WAYE SHI?{Behind the mask}

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑡𝑒𝑛:𝐼'𝑚 𝑛𝑜𝑡 𝑎 𝑝𝑒𝑟𝑣𝑒𝑟𝑡

by @autum17

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼

(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 1-6 𝑖𝑠 𝑖𝑛 𝑎𝑟𝑒𝑤𝑎 𝑏𝑜𝑜𝑘𝑠

(𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑑𝑎𝑦𝑎 𝑧𝑢𝑤𝑎 𝑠ℎ𝑖𝑑𝑎 𝑛𝑎 𝑎𝑟𝑒𝑤𝑎 𝑏𝑜𝑜𝑘𝑠)

Miƙewa yayi yana faɗin "sorry Dr ,wani uzuri ne ya kamani,zamu haɗu wani lokacin" ya ƙarashe maganar yana haɗa hannayen sa alamar ban haƙuri

Kallon sa kawai Haleemah take kamar ta samu tv,ya bata mamaki sosai! Ke nan duk maganganun da take beji ba? Wani irin tuƙuƙi zuciyar ta keyi but she masked it up with a smile "no worries" ta faɗa tana miƙewa ita ma . Gaba take yana biye da ita bayan ya kulle ƙofar office ɗin sai faman juya mazaunai take shikam bemasan tanayi ba dan gabaki ɗaya hankalinsa ya tafi akan Samha.

The nurses passing by seemed to notice what was going on,and ppl were already talking about it,ita kam Dr Haleemah Babu abinda ya dameta game da abinda mutane ke faɗa, they say' u can't shame the shameless ' wannan karin maganar yayi dai dai da Dr Haleemah

Duk tana lure da abinda ke faruwa,not just her a asibitin nan have feelings for Dr if the others are so afraid or so shy to express it why should she? Shin it's ba daban take dasu ba?

Duk inda suka wuce se kaji ana gaishe dasu, Dr Haleemah se ƙoƙarin shige masa take kamar akwai wani alaƙa a tsakanin su but there's none kowa ya sani.

The other female nurses na SE bin Dr Ahmad suke da namujiya kamar su haɗiye sa.

The male nurses ɗin kuma haushi suke ji sosai yanda kusan gabaki ɗaya all the females, idanun su na akan Dr Ahmad kamar su sauran ba maza bane

Dr Haleemah ta ɗan juyo tagani idan Dr Ahmad was even looking, Amma koda ta juyo, haushi ne ya turnuƙe ta,is this person alright?

Does he have no feelings? Ki take kamar ta rufe sa da duka,

She was so lost in looking at da batassn sun kawo karshen hallway ba kuma ya kamata su juya 'ƙum' kake ji Dr Haleemah ta gwarekai. Wata irin kururuwa ta saki saboda azaba,Dr Ahmad da ya shiga duniyar tunani ya juyo da sauri, amma other Drs were already there mata da maza se sannu ake tama Dr Haleemah. Sannu yayi mata shima kafin yayi excusing ɗin kansa ya fice completely

Ganin hakan wani kukan baƙin ciki Dr Haleemah ta saki. It was her friend Dr Ameena that helped her up zuwa office, sauran Drs sun bi su da sannu

Suna shiga office ɗin Dr Ameena ta zaunar da Dr Haleemah on one of the couches ta tafi ta ɗiba mata ruwa daga dispenser dake ɗakin

Kuka sosai Haleemah take "meyasa? Meyasa Dr Ahmad baze ganni ba ? Why can't he b lyk other men?" Sosai take risgar kuka tare da miƙewa ta na juyawa gaban Dr Ameena asking for answers

Ajiyar zuciya Dr Ameena ta sauke kafin ta zaunar da Dr Haleemah ta fara lallashinta bayan ta dena kukan ta miƙa mata ruwan ta sha sannan ta gyara zama tana faɗin"kina da duk abinda wani namiji ze gani yaji yana son mace Haleemah, shima Drn nan daki ke gani na tabbata ƙarfin hali kawai yake" sosai Dr Haleemah ta nutsu tana sauraren jawabin Dr Ameena"i can help you achieve ur goal" Dr Ameena tafaɗa tana kallon Dr Haleemah"faɗamin inaji" Dr Haleemah ta faɗa da sauri, matso wa Dr Ameena tayi whispering something (Dani dai banji ba ) cikin kunnen Dr Haleemah

Jim Dr Haleemah tayi tana kallon Ameena,why on earth didn't she think about it? Rungume Dr Ameena tayi cike da farin ciki "nagode sosai ƙawata,why didn't I think about it?"

