RA'AYI NE KO BURI?

01

by @jamilaumarjanafty

RA"AYI NE KO BURI..?

NA

JANAFTY💞

Wattpad:Jamilaumar351

1

JIGAWA_Dutse

Ringim..

....Daga labulen Dakinta tayi Ta Fito tana gyara Haban Zaninta cikin Masifa take Fadin"Ke Humaira kinga naki nace..."

Tafada tana ware ma wata yar matashiyar Budurwa dake kan Wani Dutse acikin Filin Tsarkan gidan tana wanki hannu,Dagowa tayi Tana kallon Hajjo cikin Tura baki lokaci Daya tana ware ido tace"Ni kuma...? Toh ni Hajjo mai nayi miki da zaki makomin zagi.."?

Dattijuwa ce mai akallah Shekaru 64 aduniya,Ta tsufa sosai Domin kanta yana cike ne da Furfura ammh Daga ganin yadda Take Tafiya da mgana zaka Fahimci masifaffa ce sosai.

Sake ware hannu Tayi ta sakarmata wata Dakuwa Tana Fadin"Kinci uwarki Balaraba domin bana ce Ummaru ba...Tunda ina Shaide iya Tarbiya da kwaba ya baki Ka haifi yaro ne baka Haifi Halinsa ba.."Tafada tana Jifanta da wani kallo.

Tunda taji Haka tasan kwanan Zence sai kawai ta kauda kai ta Cigaba da wankinta Lokaci Daya tana bin Sanyayyiyar Muryan Gwaninta nata cikin Wakarsa na KE KADAI NAKE SO... Baki Hajjo ta rike tana bin Humarah da kallo Cikin bakin ciki ta Takaichi.

Larai ce ta Fito Daga cikin Dakinta tana Fadin"Lafiya Hajjo kedawa kike Ta Fada Tun Safe,Nasan kuma su Auwalu sun Dade da Tafiya Makarantar Haddar Safe...? Hajjo ta waigo tana Fadin"Nida wannan Tsegeran yarinyar nan ne,wacce batajin Tsoron kowa Aisha Humairah..."

Larai Ta tabe baki tana Fadin"Me tayi kuma Hajjo..? Hajjo ta cigaba da Fadin"Kiduba kigani Larai Tun Safe da yarinyar nan ta Fito da wanki nan Ta Dauko wayar nan ta Uwarta da ta gaje ta zama nata,Bata kunna karatu ba,sai wakeken banza da Wofi in wannan ta kare sai wannan Ta Shiga kamar gidan Dan Nanaye,ko kunya kuma  bataji ina Daga Daki ina Jiyo ta tana bin Wakar kamar ta samu karatu Abun takaichi Uwarta na ciki tana jinta bazata iya Fitowa ta kwaba mata ba..".

Tafada cike da kumfar baki Yamutsa Fuska larai tayi kafin tace"Kema kenan Hajjo kin mata mgana bata jiki ba..Yo inaga wani kuma ai mallam ne kadai Zai iya mganinta game da wannan Iskancin Data Fito dashi Ko makarantan Boko fa Maijidda Ta gayamin da wayar take zuwa malami na karatu ita ta kunna wakar banza tana Saurara saboda ta raina kowa,don ma Allah ke Fitar da Rayayye cikin matattace ba,ai bai kamata y"ar Mallam Umar Ringim ace Bata da Aiki sai jin wakar nanaye na wani Katon banza ba.."Tafada tana Jefama Humarain wani Banzan kallo.

Duk Tana jinsu Da gangan Tayi musu Banza Domin Dama Hajjo da Larai Yan bakincikinta ne,Abunda ya bata mamaki wai maijidda datace da waya take zuwa makarata Shegiya,koda take zuwa makaranta da waya bata Fita kokari ba,Wlh tana da yakinin kaf ajinsu bana Biyunta haryanzu bata gama Tunaninta ba Taji Hajjo ta Dauke wayar Dake kan Dutsen Dake Kusa da ita,tana Fadin"Na karbe wayar sai naga da Wacce zaki dinga jin wakar banza da iskanci.."

Tsam Humaira ta mike tana kallon Hajjo cikin mamaki tace"Wai ni Hajjo Me na tsare miki ne acikin gida nan,Kina mganar karatu ina ce Tun Wachan Shekaran na Sauke Qur"ani yanzu fa Kan Haddata nake,kuma na tabbata kina sane kan cewa ni bana Shiga Shirgin kowa acikin gidan nan masu kawo gulmar da munafuncin,ai su nan jiya yau,shikenan kuma bani da damar da zan kunna waka acikin gidan nan sai kin Fito kina mgana..Nidai bani wayata bana son irin wannan wasan.."Tafada tana mika mata Hannu.

