KHADIJAH ko HADIZAH

6

by @azizat

CHAPTER SIX

Direban gidansu Khadija ne ya sauketa a ƙofar gidansu, ta shigo cikin gida da kaya niƙi-niƙi a leda.

Umma tana abincin dare a kitchen ta ji sallamar Hadiza.

Hadiza ta leƙo ta maƙale jikin ƙofa ta kasa shigowa kitchen ɗin tana gaishe da Umma.

Umma ta amsa tareda juyawa da sauri dan ƙanshin cake ta ke ji. Tana juyawa Hadiza ta fara ɓoye ledojin da ke hannunta. Rigan jikinta ne ya ɗau hankalin Umma dan ba kayan da ta fita da su daga gida ba kenan. Shagon da take zuwa koyon ɗinki a weekend ta ce mata za ta je kuma ƙaramin hijabi ne a jikinta da doguwar rigan Atamfa, yanzu kuma wani pink gown ta saka, gaban rigan duk ya ɓaci da Fanta. Gashin kanta kuma an baza shi ya sauka har tsakiyar bayanta, an warware mata kitson Kalaba dake kanta wanda ko sati bai kai ba da Umman ta yaryara mata su.

"Daga ina?" Umma ta tambaya ba dan ba ta san daga ina take ba, sai dan ta faɗi inda ta je da bakinta. Tun last week take mata waƙar za ta je Birthday party ɗin Khadija ta hanata.

"Umma, kiii yiiii haƙuri" Hadiza ta faɗa kaman za ta yi kuka.

"Ina kika je?" Umma ta daka mata tsawa.

"Bir...Birthdayn Nana..."

"Uwarki ce Nanan da za ki je Birthdayn ta"

Hadiza ta kama girgiza kai.

Na ce "Shi ne bayan na hanaki zuwa kika min ƙarya kika tafi ko. To yau za ki ci ƙaniyarki a gidan nan"

Tuni Hadiza ta shiga kuka tana bata haƙuri.

Ɗaki Umma ta wuce ta ɗauko belt ɗin Abba ta zo falo ta zauna a kujera ta kira Hadiza, ita kuwa ta ɓuya bayan labule sai kuka take.

"Laila, ki zo kafin in tashi a nan"

"ban dake ki ba kin fara min kuka. To kuwa dukanki zan yi sai kin faɗa mini kwaɗayin da ya kaiki gidan nan"

"Zo nan!"

Hadiza ta fara takowa a hankali.

Umma ta ɗan tashi ta cafkota, belt ɗin hannunta ta fara zuba mata tana faɗin "ba na hanaki kwaɗayi ba... To Wallahi yau idan Aljanun kwaɗayi kike da shi sai na cire miki su"

Tun ba yau ba Umma ke dukanta akan zuwa gidansu Khadija. Gidan Hajiya ma saboda Abbanta ne ya sharɗanta mata zuwa ziyara duk Jummu'ah wajen Kakarta, ba dan haka ba ko gidan Umma ba za ta bari ta taka ba.

Umma ta hanata zuwa gidansu Khadija. Idan kuwa ta je aka bata abu ta kawo to sai Umma ta daketa.

Umma bata shiri kwata-kwata da Zuwaira, Mommyn Khadija. Ya zo ya haɗu da abin da ta taɓa yiwa Hadizan lokacin tana shekara shida. Shine ma dalilin da ya sa ta hana Hadiza zuwa Birthdayn Khadija duk shekara.

A Lokacin bikin birthdayn shekara 6 da aka yiwa Khadijan ne da Hadiza ta je gidan sai kawai Umma ta ga ta dawo gida ta askekken kai, abin da aka bar mata a dogon gashinta bai kai ko ƙeya ba. Wai saboda Hadiza ta yiwa khadija dariya ta faɗawa ƙawayenta ai ita bata da gashi shine Mommyn Khadijan ta ɗau Almakashi ta aske mata gashi. Ranan ba dan Abba ya hana ba da sai ta je gidan ta ciwa Zuwaira mutunci, amma Abba ya hana ya ce matsalar yara ce kada ta shiga ciki. Gashi kuma zai sake tohowa tunda Hadizan tana da saurin fitar da suma.