"Because I'm here to that for you" Dr Ameena ta faɗa disengaging from the huge

Da sauri dr Haleemah ta kimtsa kanta tana faɗin bara inje in fara shiri,zan neme ki. Ta ƙarashe maganar tana fita daga office ɗin sannan ta rufo ƙofar

Wani irin ƙayataccen murmushi Dr Ameena ta saki sannan ta miƙe tana faɗin 'in ur dreams'

*********SAREESH******

About 12pm suka dawo cikin gidan,suna shigowa dai dai da sauko War Samha from upstairs binsu take da kallo irin na tuhuma, tun tuni da ta tura ma Dr Ahmad saƙo,she was waiting for reply but there was none and each passing minute increases her anxiety shine yasa ta fito down stairs to distract herself,se kuma ta haɗu da waɗannan kamar wa'yanda aka tsinto daga bola.

Kuma ta ga kwanakin nan kusan koda yaushe wannan me shuɗin idon na manne da mahmah, kuma yanzu ita da yayar tata don't get to spend much time together,she didn't like this

Tsuke fuska tayi tana ƙarasa saukowa,ido suka haɗa da Amreesh ta wani harare sa tana murguɗa masa baki.

Kau da kansa yayi kamar Be gani ba. The girl is obviously jealous he can see it.

Salmah ko SE rarrabar ido take kamar wata wacca tayi ma sarki laifi.

Shaking ɗin kanta Samha ta yi bayan idanun ta sun sauka a hannayen su dake sarƙe dana juna,ƙara kallon Amreesh tayi dake kallon Salmah,she seemed uncomfortable. '

'this person is changing my innocent sister, ba ze yiyu ba' ta ayyana aranta

"Are You okay" Amreesh ya tambayi Salmah,jin jina kanta tayi slowly idanun ta na dawo akan Samha, murmushi Samha tayi Sannan ta jawo Salmah tana faɗin " Mah-mah,muje zan nuna maki wani abu" A zahiri babu abinda zata nuna matan,she just wants to separate her from this person, murmushi Salmah tayi zata bi ta Amreesh yayi saurin riƙo ɗayan hannun ta, juyowa sukayi ita da Samha, yana kallon Samha yace"muje ki taya Ni wanka" yana gama faɗar hakan be jira abinda zata ce ba ya ɗauke ta chak yayi sama da ita

Samha tsaye take awurin kamar an dasa ta . How shameless!!! Ta faɗa tana buga ƙafafun ta in a frustrated manner ɗago idanun ta tayi ta kalli stairs case dai dai ya juyowa,yawani kashe mata ido! She couldn't believe it, mutumin da take ma kallon innocent Ashe Ashe, tsuki taja tana ƙunƙuni ta zauna saman ɗaya daga kujerun ta kunna tv ......

Tun lokacin da Amreesh ya ɗauke ta ta ɓoye fuskar ta,ta rufe idanun ta,she felt so shy,SE ɗaya ajiye saman gadon sannan ta buɗe idanun ta,they stared at each other kafin ta saki wani murmushin kunya tana rufe fuskar ta da pillow,he couldn't understand why the reaction?

Juyawa yayi ya shiga toilet,jin ya rufo ƙofar yasa ta tashi zaune,ta lula duniyar tunani har ya fito bata San ya fito ba. Se da yaƙaraso ƙamshin shower gel ɗin SA nashiga hancin ta, his hair was dripping wet, towel ɗaure a ƙugun sa. Sun yi kusa sosai har tanajin saukar numfashin sa a fuskar ta. Ɗan ja da baya tayi , her heart was racing,idanun ta sun fito saboda tsoro. Yayi hakan ne kawai dan ya gani if he will feel abinda yaji ɗazu but he felt nothing. Hannun sa yakai yana shafa gefen fuskar ta,rufe idanun ta tayi tana ƙara ƙame jikin ta wuri guda, jikin ta har ya fara rawa. Matso da fuskar sa yayi, slightly brushing his lips on hers,duk da haka ba abinda yaji. Ita kam lokacin da lips ɗinsa yayi brushing nata,she felt like an electric current running through her veins, numfashin ta kamar ze ɗauke. Ganin how uncomfortable she was yasa ya matsa.

Yana ƙare ma fuskar ta kallo " aren't you going to bath"? Taji saukar sexy voice ɗin sa a kunnen ta , da sauri ta miƙe ta faɗa baye ta rufe ƙofar tare da jingina bayan ta,tana sauke numfashi. Ta daɗe tsaye kafin ta cire kayan ta, ta shiga wanka.