Galala Hajjo da Larai suka tsaya suna kallon Humairah kafin Larai ta Shiga Tafa hannu,kuka Hajjo ta fashe dashi tana Fadin"eh gaskiya ne...Kin Fadi gaskiya Umaru ne kadai yasan Darajata acikin gidanan,ni kika ci Zarafi ko Humairah Wlh sai kin Raina kanki Daga ke har Uwarki Dake Daure miki gindi.."Tafada tana Share Hawayenta da Haban zanin.

Dago labulen Dakinta tayi tana Fadin"Ke Aisha kar in kara jin bakinki anan wajen in kuma ba Haka ba,wlh zan saka Nasiru in yadawo yayi miki Dukan kawo wuka Tunda ke haryanzu hankali bai game jikinki ba Sakarya kawai mara wayau.."Tafada cikin bacin Rai kafin ta juya tana Fadin"Don Allah Hajjo kiyi Hakuri Yarinta ne ke damun Aisha Haryanzu..."

Hararanta Hajja tayi kafin tace"Rufemin Baki Balaraba..Wani yarinta.? Wannan Gamsamemiyar yarinyar ce zaki kira yarinya..? Shekaranta fa in ban manta ba Goma Sha Takwas ammh ki dinga Kiranta yarinya saboda Daurema karya gindi ko.?

"Sadda kai tayi kafin ta karisa Fitowa Tana Fadin"Allah huci Zuciyarki Hajjo ammh da"ace Aisha mai jin mgana ce Da ko kallon Wayata bazata kara yi ba...Saboda Daukan wayar nan har Nasiru sai da na saka ya Dake ta ammh bata jiba...Kiyi Hakuri Tunda kin karbi Wayar Shikenan...Ke kuma maza ki bata Hakuri.."Tafada tana Kalloon Humaira Da idanuwanta Suka ciko da kwallah Saboda Takaichin Bazata saurari Muryan gwaninta ba yau kuma ta saba bata iya barci sai ta Saurari Sanyayar muryansa mai cike da gardi da Dadi.

Ganin ta tsaya tana Raba ido yasa ta Daka mata tsawa tana Fadin"bazaki bata Hakurin bane Don Ubanki..? Tafada cikin Bacin Rai na yadda Humaira ke sakawa ana Jin Muryanta acikin gidan nan Alhalin kowa yasan cewa ita bamai Hayaniya bace ga kawaichi Wani lokacin in ba Abun ne yayi yawa ba bata saka baki,sai dai ta bar Larai ta Hajjo suyi ta sakin Zencensu son Ransu.

Cikin Rawan Murya Humairah tace"Allah baki Hakuri..."Daga Haka ta Duka ta cigaba da wankinta Lokaci Daya tana Share Hawayen da suka gangaromata,Duk Fitinar Hajjo Tana girmama Balaraba saboda tana da Biyayyah kada kai tayi tana Fadin"Shikenan ya wuce...Wayar dai na karbe kuma zanga Shi Gaddafin Tunda naji labarin shi ke Tura mata wakokin,in yazo gida Hutu shima Shashasha katon Banza kuma ma Abun Haushi fa badai kiji na wani Mai wakar ba sai na wannan ya nayi da Murya kamar Andaki kato.."Jin Haka yasa Larai ta Kwashe Da dariya harda guda,Balaraba dai bata bi ta kansu ba tafada madafi domin Sha"anin Aisha yafara isarta acikin gida nan bari mallam ya shigo zatamai mganar a saka Lokacin bikinta da Sulaiman Allah barshi ta karisa karatunta agidan Mijinta..

Da sallama ya shigo gidan Da larai yaci karo wacce ta Dauki Tsintsiya ta fara sharan Tsakar gidan,Tana ganinshi ta Hau washe baki Tana Fadin"A"a maraba da Sulaimanu mutanen Zazzau yaushe kuma agari...?Tafada tana kallonsa Da Sauri Humaira Ta Dago suka hada ido Da Mirmishi Bisa Fuskarsa yake kallonta yana sanye cikin Riga da Wando,na zamani Kansa yasha gyara Dogo ne,ammh ba sosai ba baki ne ammh yana da kyau sosai da Tsari akallan Farko zaka Fahimci Sulaiman yana da Bala"in Sanyin Hali Sosai..

