ABUNDA KE 'BOYE...

10

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE....

Love And scandal💕

Arewabooks@surayyahms

⏯️1️⃣0️⃣

Wajajen karfe takwas na dare saura suka shararo kwana cikin anguwar rijiyar zaki, dakema tsohon famly house din nasu na al-mansur babban gida ne me tashen daraja sai yasaka layinsu ya shiga can can ciki inda kwata kwata babu yawan hayaniyar jama'a kebetaccen layi ne me tsafta gidan nasu yake kusan shine babban gida na farko,

Ahnkli maheer yake tukosu yana jan tsaki sabida buga musu bayan mota da wani dan adaidaita yayi shide ibaad baice komi ba har suka iso kofar gidan nasu yay horn a bakin gate mai gadinsu yazo agurguje ya buɗe snn ya shigo da su ciki batare da bata lokaci ba.

Babban compound ne sosai dake dauke da gungimemen baqin gate da bishiyoyin kwaiba da kwakwa da umbrella guda hur hudu masu daukar hankali a kowani kusurwa, kai kana ganin tsakar gidan kasan wadata da kwanciyar hankli ta zauna kusan dai babu abunda suka rasa na arziki sede a idanun prof da matarsa ne kawai suke kallonsu tamkar almajirai..

makeken tsakar gidan nasu na dauke da manyan sassa har uku masu design iri daya ko wani side akwai coridors da matakala mai dan tsayi tsakanin sa da wani sashen, sashin farko wanda shi zaka faracin karo dashi bayan shigowar ka cikin gidan shine yaksance babban morden bungalow yana da girma sosai ananne main family house falo yake me girma mei cin setin kujeru hudu da katon dinning area, sai wani dan karamin falona privacy asama, anty safeera da uncle moh da ƴayansu biyu sune suke zama ata nan fannin don sashin ya fi kowanne girma sosai, yana da extra rooms nd big luxury falo dake tsakanin sashen da sashe, sai yar medium self contain da aka tanadashi wa hajy mairo mai tuwo intazo musu hutu.

dayan Sashen da baida girma sosai su ibaad suka wuce kai tsaye dan anan ne mahfiyrsa take zama wanda na musamn bappa zaidu yasa aka sake gyara yanayin building dintan tun alokacin da mahaifin ibaad ya rasu badon komi ba saidan dan ammi karama taraini yaranta acikin nitsuwa da kwancyr hankali, hatta ibaad da baiya zama da ita sai wkends yana da nashi bed room din da closet dinsa inda ke lode da kayan sawarsa kala kala masu tsada da kyau. In ka shiga Bangaren nasa zaka san indeed shi dan gatane awajen mahaifiyarsan inyazo gida yakan xabi xama ananne sabida anan ne yafi sakewa.

karasowa sukayi cikin karamin parlournta iya muryoyinsu kawai tajiyo tamiqe zaune kadan jin motsinsu a kusa tay murmushi cikin furta kushigo daga ciki

Gyara zamanta tayi akan dark red colour daddumarta tana dada gyara zamn wata white cotton lafaya lace ajin farko data sayeshi from mum ramlat's clothing collection,tayi masa dinkin riga da zani irin maiduguri style innan dayagaji da haduwa wanda duk dama dare ne amma Wani dan uban qamshin turaren wutane na dutches da sandal wood original already yagama cikke sashenta da azaban qamshinsa traditional incence burners dake ci da wuta agefe da gefen kowani kusurwa na famar kara masa kaimi..

sanye take da farin gilashi à idonta na karatu, Gabanta kuma nadauke da hadadden royal flask sabo daga uwargida kitchen utensils collections shima badai dauke ido da rike zafi ba, tashakeshi tam da herbal tea, sai tazuba Kadan adan karamin transparent kofi na shayi tanadan zuƙa ahankli,a shekaru dai kwata kwata ammi karama bazata wuce 40yrs ba dan kuwa da danyar shekarunta mahaifin ibaad din ya aurota tun tana yar 18yrs a duniya, bayan aurenne ta haifa ibaad while she was just 23 Sai kuma tay ta samun ɓari Allah bai kara bata haihuwa sai da ibaad yacika 7yrs a duniya tana daf kuwa da haifar yar autarta safiya mijintan kuma ya rasu..

kwance tashe gashi wai har ibaad dinta yadoshi 18yrs kuma har yafara karatun dream course dinsa shida babansa wato medicine, wanda yasaka take dada mika dumbin godiyar ta ma Allah da kuma bappa zaidu dayayi tsayin daka akan rayuwarta dana y'ay'anta wajen ganin sun cika burikansu na rayuwa tun mutuwr ubansu har gobe.

da fara'a ta tarbe su maheer ne yafara neman waje akasar capert ata gefen hagunta ya xauna yana murmushi me sanyi shikuma ibaad din ya karaso tagaban ta tare da zama dab da ita kusan atare suka hau gaisheta tanamai saka musu albarka cikin fara'a da dattako.