Tsaye take gaban madubi yana shafe shafensa amma hankalinsa wasn't there at all. Daga karshe dai ya haƙura da tunanin ya ƙarasa abunda yake ya ɗauko wata riga orange color da wando jeans Black color yasa yana feshe jikin sa da turare.

He smelt so good and he looked....🤭

Bakin gado ya zauna yana ɗaukar wayarsa from bedside ya fara danna wa.

Jim tayi bayan tagama wanka . She didn't know what to do saboda bata da kaya a ɗakin and Bata sani ba ko Amreesh yana ciki. Tunawa da tayi he didn't have feelings ya bata courage ɗin fitowa daga bayen,gashin ta naɗe cikin towel tana cigaba da tsane gashin. Ga baki ɗaya jin ta take a takure,and she felt so shy Amma ta dake kawai. Miƙewa yayi ze fita,ita kuma ta kawo tsakiyar ɗakin kawai towel ɗin ya kunce ba burki se ga towel a ƙasa.and they both were looking at each other,ihu ta kurma ta juya da niyar koma wa toilet tsantsin tile ya kwashe ta,taje suuu zata faɗi, da zafin Nama ya isa wurin yana ƙoƙarin taro ta, but instead they both fell together his face buried in her chest. Ɗauke wa numfashin ta yayi na wucin gaɗi,cuz WHAT THE HELL!!!! Wannan ne karo na farko da Abu makamancin wannan ke faruwa. And she was naked under him, damn! Da sauri Amreesh ya ɗaga ta,he was so confused, hanyar fita yayi almost tumbling on his way out. He was blushing intensely,ga wani irin kunya da ya rufe sa,he had never seen a naked woman and today he was.... Fuskar shi yayi wani irin pink and his ears turned red. Zama yayi a palorn sama,ya zuba ma kansa ruwa a cup yana kwankwaɗa and the image of what happened reappeared in his eyes,ai ko ya sarƙe. Ga baki ɗaya ya rasa nutsuwar sa. Bayan ya dena tarin, jingina kansa yayi a headrest ɗin sofan ya rufe idanun sa, da sauri ta buɗe su ganin image perfectly carved in his head and weird ideas were forming in his head. "I'm not a pervert" ya faɗa da ɗan ƙarfi, karaf!, se a kunnen Dr Ahmad.

Ƙaraso wa Dr Ahmad yayi yana karantar yanayin Amreesh,duk fuskar sa tayi ja kamar tumatur, "Baka da lafiya ne zaki"? Dr Ahmad ya faɗa yana zama kusa da Amreesh, "I'm fine" yayi reply after a while

"To meyasa fuskar ka tayi jaa haka? And ur ears?? Wait don't tell me..." tuntsire wa da dariya Ahmad yayi har yana faɗowa daga kujerar,ya riƙe cikin sa ga hawaye na fita saboda tsabar dariya. Shi se yanzu ma ya gane abinda Amreesh yake nufi da 'i'm not a pervert ' Shidai Amreesh bece komai ba cuz he was still blushing,gawani ɗumi da fuskar sa tayi and to make it worse this fellow is laughing at him.

