ABUNDA KE 'BOYE...

14

by @surayyahms

⏯️1️⃣4️⃣

wani irin shiru wajen ya dauƙa ayayinda ibaad yagama daka ma sarkin fulanin nasu tsawa da wata iriyar kakkausar murya me razanarwa

"ban amince da wann auren ba, wllh yadda kuka kullashi ann haka xaku warwareshi..what in the world is wrong with u people haaaa daga taimako?...

cikin datsar numfashinsa tare da kai ma bakinsa duka dogaren sarkin yace "kaiiiiiii yaro ka iya bakinka!!kasan cewa agaban sarakuna biyu kake magana zamu iya kashe kafiri, mubinne mushen gawansa ann abanza, dan haka kama mutane shiruuuu ka rusuna kasa kayi ma sarakunanmu godiya da irin dumbin adalcin da sukamaka suka baka mata snn maza maza ka dauki matarka ka kara da gaba...

adaddafe ibaad ya miƙe tsaye jini ya taro a bakin sa still hannun sa biyu duka a daure cikin tsananin tashin hankli da bacin rai yace"wallh baku isa ba ku kukasan wani aure ni bansan shi ba, kuma baku isa ku lakamin wani auren karya ba, tunda har kunsamu yarku, ku kwance ni kawai na kara da gaba, inba tsaban hauka da jahilci ba kun sanni ne da zakumin aure???? kunsan daga ina na fito? waye ubana? haka kawai daga taimakawa yarinya akan hanya sai kucemim wai na aureta a ina aka taba daura aure haka...

Da wani irin zafi zafi dogare ya baaje rigar sa zai zaro dorina ya zanesa cikin tsananin izza da mulki sarkin buzu ya daga masa hannu snn ya kalle ibaad din cikin ido yace "kaiiii yaro kalleni nan..babu tsoro ibaaad ya daga kai ya kallesa duk mamakin yaron sai ya rufe jama'ar majiya da sukay shiru suna kallo

sarki yace duk tashen rashin kunyarka akwai wanda sukafika anan dan haka mu muka daura auran snn babu wanda ya isa yazo ya kwance shi.. akwai wasu sharuda da dole ne zamu gindaya maka akan auren nan inka gama rashin kunya da surutun banzan kan saika sanar damu ka shirya.

acikin kyabe baki sarkin fulani yace "kyaleshi, yana nufin daya lalata mana yarinya zaisha abanza ne bai aureta ba? tomu anan garin majiya duk wanda ya lalata mana yarinya yay iskanci da ita koda bamu daura masa aure ba aure tsakaninsu ya dauro..dan haka tun kafin raina ya baci na saka matasa su maka shegen duka anan gara ka fadi gaskiya snn kay niyyar tattara kafarka da matarka kubar mana gari..

atake jikin ibaad yafara rawa rawa cikin rasa abunda ke masa dadii tsaban bacin rai he was just in a total confused state kmr zai zauce...

cikin tattaro makansa nitsuwa dakyar ya dubi sarakunan yace banfa gane me kuke nufi da na lalata muku yarku nay iskanci da ita ba? ni a ina nasanta da zan lalata, wann karaman yarinyar har me zan dauka ajikinta...

cikin katse shi da hatsala juma yace" kaiii kafiri, karya kakeyi wallahi, karka sake ka raina mana wayo duk cikin mu babu wanda baigane ma idonsa abunda yafaru atsakanin ku ba...

da bacin rai "ibaad yace meyafaru wanda ban maku bayani akai ba?? me kuka gani, innalillahi wa inna ilaiji rajiun

..yallabai dakai fa awajen komi yafaru ni banyi ma yarku komi ba kuma kasani

juma baice masa komi ba ya jawo aayana a wani irin walakntcyrr ya finccikota gabansu a walakance kamar yar baiwa snn ya jefota har cikin fili tare da juyata yanamai nuna masa bayan zip dinta dake nan haryanzu a bude

yace "inba iskanci kukeyi ba uban mezai saka har kacire mata riga snn ka kulleta a motarka kana tsotsan bakinta? tunda ka riga ka lalata min yata toh fa dolene ka tafi can barikin da ita kaje ka karasa iskancin da ita acan wallah bazamu amsheku anan ba.