Dogon gashin Hajiya Hadiza ta ɗauko har ya fi na Umma cika da tsayi ma, ita kuma Khadija duk da ta ɗau kamannin Hajiya sai bata ɗauko har da gashin ba ta ɗauko ƙwaƙwus ɗin gashin Mommynta.

Abun ka da yara Hadiza bata dena son zuwa gidansu Khadija ba, duk da Umma tana hanata haka ta ke fakewa da tambayar za ta je gaishe da Hajiya daga nan ta wuce gidansu Khadija.

Dake Abba ya sa dokan kada Umma ta hana Hadiza kai wa Hajiya ziyara, babu yadda ta iya take barinta.

Sallamar Abba ne ya ceci Hadiza daga hannun Umma.

"Lafiya?" ya tambaya yana janye Hadiza dake ta kuka daga hannunta.

"Ba ka ga kayan jikinta bane. Wai Party ta tafi ba wajen ɗinki ba"

"Shine kike dukanta. To ni na ce ta je. Inda kin barta ai ba za ta miki ƙarya ba"

"Abin da za ka faɗa kenan" Umma ta faɗa tana yar da belt ɗin hannunta.

Abba ya kalli Hadiza ya ce "wuce ɗakinki"

"yanzu Fisabilillahi da yanayin jikinki kika saka yarinya a gaba kina duka"

"Ya ba zan daketa ba. Yarinya sai shegen ƙarya da kwaɗayi"

"Wajen 'yar 'uwarta ta je ba wani waje ba. Da kin barta ai ba za ta yi ƙarya ba. Ni bana so kina shiga zumuncin yaran nan. Da ita da Nana duka abu ɗaya ne"

"Da ita da Nana abu ɗaya ne, shine Uwar Nanan ta aske mata gashinta kwanakin baya"

"Ya wuce, Aisha"

"Abu ɗaya suke shine Zuwairah sai kayan 'yarta sun gama mutuwa sai ta ƙunsowa Laila saboda Almajira ta ɗauketa"

Umma ta cigaba "Yaushe ta taɓa siyawa Laila sabon abu ta ce a bata ? Yaushe ita take barin 'yarta ta zo gidan nan. Kullum sai dai tawa 'yar ta je su gama zaginta, su walaƙantata, su daketa, kuma ka ce wai ɗaya suke da Nana"

"Ya isa. Ki yi haƙuri kar ki ɗaga hankalinki" Abba ya faɗa a ƙoƙarinsa na son kashe maganar. Amma fa kamar ƙara tunzurata ya yi. Ta cigaba da faɗa, har abubuwan da bai san an yiwa Hadizan bama sai da ta faɗa.

Ya dai danne zuciyarsa ya dinga lallaɓata. Bayan Hadiza wannan ne ciki na biyar da Allah ya sa ya kai wata bakwai, ɓarinta huɗu duka basa shige wata uku ko huɗu suke fita.

A wannan cikin ne da suka dage da zuwa Asibiti ana bincike sai aka gano dalilin yawan ɓarin da take na iya zama saboda kasantuwar jininta O negative (O-) ne, shi kuma ɗan cikinta yana zuwa da jinin da yake da Rhesus factor Positive (irin na Abba wato A+). Ita Hadiza, jininta ɗaya dana Umma shi yasa cikinta ya zauna babu matsala. Amma sauran da alama banbancin Rhesus factor ɗin jininsu yake ƙwayoyin jininta ke attacking cikin.

Wannan karan tun farkon cikin aka mata allurar Rh Immunoglobulin, sannan za'a sake allurar daf kafin ta haihu da kuma bayan ta haihu.

Sai bayan kwana biyu sannan Umma ta sauƙo. Amma fa bata janye dokarta na hana Hadiza zuwa gidan su Khadija ba. Itama Hadizan tun da aka mata wancan dukan ta nitsu ta dena maganar za ta je gidansu Khadija. Ta cigaba da zuwa Makaranta, Islamiyya da kuma shagon da take koyon ɗinki a ranakun weekend.

Ba a jima ba cikin Umma ya shiga wata tara. Da haihuwar ta zo, sai ta kasa haihuwa da kanta. Suka ce mahaifarta ya yi rauni, ga shi ta juma tana Labour haihuwan bai zo ba, sai kawai aka ce za a mata CS.