Se da Dr Ahmad yayi dariyar me isar da sannan ya tashi ya zauna yana dafa kafaɗar Amreesh yace "man ke nan Madam koro ka tayi daga ɗakin?" Ture hannunsa Amreesh yayi daga kafaɗar sa yana faɗin ''banson sa ido'' sakin baki Dr Ahmad yayi yace ''lallai,kaji Hausa,my man, amma dan Allah ka daure ka faɗamin abinda ya faru'' Ahmad ya ƙare maganar da wata sabuwar dariya,ɗan ƙaramin tsuki Amreesh yayi sannan yace ''leave me alone'' ya faɗa yana ƙara tsuke fuska tare da lumshe Idanun sa. Shiru wurin yayi after wards na Yan mintuna kafin Dr Ahmad ya gyara zaman sa in serious tone ya dafa kafaɗar Amreesh tare da faɗin ''man, yaushe zaka tafi zakee family residence "? Shiru Amreesh yayi kamar be jiba cuz shi har mantawa ma yake wai yana da wani family can, he has spent his life all alone ba kowan da ke neman sa and he was too cold to care, acikin familyn there's only one person he calls from time to time it's 'Old man zakee' granpa ɗin sa, jin yayi shiru yasa Dr Ahmad faɗin ''yakamata ka manta da komai,ka tafi can and introduce ur wife to them Dan ba asan Abinda gobe zata haifar ba! And ur dad also has the right to know,so pls'' Dr Ahmad ya faɗa duk da besa ran Amreesh zai amsa ba.bayan wani lokaci yaji yace'' i have no plans on going there anytime soon in bada wani dalili ba'' kallon sa Dr Ahmad yayi,yayi mamakin jinsa yayi magana me tsawon haka, ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin ''Allah ya kawo dalilin ''ganin kallon da Amreesh ya ke masa yasa shi saurin ƙarawa da "dalili me kyau'' ya ƙarashe maganar yana kashe masa ido guda, girgiza kansa Amreesh yayi yana faɗin 'Allah ya shiryeka' sannan ya miƙe yanufi ɗaki,se kuma ya tsaya for few seconds kafin ya juyo ya nufi downstairs. Shidai Ahmad se binsa yake da kallo yana gimtse dariya. Dawowa saitin Dr Ahmad yayi yace ''find school for that brat!'' "wa?" Dr Ahmad ya tambaya duk da yasan Samha yake nufi ''Samha'' Amreesh ya faɗa a taƙaice "meyasa'' Dr Ahmad ya sake tambaya ''tana damun mu nida matata '' ya ƙarashe maganar yana sauka down stairs

Ahmad kam shiru yayi kamar wanda ruwa ya cinye 'is this guy being possessive?' ke nan ansamu cigaba in his condition ' wannan tunanin yasa Dr Ahmad jin wani farin ciki. Miƙewa yayi ya nufi ɗakin sa his thoughts drifting back to Samha ko ina take? Tura ƙofar ɗakin yayi dai dai tazo fitowa sukaci karo, baya baya tayi zata faɗi yayi saurin taro ta by holding her waist,ita ko ta wani irin waro ido, saboda batay tsammanin zai zo ba , lokacin da Amreesh ya ɗauke Salmah suka tafi upstairs bayan tagaji da kallo she decided to go and check ko yayi mata reply,amma lokacin da ta hauro ta ɗan tsaya tana kallon corridorn wurin there were about three rooms and a corner '' to waɗannan ɗakunan na waye" tayi tambayar a fili kafin ta fara bi tana buɗe su one by one,ta fara daga corridorn inda yar kwanan nan ,tayi mamaki da taga study room ne, everything was neatly arranged, se ɗakin dake bayan nasu ba kowa ciki, se ɗakin su and the final one daya kasance na dr Ahmad, shiga tayi ɗakin dr Ahmad ɗin straight ta wuce gaban madubi inda taga turaruka daban daban, ɗauka tayi ta fesa kowane daga ciki, sannan ta haye gadon tana tsalle tsalle tana dariya she was so happy. Se da tayi ta gaji sannan ta sauka ta nufi ƙofa,har zata fita wani turare ya kama idon ta,komawa tayi ta ɗau turaren me suna 'heat' ya bala'in yi mata kyau,ga ƙamshin sa na daban '' na samu'' ta faɗa tana tura sa cikin aljihun wandon ta sannan ta nufi hanyar fita, tana tsaye bakin ƙofar aka turo ƙofar and here they are...

Kallon juna suke, their hearts beating wildly,ga ƙamshin turaren da ta baɗa duk ya cika masa hanci,yana rikita masa tunani,itako zuciyar ta se bugu take for 2 reasons. Na farko saboda turaren da ta ɗauka,na biyu kuma for the fact that she missed him and she didn't expect to see him and she missed his scent and everything about. Da sauri ta saita yanayin ta, sannan ta miƙe tsaye tare da cire hannun sa daga waist ɗin ta,shima gyara tsayuwar sa yayi sannan yace'' me kike anan?'' ɗago kanta tayi taga kallon ta yake,ta ɗan turo baki sannan a shagwaɓe tace '' kawai fah ina duba gidan ne'' kallon gadon sa da ta gama ɓatawa yayi sannan yace '' oh really? Idan mutum na duba gida se akace yayi ma mutane ɓanna ko?'' ya ƙarashe maganar in a sexy tone yana ƙara matso ta,ɗan matsa wa tayi tana faman zare idanu alamun rashin gaskiya tattare da ita, ''do You miss me"? Taji Muryar sa unexpectedly ''a'a'' ta faɗa tana zagaye sa ta nufi hanyar fita har ta riƙe handle ɗin ƙofar taji yana faɗin ''I missed you so much, a kowane dare da rana sai nayi tunanin ki'' tsaya wa tayi chak,jikin ta na shaking slightly,ga wani rush of excitement da take experiencing juyowa tayi slightly suka haɗa ido,wata irin kunya ta kama ta,ba shiri ta buɗe ƙofar ta fita da gudu kamar zata faɗi. Dariya Ahmad yayi,her reaction shows that she feels something koda Bata faɗa ba,and he couldn't help but feel happy.

