KHADIJAH ko HADIZAH

5

by @azizat

CHAPTER FIVE

Bayan kwana biyar da haihuwan Hadiza matar Barr Halliru Tafida itama ta haiho 'yarta ta biyu a lokacin. Nan fa 'yan'uwa aka manta da batun haihuwar Aishatu. Dama tunda ta haihun mutane kaɗan ne suka leƙata. Wanka ma sai wata babbar yayarsu Malam Salisun ce ta zo daga Kano take wa yarinya wanka. Ga 'yan'uwanta nan jibge a Kaduna da Zaria amma babu wanda Hajiya ta aiko.
Da ɗan abinda Malam Salisu ya tara suka shirya 'yar ƙaramar Walimar suna.
Abin mamaki mutum biyu ne suka zo mata, suma kuma da suka zo sai suka ce wai gida ɗaki ɗaya ba zai ɗauki Familyn Tafida ba shi yasa Hajiya ta ce kowa ya yi zamansa su da suka zo ma sun wakilci sauran.

Dake itama Aishatun akwaita da zuciya sai ta ce ba komai ta gode amma su tattara kayan da suka kawo su kai can Tafida House su ajiye gidanta ɗaki ɗaya ne ba zai iya ɗaukan manyan kayan da suka kawo mata ba. Da suka ƙi komawa da kayan sai ta kira wasu yaran maƙotansu guda biyu ta basu kuɗin machine ta ce su mayar da kayan. Da Malam Salisu ya zo wata ƙanwarsa ta faɗa masa abinda ya faru sai ya ringa faɗa ya ce bata kyauta ba.
Ita kuwa ta ce da ta karɓi kayan da Hajiya ta aiko mata gara ta zauna bata da komai.

A ɓangaren 'yar da aka haifa a gidan Barr. Halliru Tafida kuwa, ranan suna aka sha shagali na ban mamaki. Har da raba souvenirs kala-kala ɗauke da hoton yarinyar da ta ci sunan Hajiya, NANA KHADIJA.

Har gida aka zo aka gulmatawa Aishatu hidimar da aka yi, aka kawo mata Casette ɗin video coverage na bikin sunan, ta kalli yadda Hajiya ta sha gwagwgwaro tana ta jefa Nera tana rawa. Abinda ya ɓata mata rai ma shine, hatta yayarta Fatima dake Abuja ta zo sunan 'yar yaya Halliru amma bata zo nata ba.

Lokacin da Alhaji ya dawo ya ji labarin abinda ya faru sai ya fusata matuƙa. Ya yiwa Hajiya faɗan da bai taɓa mata ba. Da kansa ya sa Direbansa ya kawo shi gidan Aishatun. Da ya zo aka kawo masa  yarinya ya karɓeta ya mata addu'a.  A take a wajen ya bawa Baby Hadiza kyautar wani ƙaton gonarsa. Aishatu ta masa godiya.
Bayan ya tafi daga baya sai ga Direba ya dawo cike da kayan abinci, kayan Yara har da babban Rago.
Da dare Malam Salisu ya je ya yiwa Alhaji godiya.
Lokacin da kuɗin hayarsu ya ƙare a gidan da suke sai Malam Salisu ya kama musu gida mai ɗakuna biyu da falo har da kitchen. Aishatu ta yi ta faɗa wai ya zai kashe kuɗi ya kama babban gida bayan ya san yanzu hidima sun ƙaru musu. Ya ce ba komai, yana so Hajiyarsa, kamar yadda yake kiran Hadiza ta taso a gidan da zata samu filin wasa ne.

Kwata-kwata ba ya son a ce ya gaza wajen hidimtawa iyalinsa tunda ya san gidan da Aishatu ta fito ya fi inda ya ajiyeta nesa ba kusa ba. Dan haka bayan koyarwa da yake yi yana karɓan albashi, sai ya fara fita Kasuwa yana siye da siyarwa. Tun ba shi da shagon kansa har ya ɗan kama kiosk, daga nan kuma har ya kama proper shago, idan ya taso daga Makaranta sai ya wuce Shagon. Daga safe zuwa rana kuma akwai yaron dake zama masa.

