ABUNDA KE 'BOYE...

11

by @surayyahms

ABUNDA KE ƁOYE....

Love And scandal💕

Arewabooks@surayyahms

⏯️1️⃣1️⃣

the same day

6.30am

thursday

garin majiya

Azaune kusa da inda inayah ta idar da sallahnta na fajr data dawo yinsa a zaune wani bacci me mugun nauyi da minshari yawuce da ayaanah, duk dama sanyin safiyane amma su biyune kacal acikin dakin maman nasu

daga inda inayan tay sallan tazuba farqren raunattacun ruwan idanuwanta masu cike da rauni da tsumayi akan kyakkwar fuskar kanwarta ayaanah wanda hasken kwan fitila mai gauraye da ketowar hasken alfjr ne kadai yake dada illuminating dakin wanda ya dada kawata nitsattsen kyaun ayaanah mai tsananin sanyi da kawata ruwan idanun duk wani mai kallo,

daga gani baccin kawai takeyi amma da alaman cewa batasan yaushe baccin ya dauketa ba dan tun da addanta tafara ciwon nan itama ta kasance sam bata samun wani nitsuwa...

wani irin shiru dakin yay tamkar babu kowa aciki dan akai akai inayahn take sauke ajiyan zuciya me nauyi da kuma tsananin rauni ayayinda ruwan idanunta suke akafe akan kyakkwar fuskar yar uwata ayaanah datake matukar kauna

can sai taji tsillin hawaye me tsananin zafi yana sauko mata akan kuncin ta, hannu takai zata goge su sai kuma taji gabaki daya hawayen nata yana kara tulowa da masifar yawa da tsananin zafi mai tsaga kahon zuciya..

wani irin lumshe ido tay dan aranta ji kawai take kamar yaune ranar ta na karshe da zataga fuskar yar uwanta a rayuwarta, dan ciwukan datakeji ajikinta haryau bata isa ta faɗi irin azaban da suke dandana mata agangan jikinta ba, itade aranta bata kawo batun mutuwa, ko rabuwa ba, amma tabbas tanaji kmar kallon karshe kawai takey ma ayaanah yanxu batasan kuma meyasa takejin ahakn aranta ba.

tun wajajen biyar da rabi tawuure ta saci jiki taje jejin daketa bayan gidansu neman wa inayan saiwowi na magani dan yau kusan sati guda kenan suna fama da jikinta, yau yay sauki gobe yay muni, gashi maganin datake yawan batan kafff ya kare da kyar da wahala juma ya sauko daga fushinsa harma ya janye kalamansa na cewa koda kofar gidansa ta taka toh abakin auren ta, anguwar tudu kuwa haryau yana kan bakansa nacewa inhar ta taka kafafunta taje tudu batare da izininsa ba ta dauka kawai tamkar ya saketa saki uku kenan har abada, ahakan ma wai saida yaga zahiri jikin inayar yana dada ragwabewa kullum da matsancin ciwon ciki me tsanani ne kafin ya basu wnn dama

ciwon cikin inya tashi mata har kamar kyarman mutuwa takey, hakan daya lura yagani ne yasaka ya kyale taawure tafara fita cikin jeji tana neman saiwowi wanda duk dq ta jika su tana bata amma duk baima inayan komi.

yauma da asubahin fari ta sake komawa jejin dan ta zanzo wasu saiwowi, dan izuwa yanxu ita kanta duk ta galabaice zuciyarta da jikinta sun fara sanyi da yanayin ragwabewr jikin yarta inaya, inaya bata iya cin abinci ta rame sosai, duk tasa abu abaki saita amar dashi, ga rashin samun bacci, ga ciwon ciki me tsanani mai kumburi da uban zafin ciki duk inayahn ta rame ta kanjame kamar ba ita ba kusan kominta ynxu a zaune takeyinsa daga bayi, wanka har sallah sam bata iya mikewa da jikinta a tsaye kamar normal mutane.

tun asuba taawure ta fita amma kafin ta samu wasu saiwowin saida ta kure tafiya can can cikin jejinsu dakyar ta debo ganye da saiwowin binida zugu, lemon grass na jeji, da goruba,goga masu da ganyen kuka dana rai dore da wasu saiwowi na jejin fulani duk takamo hanyar gidanta dasu cikin sauri dan already har karfe bakwai ya kifta sosai, saida ta zo daf zata fice acikin jejin snn taci karo da wani mutum acikin ciyawa yana tattaran itace akan kekensa,

kallo daya ta masa tagane Dandanko ne, da wurwuri ta dauke kanta bata ko masa magana ba, cos just as his name implies, dankando mutum ne daya kwarance wajen iya yaɗa gulma da ƙarya dan kawai ya tada zanne tsaye.