hirar karatu suka fara da maheer kadan dake sun saba da juna sosai akabar ibaad din yana kalle kalle, can cikin katsesu yace Ammi yana ganki ke kadai anan, safiya fa? badai taje tazuba kananan idanunta tana kallon indian series ba. dan murmushi ammi karama ta yi tace.."a'a..tasan ai zaka zo, so i am sure tana can dakinta tana fmr duba karatu...tun kan ya fara mita tay saurin maida hanklinta kan maheer tana cewa babban mutum tashi ka zauna kan kujera toh bare naje na kawo muku abin taɓawa, kan maheer a kasa yana dan murmushi ya amsa da toh dan bakaramin kaunar tsaftaccen qamshi da taste din girkinta yake yi aransa ba, shi hasalima abunda yafiye sakawa yake mutuwar son babansa ya aurota kenan, tana da tsafta, gayu, ga kamala, da nutsuwa snn yafiso ace sun zama tamkar uwa daya uba daya da su ibaad acan gidansu,bai fiye nuna wannan raayin nasa ma kowa bane sabida baison mahaifiyarsa ammi babba taga kamar yaci amanarta har tay fushi da shi.

ammi karama tana wucewa kitchen bada jimawa ba sai ga 10yr old safiya ta fito kanta babu dan kwali tanata callara wakar tashar style life its a beautiful world sabida batay tsammanin har sun iso ba. wani yaye labulen tayi caraf kuwa suka hade ido da ibaad da wani irin sauri ta sunkuyur da kanta kasa jikinta ya fara rawa ahnkli ta mannu da bango tace "i ii na wuni yaa ibaad? sama da kasa ya kalleta da daurarn fuska muryansa a mugun shake yace 'sallamarki kenan?

wani zirr hawaye ya ciko mata a ido cikin matsanancin jin tsoronsa ta girgiza kai tace" a'a, sai kuma ta fashe da kuka ahnkli, mikewa yay kamar zai falla mata mari, tay sauri taje taɓuya ajikin maheer da yay saurin tarota jikinshi dan bakaramin tsoron ibaad takeji ba, wani uban tsawa ya daka mata .."kee, uban me aka miki da kike kuka anan, ina wasa dake ko? dada shigewaa jikin maheer tay sosai muryanta na rawa tana cewa kayi hakur yaa aini bansan kazo bane, cikin kara daka mata tsawa yace au sai nazo gidan nan kenan kike abu kamar mutum ko,? toh maza kiwuce kije kisaka dankwali akanki, snn ki dawo nan..ina dai saikinji zanzo ne kike karatu, seee, i am giving u 3 scnds to grab all ur books and come back here yau saina ci ubanki...

da wani irin mugun tsorata ta saki jikin maheer din taballa da gudu kamar zata fadi kasa ta koma ciki tana kuka sosai, maheer dai kallonsa yake yasan dai wann bacin ran bana lfiya ba dan jikinsa nata bashi cewa lallai da akwai abunda ya bata ma ibaad ransa yau sosai,

kmr kiftawa da bismillh sai ga safiyan ta dawo da jakarta na makaranta tun daga kofar falon ta doka musu fulll sallama jikinta sai rawa yake hawaye na zuba mata tana kan tarewa da oversized veil din data rufe kanta dashi ,wani irin mugun kallo ibaad ya mata snn ya bata izinin shigowa ciki, still ta gefen maheer din taja ta tsaya, yaja tsaki yana juyowa zai kwace jakar suka hade ido da maheer girarsa sama a dage ahnkli yace hey mr temper, please kabarni da ita i will take it frm here..ibaad baice masa komi ba ya kalli safiyan yace ke zo nan..da dan uban sauri ta karaso ta tsuguna agabansa, yar nasiha maheer din ya mata akan tana nitsuwa, snn ta rage kallon series at dis young age ta fuskance karatunta kawai, ya mammata nasiha cikin lumana, ibaad na shiru bai kara cewa komi ba, dede ta bude assignmet dinta na farko da batay ba kenn sai ga ammi karama ta dawo da katon tray a hannunta mai dauke da manya manyan matured colour cooler dan kusan duk kayan kitchen inta daga wjen uwargida collection kawai take odersu.. cikin nitsuwa ta shigo tana cewa i am sorry i kept u waiting ko wsu ababen packagin nake nema bansamu da wuri ba.. tun bata gama surutun nata ba cikin sauri ibaad ya miqe yaje ya amshi tray din a hannunta suka karaso cikin falon tare, murmushi me sanyi tay ganin maheer na kan nuna ma safiya yadda zatay asigment dinta ayayinda safiyar ta bashi hanklinta sosai ta nitsu..