Tana shiga ɗakin su ta faɗa saman gado ta rufe fuskar ta da blanket. Farin cikin ta knew no bound،bata taɓa tsammanin jin haka daga gare sa ba, kuma bata yi tsammanin zata yi farin ciki har haka ba, dariya take ta tiƙa ba ƙaƙƙauta wa. Ji tayi an ƙwanƙwasa ƙofa, gyara yanayin ta tayi Sannan ta je ta buɗe ƙofar,it was Amreesh. Kallon juna suka ɗan yi na few seconds kafin kowa ya wani basar....jin gina tayi da ƙofar sannan tace '' me kuma ya kawo ka?" Ta faɗa fuskar ta ba walwala,har yanzu bata manta da abinda yayi mata ba ai ɗaxu da yawani sunkuce Mahmah wai tazo ta tayashi wanka ba ko kunya. Be amsa ta ba, ya tura ƙofar ɗakin ya shiga tabi bayan sa da harara, thats all she could do ai.

Directly wardrobes ɗin su ya nufa ya ɗauko hijabi pink color wanda atleast ze kai guiwa sannan ya juya ze fita,ita ko Samha se ƙunƙuni take,se da yakai bakin ƙofar bayan ya buɗe sannan ya juyo yace ''zan yi maganin ki ai'' ta waro ido tana faɗin ''me nayi kuma''? Amma har ya tafi, ɗan ƙaramin tsaki taja sannan tace kanka ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya. Sannan ta ƙara komawa ta haye saman gado ta shiga duniyar imagination.

**********SALMAH******

Tun lokacin da Amreesh ya fita tayi sauri ta shige closet ɗin sa ta zaƙulo wasu riga da wando,da boxers cikin kayan sa tasa. Sannan ta fito tana tafiya kamar bata da laka, she felt so embarrassed da abinda ya faru ɗazu, gaban madubi ta tsaya ta shafa lotions ɗinsa sannan ta fara ƙoƙarin kwashe gashin ta,amma ta kasa gashi duk ta gaji. Buɗe ƙofar Amreesh yayi ya shigo suka haɗa ido ta madubi, sauke idanun ta tayi , ajiye hijabin dake hannun sa yayi saman gado kafin ya isa inda take,'' let me help '' ya faɗa yana zaunar da ita saman kujerar gaban madubi

Ɗan ranƙwafo wa yayi,hakan yasa ta ɗan riƙe numfashin ta,yana lure da hakan amma se kawai ya miƙa hannunsa ya dauki comb ya fara combing ɗin gashin ta his light touches sending shivers down her spine

SE da yagama sannan yayi styling ɗin gashin style me kyau. Murna tayi sosai bayan ya gama and she looked at it through the mirror

Shi dai ya ja gefe yana kallon yanda take murnar and he felt something shima kamar farin ciki

Bayan ta gama yaba kitson ta dawo kusa dashi holding his hand idanun su cikin na juna '' thank you '' tace tana sakin murmushin daya sa dimples ɗinta lotsawa ''uhm'' kawai ya faɗa yana shafa kanta, lumshe idanun ta tayi Sannan ta rungume sa,

Tsaye yayi without making any efforts to hug her back. Ɗago kanta tayi Sannan tace '' ya akai ka iya?"

''mama na ta koyamin'' ya faɗa looking distant. Ita da bata fahimci yanayin sa ba taƙara cewa ''yaushe za ka kaini in ganta''

''she's no more" ya faɗa yana kallon ta

''sorry'' ta faɗa hugging him tighter,shiru su biyu suka yi listening to each other's heart beat

Ganin lokacin sallah yayi yasa suka yi disengaging from the hug sannan ta riƙo hannunsa they both entered the toilet together sukayi alwala tare

Bayan sun fito excitedly tace ''idan ka dawo daga Masallaci, let's cook together pls'' ta ƙarashe maganar holding his arm making a very cute and irresistible gesture

''okay'' ya faɗa, tsalle ta fara tana faɗin ''thank you''

Fita yayi daga ɗakin daidai Dr Ahmad yana fitowa shima

Dariya Dr Ahmad ya fara, Amreesh ya tsuke fuska yayi gaba abinsa

Saida dr Ahmad yay me isar sa Sannan yabi bayan Amreesh tare suka fita.

