4
by @azizat
CHAPTER FOUR
"What!" Deej ta faɗa tana kallon Hadiza.
"Wasa kike, ko gaske?"
"Ina ruwana da shi da zan miki ƙarya"
Ɗan rage gudun motar ta yi tana raba hankalinta kan titi da kuma Hadizan da ta ce mata wai ta ga Yaya Khalil.
"Shi yasa ban faɗa miki ba sai da muka fito dan na san za ki ce sai mun je mun gaishe shi"
"Oh my God! Deeza, kuma ya gane ki? Me ya ce miki? Me kika ce masa?"
Hadiza ta ce "To albishirinki, ko gaishe shi ban yi ba"
Sai da Deej ta kusa taka birki tsabar ruɗewa.
"ba ki gaishe shi ba, as how?"
"To me zan ce masa?. Ya ɗauka ke ce, ya ce Nana, na ce masa ba ita ba ce, shikenan"
"Kut! da gaske Hadiza ba ki gaishe shi ba"
Hadiza ko a jikinta ta ce "Ban gaishe shi ba"
"Allah zan haɗaki da Hajiya ta min maganinki. Ba ki da mutunci, Allah"
"Eh ɗin!. Ni kai ni gida ina so na kwanta"
"kar ki sa na juyar da motar nan mu koma Asibiti, kuma na kaiki har office ɗinsa ki gaishe shi"
"Wallahi kar ma ki fara. Kin san halina"
Haka dai suka yita faɗa har Khadija ta kawota gida. Tsabar haushi ko ciki bata shiga ba ta ce ta gaishe mata da Umma, Hadiza ta ce ba za ta gaisar ba.
Lokacin da ta shigo gida Umma tana zaune a falo tana saka zip a rigan Hajiya.
Gaishe ta ta yi za ta wuce ɗakinta Umma ta ce ta ajiye mata Maltina da Madara a ɗaki ta je ta sha ta kwanta.
"Kai! Umma, nagode"
"idan kin yi sallah sai ki kwanta ki huta"
"To" ta wuce ciki.
Tana shiga ta ga flask ɗin abincinta da kuma Maltinan gwangwani guda biyu da madarar ruwa na Peak guda ɗaya.
cire kayan jikinta ta yi ta saka na zaman gida sannan ta zauna ta buɗe flask ɗin abincin, farar shinkafa ne da miyar Ugwu da Alayyaho da manyan bushashshen kifin Catfish guda biyu.
Ko dan wannan kayan daɗin ai dole ta cigaba da bayar da jininta.
Ta yi murmushi ta ɗau cokali ta zuba abincin kaɗan a plate tana ci tana kora Maltina.
Washegari tun da safe Umma ta ce mata za su je gidan Hajiya. Hadiza ta amsa da to.
Da wuri suka gama abincin dare. Biyar da rabi ma suna cikin Keke.
Aka sauke su a bakin gate dai-dai lokacin da wata haɗaɗɗiyar mota ta fito daga gidan. Ko Uncle Mustafa ne ko wani ne daban Allah ne ya sani.
Hadiza tana ɗauke da ledar kayan Hajiya suka shigo gidan. Masu gadi suka fara gaishe da Umma suna mata ya shirin Azumi. Ta amsa musu fiska a sake.
Haka suka wuce ɓangaren Hajiya Umma tana lura da sabbin tsare-tsaren da aka yi a gidan dake ta kwana biyu bata zo ba. Shekaru sun ja, yadda fasalin gidan nasu yake sadda Alhaji yake raye yanzu duk an chanja komai.
A babban falo suka tadda Hajiya da masu aikinta da wasu yaran 'yan'uwa da suke zama a gidan tana zuba bayani. Kamar dai wani aikin ta saka su basu mata dai-dai ba.
Suna shigowa da ta ɗaga ido ta kalli Umma sai ta fara faɗin "Lale Marhaban! Ashe matar Principal ce a gidan"
"Ma'u tashi maza ki kawo musu ruwa"
Hadiza ta ƙariso wajenta ta ɗan risina ta gaisheta. Hajiya ta ce "ke kuma daga ina na ga kin yi wani fayau dake. Ba a biya Ubanki albashi bane?"