"babban mutum ka kyaleta kazo kaci abinci safiya kam ma ai na gaya mata aure zan mata kwanan nan dan naga gabaki daya wasa ne aranta bata kaunar karatu sai ta ganku, gidan nan dai duk wayake suwa 3rd position a schl in ba ita ba, ko kunya fa bataji

maheer na murmushi me sanyi yace aa Ammi haba aibaza ai mata haka ba she will grow up nd bcm a very succesful Data anlyst dan naga tafi iya lissafin computer ko ba haka bane safiya?

hawayenta ta share snn ta dago kai zatay magana wani mugun harara ibaad ya kara balla mata da sauri ta maida kanta kan littafin bata kara dagowaba.

suna kammala zama akan dinning ahnkli ibaad yakasa haquri with serious tone a muryansa yace ammi dan Allah kidena saurin gayamata cewa aure zaki mata da wuri karma ta sa shirmen soyayya aranta taki yin karatu, cikin katsesa da mamaki maheer yace dude relax, this is all fluff.. tsorata ta kawai ammi takeyi dan ta nitsu, cikin kyabe baki ibaad yace "auren ne zai sakata nitsuwa? in ana gaya mata haka babu wani tsoratar da zatay saidai ma ta kara saka abun aranta if not at dis age menene take kalla a indian series inba shirmen soyayyar karya ba, dahaka ne da suke saka abun aransu kaga yarinya karama wai tafara bin namiji... ammi dake kan jinsu batace komi ba tanakan bude warmers inta ahnkli wani irin qamshi ya katsesu maheer zaiy magana cikin katsetsa tace ya isa haka nifa bance kuzo kuyita musu agabana ba abinci kawai zakuci maheer please grab ur plate for me..da zumudi maheer ya bar maganan ya tura mata plate dinsa dake ta gabansa

wani dan ubansun Dambun Shinkafa da Nama tay irin nasu na mutenen maiduguri she steamed it with beef, onions, garlic, and butter, but she infuses it with Arab baharat spices dan ya kara masa dandano na musamman.

wani irin lumshe ido ibaad yay cos dambun shinkafar mamansa is his long time favourite maheer yafara lashe baki tun bata gama zuba masa ba ya dau cokali ya rike suna kallon juna da ibaad da tunanin irin dukan da zasuy ma abincin

ganin yanayin reaction dinsu yasa ammi ta zuba wata sasasnyr murmushi, tana gama zuba ma maheer nashi ta zuba ma ibaad shima snn ta bude wani cooler ta debo surprise din data ce zata masa yasha mamaki kuwa da yaga Fattah Lahm, special shuwa danderu ne da bata fiye yi ba dake da flat bread ake cinsa kamr shawarma. yana da mugun dadi dan is A whole hearty dish of slow-cooked lamb in spiced butter, layered with irin torn flatbread din nan, and the whole combo is soaked into a rich romon nama dayake tashen kayan yaji dana qamshi.

maheer nakaiwa baki yace wayyo Allah na ammi kin kasheni this is the besttttt food ever, dariya ammi ta farayi ganin banda bismillah ibaad bai ce komi ba kawai cin abincin yake kmr wanda yay shekara baici abinci ba, duk hirar da suke sai dai kaji ana uhmm uhm

safiya ta kafe kanta a asgment qamshin abincin yacikata amma sabida ibaad yasa batakoy gigin dago kanta ba.

bayan sun gama ci to the fullest ammi ta basu herbal tea inta me lemon tsami aciki suka sha, suna kan sha ana hirar karatu sama sama wayar maheer din ya fara kara ganin lambar mamansa ne yasa yayi excusing dinsu yabar sashen cikin gaggawa dan ya san halinta sarai ta tsani taji zancen yabiyo ibaad sunzo wajen ammi karama.

fitar maheer bada jimawa ta kalle ibaad din dake famar gode mata da abincin ahnkli tace its okay, dama haka kawai yau naji in maka abincin daka fi so yau and since u liked it ai shikenan

..ynx tayani tattarawa muje kitchen i want to have few some words with you alone.

..baice komi ba ya miƙe dan shikansa badon wnn yummy food treat din nata daya samu ba hala da tsananin bacin rai daya kwaso agidan kawu babba dazu zaiyi bacci..

cikin tsaftaccen kitchen inta dayaji jeren yan gayu suka shiga dede wajen sink ta juyo ta amshi tray in a hannunsa snn ta bude fridge ta fito masa da ruwa me sanyi wajen miƙa masa suka hade ido

daya kalleta saikuma yaji mugun tausayinta da kuma haushin shirun dayayi dazu ana zagar masa ita

suna daga tsayen taga mood dinsa ya fara canzawa cikin nitsuwa ta juyo dakyau tanata kallonsa ahnkli tace 'yadai rayyan, nikam ko baka jin dadi ne nide tun jiya kaketa faɗo min araina..ina fatan..

