1
'Yan uwa
Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,
duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su
Sandal flakes
Hawee
Gabgab
Halut
Dorot
Coconut chips
Dufr(farce)
Black khumra
Brown khumra
White khumra
Oil perfumes da
Body sprays
Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.
Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka
Call/WhatsApp
***
Location:Gonan Ganye,zaria
Kaduna state
Nationwide Delivery
1
SHIMFI'DA.
Sunana Amina Malam Salisu wanda ake kira da (Mai wankin hula) Ni tela ce k'wararriya sannan kuma malamar makarantar boko ce ta gomnati. Ina koyar da yara harshen hausa a firamare ta gwale local goment. Bazawara ce ni a yanzu mai yara biyu dukaninsu maza. Babban sunansa Kamalu sai d'an'uwansa Yusuf wanda muke kiransa da Yusi. Mahaifinsu ya rasu shekaru hud'u da suka gabata tun lokacin Yusi din yana da shekaru bakwai a duniya. Tazarar da take tsakaninsa da d'an'uwansa Kamalu ta shekara daya ce. Ni da Babansu Allah ya jikansa da rahama muna hasashen daga yin arb'anin din haihuwar Kamalun ne na yi katari da cikin Yusuf din. Tsiran da yake tsakaninsu dai bashi da wani yawa. Yanzu Kamalu yana da shekara goma sha biyu, yayin da Yusi yake da goma sha d'aya.
Tun bayan rasuwar Yaya Aminu mahaifin yarana na koma gidanmu da zama domin dama gidan da muke zaune dashi na haya ne kasancewar akwai rashin 'karfi da rashin 'kwa'kkwarar sana'a daga 'bangaransa. Cikin ikon Allah sai aka yi sa'a d'akin da muka yi 'yan matanci ni da 'yan'uwana yana nan sai dai shirgi da matan gidan suke ajiyewa. Anan na ra'kube da 'yan kayana na zauna nake gurgura rayuwar kafin mu ga hukuncin da Allah zai zartar.
Zamantakewatar auran da muka yi ni da Yaya Aminu na tsayin shekara goma sha uku kusan ni ce 'karfin gidan saboda Allah ya ri'ka mini Ina aiki, sannan ina d'inkin mata da 'yan gyare-gyare, bayan haka kuma ana kawo mini aikatau na jaka 'yar pose da huluna irin na yadin hijabai. Sosai Allah ya huwace mini. Duk wata zan d'auki albashi sana'ar d'inkin da nake yi kuma tana taimaka mana sosai har mu iske sabon wata ba mu galabaita ba.
Ban ta'ba yin nadama ko na ji wani abu na 'kyashi a raina ba a duk lokacin da Ya Aminu zai nemi wani abu a wurina muddin ina dashi babu jayayya ko gardama nake d'auka na bashi. Babban burina ace asirinmu ya rufu gabad'aya, kuma dama tun lokacin da muka yi aure na yi alkawari cewa 'In dai Allah ya ri'ka mini sai Ya Aminu ya fi karfin komai a wurina, sakamakon irin hallacin da ya yi mini a rayuwata.
Duk da cewa albashina bashi da wani yawa kasancewar firamare nake koyarwa, amma ana yin salary nake ware masa kudin transport, tun bayan korarsa da aka yi a kamfanin da yake aiki sakamakon tashin ciwonsa, to sai ya koma kasuwa yake buge-buge. Dalilin da ya sanya kenan Ina kar'bar albashina nake ware masa
wanda za su ishe shi zurga-zurga a wata saboda lalurarsa tunda bashi da abin hawa kuma daga unguwarmu zuwa kasuwar da yake hurd'odinsa akwai akwai nisa sosai.
Ni da Gwaggwo mahaifiyarsa ba mu ta'ba sanin yana da wani ciwo ba sai da kawo shi ranga ranga daga wurin aiki tukkuna likita ya tabbatar mana da cewa yana da matsananciyar asma bayan ita ma har da sanyi wato limoniya sune suka tayar masa sakamakon yawan shiga ruwa da yake yi, da kuma shakar iskar asubahi. Tunda ana idar da sallah yake fita kuma a 'kafa yake tafiya dalili kamfanin babu nisa a tsakaninmu, bayan haka kuma yana da matsalar k'afa guda d'aya a dogare take dunduniyar bata taka k'asa. Likitan ya tabbatar mana da cewa
iskar da yake sha'ka da tafiyar da yake yi mai tsanani duk sune suka had'u suka tayar masa da ciwon.