tun hangota dayayi ya gama saka mata ido yakarance duk ganyen magani da saiwar dake hannunta, dama kuma yaji kishin kishin anacewa acikin yaran juma akwai wacce take kwance tana ciwon ciki aransa kawai ya riga ya kudura hala cikin shege ne tunda ya jima yana kawo suka da tsegumi ma juma akan barin taawure dayayi tana zuwa tudu tay watanni acan tana kasuwanci da yaransa mata, acewarsa ai tudu kamar bariki ne kuma yayansa duk balagaggu ne zasuje ne su koya halayayyar banza mazan bariki zasuna kwana dasu acan, ya jima yana cusa wann maganan a kunnen mutane bai samu nasara ba, dake juman bawani zama yake a gari sosai ba idan yaje can boda yin kasuwanci dayaga ya dawo kiwo ko noma kawai yakeyi gulma bai fiye riskansa ba....

tun dayaga taawure da saiwowi haka ya dinga binta yana mata tambaya akan wasu ganyykin maganin data debo duk dama taki sam ta kulashi amma be fasa ba

adai dai kan gaba suka rabu, tay sauri ta shigo cikin gidanta bata ko leƙa yaran ba ta wuce madafi ta samu har ayaanah ta farka ta fito ta kunna wuta ta dora ruwan kunu ta kuma shirya dumamen tuwo cikin tukunyarsu na kasa amma bata dora ba.

Albarka tasaka ma ayaanahn a zuciyarta dan tunda inayah tafara ciwo ayaana ce ke kkrin yin aikin gidan sosai. nan ta aje mayafinta kafin ruwan kunun ya tafasa ta jawo wano baho ta zuba maganin aciki tana wanke kasa da dattin dake jiki, sai can data mike tsaye zata lekasu ta windo snn tafara tsinkayo sautin karatun qur'ani da ayaana take rerawa addanta dake fita ahankli dan kar juma yaji, ganin suna nan yadda ta barsu yasa ta koma madafin ta dama kunun tay marmaza takaima juma nashi har cikin turarkarsa ta same sa haryanxu yana sharar bacci da alama ko sallan safiya baiyi ba gashi har ana neman karfe takwas ynxu,.

koda tay mai magana acikin baccin ya dura mata ashar ya kara juyi abunsa, fitowarta waje kenan ta sharo kwana bangarensu taji wani irin kuka mai kara muryan inayah na fitowa a raunace tana cewa" wayyo Allah na, innalillah wa inna ilaihi rajiun, umma, umma mutuwa zanyi, wayyo ayaanah huramin cikina cikina hasbinallah wa neemal wakeel

sanda jikin taawure ya fara rawa ma bata sani ba kusan a guje tayo dakin ta samu ayanah ta riƙo inaya dake murmukukusu akasa da wani irin matsanancin ciwon ciki wanda tsabar zafinsa har wani tsinkakken yawu ne yafara zuba mata abaki kamar ruwa.

taawure tana zuwa ta amsheta ahannun ayaana ta rungumeta ajikinta already tafara zubar da hawaye sosaiii

subnallah innari?? meya faru, chikiin ne?

kiyi hakuri innari am na samo miki magani ajeji ynxu zan sarrafa mikichi kisha kiji sauki

sai nishii me zafi kawai inayah take y tana furta innalillah wa inna ilaihi rajiun dukkansu saida suka raunatu yayinda ayaanah ma ta kara fashewa da kuka me sanyi tana cewa 'sannu adda Allahu yashfiki.. ganin ciwon yaki saketa taawure tay tamaza ta kwantar da ita ajikin gado snn tace ma ayaanh tazo ta daukar ma inayan kunu halama ulcer ne yake motsa ma inaya jiki,kusan da gudu suka fito ayanah ta dauko kofin kunun da abun sassaitawa ita kuma tawure ta sauke dumamen tay sauri tadora wasu ruwan maganin a wuta danta sarrafashi agurguje, wanda kuma bana tafasawa bane tahau sarrafa su...ayaanah tana kuka tana fifita kunun a ludaye tana kaiwa bakin addanta, wanda a loma na biyu ta fetto kunun waje, jin gefen cikin inda ya kumbura sosai ya kara tokarinta da wani irin matsancin zafi ga wani dan uban kakarin amai me gigita yanayi dayake kkrin tason mata