cikin katseta yace "Ammi, i am fine. kidena daga hanklinki pls

cike da yar maraicewa tace hmmm, badon kar yaa zaidu yay fushi ba yau danace ka kwana min anan but i get it, akwai schl kuma dama shi zaifi saka maka ido acan kayi karatun saidai bansan matarsa ba..did she still treat u diffrntly.,

ahnkli ya girgiza kai yace aa, cikin kauda hirar yace ammi, bappa bai gaya miki cewa kawu babba ya kirani gidansa bane???

waje ta kwalo idonta tace wani kawu babban? kana nufin bappanka prof zayyanu ya nemeka gidansa dabai barin uban kowa yaje?

tun be amsa ba adan tsorace tace 'why? wani abu marar kyau yakara shiga tsakanin ka da yarsu ko rayyan? dan Allah ka rufa min asiri mana ka fita aharkan yarinyar nan..ransa a hade cikn katseta yace haba ammi in fita aharknta kode sufita aharkata? tace ban gane su fita aharkan ka ba bayan kaine ka dakar musu yarsu yar kwai, wai kuma kana tunanin zasu yafe maka ne cikin sauki?

yace but dats like many months ago ammi. karamin scoff tay tace" okay, just tell me what was the meeting all about. kar ka boyemin komi..bana son wani fitina ya shiga tsakaninka da su musmn ma akan yarsu kana gani dai har hajy mairo prof bai kyaleta akan yarsa ba bare kai da baka da ubanka araye.

dan lumshe idon sa yay kadan kafin nan ya bude ya kalleta da sanyin jiki snn ya fara gaggaya mata duk abubuwnda suka faru muryansa kamar na wanda zai mata kuka, yace ammi, bayan cin fuskar da sukamin wai they still want me ina zuwa gidansun akai akai dan kawai hankalin yarsu yana kwanciya, nide ammi dan Allah u have to talk to bappa zaidu abt this, inajin nauyin inje ingaya masa kai tsaye cewa bazan kara zuwa ba batare da na bashi kwakkarn dalili ba,amma wallh bazan iya kula musu da yarsu ba,akan me? ni kaina abubuwa sun fara min yawa na karatuna i need to focus..nd for god sakes bazan je inda za'a na zaginki da sauran yan uwana a gaban idona ba..

wani irin shiruuuu ammi karama tay batace masa uffan ba for almost five mins tana jinjina maganan sai can taja ajiyan zuciya tace hmmm toh Allah ya kyauta,

cikin kwayar idanunsa ta juyo takalla ahnkli tace "rayyan, toh duniyar ma nawa take bare abun cikinta.. jarabawa ne kawai ..kaima kasan kafi karfin amaka gori da maraicinka tunda ban mutu ba ina raye kawai hakuri duk zamuyi dasu. bt in sha Allah zan yi magana da bappan naka kai kuma sai ka cigaba da masa biyayya dan Allah kar kadinga saba masa, know dat i am alwys here for you..Allah zai kawo mana sauki, kaji ko? ajiyar zuciya me nauyi ne ya kusan kufce masa ahnkli yace toh Ameen ammi and thank you alot for spoiling us i wish i can eat dis all day long.

..kyakkwn fuskarsa ta shafa kadan tana yar murmushi tace karka damu i hve packed some acikin take aways wanda zakuje gida dashi sai kuci dede nan aka kwankwasa kofar kitchen din maheer ne ya shigo looking so awkward, ya samu dede ammi tana kkrin ciro take away rubbrs din madaidata har guda uku babu jira ya shiga tayata har suka gama tasa musu a ledoji, wani sabon shafin hirar sukayi cikin wasa da dariya wajajen 9:40 suka ce mata zasu koma gida lokcin safiya ta gama duka asigment dinta still ibaad ya mata fada akan kallon series snn yace mata bazata kara cin abinci ba kawai ta wuce taje ta kwanta haka kuwa tawuce daki taje bacci har suka bar sashen sukaje suka gaida uncle moh da anty safeerah a shashensu snn suka bar gidan mai gabaki daya

cikinsu a matukar koshe suka kamo hanyar GRA maheer yana ta tsokanan ibaad wai kodan abincin da sukaci ne yasa yadan saki ransa, shide bai wani bashi amsa me kama hankli ba har suka isa gida me gadi yana bude musu gate sukay parking suka sauko da ledan abincin riki riki ahannun maheer suna isowa sama ibaad ya mika masa key din mota yay sauri ya haura gaba, da wani abu aran maheer yace hey Dan Allah kazo muje wajen baba atare mana waime haka inbazaka je bama ka amshi ledar abincin toh ka rike, ibaad yana ci gaba da tafiya akan stairs yace aa bazanje wajensa yau ba kaidai kayi sauri kafin afara wasar psg da chelsea bakazo ba, kai tsaye dakin maheer din ibaad ya nufa tun be amsashi ba, dake shi maheer har tv yana dashi adakinsa.