muryan ibaad na rawa rawa cikin tsananin tashin hankli da rudewa mai gauraye da bacin rai ya lumshe idonsa ahnkli yace "To hell with you malam!! ni ba dan iska lallatacce bane, kuma babu abunda ya hadani da yarka face mutuwar da ta tashi yi na ceto ran ta waiku wasu irin mutane ne haka abunnan ya faru a idonku ne snn kazo ynxu kana kawo wani xancen...just let me go out of this damn place

nan take juma ya hatsala yace au zagina zakayi da yaren ku na kafirai?dan iska kawai makaryaci, baqin kafiri, lallataccen banza dan wuta,..karya kake wallhi

ibaad ya rasa mema zaice dan ransa ya mugun baci, nan take ya bushe idonsa yafara amsa juma azafafe suka fara musu sosai yana cewa shi be lalata musu yarsu ba kuma shi bazai aureta ba infact babu inda zaije musu da ita.

wajen ya cikke da hayaniyar musu tsakanin uban amarya da ango da kuma dukan dattijan fada suka nunamai karara cewa basu aminta da shi ba..cewa ma sukay guduwar da ayanahn tay dama wajensa tadosa.. case upon case ya tashi.

ga matasa birjik sun fito da wukake sanduna da adduna suna jirane kawai sarakuna su bada oda ahau kan ibaad da duka da sara..

basuy tsammanin har zai iya tsaurin idon tambatsa taurin kai da muna zafin kai meyawa agaban sarakunan su ba espclly knowing dat shidayane kuma bai da makami....

sosai lamarin ibaad ya daure musu kai basu taɓa tsammanin akwai tsegeru irinsa ba, suna fada yana fada, ko sarki ne yay magana kuwa sai ya amsashi.

Wani irin runtse idanu aayanah tayi tanata kuka mai zafi atsakiyan wann hayaniyar cikin yanayin tsumayi jikinta na rawa rawa da alaman tana cikin yanayin tsananin neman temakon gaggawa daga alkaryar wannan mummunan qaddara dayake shirin tunkarota yanxu..

batasan waye ibaad ba amma haka kawai aranta sai tanajin kamar ta gwammci ya

tafi da ita kawai danta bar garin ta denama ganin babanta da sauran mutanen da alama dataga kmr kowane ya tsaneta..

tambayar duniyan nan ibaad yay mata akan cewa ta fadi abunda ya faru tsakanishi da ita da bakinta koda su juma zasu yarda amma haka tayi masa shiru tanata kallonsa banda kuka batace komi ba,

duk sai akaga kamar eh dagaske ne hala shine kawai baida gaskiyaaa tabbas iskancin sukayi a motarsa shiyasa ma yake budewa aayanah ido agaban mutane har takasa budan baki ta fadi gaskiyan abunda ya afku.

kan ibaad har juyayi yake tsabar baqin ciki da bacin rai the worst was when aayanah taki sam tay magana dan ta wankeshi daga zargin zina, infact emotional kukan datake tanakan kallon kwayar idonsa da wani siga tana dan girgiza masa kai sai yadada sawa aka dada maidashi makaryaci taɓabbe.

gabaki daya ransa ya hautsina ya mugun baci yadda ya ki sam ya karbi auren yasaka ran juma ma ya matukar baci dashi, yafara cewa abashi sanda kawao wann yaron bai daku bane shiyasa yake da bakin yin musu dasu...

ibaad na tsaye in total shock anger nd intense disbelieve har aka kawo mukeken sandan juma yakarba azafafe yay wuf ya daga sama zai warɓa masa akafarsa niyyarsa ya masa jina jina da duka koda zai dawo hayyacinsa ya amshi auren...