Hadiza da ta riga ta saba da irin maganganun Hajiya ta ce "Eh kuwa, shi yasa na zo na kwashe Gwalagwalanki mu samu na siyan kayan Azumi" hanyar ɗakin Hajiya ta nufa Hajiya ta harzuƙa ta ce "Wallahi kika taɓa min wani abu a ɗaki sai na saɓa miki. Dukiyar da ke ɗakina ya fi Albashin Ubanki na shekara hamsin"
Hadiza ta ce "Iyi!" "shi yasa zan kwashi rabona ai tun kafin ki gangara"
"Ke Hadiza kar ki shiga min ɗaki, Ma'u kamo min ita" Hajiya ta faɗa hankalinta a tashe dan Hadiza ta san komai na ɗakin nata. Har inda take saka wasu abubuwanta da masu aikinta ba su sani ba ita ta sani. Yarinyar kamar Aljana.
Umma tana jinsu bata ce komai ba. Tunda ta samu Hajiya ta amsa gaisuwarta sama-sama ta ja ta yi shiru.
Ganin Hadiza bata fito ba sai Hajiya ta tashi da kanta ta yi ciki.
Tana shiga ta ga Hadiza tana jera mata kayan da suka kawo a Closet ɗinta.
"Uwarki ce ta ɗinka ko ke?"
Hadiza ta ce "Umma ce ta ɗinka miki da hannunta mai albarka"
"Ba ta rantse ba za ta sake min ɗinki ba"
"Abba ne ya lallaɓata ya ce ta ɗinka miki ba dan halinki ba. Dan haka idan ya zo ki masa godiya"
"Ja'ira, mu ga Leshin?"
Hadiza ta warware mata doguwar rigar Leshin da aka yi mata ɗinkin BouBou, ya yi kyau sosai.
Hajiya ta shafa Lace ɗin ta ce "Wannan ai ƙaramar ce, dubu sittin ake sai da ita"
Hadiza ta juyo ta ce "To Hajiya idan ya siya miki Original ɗin nawa zai rage a Albashinsa"
"Hajiya Hadiza Gambo Tafida ba ta saka jabun kaya"
Hadiza ta karɓi kayan daga hannunta ta ce "shikenan, barin je na bawa Maman Ma'u kyautan kayan. Kai! Baaba Asabe zan kai wa tunda size ɗinku ɗaya ne"
Hajiya ta ce "Za kuwa ki ci gidanku. Ki yi maza ki fito bana son bincike"
"Aww! wai Dalolin (Dollars) da kike ɓoyewa ne ba kya so na taɓa ko me?"
"Ja'ira wa ya faɗa miki akwai Dollar a ɗakin nan"
"ƙanshinsu nake ji tunda na shigo" Hadiza ta faɗa tana dariya.
"wuce, maza ki fita min daga ɗaki, Ja'ira kawai"
Hadiza ta sa dariya. Har suka fito dariyan take. Tun tana jin haushin yadda Hajiya ke yawan kushe Abbanta har ta zo ta dena, duk abinda za ta faɗa za ta bata amsa dai-dai da ita.
Shi yasa mutane ke cewa Hadiza ce dai-dai da Hajiya, dan ita ce ke iya mayar mata magana dai-dai abinda ta faɗa.
Da suka fito sai Hajiya ta cewa Umma kayan da aka kawo kala ukun duka ba su wuce dubu ɗari da hamsin ba.
Umma ba ta ce komai ba. Hadiza ta ce "Hajiya, daɗin abin dubu ɗari da hamsin ɗin halaliyarsa ce ba roƙo ya yi ko sata ya samo su ba"
Dake dai Hajiya ta dage sai ta saka Umma magana, sai ta kalleta ta ce "Ki ce masa ya yi ƙoƙari, tunda ya zama Principal ya dena aiko mana da tsumma"
Daga yanayin fiskar Umma za ka ga ranta ya sosu da abinda Hajiyar ta faɗa.