Sai sannan Gwaggo ta tuna a lokacin da yana yaro ya ta'ba yin irin haka da 'kyar aka shawo kan matsalar. To tun daga sannan ni dashi muke kaffa-kaffa ko fita ya yi ya manta da inhele sai ya dawo ya d'auka. Ni ma kuma kafin ya fitan na kan tuna masa sai ya d'auka ya sa a aljihunsa ya tafi.
Tunda aka sallame shi daga aiki. Muke kame-kame, taimakon da Allah ya yi mini ina da hanyar samu da ban san ya za mu yi ba. Takaici da bakinciki ya hana shi sakat kullum idan muka zauna maganarsa Alhaji Tajo bai yi masa adalci ba. Ya sallame shi babu uzuri, sannan bai bashi komai ba duk irin wahalar da ya yi masa. Ni kaina sheda ce Yaya Aminu ya bautatawa mutumin sosai. Amma bai duba hakan ba. Na dinga 'karfafa masa gwiwa akan ya yi hak'uri ya cire damuwar hakan a cikin ransa. Idan ni ce ba zan ta'ba d'aga masa hankali ba, da dadi babu dadi zan zauna dashi. kuma ya je kasuwa ya nemi arziki, Allah ne mai bayarwa. Kalamaina suna 'kara masa karfin guiwa a lokacin zai shirya ya fita duk da bai san inda zai nufa ba amma zan ta 'karfafa masa guiwa. Wasu lukutan ya dawo da d'an abin sarrafawa, wasu lukutan kuma ya dawo sannu rabbana da kukan k'afafunsa na yi masa ciwo.
Tashin ciwonsa na biyu shi ya kasance ajalinsa ya kwanta jinya a gida da tunani da takaicin abubuwa da yawa, domin har zuwa lokacin bai manta da wula'kancin da akayi masa ba. Da ba'kincikin Alhaji Tajo Yaya Aminu ya koma ga Ubangijinsa.
Komawa ta gidanmu da zummar yin zawarci sai abubuwa suka ru'banya rinca'bewa. Kuncin dana riska na yanzu ya fi na baya inda Allah Ya taimakeni ina da abin yi sai na samu sassauci ta nan 'bangaran. Amma dai dukda haka wataran idan masifar ta ishe ni 'kunshe kaina nake yi a d'aki na ci kukana na 'koshi. Wata zuciyar ta dinga raya mini kawai na sanya dillalai su cigita mini gidan haya wanda ba zai gaza dubu hamshin ba a shekara na san tunda ba'a zaune nake ba Allah zai agaza mini, saboda wata masifar Kamalu ne yake janyo mini ita, yaron bashi da ha'kuri kamar d'an'uwansa gashi dai shine babba,amma kullum kuka ake yi dashi a gidan. Ya yi ta tsokanar yaran jama'a dana ma'kota Ya ci zalin wanda ya fi karfi. Iyayensu su fito su yi zage-zage da gore-gore. Da barazanar sanar da maigidan Babanmu akan ya tursasani mayar dasu dangin Babansu.
A wancan zaman na baya na fuskanci uk'uba ba da 'kunci na garari. Farko na rashin uwa majinginta. Na biyu kuma yadda na zama 'yartsakargida wula'kantacciya wadda ba ta da 'yanci kamar sauran 'yan'uwanta. Na uku jarabbawar da Ubangiji ya yi mini a lokacin mun taso mu biyar duk 'Yan mata amma gabad'aya sai da aka aurar dasu ni ina zaune babu ma wanda yake sansanta. Sai da kaddara ta gifta tukkuna Yaya Aminu ya nuna sha'awar aurena muddin ina sonsa tunda dai shi ga yadda Allah Ya hallice shi.
WANNAN KENAN.
****
Kasancewar na raba dare ina yanka din'kunan mutane da suka jima a hannuna ban samu sukunin dinka musu ba sai da aka yi wa yara hutun makaranta tukkuna. Dalilin da ya assasa mini bacci mai nauyi kenan da k'yar na tashi na gabatar da sallar asubahi. Na tashi yarana sai da na tabbatar sun fita zuwa massalaci tukkuna na koma na kwanta baccin dai ya 'kara surata. Sai na ji sautin kukan Yusi a cikin kunnuwana na bud'e idona da saurin gaske na tashi zaune sai na ganshi a ra'kube a jikin bango. Saminu 'kanina da muka had'a Uba d'aya dashi da tsintsiyar kwakwa a hannunsaa yana shaud'a masa.
Da sauri na fizge ina fad'in." Kai akan me ka ke dukansa, me ya yi maka?"
Ya ce.'' Kashi ya yi a bakin masai.
