komi ahankali. i need u to focus on ur studies more, be who you are meant to be. kowani namiji kikeso zaiso ace ya aureki ne idan kika zama wata abu a duniyan nan. snn ki dinga tuna cewa kece kadai magajiyar babanki komi sai kinbi ahankli. idan ina raye kome kikeso a duniyanan zaki sameshi, nothing shud break u kinji ko?
da wani irin tsananin farinciki aranta tace naji dadyna..i love u soo much. kuma tunda har kamin haka toh duk abunda kakeso nayi zanyi, nd i will make sure i make our dream come true.
dada zurman da ita yay akan zai tsaya mata akan batun ibaad ita kuwa ta dinga masa alkwari ma cewa zata maida hankalinta akan karatu dosai
bayan sun gama wayatr wani miƙa tayi game da lumshe idanuwanta ahankli jin kanta a wani matsayi nadaban dan tasan lallai ita din na daban ce, a doughter of a multi billonaire and probably a queen with a brigh future,to meye ynzu ta rasa a duniya tunda babanta ya fara kkrin jawo mata ibaad cikin rayuwarta?
Yawan Girman kai da jiji dakai da shaidan yay mata wahayinsa ayau ta kuma amsa na daban ne, Dan kuwa ji take kamar ma ta rigada ta auri ibaad din ta gama tunda har babanta ya fara shiga lamarin.
Kyakkwar Juyi tayi tanamai sake pillolin dasuke kanta izuwa kasa, Ayayin da kamshin hot coffe dake aje neatly akan tray tare da nutella agefen gadonta ya wani mamayeta wanda bata ma lura da shi ba sai yanxu..
Ahankli ta Lumshe idanunta snn ta budesu ta kalli kan tray din tare da sakin dan tsiririn tsaki jin Wani qwiyuwar daukar coffe cup din takeji har kaman zata dauki wayarta ta kira downstairs domin a turo mata maid tazo ta miƙa mata coffe din sai ta tuna da cewa ashe itace jiya ta basu umarnin karsu kara tsayawa akanta intana barci.
Tsaki mai kauri taja snn ta jefar da wayar akan gado adan dole tadaure ta dauki coffe din tasha kadan,snn ta aje shi ta dauki nutellan ta tafara sha،dan duk duniya babu wani abunda tafi kauna a rayuwarta sama da taga tana kwalliya, bacci, shan chokolate na karshen su kuma mafi muhimmancin shine zuwa "shopping".dan har gani take kamar bazata taba rayuwa in bataje shopinh ba a sati kusan sau goma ma zata iya fita shoping bai kuma dameta ba.
A kasaitacciyar yanayi mai daukar lokaci ta fada wajen wanka inda tay umarni ma maid inta elizabeth akan ta cikka bath tube da kumfa sann aka kawata wajen wankan da wasu irin flowing red flowers da kuma red candles da hot coffe.
daga yau har kullum haka ta umarce Elizabeth datana shirya mata wajen wankankart dan babu shakka tasan damuwa rta yadau hanyar gushewa dan arayuwa bata taɓa sanin wani abu waishi rashi ba, bare kuma kalmar qaddara,toh inma akwai qaddarar to nata qaddarar kenan na zamowa matar ibaad a future.
Bayan ta kammala wanka ta fito aka fara shiryata kanta nitse,ta saka white mcqueen maxi gown mai makahon tsada
Saukowar nata ma daban ne dan haka kowani masu aiki kusan shida ne suka matso kusa domin serving mata abunda zata karya dashi.
Ita kadanta ta zauna akan doguwar royal dinning table dinsu 45 mtrs long maicin royal chairs guda sha biyu, maids din dake a tsaye akanta tana zama suka fara aikin jejjera mata dishes kala kusan sunfi goma da uwarta hajya hamida tasa aka dafa mata da safen nan musammn dominta
Saida ta kammala karewa abincin kallo kafin da kyar ta samu ta tattaba abincin kan plate daya tanaci kmr wanda kwai ya fashe mata aciki can dai tamiƙe tsaye tareda ce musu sutattara sauran su zubar ta koshi.
daga inda take ta kwallawa mum dinta kira batajira amsarta ba tace "mum nikam na tafi shoping da driver, tana fadi hakan kuwa tayi ficewarta.
ba ita da dawowa ba sai wajajen karfe sha biyu na rana, jakar sayayya yakai takwas da masu aiki suka biyota dashi ciki, tabi ta daga wa kowa hnkli tun karfe daya aka fara mata spa har izuwa 2:30 kafin tay wanka aka zauna mata kwalliya wajen zaben kayan da zata sakama saida har taji elizabeth tafara cewa ga baƙon nata ya iso yana gate snn ta iya zaɓa.
wajajen 5pm na yamma ibaad sharp yay horn agaban gate dinsun dat took almost forever to open sabida scanning dinsa da masu kula da cctv cameras sukeyi kafin can dai suka budemai gate din ya shigo.
security ne aharabar gidan here and dere amma dake anriga an gaya musu wani yaro zaizo sai basu wani damu su tambayesa ba, calmy ibaad ya kashe mota ya sauko daga shi sai wayarsa
wani security yaxo suka gaisa daga nan baice masa uffan ya masa jagora suka shiga cikin gida...#surayyahms
share
***