Abba ya kira yayunta dake kusa wato Barr. Halliru da Mustafa ya ce a faɗawa Hajiya za a yiwa Aishatu aiki.

Babu wanda ya zo a lokacin har aka ciro yaro, sai can yamma sai ga Baaba Asabe wata da take kamar ƙanwa a wajen Hajiya ta iso Asibitin. Ko lokacin da aka haifi Hadiza ma ita ce ta zo a madadin Hajiyar.

Abba ya ji zafin hakan. Wannan shine karo na farko da ya ji zafin halin ko-in-kula da Hajiya ke yiwa Umma dan kawai ta aure shi.

Yaro dai lafiya aka haife shi, amma ita Umman sai aka samu Complication tana ta bleeding sai da aka sake mata wani aikin kwana biyu bayan haihuwar.

Sai da Umma ta yi sati biyu a Asibiti kafin aka sallameta. Mutane dai sun zozzo sun dubata amma Hajiya kam bata tako Asibitin ba. Duk haƙurin Abba ya ji zafin hakan ba kaɗan ba.

Dake haihuwar ta zo da haka sai ba a yi taron suna ba. Yaro ya ci suna Muhammad Bashir.

Hadiza kam lokacin da aka riƙe Umma a Asibiti gidan su Khadija ta tare daga nan take wucewa Makaranta ko ta taho Asibiti.

Bayan Umma ta warware sai ta cigaba da kula da yaronta. Ko maganar rashin ganin Hajiya a Asibiti ko a gidanta ba ta yi da Abba ba, ta bar abin a zuciyarta yana cinta.

Abba kam tuni ya watsar da abin a ransa ya cigaba da zuwa gaishe da Hajiya kamar yadda ya saba. Itama Umman bayan Bashir ya yi wayo shi da kansa ya ɗaukesu a machine ɗinsa suka je gaishe da Hajiya. Hajiya da aka bata Yaron sai ta ke cewa wannan kam jinin mutanen Zango ne ga shi nan da ƙaton kai kamar Ubansa. Babu wanda ya tanka mata cikinsu. Hadiza da ta ɗauko kamannin Hajiyar ma lokacin da aka haifeta sai da ta kusheta balle wannan da ya ɗauko kamannin Abba.

Haka dai rayuwa ya ci gaba da tafiya. Daga gida mai ɗaki biyu, suka koma gidan da Abba ya siya mai ɗakuna uku. Daga nan kuma Allah ya sake buɗi ya sayi Mota.

Tunda ya zama Principal a Makarantar da yake aiki da Hajiya ta ji sai ta fara kiran Umma da Matar Principal. Duk inda ta samu waje sai ta kushe shi.

Wani abu da Umma bata sani ba shine, duk abinda Hajiyar ke faɗa dan ta kushe Abba tana hakan ne saboda bata so ta yarda a ranta cewa mutumin da Umman ta aura mutum ne na gari a gareta. Ga shi dai ba shi da kuɗi sai rufin asiri kawai, amma aurensu akwai jin daɗi da farin ciki. Sannan duk gorin da take masa bai taɓa rage girman da yake bata ba.

Itama kuma Umman duk da dai bata da wadata irinta sauran 'yan'uwanta amma tana cikin rufin asiri. Tana ɗinki tana kuma saida Materials da Atamfuna, kuma ba laifi tana samu. Bata taɓa roƙon Naira ɗaya a wajen Hajiya ko Yayyunta ba. Tun daga rikicin gado ta shatawa kanta layi da su akan ko mutuwa za ta yi ba za ta roƙi wani abu a wajensu ba. Hakan ma sai ya siya mata mutunci dan kaf ɗinsu babu wanda ya ke renata. Sun san dai bata da shi kamarsu amma kuma ba su isa suce tana cikin wahala ba.

Ko biki ake a dangi aka fitar da kaya duk tsadarsa sai ta nemo kuɗi ta yi. Ga kuma kwanciyar hankalin dake shimfiɗe a fiskarta kullum, wannan kaɗai ya hana su yi mata gorin Arziƙi. Yawancinsu da suke auren masu kuɗin ma ba su da nitsuwa da farin cikin da Aishatu matar Malam Salisu Zango take da shi.