Ganin ina ta Share kwallah Lokaci Daya ina Maida kaina kasa na cigaba da wankin Danakeyi Dama kayan Innata ne dana Kanwata Mujadala,sai Uniform din makarantana ammh Dayake bani da Saurin wanki shiyasa na Dauki Tsawon Wani Lokaci ina yi ban gama ba.

Tunda ya ganni cikin Damuwa Mirmishin Fuskarsa ya kau yake kawai yayi kafin ya ramkwafa yana gaida Larai ta amsa cikin Farin ciki Lokaci Daya Tana ji Dama Maijidda ce ta samu damar da wannan Shashhar Aisha ta samu na Auran Sangirin yaro irin Sulaimanu.

Sun gama gaisawa kenan sai ga Innata ta Fito Daga Madafi,Cikin kunya Suka gaisa bata bari ma Sun kalli Juna ba ta Shige Daki Abunta,larai ko saboda Munafunci sai ta cigaba da Shara ganin haka yasa Sulaiman yace"Baba yanaga kina Shara da kanki inayaran gidan ne..?

Tabe baki tayi kafin tace"Kai dai bari Wlh Duk suna makaratantar Islamiyar safe maijidda ce ke da Sharan yau kuma tana ciki bata jin Dadi tana Fama da Masassara..."Kada kai yayi yana Fadin"Ayyah...Allah bata lafiya..."Yafada kafin ya karisa kusa da ita yana Fadin"Kawo na karisa Sharan Baba.."Mirmishi ta saki kafin tace"a"a sulaimu bazai a Haka ba...Suruki guda da shara ka barshi kawai zan karisa Sharewa..."jin haka yasa yayi baya kawai batare Daya ce komai ba Balaraba na cikin Daki tana Hangosu cikin ranta tayi Mirmishi Domin Jiya bata bar yau ba game da Munafunci larai akanta ita da ya"yanta.

Inda nake Duke ina Wanki ya Nufa Lokaci Daya yana Durkusawa kan Kafafunsa yana kallona Niko naji Wanzuwarshi Awajen ammh nasha Kunu sai ma kara gyara zaman Rigar atamfar Dake Jikina nayi ganin kamar mai Budaddan Wuya ce,Mirmishi ya saki kafin yace"Waya taba min  Humaraitah....?"Yafada cikin kwantar da murya mai cike da Salo..

Karaf Hajjo ta Dago Labulenta Tana Fadin"Nice nan Sulaimanu ....Ko zaka Rama mata ne...? Tafada tana kara Leko da kanta,Sunkunyar dakai yayi yana Fadin"Hajiya Hajjo barka da Safiya..."Yafada yana sosa keya alamun kunya yar Dariya tayi tana Fadin"Lafiya lau sulaimanu...Saukan yaushe...? Ina ma kake karatun naku na zamani..?

Yace"Zaria ne Hajjo..."Baki ta tabe tana Fadin"Hmm..Ni bansan miye amfanin wannan karatun Nasaran ba,mufa bamu sanshi ba Tun Iyaye da kakanni Karatun Allo muka sani,Ammh dubi yadda ku yaran zamani kuka saka kanku cikin Wahala duk kunbi ku rame haka yaron nan Gaddafi yana chan yana Wahala in ya Dawo kaga yadda yayi Dan Wuya..."Tafada tana Jefa Goro cikin Bakinta.

Sulaiman ya murmusa yana Satan Kallon Aisha yace"Hajjo ai Zamani ne yazo da Haka kuma...ance anemi duka ilimin zamanin dana Muhammandiyan.."Larai ta karbe da Fadin"Kema dai Hajjo toh miye ya Raba su Sulaiman din da mazan kauya nan in ba Karatun Boko ba,kuma karki manta Shiganshi maigari Hayatu yana da Ilimin boko kinga ko Yasan Muhimmancin Abun sosai Shiyasa bai bar ya"yansa kara Zube ba..."Hajjo ta kada kai tana Fadin"Ai hayatu tun yana yaronsa mai Nacin karatu ne...ba Daya suke da Umaru ba...Shi Umaru barshi a maida kai ga karatun addini bai bari Karatun Zamani ya Rudeshi ba.."Dariya Sulaiman da Larai suka saka Saboda kalaman Hajjo kamar Daga Hayatun Har Umar din ba ya"yanta Bane.