Bayan Amreesh ya fita ɗakin su ta ruga taje ta kwaso kayanta, ta dawo da su ɗakin Amreesh

Sannan ta kabbarta sallah.

***********************

Lokacin da Salmah ta sauko bayan tagama Sallah,samu tayi duk suma suna ƙasa dr Ahmad da Amreesh ina one sit Samha on the other tana kallon cartoon, Amreesh da Dr Ahmad kuma suna magana

''Yaushe zaka koma office?'' Dr Ahmad ya tambayi Amreesh daya kafe wuri guda da ido

Jin tambayar Dr Ahmad,batare da ya kallesa ba yace 'monday' 'okay' Dr Ahmad yace Sannan ya maida hankali ga cartoon ɗin da Samha ke kallo

Kallon ta yayi daidai ita ma ta ɗan saci kallon sa,suka haɗa ido ,ɗauke kai tayi tana faman tsuke fuskar ta

Shi dai bai ce komai ba.

Ƙarasowa parlorn Salmah tayi,jin Amreesh zai koma office duk taji bata ji daɗi ba, gaida wa sukayi da Dr Ahmad,

Kafin ta je wurin Amreesh tana turo baki tace'' baka faɗamin zaka koma office ba ai'' ta ƙarashe maganar kamar zatayi kuka,ɗan satar kallon ta Samha tayi jin yadda take maganar

She really wanted to laugh, and idan ya tafi Ba ga taba? Me yasa mahmah zata wani damu?

Kallon ta Amreesh yayi kafin ya miƙe ya riƙo hannun ta suka tafi kitchen,Samha da Dr Ahmad sukayi exchanging ɗin glances each with their thoughts

Dr Ahmad yaji daɗi sosai there's really a massive improvement a condition ɗin Amreesh, ita kuma Samha she felt jealous Saboda,meyasa yanzu attention ɗin Mah-mah yafi karkata akan sa? Miƙewa tayi zata bi su, Dr Ahmad yayi saurin riƙo hannun ta se kiciniyar ƙwace hannunta take, amma takasa, se baki take, she really amused him,with a single pull ya jawo ta, ta faɗi zaune gefen da tana huci,'' calm down my lady'' Dr Ahmad ya faɗa yana kallon fuskar ta with an amused face ya ƙara da faɗin ''ki bar su,su sha love mana uhm? Don't be the jealous one!" A fusace tace '' I'm not jealous, he's taking my sister away! Duk kulawar ta, ta koma akan sa we rarely spend time together,koda yaushe yana nan biye da ita like a tail!!" Ta ƙarashe maganar tana kuka,its really rare to see her cry. Jikin Dr Ahmad ya yi sanyi ganin yanda take ƙoƙarin riƙe hawayen ta she meant every word she said daga ƙoƙon zuciyar ta

'' I'm sorry'' ya faɗa

''Bakomai '' ta faɗa tana share hawayen ta ganin Hakan yasa,yayi ƙasa da murya yace '' I Will love you,idan kin bani dama'' kallon sa tayi da sauri,se kuma ta fara ƙoƙarin ƙwace hannun ta ''dan Allah samha'' ya faɗa yana marai raice fuska

''sake ni'' ta faɗa tana hararar sa

Sakin ta yayi ta matsa nesa da shi

Amreesh lokacin da suka isa kitchen,ɗaukar Salmah yayi ya aza ta saman counter yana goge mata hawayen da suke ta zuba kamar an buɗe tap

''tell me,me yasa kike kuka?" Ya faɗa yana tsaya wa tsakanin ƙafafun ta, his blue eyes fixated on her

ƙasa tayi da kanta ba tare da wani ɓoye ɓoye ba tace '' I'm already missing you '' ta faɗa her teary brown eyes into his blue ones,kunya ta ji sosai,tana ƙoƙarin maida kanta ƙasa yayi saurin riƙo haɓar ta and she refused to meet his gaze

''look at me '' ya faɗa in a low and sexy tone,ɗagowa tayi daƙyar suka sake haɗa ido yace'' acikin kwanakin da suka rage before I resumed, I will b yours'' ya ƙarashe maganar yana ƙara matso da fuskar sa gab da tata har suna jin numfashin juna,ga wani irin luguden da zuciyar ta keyi,they stared at each other intently something like magnet pulling her in kafin slowly she placed her lips on his....