FreeArewaPen original
KHADIJAH ko HADIZAH
- 1views
- 46chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Youtube: Marubuciya Azizat Hamza ***: Azizat_Hamza Tiktok: Marubuciya Azizat Instagram: Marubuciya Azizat ***: ***
Sample · 1
CHAPTER ONEKaduna, Nigeria.***DR. I. B. TAFIDA ya tsani ganin Mace akan Acaɓa.A ra'ayinsa, machine ba abun hawar Mata bane kwata-kwata. Wannan ya sa lokacin da wata Budurwa ta zo ta yi over-taking motarsa da gudu sai da ya ja doguwar tsaki a ransa yana mamakin wannan gangancin. Wai yaushe ma Matan Hausawa suka fara tuƙa Machine ne? ya tambayi kansa duba da cewa yarinyar dake falla gudu akan machine ɗin sanye take da Hijabi. Hijabin mai hannu ne wannan ya bata damar riƙe kan machine ɗin da kyau dana falla gudu. Rabin wandon Jeans ɗinta baƙi dake bayyane saboda tattare hijabin da ta yi ta zauna a kai ya saka Dr. I. B. Tafida ganin sarƙar ƙafa (leg chain) da ke ƙafarta. Subhanallahi!. Shima kamar gama-garin mutane yana da ayar tambaya ga duk macen da take saka sarƙar ƙafa ta fito waje. Wai minene amfanin saka hijabin nata tunda dai gashi ta kwaye rabin ƙafarta ta bayyana skinny jeans ɗin da...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.