Dake Hadiza tana danna waya bata ji me Hajiyar ta ce ba balle ta bata amsa.
Umma ta daure ta ce "Hajiya, mun gode. Za'a isar masa da saƙonki"
Hajiya ta yi shiru dan ba amsar da ta ke so Umman ta bata ba kenan. So take ta fitar da abinda ke cikinta ta samu damar cigaba da yaɓa mata magana.
Hadiza dake zaune akan kujera tana chatting sai ta lura da wani pink jaka mai kyau a kusa da ƙafarta. Ɗaukan jakar ta yi tana tambayar yaran dake kallo a falon na waye?
Wata a cikinsu ta ce "na Baby Fadila ne".
Hadiza ta buɗe jakar ta fito da littafin dake ciki da kuma ƙaramin Teddy Bear, da babyn Barbie.
FADILAH IBRAHIM TAFIDA aka rubuta da CAPS letter a jikin littafin.
Daga gani ta san Ubansu ne ya rubuta sunan. Dama an ce Likitoci ba su iya rubutu ba. Ji bi yadda ya wani rubuta R ɗin kaman wani 8 ta faɗa a zuciyarta tana tsaki. Wani abu ne ya daketa. Sai yanzu da ta riƙe textbook ɗin sannan ta fahimci ƙanshin da ta ke ta ji tun da ta zauna a kujerar iri ɗaya da ƙanshin dake jikin littafin yarinyar.
Ta taɓa jin irin ƙanshin nan ai.
Ta sake kai littafin hancinta tana shaƙar ƙanshin, a hankali sai ta tuno haɗuwarsu a Asibiti ranan. Duk da briefly suka haɗu amma a hakan sai da brain ɗinta ya iya connecting ƙanshin wancan mutumin da kuma ƙanshin dake jikin littafin hannunta.
Ta yi saurin mayar da littafin cikin jaka ta tura jakar kusa da yaran dake kallo.
Ma'u ta ce "Mantawa suka yi ɗazu da Daddynsu ya zo ɗaukansu"
Hadiza ta kau da kanta gefe dan ba ruwanta da shi balle abinda ya shafi 'yarsa.
Hadiza da Umma ba su bar gidan ba sai bayan Maghriba. Da suka shiga Keke Umma ke tambayarta me Hajiya ta ce gameda kayan da suka shiga ɗaki?.
Hadiza ta ce cewa ta yi sun yi kyau.
Umma ta girgiza kai kawai dan ta san Hajiya kam ba za ta taɓa buɗan baki ta yaba ɗinkin ba.
***
AISHATU IBRAHIM TAFIDA shine cikakken sunan Umman Hadiza. Mahaifinsu Alhaji Ibrahim Tafida babban ɗan kasuwa ne da ya yi fice a zamaninsa a cikin garin Kaduna. Mutumin Zaria ne, kasuwanci ya zaunar da shi a Kaduna har ƙarshen rasuwarsa.
Matarsa ɗaya, wato Hajiya Hadiza Gambo. Allah ya azurtasu da 'ya'ya 6, maza 4 da kuma mata 2. Bello shine babba, sai Usman, Halliru, Fatima, Mustafa, da kuma autarsu wato Aishatu.
Tun kafin Bello ya gama karatun Degree ya buɗe Kamfaninsa. Yana gama Makaranta ko Bautar ƙasa bai fara ba ya auro Maryam. 'yar Jigawa ce a ƙaramar hukumar Kazaure, amma iyayenta a Dutse suke.
A shekarar farko da aure ta haifi ɗa namiji ya ci sunan Alhaji Ibrahim Tafida, ana kiransa da Khalil.
Khalil shine jikan gidan na farko dan haka ya taso cikin gata, Alhaji da Hajiya duk suna matiƙar sonsa, yawanci ma a gidan Kakkanninsa yake wuni.