cikin girgiza kai maheer ya rabi hanya yawuce sashen bappa zaidu har ya kai kofa da sanyin sallama a bakinsa samunsa yay a zaune akan arms chair shi daya yanata kallon tashar larabai wanda tunkan ya amsa sallamar daddn qamshin abincin ya fara bugosa nd its sound really familiar dan yasan irin wnn qamshin inba girkin fatima ba toh saidai in mamansa hajy mairo mai tuwo ce ta dawo

cikin ladabi maheer ya rusuna yace ina wuni baà, idon bappa nakan ledan abincin yace lafya har kun dawo? ya mutane gidan kuma.. yace lafyarsu kalau dama uncle moh yace in gaya maka wai zaizo ya sameka da safe a office akan batun dawowar hajiya..

bappa zaidu yace "toh Allah ya kawosa sunyi waya da hajyar ne? inaga karshe ibaad kawai zamu tura ya dawo da ita tunda abokin fadanta ne amma kuma tafi saurararsa. gskiy she needs to come home yanxu kauyukan nan are not safe att all.

maheer yace hakane uncle moh yafara gaya mana wai jiya an mata satar generator a shagonta case kawai ta wuni tanay a police station da mutane acan..

bappa zaidu yace hmm mama kenan koda tana da kudin siyan dubunsa sai ta so akama barawon nan just to put him into justice nd dats way more scarier, ynxu fa duniyar ta zanca mai gaskiya bayayin farin jini. ina shi ibaad din inafatan dai baka barsa acan ba?

dan shiru maheer yay kafin ya dago a nitse yace aa tare muka dawo amma yana can daki na.'..

bappa yace ohh, to mesa bakuzo nan tare ba, lfya kuwa naga bai gaya min komi game da zuwansa gidan kawun nasa ba..

cikin gyaran murya maheer yace umm about that.....

bappa zaidu ya dada mikewa zaune yana kallonsa cikin nitsuwa yace "wani abu yafaru ko?

kansa akasa yace baa is not like he talked to me directly amma i overhead him yana gaya ma mum dinsa cewa wai so kawai suke yana zuwa gidan dan hanklin yarsu ya kwanta and.....sai yay shiru...

bappa ya masa wani irin kallo yace and what maheer karkay wasa dan hanklina anan mana..

yanadan sosa keyan kansa ahnkli yace 'baa, i dont think they treat him well..he mention sumtin abt zagin da sukama mahaifyarsa agaban idonsa akan zainab, baba cemishi fa sukay wai hala dad dinsa yana dukan mum dinsa ne yana gani shiyasa shima ya girma ba'a bashi tarbiya ba kuma wai duk yunwa ne ajikinsa, they even cooked him a separate meal hmm maganan dai da yawa..

komawa jikin chair bappa zaidu yay yana girgiza kai ahnkli ya furta hmm, snn yace "rubbish, sai kaga mutane kamar sun waye but they are so petty

..wann ai karanta ne. dama nasan za'ayi haka, idankaji kiransu badai don Allah bane saidai in suna buktar wani abu ajikin mutum suke kulasa, but i wont let them insult him again karya suke wallah, kai.. tashi kaje nasan me zanyi ai bakomi..

maheer baice komi ya aje keys din benz din akan table zaija ledarsa ya fice kenan bappa zaidu yy gyran murya yace "waimeye ne acikin ladan nan ka shigomun dashi me qamshi...

da zumudi maheer ya juyo yace ammi karama ce ta mana abinci me masifar dadi dama sauran ne tabamu wai mukawo gida mu karaci...

cikin mugun muradin son yaga yaci abinci me tattare da wata iriyar kamiya bappa zaidu yace ohhh toh dama wakanku kawai kuka kawo kenan..

maheer yace a'a ai tabamu hada extra nagawai baka cin abinci ne in dare yay sosai, but if u will like to eat saina serving maka, cikin jan aji bappa zaidu yay shiru sai can yace kawo dai in gani, what did she have here dan ban fiye son cin abinci late ba..

nan da nan maheer ya bude ledar ya ciro roban take away din guda daya ancika shi dam ga dambun ga babban sokar nama ga kuma phatta lahm da romonsa agefe an shiryashi very neatly komi gwanin sha'awa, ana mika masa tunbai kai ga gama budewa ba qamshin yasakashi lumshe idon dole domin karyay zumudi agaban dansa ya dan hade rai maheer yana ta batun kawo masa spoon yaga gogan har ya buɗe abincin ya aje murfin akan table yana kkrin tashi yaje ya wanke hannu a hand washing sink dake falon aikuwa suna hada ido ya balla masa wata dakalken kallo yace" kai baynxu kace min kunci naku abincin acan gidan ba to uban me kake ta kallon nawa kuma??