Cike da b'acin rai na ce." Saboda ya yi kashi a bakin masai sai ka dake shi Ina ce kai ma kana yi, ko kai kake wanke bandakin ne?" Cikin rashin kunya ya ce.'' Ai bayan haka ma d'azu kina bacci Kamalu ya tsinkawa Ashiru mari, babu abinda aka ya yi masa, shine nake ramawa a kan 'kaninsa ni ma."
Cikin takaici na ce." Dallah fita ka ba ni wuri shashasha kawai." Ya kama hanyar fita yana
wa'ke-wa'ke.
Na girgiza kai tare da mayar da hankalina kan yaron na ce." Yusi ban ce idan za ku hau masai ku dinga nutsuwa ba?"
"Mama matso ni ya yi. Kuma Saminu ne a cikin bandakin da yaga ina jin kashin sai ya'ki fitowa daga band'akin, yana leko ni yana yi mini dariya. Na fadawa Ummansu ta yi mini banza. Sai da Yaya Usaini ya yi masa magana sannan ya fito na shiga ban san na yi bakin masai ba."
"Yanzu ina Kamalun yake?"
"Ya d'auki kudi a jakarki ya tafi sayo kunu da awara."
Na kalli agogon da yake bangon d'akin, takwas saura mini goma. Na ce." To tunda an yi hutun boko sai ku yi shirin allo idan kun karya ba zan iya cecekuce da rabon fad'a ba."
Ya ce." To Mama." Kamalu ya shigo da jug din kunu da awara a bakar leda Yana cewa." Mama na d'auki dari biyar a jakarki na sayo awara ta d'ari uku kunun dari biyu, yanzu darin sukari za ki bayar."
Na ce." Kamalu kai kullum burinka ka janyo mini magana ko? kullum sai na zaunar da kai na yi maka fad'a, amma magana tana shiga ta kunnan dama ta fita ta kunnan hagu ko? Ba za ka ri'ke maraicinka ba Kamalu abinda kake yi fa shi d'an'uwanka zai kwaikwaya, ba za ka barni na ji da abu daya ba sai ka jefa mini damuwa da zullumi a cikin raina ko Kamalu."
Ya zauna jiki a sanyaye ya ce." Mama don Allah ki yi hakuri kin ji, ba zan kara ba."
Na ce." Haka kullum kake fad'i Kamalu amma kana fita zaka sanya kafa ka shure maganata, me yasa kake dukan yaran mutane kana d'auko mini magana, bakin jama'a a kanka, kowa Kamalu kowa Kamalu, so kake yi baki ya kamaka ko?"
"Mama ki yi hakuri ba zan sake ba."
Girgiza kaina kawai na yi cikin zuciyata nake masa addu'ar shirya. Na ce." Ka je ka zuba mini ruwa a buta zan wanke bakina."
Da sauri ya tashi ya d'auki buta ya fita. Sai gashi ya dawo yana cewa."Mama sun d'auke gugansu. Na tambayi Ummansu Saminu ta ba mu aro wai ba zata bayar ba tunda kina sana'a ki saya mana."
Kaina ne ya d'aure da jin maganar. Na ce." Umman Saminu ce din ta fadi haka?"
Ya ce." E, wallahi." Ban yarda ba sai na tashi na fita da kaina na tsaya a bakin kofar dakinta na ce.''Umma ina kwana?" Tana rabawa Yara karin kummalo ta amsa a dakile.
Na ce." Guga za ki d'an ban aro zan ja ruwa."
"Amina ki sayi guganki don Allah, kullum sai kin ara, bayan Allah ya hore miki, kada ki ce za ki yi gadara domin ba babanku ne ya saya ba, kowa da kud'inta ta saya. Yawan jan ruwan da Kamalu yake yi miki, duk gugana ya fatattake."
Kafin na ce wani abu. Ummansu Hadiza ta le'ko tana cewa." Kin ga zo ki d'auki nawa ki yi abinda za ki yi gugan me da har za ki tsaya ana yi miki gori akansa."
Hakan sai ya fusata Ummansu Saminu. Kamar dama kiris take jira, ta fito tsakar gidan tana cewa." Aikin banza da wofi. Murja sai yanzu ne za ki nuna mata k'auna waye bai san irin jifan da ki ke yi mata ba. Ba zan bayar da gugan ba, tunda ba ubanta ne ya saya ba.''
Ni dai ban ce komai ba na je na d'auki gugan na wuce bakin rijiya ina jin su suna ta masayar yawu. Na kud'ire a raina idan na fita kasuwa sayo kayan d'inki zan tsaya na siyo gugana da duk abinda na san za a yi mini gori a kansa.