Khalil na shekara uku Allah ya yiwa Bello rasuwa. Wasu kaya ne da ya yo order su aka ce ruwa ya cinye. Daga jin wannan labari Heart Attack ya kama shi ya yanki jiki ya faɗi, kafin a kaishi Asibiti ya cika.
Wannan mutuwa ta girgiza Matarsa da Iyayensa sosai. Lokacin Maryam na da ƙaramin ciki amma saboda tashin hankali kafin bakwai ɗin rasuwan cikin ya zube.
Da ta gama Takaba ta ce za ta tafi sai Hajiya ta hanata tafiya. Ta zauna a Family House har shekara ɗaya kafin daga baya Iyayenta suka ce sam ba su yarda ba ta dawo gida har yanzu da ƙuruciyarta. Abin bai yiwa Maryam daɗi ba dan Hajiya ta hanata tafiya da Khalil. Hajiya ta cigaba da renonsa yana shekara huɗu da 'yan kai a lokacin.
Bayan Maryam ta koma Dutse sai ta koma Makaranta, ta je ta yi Nursing School. Sai da ta gama kafin ta sake wani auren a nan cikin Dutse. Allah ya sake azurtata da haihuwan 'ya'ya 4, uku mata, ɗaya namiji.
Shi kuwa Alhaji Usman Tafida wato ƙanin Bello kasuwanci ne ya kai shi Lagos da shi da iyalensa. Yana da Mata ɗaya da 'ya'ya shida. Ya sha yunƙurin zai ƙara aure amma Hajiya tana hanawa. Dake matarsa ta samu ɗaurin gindin Hajiya daga ta ji ƙishin-ƙishin yana neman aure sai ta kira Hajiya ta faɗa mata. Nan fa Hajiya ta kasa ta tsare har sai ta saka shi ya fasa. Yana matuƙar girmama Hajiya shi yasa ba ya son abinda zai ɗaga mata hankali.
shi kuwa Alhaji Halliru Tafida riƙaƙƙen ɗan Boko ne kuma ɗan Siyasa. Babban Barrister ne da yai fice a Arewacin Nigeria. Matarsa Ɗaya wato Zuwaira, 'ya'yansu 4. Sadiq shine babba, sai Nana Khadija da ta ci sunan Hajiya, sai kuma Aliyu, da autarsu Zainab, suna ce mata Zee Baby.
Hajiya Fatima Tafida kuma tana aure a Abuja. 'ya'yanta 5, uku Mata, biyu Maza. Wani babban ɗan Siyasa ta aura. Mijinta ya yi Senator a lokacin Mulkin Shugaba Obasanjo, kuma har yanzu ana damawa da shi a harkar Siyasa. Matansa dai a yanzu uku ne, Fatimar ce dai Uwargida.
Alhaji Mustafa Tafida kuwa shi ya gaji kasuwancin Mahaifinsu. Bai yi karatu ba dan ko Sakandare bai gama ba, amma ya ci moriyar shiga jikin Alhajinsu da ya yi, dan ya koyi kasuwanci a wajensa sosai, har ya zamana ma tun kafin rasuwarsa kusan shi yake jagorantar komai.
Mustafa ne dai ya ciri tuta ya bijire wa dokar Hajiya ya auri mata biyu. Da ke shima taurin kai gareshi kamar Hajiyan bai ma faɗa mata zai yi aure ba sai da aka ɗaura auren ya shigo ya ce mata ya yi Amarya. Hajiya ta dinga kumfar baki tana bata yarda ba musamman saboda Aurensa na fari ma ko shekara huɗu bai kai ba. Shi kuwa ya tashi ya kaɗe jikinsa ya ce ta sa masa Albarka kawai aure kam an riga an ɗaura. Yanzu haka Hajiya ta fi shiri da Amaryar akan Uwargidan.
Alhaji Mustafa shi ya ci gadon ɓangaren Alhajinsu dan haka tsarin ginin kawai aka canza aka mayar da shi beni mai hawa biyu. A nan yake zaune da matansa duka biyu.