maheer yay kamar zaiy dariya yabi ya gintse kayansa ya kama hanyar waje

bappa zaidu yana gama wanke hannu ya jawo abincin hannu abaka yay bisimillah yay wata makahuwar loma wa dambun ya kai bakinsa wanda tuni yaji wani nitsuwa dan baisan wani dunia dadin girkin yakai sa ba,.. ahankli lumshe idonsa ahnkli yana furta kai masha Allah, but fatima can cook oo, da ynxu ninace tamin irin haka bazata taɓayi ba saraunyar kunya...

kusan kasar wuyarsa ya furta hakan amma xurum kalaman nan suka fada acikin kunnen matarsa ammi babba da zuwanta kenan ko sallama batay masa ba tun ganin maheer da tay awaje da ledan abinci tasan za'a rina, ranta a dagule ta shigo tana kan huci ta bi ta tsaya masa akai a mugun tsime tace "yaa zaidu kenan ma aka samu haka aketa hanɗama kamar baka tabacin abinci aryuwarka ba"

..romo dumu dumu abakinsa ya dago kai ya kalleta yace" yaran nan ne suka dawo dashi daga can gidan shine nima suka sammin".

wani irin runste ido tay cikin daga murya tanamai cewa "aa malam dakata min, karka raina min hankali mana kawai ka fito fili kace dai kaine ka aikesu wajen tsohuwar farkanka da Allah baiyi zaka aurota ka tozartani akanta ba, sunje sun karbo maka abincinta kazonan kana ci ham ham sai kace bantaba maka girki agidan nan ba yaa zaidu gaskiya cin fuskr da kake min agidan nan fa ya fara isata..

cikin katseta da dakakken muryansa me razanarwa yace keeee, da Allah ya isheki haka baki gani inacin abincine kifita kawai kiban waje inci abinci na cikin kwancyar hankali dan duk wnn kananan maganan dakikey duk ke kika san su can miki.

wani kukan kura tay zata kwace kwanon ya wapce abunsa gefe suna hade ido yace raihanatu am warning you.. kinsan dai idon yaran nan biyu basuy bacci ba banason inci mutuncin ki anan wjn agabansu kiga lefina so just get out...inna gama ci kya dawo kiyi baccinki...

tsabar bacin rai kirjinta har na dokuwa take harararsa a zafafe tafara daga murya tana cewa ohh hakama zakace min?

toh wallh wallah ba a isa ba

ganin bakulata zaiyi ba kuma bai fasa cin abincin ba yasa ta fashe da kukan takaici ta fice waje a mugun zafafe..

dakin maheer din ta nufa kai tsaye tahau bubbuga kofaraa kamar an korota lokcin har sun kunna tashar ball sun fara kallon kwallo shida ibaad, it was hell of a ryd tsakanin chelsea da PSG...

buga kofar datay da karfi yasa suka razana maheer ya mike tsaye cikin sauri ya fito, da mugun sauri ibaad shima ya taso yana biye dashi abaya baya

..suna bude kofa suka gan ammi babba atsaye sai huci take kamar kububuwa hawaye taf fuskarta

kan maheer a daure yace mumy lafya kuwa? muryanta har na sarkfewa tace "Ina tsinannen abincin da ka kawo gidan nan

zai magana sai wani tasssss yaji diran yatsunta akan kuncinsa shikansa baisan sanda tasakar masa wata makuhar mari me kara ba..

ranta a mugun bace cikin dakamai tsawa tace Baqin munafuki kawai... Allah wadai naka ya lalace,.maheer wato ma dakai ake haɗamin baki anayin barbade ana asirce ubanka ta hanyar abinci ana kawo masa gidan nan haryana walakntani akai dan kawai a fitar dani agidan mijina wata shegiyar karuwa ta shigo toh wallh wallh bari kaji inma baka sani ba ranar da kasaka fatima ta shigo gidan ubanka ƴayanta ne kawai zata cigaba da cusawa a zuciyar baban na ka kai da kanwarkan kuma saidai ku kare abin titi kamr marayu, ince dai nice kawai baka so agidan nan? wawa, banza kawai shashasha wanda baisan abunda yakeyi ba...munafuki kawai.

wani irin shirrruuu dukansu sukay sunata kallon ta har hawaye yafara zubowa idanun maheer musmn data juyo kan ibaad ta fara zaginsa ta uwa ta uba tana kiran uwarsa karuwa, mushrika shikuma ya daure sosai sai haquri kawai yake bata sabida yana mugun ganin girmanta

kusan a zuciye maheer yasake kofarsan da karfi jin abin yafara ishenshi kusan tureta yay ya wuce ya fice can can waje da mugun sauri yana wani irin hawaye me zafi, tana tsaye har ibaad ya sauko shima yabi bayansa hanklin sa atashe saida suka kai kusa da gate snn yaci nasarar riko sa suka ja gefe dukan su da hawaye kwance akan fuskarsu...