yana daga sandan sama zai rafta kusn ajarumce ibaad yay wufff ya riƙe tamm da daurareen hannunsan jajayen idanunsu suka sarkafu acikin na juna

shikansa juma yasha mugun mamakin irin karfi da taurin ran da yaron yake dashi

matasa masu ruke da adda nan suka fara shirin shigowa fili ganin haka ayaanah tay sauri tazube gwiwarta a kasa jikinta nawani irin rawa ta kama kafafun juma da wani irin kyarma me tattare dakarfin tsumayi kanta acan kasa kamr baiwa muryanta bai fita sosai tsabar kuka take cewa Baba, baba, baba, miɗo waɗi hakuri...dan Allah ka tsaya.

duka suka tsaya kallonta cikin lumshe ido takara fashewa da kuka mai karfin tsumayi tace "hoto maa ɗakku mo, baba karka dakeshi, kayi hakuri karka dakeshi ko fii Allah . Mi waɗi woni waɗde mo,..da mugun karayar zuciya takuma cewa "min njahi jooni kay hakuri...wallh zan bishi mutafi yanxu..

wani irin shiru wajen ya dauƙa dukansu rike da sandan jikin kowa na ɓari da tsananin bacin rai, ibaad ne yay saurin sakewa ahnkli dan duk da mugun haushin da ayanah tabashi, sosai yanayinta ya ragwabar mai da jiki yanajin kmr hawayen ta nasakamai raunin da bai taɓajin irinsa a aduniya ba

jin ibaad yasake sandan yasaka juma ya hankadeta tareda fettataa da kafarsa data kama tafado kasa

cikin masifa da hatsala yace "haa lewru, wawiya kawai..ki tafi,karda kisake barin wnn walakantaccen hannun kin ya kara tabani.."Hoto ɗuum wakkitmo am, da wani irin tsawa yace "Yah!.... Miɗo yi'i maa heɓɓude, tsinanniya kawai, tunda har ni zaku tozarta, ita tay cikin shege, ke za kibi mijinki kafiri mazina ci.., ya kalle idon ibaad da hatsale yace"marar kunya ma irinsa kwarto lalatacce..kuje can gaku ai ga duniyar.

wansu irin zafafan hawaye masu daci ibaad yaji sunciko masa a idanunsa our of no where yaji kansa na juyawa kawai ya tsaya yanata kallon ikon Allah

...daga ganinsa kasa he is very very angry and emotionally dis-armed,yaji mugun haushin ayaana, amma ko kadan bayajin dadi ganin cin zarafi da zagi da akemata at this little fragile young age gata da serious ciwo ajikinta abun sosai yadaga mai hankalinsa bana kadan ba

aayanah tana kuka jikinta na rawa rawa ahnkli ta motsa kanta dake kallon kasa da niyyar zata dan miƙe daga tsungunen datake ta tashi tsaye, tana yin motsi wani jiri me karfi ya debeta tayoo luioo zata fado jikin juma memakon ya riƙeta sai yy saurin yaja jikinsa gefe wani rigib tay tangal tangal kamar zata sulale kasa daf da kafarsa agarin gyara tsayuwa by mistake saita wantsolo mai ruwan datti ajiki dake wajen a jikke yake sosai.

wani irin ihu yay ya kalleta suna hade ido a mugun tsorace ta mike tsaye dakyau ta fara bashi hakuri, dama kmr babban burinsa ne ya ga ya daketa cos all his life ita tafi bashi haushi

yana huci ya daga sanda sama zai warba mata ajiki da wani irin tsorata ta fasa ihu from no where taji ibaad ya ture juman gefe da karfi ya sha gabansa tareda kareta inda sandan direct ya sauka masa atagefen goshinsa duk da haka suga baiko motsa ba yana tsaye yana kareta ita kuma ta boye fuskarta ata bayansa tabi ta tantame rigarsa ta baya amatukar tsorace

....cikin ido suke kallon junansu da juma kowa idanunsa yay matukar jajur, tunkan juma yay magana cikin runtse ido da budewa ibaad yace "ya isa haka!! ka kwance min hannu na kawai ai nace zan tafi da ita....

wani irin mugun sanyi ayanah taji daya furta hakan, batasani ba shi niyyarsa shine in ya dauketa sukayi nisa zai jefar musu da yarsu awani waje ajejin ya kama gabansa inyaso ita tasan nayi dan shide yasan bazai iya kaita gidansu yace komi akanta ba....