Aishatu Tafida ita ce Autar gidan. Alhaji na matuƙar sonta, kuma ya sakaltata ba kaɗan ba. Dan a kaf gidan idan kana so ka ga fushin Alhaji to ka taɓa Aishatu da ake kira Ummi saboda sunan Mahaifiyar Alhajin ta ci.
Tana aji shida a Sakandare ta kamu da son wani sabon Malamin English ɗinsu ɗan Bautar ƙasa. Aka ci sa'a shima Malam Salisun ya ji yana sonta dan Aishatu Tafida kyakykywace sosai ga ta da baki. Sai dai, bai bayyana mata soyayyarsa ba saboda na farko ita ɗalibarsa ce, na biyu kuma an faɗa masa ita ɗin 'yar gidan masu kuɗi ce.
Wannan bai dakatar da Aishatu ba dan ita ce bashi letter da cards a duk sadda ta samu dama.
A haka dai yana kakkauce mata har suka zana WAEC, sai a lokacin ya bayyana mata soyayyarsa. Dake boarding School take tana komawa gida ta ce wa Alhajinsu ba za ta cigaba da karatu ba lokacin da yayyun ta suka kawo mata maganar rubuta JAMB. Da aka tambayeta dalili ta ce aure za ta yi.
Dake yayarta Fatima ma daga aji ɗaya a Jami'a ta yi aure sai Alhaji bai wani ɗaga hankalinsa ba. Ya ce idan tana da wanda take so sai ta turo shi. Caraf! Hajiya ta ce ai 'yar gida za a yi. Akwai wani ɗan yayan Hajiyan daga Katsina da ya dawo daga ƙasar waje sunansa Isma'il. Wai dama ya mata magana yana son Aishatun kuma sun riga sun tattauna da yayanta. Ita kuwa Aishatu ta ce fau-fau bata san zance ba, tana da wanda take so ba za ta auri ɗan'uwanta Isma'il ba.
Alhaji ya ce ta turo shi. Ta je Makarantarsu dan Service ɗinsa da ɗan saura kafin ya gama. Da suka haɗu ta ce masa Alhajinsu na son ganinsa. Malam Salisu ya shiga damuwa ita kuwa ko a jikinta dan ta san Alhaji ba zai ƙi shi ba. Ta bashi address ɗinsu ta faɗa masa ranan da zai zo.
Malam Salisu ya ɗauki wani abokinsa suka sha manyan kaya suka tafi gidansu Aishatu. Sai da suka zo gidan ne ma ya fara mamakin me Aishatu ta gani a jikinsa ta liƙe masa, dan kuwa gidan data fito da kuma na su gidan akwai tazarar arziƙi sosai, ko kusa babu haɗi. Aishatun da yake gani a aji fa asalin 'yar gata ce.
Da aka iso da su wajen Alhaji Tafida sai ya musu tarba mai kyau. Ya tambayeshi shi mutumin ina ne? ya ce daga Kano. cikin bayanin da ya masa sai Alhaji ya fahimci ai ya san gidansu ma, dan Kakansa babban Malamin ɗariƙa ne a Kano, kuma duka 'yan gidan Malamai ne, Mahaifin Salisun ma Malami ne sosai.
Ya tambayeshi me yake yi yanzu? Salisu ya ce yana Bautar ƙasa ne saura wata ɗaya su gama. Alhaji ya ce madalla suka rabu cikin mutunci. Amma zance bai yiwa Hajiya daɗi ba da ta ji cewa Malami ne, bautar ƙasa ma yake yi. Ta ce allankatafir bata yarda ba.
Wasa-wasa fa ƙaramar magana sai ta zama babba. Alhaji ya ce saboda dattakun gidan da Salisu ya fito zai bashi Aishatu amma ita Hajiya ta ce 'yarta ba za ta auri Ticha (Teacher) ba.