ganin yanayin maheer yasaka ibaad ya share hawayensa cikin dauriya dan maheer yakai minti goma yana hawaye ji kawai yake ibaad din na danne nashi yanata bashi haquri amma bai iya dena kuka ba..

sai can ibaad yace 'okay fine tunda baza kace min komi ba gara naje sama ynxu na same bappa na gaya masa ni zan koma gidanmu kawai, i can't deal with this shit...kusan a sanyaye ibaad ya sakeshi ya juya zai bar wajen sai ji yay maheer din ya damko hannunsa da karfi tun kafin ya gama juyowa ahnkli yaji ya fado mai ajiki suka dan rungume juna araunane...

tantame ibaad din yay yana hawaye muryansa na rawa rawa yana cewa ibaad dan Allah kayi hakuri karka gayama baba ko Ammi wann maganan izuwa ynzu kusan kowa ya san halin mumy amma nasan da ciwo ana alakanta mahaifyarka da wann kalmomin datake furtawa, i am begging u pls dont take it to heart wallah baaba yana kaunarmu tsakani da Allah nasan duk abunda take fada maka borin kishi ne kawai pls dont take it to heart....shikansa inyaji wann maganan zai iya mata hukunci me tsauri musmn ma ynxu inkaje kace mai zakabar gidan nan sabida ita..

cikin katsesa ahnkli ibaad yace "i am not leaving maheer..'i am apologising to u sabida nine nake jawo muku matsalar ita kuma ai mahaifyrkace, maheer dan Allah kadena kukan nan ya isa haka wnn misundertanding ne tsakaninsu mukanmu bazamu taba iya ganewa ba kawai mubar komi wa Allah

..dakyar maheer ya shanye emotions dinsa ya dago ya share hawayensa ya kalle ibaad cikin ido yace "promise me bazaka bar gidan nan sabida halin mummy ba..

..ibaad zai budi baki ya kara katsesa sounding desprate yace please ibaad..for his sake..nd for my sake..i know ure going tru alot amma kasani i wll neva let u carry all this burden alone

..i will alwys be der for u as my friend nd brother, nasan abubuwa suna maka yawa nd i am sorry, i also overheard abunda kawu babba suka maka agidansa u dont have to worry abt all these things.

...cikin lumshe ido da budewa ibaad yace ohh please, lets not talk abt that..'

maheer yace "we will, dan nina gaya ma baaba iya abunda nasani, duk abunda suka maka wanda naji nagaya masa.

cikin kwalo ido da mamaki ibaad yace kumawai a ina kaji?

..maheer yace just forget it, nide nafiso koma me zamuyi lets not do anything da zai kara raba kan familyn nan u need to just hold on abit..

yace what? "maheer, did you think i am not holding on? inba dan ina danne zuciyata ba wallah da bazantaba zuwa gidan ba har abada dan yarinyar ne kawai gabaki daya bata min ba, yes, she is fine princess, with her insanely rich parent, but she is this batterly spoilt, damn arrogant, mannerless nd so so much more.... classeless... halayenta da i cant even stand them..duk da ban taba mafarkin yin soyayya ba, but i know in my hrt dat i wont eva be able to like Zainab arifah..she is not my type and she is not going to be.

kafadunsa maheer ya dafa ahankli yace 'But Ibaad, somtimes u cant beat a river into submission if not it will drown you, mafi maka alheri shine try and submit to the waves ahakane kawai zaka iya kwatar kanka, i think she is just obessed with u..in ita yarinya ne ai kai ka girmeta. nd by the time tazo fa mallake hanklin kanta she will grow tired of ur attitudes and plus i am sure kawu babba ma zaizo ace mawani mashurin mai kudin zai aurar da ita...just chill with her for now kay hakuri kawai ka biye musu..wani fadar ba acinsa da yaqi.

ibaad baice komi ba kawai ya dan lumshe idonsa for a while kafin can ya bude idon cikin kyabe baki yace ure probably ryt, i may need to just let it be, cos i bet bfr she reaches 18yrs ma hala ta tsaneni dan ba lokacin ta zanyi ba

..dariya mai sanyi maheer yay baice komi ba ya girgiza kai snn suka samu waje suka zauna awajen subiyun su suka dan kara tattaunawa akan wasu abubuwa dake gudana acikin gidansu harma da batun dawowar hajy mai tuwo gida, after a while arnd 12.30pm na dare suka koma cikin gidan suka samu waje yay shiruu tvns maheer ne kawai a kunne harma angama ball din daga sai kawai kowa ya wuce room dinsa ya kwanta....