Haka rayuwa ya dinga tafiya Malam Salisu yana nunawa Hadiza gata sosai, duk wani kayan yayi na yara sai ya nemi kuɗi ya siya mata. Duk Jummu'ah idan zai je gaishe da Alhaji da ita yake zuwa. idan suka je sai Alhaji ya ɗauketa ya ɗaurata a kan cinyarsa yana cewa Amaryarsa kullum ƙara girma take.
Dake an fi kawo Hadiza wajen Alhaji sai Alhaji ya fi sabawa da ita akan ɗaya jikar tasa wato Nana Khadija. Ga shi dama ita Hadiza yarinya ce mai shiga rai akwai ta da wayo da ƙiriniya, ga ta kullum cikin dariya. ita kuwa Khadija ko an kawota ba ta yarda da mutane, sai kuka idan an ɗauketa. Itama uwartata saboda fita aiki take kawota gidan. Hajiya ta goyeta ta yita lallashinta tana mata wasa. Amma fa ba za ka taɓa ganin ta ɗauki Hadiza ba, balle har ta goyeta.

Lokacin da Aishatu ta yi Freedom a wajen da take koyon ɗinki, Alhaji da kansa ne ya siya mata sabon Keken ɗinki mai kyau. Shima Malam Salisun dama yana ta tara kuɗi zai siya mata sai Alhaji ya riga shi.
A cikin gida take ɗinkinta, kuma ba laifi tana samun mutane dan ta iya ɗinki sosai.

Hadiza na shekara biyu Aishatu ta yi ɓari. Suka ɗauki ƙaddara ba su faɗawa kowa ba.

Da aka tashi saka Hadiza a Makaranta lokacin tana shekara uku sai Aishatu ta ce a mata Register da Laila kawai kar a sa Hadiza. Shi kuwa Malam Salisu ya ce Hadiza ne sunanta kuma suna ne mai kyau dan haka ya mata Register da Hadiza Salisu Zango.

Wasa-Wasa a tsakanin lokacin da Hadiza ta cika shekara bakwai Aishatu ta yi ɓari har sau uku. Na farkon ba su faɗawa kowa ba, amma da na biyu dana uku duk Malam Salisu yana zuwa ya faɗawa Alhaji amma ko sau ɗaya Hajiya bata taɓa zuwa ta musu jaje ba.

A lokacin ne kuma Alhaji ya fara jinya aka fita da shi Germany suka je dai jiki babu kanta Alhaji ya ce a dawo da shi gida. Sati biyu da dawo da shi gida kuwa Allah ya masa rasuwa.

Kaman kowanni Musulmi bayan rasuwar aka tara iyalensa aka fara maganar raba gado. Lokacin da aka zo ana tattara dukiyar Alhaji ne Alhaji Mustafa ya kawo maganar akwai wani copy na wani gonar Alhaji da bai ga original takardun ba. Wani tudu, wani gangare aka zo aka ce ai takardun filin suna hannun Aishatu. Da aka nuna mata copies ɗin sai ta ce 'eh' original ɗin na wajenta saboda Alhaji ne ya bawa 'yarta kyauta lokacin da aka haifeta.

Abunka da dukiyar gado mai haɗa fitina nan fa 'yan'uwan suka ce ba su yarda ba ai Alhaji bai faɗawa kowa ya yi kyautan gonar ba, Hajiya ma ta ce bata sani ba. Suka haɗu suka ce shima gonar ya faɗa cikin gado.

Aishatu bata taɓa tunanin ƙiyayyar da Hajiya ke nuna mata tunda ta auri Malam Salisu ya kai har haka ba sai da Hajiya ta ce wai ta kawo takardun gona tunda babu shaidar Alhaji ya yi kyauta da filin.

Haka ta koma gida ta sha kuka. Da Malam Salisu ya dawo ta ce ya bata takardun gonar da Alhaji ya basu. Da ya tambayi ba'asi sai ta faɗa masa abinda ya faru a wajen meeting.
Ya ce ba za a yi haka ba shi shaida ne Alhaji ya yi kyautan gonar dan haka gona ta Hadiza ce bata cikin gado.
Aishatu ta ce ita sam za ta mayar musu da kayansu. Dama ai sun wareta gefe ne suna ganin tunda ta auri Talaka za ta walaƙanta to kuma har yanzu suna nan asirinsu a rufe.

Da aka sake zaman raba gado sai Aishatu ta taho da takardun filin da Alhaji ya bata. Ta kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce "Wannan takardan filin kyauta ce Alhaji ya bawa 'yata Laila. Amma tun da kuna jayayya da hakan ga shi nan na bar muku, duk ranan da kuka gane gaskiya kwa nemeta ku mayar mata da kayanta. Hajiya ga shi" ta ɗau file ɗin ta ajiye a cinyar Hajiya.

Alhaji Usman Tafida ne ya yi saurin cewa "Aishatu ba a gama magana ba. Fili dai za a baki fili idan muka gama tabbatar da gaskiyar al'amari. Akwai mutane da yawa..."