Kuma aka yi sa'a kuwa Malam Salisu na gama Service ɗinsa ya samu aikin koyarwa a wata Sakandaren Gwamnati a nan garin Kaduna. Dama tun asali yana da sha'awar aikin koyarwa.
Tun ana magana ƙasa-ƙasa har Hajiya ta fito fili ta sa aka kira mata Malam Salisu ta gargaɗeshi akan ya rabu da Aishatu.
Ya ce Insha Allahu zai yi hakan.
Ita kuwa Aishatu sam ta ƙi yarda da maganan Hajiya, ta ce ba za ta auri kowa ba in ba Malam Salisu ba. Haka aka yita jan magana har shekara ɗaya ba a cimma matsaya ba. Ita Hajiya ta ƙi, itama Aishatu ta ce ba za ta janye ba duk da kuwa shi Salisun ya nemi su rabu tunda Hajiya bata so.
Da Alhaji ya ga Aishatu tana zaune a gida zaman banza ta ƙi karatu kuma ta ƙi amincewa da kowa sai kawai ya ce da Hajiya zai yi magana da Salisu ya turo magabatansa kawai.
Abu dai ya jawo faɗa sosai a tsakaninsu dan Hajiya fa ta ƙi wannan haɗin, daga ƙarshe babu abinda za ta iya haka Alhaji ya mata ƙarfa-ƙarfa ya bada auren Aishatu wa Malam Salisu.
Aka ɗaura auren Aishatu Ibrahim Tafida tana shekara 19 wa Malam Salisu Muhammad Zango yana Saurayi ɗan shekara 28 a lokacin.
Dake Hajiya bata son auren sai sauran 'ya'yan nata ma suka goya mata baya. Barr. Halliru Tafida ne kawai ya bada support ɗinsa ya ce Aishatu tana da 'yancin auren wanda ta ga dama tunda dai a dokar Nigeria adult ce, tana da 'yancinta.
Haka aka yi aure Aishatu ta tare a gidan da Salisu ya kama musu one bedroom, ciki da falo dai-dai ƙarfin albashinsa. Alhaji ya bashi kyautar gida ma 3-bedroom flat su zauna a ciki ya ƙi karɓa. Hakan ya ƙara jaddada masa Salisu mutumin kirki ne, ba kwaɗayi ya kawo shi wajen Aishatu ba.
Wannan shine mafarin gaban dake tsakanin Hajiya da Umman Hadiza.
Bayan aure Aishatu da mijinta suna zaman lafiya. Ya ce mata zai siya mata form ɗin NCE ko Nursing ta cika ta ce ba za ta yi karatu ba. Dama tun asalinta bata da dogon burin yin boko. A gidan hayar da suke ta fara koyon ɗinki a wajen wata maƙociyarsu, Igala, ta iya ɗinki sosai.
Bayan wata huɗu da aure Aishatu ta samu ciki. Cikin ya zo mata da sauƙi, ba wani laulayi mai zafi.
Suka cigaba da renon cikin lafiya-lafiya har Allah ya sauketa wata ranan Alhamis da daddare, kusan Asuba.
Da safiyar Jummu'ah bayan an sallamosu Malam Salisu ya wuce gidansu Aishatu dan ya sanar da su. Ya tarar Alhaji baya ƙasar ya sa aka masa sallama da Hajiya.
Da ya shiga babban falonta sai ya gaisheta cike da girmamawa. Har gobe yana mutunta Hajiyar saboda ya san darajar uwa.
Ya ce mata Aishatu ta haihu, an samu takwara, ya mata huɗuba da suna HADIZA, inkiyarta kuma LAILA.
Buɗan bakin Hajiya ta ce bata son iyayi. Ita bata saka shi yi mata takwara ba, tun da dai sun bijire mata sun yi auren a sauka lafiya.
Jiki a sanyaye Malam Salisu ya bar gidan. Ya ɗauka tunda Aishatu ta haihu Hajiya za ta sauko ta dena fushi da su, ashe abin ba haka bane...
# BestHausaNovel2025
©MarubuciyaAzizatHamza2025