washe gari sa safe tun bayan fitarsu sallahn fajr da suka dawo suka fara fahimtar kmar tsakanin bappa zaidu da ammi babba ba ai kwanan lafya ba,dan kwata kwata wani gigin rashin mutunci ne a idanunta, yaran nata na cikinta ma kaf tadena amsa gaisuwarsu tace duk munafukaine suna goya ma babansu baya yana soyayyarsa a boye da ammi karama, haka kuma batay breakfast a gidan ba, hasalima wakokin zube na hausa masu cike da tsagwaron habaice habaicen banza da wofi ta kunna asashentan jiddidin wala hairan tanatajinsu shikuma bappan zaidu ko ajikinsa dan tun jiyan dq sukayi fada akan marin maheer datay sai ko kala bai sake ce mata agidan ba,abincinsa dana iya wanda yaransa zasuci kawai yakeyin oder daga restaurant akawo musu suci snn kowa ya wuce makaranta, mugun shareta data ga kowa yay sai yayi mata ciwo aranta bana kadan ba musmn ma maheer daya fara nuna mata danyen kai da fallin balaga waidan ta maresa shima sai yadau zafi da ita sosai tsakaninsu daga gaisuwa baiyace mata komi haka zai hade ransa yawuce schl, kai ko irin hakurin nan na lallashin uwa baizo ya mata ba, haka tay ta fushi tana cin magani tsanar datake ma ibaad kuma sai ninkuwa yakeyi aranta, gashi ansama ma sultana private lesson teacher ba wuni takeyi a gidan ba har yamma tana schll haka zata wuni ita daya agidan tana famar sake sake

saida aka ci kusan kwana hudu tana wann haukar borin kafin ita dakanta tayi yaji tabar musu gidan can da dare kuma wani babban yayanta wanda baiya daukar nonesense yadawo da ita gidan yamata masifa snn yayita bawa bappa zaidu hakuri akadan yi musu nasiha snn ta dawo daidai.

a satin gabaki daya gidan ya kasance sam babu wani armashi, Maheer yanata kkrin fara exams ne dake law yakeyi ayayinda ibaad din shima yake fafutar nasa karatun a fannin medicine wanda acikin satin ne kuma prof da yarsa zainab arifah suka fara kafamai ƙahon xuka, duk yamma ko dare sai ya kirasa awaya snn yabi ya hadashi da zainab Arifah hirar dole, surutun banza da wofi dana tarukucen yaranta duk zatayi ta masa akunne kuma agaban babantan sam batajin kunyar kowa,

hakama tun daga daga schl prof zai aika driver ace ma ibaad maza ya samesa a office dinsa

yana zuwa kuwa zai bashi key yace masa yajeshi makarantar su zainab Arifah din yadauko masa ita a schl yakaita gida, ko yace masa bata da lafiya tanata kuka taki tabi driver wai sai shi, ko yakawo masa wani silly uzuri nadaban dan kawai suna kasancewa tare.

kwana biyun nan prof bakaramin zagewa yakeyi yanata kkrin cusa yarsa acikin rayuwar ibaad ba,

gashi kai tsaye yake nuna iko da gadara dashi sam sam baiya masa uzuri, badon komi ba saidan kawai yarsa tasamu tagama cire ciwon damuwar soyayyr nan nasa aranta tanitsu har tay karatu dan bakaramin bright future ya shirya mata agaba ba.

tun bappa zaidu yana dakatar masa har abun yaso ya dawo musu babban rigima ganin sosai da sosai suka fara takurawa rayuwar ibaad din.

dan haka kawai in ya kira Ibaad zai sakashi yin wani silly abu wa zainab din daga yace bappa zaidu yace a'a prof ne dakansa yke kira ya zage zage yayta bori yanamai cewa wai anaso ne anuna masa warayya akan ibaad in har bai isa yay iko da ɗan yayanshi ba. tun bappa zaidu yana fito na fito dashi har ya hakura ya dawo bawa ibaad din hakuri, ita kuma zainab arifah rayuwa ta dawo mata sabuwa mai cike da nishadi da jin dadi, dan tsabar ta samu daurin gindi da dama kusan duk snda taji aranta tanason ganin ibaad haka zata narkewa babanta har sai an nemo matashi..

satin nan kusan shine masa lokaci mafi wahala da takurawa, ga fitinan ammi babba agida ga kuma prof da yarsa zainab arifa ga karatunsa...

bayan kamar sati guda wani tunani bappa zaidu yay yau sassafe ibaad ya fito daga sallah zai wuce daki kenan ya kirasa agefe yace masa ya shirya kawai daga ya dawo daga schl yau zai bashi mota yajeshi anguwan tudu domin ya duba musu meyake faruwa da case dn sata da akeyiwa hajy mairo mai tuwo acan, snn in abun bazaiyu ba kawai ya lallaba musu ita tabar kauyen ta dawo nan gida.

ibaad baiwani son yin tafiya on short notice musmn ma da bada maheer ko dayan kaninsu mujaheed zasu je ba, but, the joy of geting a break daga fitinar zainab arifah da mahaifinta yasaka yay murnan wann tafiyar aransa sosai.....

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 👇🏻

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025