marmaza ayaanah ta rikota suka fito bakin kofa tafara aman wanda yawu ne mafi akasari yake fita sai dan ludayi daya na kunu data kurba shima kamr zata fidda ranta yake fita

jin tana aman tana wayyo wayyo cikina innalillah umma zan mutu yasa taawure tay saurin tahowa da kwaryan maganin datake hadawan a hannunta, tun ma bai tafasa sosai ba, cikin sauri ta rike kan inayah tana mata addua tana kuma sassaitawa zata kai mata baki kenan sai ga dandanko ya doka sallama daga waje yana lekowa taciki..

tun basu ma gane shi ba yafara daga wargajin muryansa daga kofar xaurensu yana cewa ba'a amsa sallama ne agidan nan? kai malam juma kai buzu juma salama aleku... waye yake amai haka..

taawure ta daga kai zata amsa sai ga juma ya fito fuskar sa a mugun dore yana kkrin kafa hularsa akansa ko kallonsu baiyi ba yasakai zai fita..

tunda taawure ta bawa inaya ruwan maganin sai aman kawai takey jikinta na wani irin kyarma kr kar kar ayanah ta riketa sosai tana hawayen itama

daga kofar zaure juma ko amsa gaisuwar dandanko baiyi ba yahaushi da masifar katsemai baccin da yayi da sallamrsa

shikuwa nan ya fafuko makirci ya soma gaya ma juma ai ya gamo da tawure ne ajeji ta debo magani shine yazo ya dubasu ko lafya

suna cikin wanga tattunawa suka kara jiyo sabuwan ihun inaya tana cewa wayyo Allah cikinta cikin matsancin yanayi mai rikitarwa ga ruwan maganin na fitowa ta baki ta hanci,

da wani irin mugun tsinkakken gulma da tsegumi dandanko ya kusa ture juma ya shigo ciki har suna rige rigen karasowa tsakar gida

jikin juma har na rawa yahau cewa kai kai kai lafiya kuwa innari meye haka kukam kun shigga uku da wanga kazanta wani irin ragoncin ne haka?

cikin katseshi taawure tace me gida ciwon cikintan ne ya tashi..

wani caraf dandanko yace ciwon ciki ne har shine take amai? kai taawure ki rika fadin gaskiya kode taciyo wani abu awani waje awajen maza?

banza tay dashi ta kyalesa da juma dayake tuhumarsa akan manufar maganansa, ita kam zage karfi tay ta dauke inayan cak takaita kan tabarma ta dan wanke mata jiki snnn ta shimfidata tana mata fifita ayanah kuma tuni ta dau tsintsiya da abun kwashe datti tafara kwashe aman tana gyarawa..

musu ya kaure tsakanin juma da dandanko dan har waje ya rakasa yana tuhumwr sa akan abunda yke nufi da yarsa

dake dandankon mugun annamimi ne sai bai fito fili ya gaya masa cikin shege yake harsasshe wa inaya ba, baqaqen magana da misalai na yan matan kauyen da suka taba gumtso cikin shege kawai ya dinga kafa masa misalin ciwon inayan dashi yanamai ce masa saishima yay hankali, dan yanzu haka sarakunan garin sunsaka doka muddin yarka ta mutu d cikin shege bazasu mata sallan gawa ba shureta kawai zasuyi a rami kamar dabba snn su binneta a walaknce dan karta lalata musu kasa da kazantan zina.

duk dama juma mutum ne mai kaifin tunani yakuma san halin dandanko da gulma da son yaɗa karya dan ya tada zanne tsaye saidai sosai maganganun suka fara taɓa mai zuciya dan yawancin zarginsa akan yaransa yana tsayawa ne akan su mazinata ne kuma abun kunya kawai zasu jawo masa

da wnn tunanin aransa yaƙi ma dawowa gidan kawai ya miƙa sawun kafarsa ya shiga gari neman abincin karyawa da zimman kafin ya dawo hala innarin ta dawo cikin hayyacinta zai hadasu duka yaci ubansu har sai sun amayo masa gaskiya game da ciwontan nan...#surayyahms

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025