Ina jinsu suna Hiransu ban saka musu baki ba sai da na gama Dauraye kayana zan Shanya Sulaiman ya mike yana Tayani Shanyar ammh Duk da Haka ban sakin mai Fuska ba da kallo Hajjo Tabimu kafin tace"Kai sulaimanu ka daina Shige mata Haka nan,sai Wulakanta take,ai yau bazaka samu kanta ba na kwace wayar datake kunna mana Shegen wakar mawakin nan da bansan Wani Dadi Humairah keji acikin Wakarsa ba Saboda Iskanci Harda na wasu yare sai kaji ta saka ta kara kara kamar gidan Giya ko bariki..."

Sulaiman ya kalleni yana Fadin"Wai shi ne ma Dalilin Fushin...? Kai na Dagamai Da Sauri Sanin Yadda baya son bacin Rai na,kuma nasan zai iya karbomin Wayata wajen Hajjo Mirmishi ya saki yana Fadin"karki damu ki daina bata Ranki abanza...Indai kan wayace zan baki nawa kiyi ta amfani da ita har na tashi Tafiya,kafin Lokacin kuma Zan siya miiki taki da Memory kiyi ta shan wakarki bamai Kara Takura miki.."Baki na Washe ina Fadin"Da gaske kake ya sulaiman...?

Kai ya gyadamin Tsalle na Daka ina Fadin"Ina godiya sosai Yayana..."Daga larai har Hajjo baki suka saki suna kallonmu kyafci Hajja tayi tana Fadin"Eh lalle...Wlh matukar ina gidan nan sai dai in bazata cigaba da Kunna mana wakar banza ba sai na karbeta.."Baki na Tura ina Hararan Hajjo butar Dake kofar Dakinta ta Raruma ta Wurgomin Sulaiman ya Tare yana Fadin"Don Allah Hajjo kibar Humairata ta Huta hakanan...Wakar kuma data ke sakawa kwana nawa ne..? Ki kyaleta mana Kinsan kowa akwai Abunda yafi kwanta mai acikin Rai ita Humaraih wakar ABDULMUTADDIF SA"ED MAI NASARA itace gwanarta ni banga laifinta in ta Saka wakarsa Tana ji ba Tunda baya Hanata karatu...".

Tsaki Hajjo taja tana Fadin"Kai Rufemin baki sakarai Sauna...Bari Duka uban nin naku su Shigo zan gansu...In su suka Daure muku gindi suzo muyi mgana su sanya Lokacin Auren naku Kuje chan ku karata..."Kallon kallo mukayi Nidashi cikin Faduwar Gaba nabi Hajjo da kallon Sanin indai tayi wannan Mganar angama domin Daga Baba maigari har Babanmu Ba mai iya Tsallake mganar Hajjo ni kuma acikin Wauta ta da yarinta Ni MAWAKI ZAN AURA...

A wauta na da kuma kuruciya ko kuma nace Soyayyar makatance ta sameni Tun ina Shekara goma Sha Biyar Aduniya na wayi gari ina bala"in son mainasara mawaki sakamakon maida kaina da jin Wakokinsa Tundaga na Hausa har zuwa na Turanci Tun Ina Tunanin Mainasara burgeni yake har na Fahimci na Fada Cikin Kogin Sonsa,Ina ina Sauraran Wakarsa sai naji bani da wata Damuwa duk nan Duniya In ina Sauraran Muryansa sai na samu kaina cikin Farinciki...In ana so aga bacin Rai a kushe wakar Mainasara yanzu Raina zai baci Gabadaya Wayar Innata na cikata da Duka wakokinsa Wanda Ya gaddafi ke Turamin Duk Sanda yazo gida Hutu.

