GUDUN AURE

2

by @bintaumarabbale

'Yan uwa

Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,

duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.

Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su

Sandal flakes

Hawee

Gabgab

Halut

Dorot

Coconut chips

Dufr(farce)

Black khumra

Brown khumra

White khumra

Oil perfumes da

Body sprays

Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.

Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka

Call/WhatsApp

***

Location:Gonan Ganye,zaria

Kaduna state

Nationwide Delivery

2

Babanmu ya fito daga d'akinsa da shirin fita hannunsa da hulunun mutane da yawa. Ya tsaya yana tambayar ba'asin hayaniyar da suke yi. Babu wadda ta ba shi amsa a cikinsu. Kamalu ya ce." Saboda gugan jan ruwa ne, Ummansu Saminu ta c... Na daka masa tsawa sai ya yi shiru yana kallona. Na ce." Wuce ka je ka d'auko mini d'an bokitin nan.''

Ya bar wurin da sauri. Na dan risina a lokacin da ya kusa k'arasowa bakin rijiyar da niyyar fita. Na ce." Baba ina kwana"

Ya amsa ya dan tsaya yana kallona kafin ya ce." Ko zan sami dari biyar a wurinki Amina yau haka na wayi gari babu ko kwabo, wad'annan matan kuma suna nema su tona mini asiri da sanyi safiyar nan."

Na ce." Ina da ita Baba." Sai ya ce." To ki aiko Kamalu ya kawo mini, zan aike shi ya sayo mini shayi."

Na ce." Baba don Allah ka rage cin borodin nan kwanan nan fa ka tashi daga lalura basir ne da kai mai muni."

Ya ce." Ai kad'an nake ci, kuma shayin tsura nake sha ba madara.

Na ce." Dukda haka dai Baba, hanyar lafiya a bita da shekara."

"Amina abinda ya tashi basir din nan fa zama ne, da kuma cin rogo da gyad'a dana dimanta amma zan kiyaye dai."

Ya kama hanya ya fita yana gyara tarin hulun nan da suke hannunsa. Sai da na cika butocina da babban bokitina mai murfi sannan na mi'ka mata guganta.

Muna karyawa na ce." Wallahi Kamalu duk lokacin da ake hatsaniya a gidan nan na ji ka kara sanya bakinka sai na sanya an zane mini kai, kaine mai bakin magana ko?"

Shiru ya yi. Na k'araci yi masa fada bai ce uffan ba.

Na kunna kurfoti na d'ora musu ruwan wanka suka yi suka tafi makaranta.

Na had'a wankinmu da ya taru, na sanya sabulu a ciki na daure. Sannan na juye ruwan dana dora na je na yi wanka a gurguje na shirya da zan fita na yi musu sallama. Kafin na wuce kasuwar sai da na tsaya a shagon Babanmu na bashi dubu daya kamar yadda na yi masa alkawari kafin ya fita.

Da ya tambayeni Ina zan je na ce." Kasuwa zan je na sayo kayan d'inki.

To da yake motar sabon gari bata wahala ina fita titi na samu. Sai dai gosolw da ya ri'ke mu a hanya daidai sabon titi gidan 'kankara.

Na rasa cunkuson menene direban da yake jan mu ya ce.'' Rasuwa akayi nan cikin Sani mainagge shine Alhaji Tajo ya zo gaisuwa wad'annan zungura-zunguran motacinsa ne da jama'arsa."

Na ce.'' Na d'auka ai dan kasuwa ne ba 'dan siyasa ba ne."

Ya ce." E, d'an kasuwa ne sosai, ai ba sai lallai d'an siyasa za a yi wa wannan cunkoson ba. Shi ma babban mutum ne a garin nan."

Na girgiza kaina. Ban yi mamaki ba tunda sananne ne. Akwai d'aruruwan mutane dake 'kar'kashinsa. Bayan haka ma har kalandarsa na ta'ba kafewa a d'akina a lokacin da Abbansu Yusi ya yi aiki a kamfaninsa na sarrafa robobi. Kafin ya sanya soke sunansa daga jerin ma'aikatansa...

Matar da take zaune a gefana ta ce." Ai Kam gaskiya ba laifi wannan bawan Allan ya ma fi wani dan siyasar. Yadda yake taimako shi zai nuna maka cewa yana da tausayi da zuciyar imani idan har zai yi mulki za a ji dadinsa saboda gwanin adalci ne, muddin jama'a sun san abinda suke yi to zahiri shi za su dangwalwa kuri'arsu. Ni dai ko yanzu ya fito takara sai na za'be shi."

Cikin ha'ki'kancewa da kwarin guiwa ta kammala maganarta. Yadda ta dage take bayar da sheda akansa shi yake nuni da cewa lallai akwai abinda ya ta'ba yi mata ko wani nata.

Tunanina ya katse a lokacin da na ji matukin adaidaita sahun na mu yana cewa." Gaskiya ni ma 'kuri'ata tasa ce, domin yayyuna biyu a kafamninsa suke aiki, sun yi gida, sun yi aure kuma suna ri'ke da iyalinsa. Ko yau zai sallameka daga aiki zai baka kudin da za su isheka jari domin yin wata sana'ar, ai mutumin yana da girma da halin dattako wallahi."