"Ka yi haƙuri Yaya Usman, ina da sauran magana" gaba ɗaya sai suka ƙura mata ido suna kallonta.

Ta ce " Alhamdulillahi dukkanmu a nan magadan Alhaji ne, dan haka tun da maganar gado ake ina so na faɗa muku cewa ni Aishatu Ibrahim Tafida na yafe gadon Alhaji duniya da lahira"

"Wani irin magana ne wannan kuma?" Alhaji Usman ya faɗa a fusace.

Barrister Halliru kuwa cewa ya yi "Aishatu, calm down. Wannan zama ba na faɗa bane..."

"Ina ce ya halasta Mutum ya yafe gado?"

Mustafa ya ce "Ummi, babu maganar yafe gado a nan. Dan an yi maganar fili jiya ba shi zai sa ki hau fushi ba"

Haka dai suka haɗu suka mata chaa!. Hajiya ko uffan bata ce ba. Aishatu dai ta haƙiƙance kar a raba gado da ita ta yafe. Alhaji Usman ya ce ba za a yi haka ba, idan an bata sai ta karɓa ta yi abinda ta ga dama da shi, amma za a raba da ita.

Bayan ta koma gida sai ta faɗawa Malam abinda ya faru. Kamar kullum sai da ya fara da tausanta saboda saurin fushinta. Ya ce mata bai halasta ta ƙi karɓan gado ba,  Allah ne ya ce a raba da ita. Sai dai idan aka bata za ta iya karɓa ta yi kyauta da shi ko sadaka.
Da wannan ta ɗan sauko daga fushin da take.

Sai bayan wata uku da rasuwar Alhaji Tafida kafin aka ƙarƙare haɗa alƙalumman dukiyar da Alhajin ya bari bayan an biya basussuka, an kuma cire dukiyar da ya ware na Sadaƙatul Jariya a wasiyyarsa. Abinda ya saura shine aka rabawa Magadansa.

Aishatu ta samu gida, da wasu shaguna da kuɗaɗe masu yawa har da ɗaya daga cikin motocin Alhaji. Da aka damƙa mata komai ta musu godiya ta tafi. Ai kuwa washegari sai ga labari ya iso musu wai Aishatu ta kai gadonta Masallaci ta yi sadaka da komai, ko ƙwandala ba ta bari ba.
'yan'uwanta suka dinga zaginta suna mamakin wautarta da shegen taurin kanta. Kuɗi ne da zai canza musu rayuwa ita da Mijinta amma ta kyautar da komai. Gonar da aka yi rikici a kai ma sun yi magana sun dawo ma Hadiza kayanta amma ta ƙi karɓa ta ce idan Hadiza ta girma ta mallaki hankalin kanta su bata da hannunsu.
Hajiya ta riƙe takardun gonar a wajenta itama girman kai ya hana ta lallaɓa Aishatun tun da sune suka fara mata ba dai-dai ba.

Hukuncin da Aishatu ta ɗauka ya matuƙar jawo rikici tsakaninta da Malam dan ba su taɓa faɗa irin wannan ba tun da suka yi aure sai a lokacin.
Ƙarshe da ta sauko sai ta bashi haƙuri ta ce ta yi sadakan ne saboda Allah ya kai wa Alhaji ladan sannan kuma Allah ya sa cikin da za ta sake ɗauka ya zauna. Da wannan ta rufe bakin Malam Salisu. ya ce mata Allah ya karɓi niyyarta ya sa a dace.

Daga lokacin Aishatu ta ƙullaci 'yan'uwanta, ko abu ne ya taso a family idan ba a sakata ciki ba ba za ta je ba. Gidan Hajiya kuwa Malam ne ya ke tursasata akan sai ta je, duk bayan sati biyu zai ce ta je ta gaisheta. Ko ta je kuma Hajiyar ba kulata take ba. Haka za ta je ta ƙarishi zamanta ta dawo. Tana dai danne zuciyarta duk wata baƙar maganar da Hajiyar za ta faɗa mata ba za ta tanka mata ba.
Idan ta je haka za ta shiga ɗakin Hajiya ta gyara mata, idan ta tambayi mai aiki ko akwai kayan da za a ɗinkawa Hajiyar sai ta karɓa ta je ta ɗinko ta kawo. Ko sannu Hajiya ba za ta faɗa mata ba.
Idan ta lura Hajiyar na sha'awar wani abu sai ta shiga kitchen ta yi mata.  Ba dan Malam da ya sakata a gaba ba da tuni ta watsar da zuwan da take saboda koyaushe ta je sai Hajiya ta mata gori.

# BestHausaNovel2025
©MarubuciyaAzizatHamza2025