Kaf yan gidanmu kowa ya Shaida Ni Bani da wani gwani sai  mai Nasara,Babu wanda na taba Furtama Halin Dana ke ciiki sai Kawata Daya Tal Aliya wacce kanwa take ga Sulaiman Ubansu daya Wanda aka mana alkawarin Aure dashi..Zuciyata ta riga tagama narkewa cikin Mayen son Wanda banta ba gani ba ban kuma ban jin Muryansa a zahiri ba sai da awaka ammh Duk da Haka ina ji araina watarana zamu hadu ido cikin ido

Ruwan Hannunsa ya yarfamin na zabura na dawo Daga Dogon Tunanin Dana Fada,cikin Shagwabe Fuska nace"Ya sulaiman toh kana da wakokin Gwanin nawa ne a wayar naka..? Mirmishi ya saki yana Shayamin Hijabin makaranta na yace"Ba dole ba...Ai Tunda ya zama gwanin Humairata nima Tuni na Koyama kaina son wakokinsa,a makaranta wani abokin karatuna Yakubu ke Turamun Duk sanda yayi Sabuwar waka Domin Shima na Lura gwaninsa ne..."Kai na gyada cikin Murna ina Fadin"Nagode Yayana...Har na Fara Tunanin Taya zan iya barci ban ji Muryan gwanina ba.."

Wani kallo ya sakarmin kafin yace"Anya Humairata...Ba zan Fara Kishi da Mainasara mawaki ba.."Ido na waro ina Kallon sa kafin nace"Saboda mene Yaya...?"Ajiyar zuciya ya Sauke kafin yace"Naga kamar Zuciyarki Tana Sonsa ne...Duk  da ko baki Taba ganinsa ba.."Yafada kai Tsaye yana kallonta Sunkuyar Dakai nayi Ina Kallon kasa,ban yi mgana ba kawai na Juya ina Cigaba da Shanyata ammh kasan Raina cike da Rauni in da ina Da Hali dana ce ma Ya sulaiman eh ammh kuma Tsoro ya cika Raina.

Da ido yake rakani har na gama na tattara Duka botikan Danayi amfani Dashi Tsaki mukaji an saki atare muka waiga Muka ci karo da maijidda ta Fito Daga dakinsu tana wani Mele baki kallo Daya nayi mata na kauda kai Wuceni tayi Tana Fadin"Aikin banza iska na wahalar dame kayan kara...Mutum yana ta wahala kan wani mawakin da har ki mutu bazaki Taba ganinshi ba gwarama ki Rumgumi Abunda kika samu Kamar zai fi miki wannan Wahalar da kan da kike..."Tafada tana Daukan Buta ta Wuce Zuwa makewayi Harda wani Juya mazaune.

Dukkanmu da kallo muka Bita kafin na Kada kai ina Mirmishin yake Daga larai har yarta maijidda Mugayen munafukai ne yanzu haka ita taje ta taso ta Domin Tun Dazu take ta zagaye Sharan ma ta hakura ta ijiye saboda makirci Tunda Taga muna Hira Da ya Sulaiman ba Tun yau ba na Fahimci Maijidda kamar son Sulaiman take Larai kuma najin Takaichin yadda Sulaiman yazabeni bai ce yana son yarta ba.....

Tabe baki nayi banyi Mgana ba ya Zaro mim karamar wayarsa cikin Aljihun wandonsa yana Fadin"Gata Humairata...Tsaraban ki kuma sai gobe zan kawo miki yanzu ma nazo gaida mallam ne Naji Idanuwana na kewar ganinki..."Yafada yana sakarmim manyan idanuwansa..

Mirmishi na saki kafin na saka Hannu na karba ina Fadin"Thanks Yaya Allah ya saka maka da alheri..."Da Ameen ya amsa yana kallona kafin ya Daga murya yana Fadin"Baba,Inna na tafi.."Da sauri larai ta leko tana Fadin"Har zaka tafi..? Toh ka kaida su hajiya da mairo..."Kansa na kasa yace zasuji Balaraba na ciki bata Fito ba Hajjo ko har Dakinta ya iske ta kwanta Har Zaure na rakasa kafin muyi sallama sai gobe zai dawo...

Cikin Farinciki na Dawo cikin Gida Don kar,na shiga Dakin Innata tamin Fada karban Wayar Sulaiman Duk da waya biyu yake amfani da karama da Babba,Shashen Matar ya Nasiru na Nufa Rabi domin muna bala"in Dasawa sosai Duk da bana Wani Shiri da mijinta baida Sakin Fuska nafi Shiri Daya gaddafi Domin yafi shi jana ajiki.

Ina jin Fitowar Maijidda sanda zan Shige Shashen Rabi na kalleta na Dagamata wayar Hannuna ina mata gwalo Tsayawa Tayi tana kallona niko na Shige ina Dariya,domin Haka nake mata domin na Kular da ita Gashi dama yau ita keda Dafa Abincin Rana ni ni kuma nayi na Dare Batason aiki Shiyasa take wannan kunci.