Na ce" Ban tari numfashinka ba, irin wad'annan mutanan fa suna zama da mutum ne idan sun ga zasu amfanu. Babu yadda za a yi ku ce Alhaji Tajo ya cika cif kowane d'an Adam za ku same shi da da aikata wasu kusakuran. Ni dai wallahi duk inda za a je ba zan bayar da sheda a kansa ba. Domin ni ma mijina ya yi aiki a kamfaninsa na robobi kafin rasuwarsa, kuma daidai gwargwado ya yi masa bauta. Amma tashi d'aya ya sallame shi bai duba uzuri da lalurarsa ba. Kuma bai ba shi ko sisi ba."

Matar da take kusa da ni ta kalleni tana fad'in." Anya kuwa, gaskiya ban yarda da maganarki ba, mutumin nan adali ne, sai dai idan ma'kar'kashiya aka yi wa mijinki a kamfanin. zahirin gaskiya daidai gwargwado yana yi wa ma'aikatasa adalci.

Na ce." Ko annabawan Allah suna kuskure ballanatana mutum, ba wai na ce dole ku yarda ba ne, ni ma kuma babu lallai ne na aminta da hasashenku akansa ba domin lokacin da aka bawa maigidana takardar sallama mun shiga tashin hankali sosai, shiyasa duk lokacin da na ji sunansa sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi."

Direban ya dinga dariya yana cewa." Lallai hajiya kenan ko da zai fito takara ba za ki zabe shi ba?"

Kai tsaye na ce." Babu lallai gaskiya."

Har goslow din ya tsaigaita muna jayayya suna fad'in ra'ayinsu ni ma ina fad'in ra'ayina akansa. Direban dai in banda dariya babu abinda yake yi mana ganin yadda ni da matar dake kusa da ni fad'a ya kusa ya kaurewa sai ita ta gaji ta yi mini shiru, fad'i yake "Hajiya za ki yi kyau da aikin jarida na lura ba a kada ke a magana, ko dai 'yar siyasar ce ke me.'' Na ce." A a ban ta'ba sha'awar siyasa ba, asalima ni malamar makaranta ce. Ya ce." Haba koda na ji shiyasa duk maganganunki suke fita cikin azanci da hikima. To Ubangiji Allah dai ya yi mana za'bi nagari." Gabad'aya muka amsa da 'Amin."

**

Cikin kasuwar sabon gari nake kutsawa na sayo kayan dinki cikin sau'ki da rahusa. Shiyasa nake rufe fuskata da nikabi gudun had'uwa da idon sani, wasu mutanan basu da gadonka amma suna da gadon magana akanka. Na kammala duk abinda zan saya da ya danganci sana'ata. Na fito bakin kasuwar na sayi kayan miya na k'arasa 'yan kura na sayi kifi d'anye da sauran abubuwan buk'atata.

Na tari shatar adaidaita sahu muka tsadance zai kai ni har kofar gidanmu dake kofar kabuga d'ari takwas. Ya taimaka mini wurin sanya kayan a babur din. Na shiga na zauna babu jayayya domin na san ya yi mini adalci sosai a yadda mai yake tsadar nan wani ma zai iya cewa sai na bashi dubu daya da d'ari biyar.

Gidan namu a bushe da alama Babanmu bai yo aiken kudin cefane ba, tunda sau tari sai ya fita abinda ya samu zai aiko musu su sarrafa. Kowacce tana dakinta. Yara kuma sun fita. Na bude dakina na shiga na zube kayan a gefe. Na cire nikab da hijabi na zauna ina mayar da numfashi.

Yusi ya shigo a guje ya zube a jikina Yana dariya.

"Mama me ki ke sayo mini?" Tambayar da ya yi mini kenan. Na ce." Ina Kamalu yake? Ya zo ya d'auki wankin nan ya kai wa Halima tun jiya na fad'a mata zan kawo mata wanki."

Ya ce." Muna tasowa daga makaranta shi da Saminu suka d'auki buhu."

"Suka d'auki buhu suka je ina?"

Ya ce." Tsince-tsince suke yi a bola su kai kangon Jadda ya basu kudi."

Raina ya 'baci ainun! Na ce." Yusi kada ka yi mini karya ka fad'a mini gaskiya tun yaushe suka fara jari bola."

Ya ce." Ni dai na gansu kusan sau uku, ni ma na ce zan bi su, Saminu ya koro ni gida."

Sai kawai na ji idona ya ciko da ruwan hawaye. Wato duk ko'karin da nake yi akan tarbiyar yarana Saminu sai ya rugaza mini. Ba na son yawon nan da suke yi lungu-lungu. Abin har ya kai su d'auki buhu su hau bola suna suna tsince-tsince bayan duk rintsi ana basu abinci . Na tashi na nufi wurin Ummansu Saminu domin na ji shin ta san abinda yake faruwa.