Rai abace juma ya ciro wata wuka snn ya saka wukan akan igiyan hannun ibaaad yana gurzawa har a garin kwanceshi saida ya ji masa ciwo sosai a hannnu snn aka kawo su tsakiya aka gurfanan dashi agaban sarakuna aka kira wata muguwar bokanya tasha jan yadi da bakin mayafi wanda daga ganinta kasan da mugayen aljanu datake aiki dan kuwa baqar buzuwace.

nan akafara sakamai dokoki tsaurara, akace tunda har ya amince zai tafi musu da yarsu zasu na tracking insa ta hanyar tsafi, sharadin shine idan har yaje yar musu da yarsu toh duk inda yake a duniyar nan zasu kashe shi, tunda har shi ya lalata dolen sa ne kawai ya zauna da ita,.. cewar sarkin buzaye ahakan ma gata sukamata, sbida hannun su bazai rube su yanke su zubarba

..duk dama yayan juma sun jawo musu tozarci me tsanani yazamana dolene dodon tsafin su na garin yakaresu snn atabbata sundawwama acikin ynyin tozarcin da suka zabar makansu snn duk wnda ya lalata musu yarsu dolensa ne kawai sai ya aura.

ibaad yaki cewa komi har suka gama maganan su shide yana rike da hannunsa da juma yaji mai ciwo da wuƙa dan har jini ke diga awajen sosai,

babu kalar tsoratar dashi da bokan batay ba, har dakinsa saida ta nunamai acikin kokon tsafinta, snn ta gayamai tarihin gidansu, da komi da komi, tace mai uwarsa dayafison zasu fara kashewa muddin yabar Aayana ta bata ahannunsa, idan kuma shine yaje ya yarmusu da ita toh shi din zasu kashe...

shide yasan basu isa sumai komi wanda Allah bai masa ba amma abun sun ya mugun daga masa hankli sosai.

bayan komi ya lafa hakanan aka sakaso agaba dashi da ayaana

dandazon matasa da sanduna da adda da wukake suka sako su agaba sukarakasu har gaban motarsa ajeji lokacin sosai magriba ya rufa ga garin yayi wani irin mugun sanyi

a seat din baya ayanah ta zauna ta hade kanta da gwiwarta tanata zubda hawaye cikin rasa mema takeji akanta ynxu...

wucewarsu bada jimawa ba aka naɗawa juma lambar yabo sabida jarumtar da ya nuna wajen hukunta yayansa dukansu biyu bisa tsarin al'ada akan washe gari duk zaa hadu za'a tattauna tsakanin sarakuna asan wani matsayi za a bashi agarin sabida jarumtar da ya nuna wajen kare mutuncin garin majiya da kuma al'adarsu.

bangaren ibaad kuwa tuki kawai yakeyi yana tsaga jejin da gudu amma gabaki daya hanklinsa baiya jikinsa

tunda suka kama hanya zuwa tudu basuce ma junansu komi ba sai kuka ayaana takeyi tun yana jinta haryazo ya dena jinta gabaki daya

within 20 minutes drive suka danno kwana gidan hajya mairo jinin dake famar diga agefen kansa da hannunsa gabaki daya suka bata mai farin rigansa baja baja ransa a mugun bace kowani sake kula yatake baiyi ba yana tsayawa akofar gidan hajya mairo ya sauka a motar ganin kofar gidan akulle da kwado kai tsaye ya wuce ya samu wasu dattijan maza su biyu akofar gidan ya musu sallama sunata kallon jnin daya batamai jiki dai suka amshi adar dar, bayabo ba fallasa ya tambayesu ko hajy mairo tana ina yaga kofar gidanta akulle

dayan dattijon ne yay jarumta yahau gaya masa ai hajiya kam bakanta yau babu kanta tana can asibiti ance jikarta inayah ta rasu snn yar rikontan ma taawuren ta bace a asibitin badq jimawa ba kuma asan ina taje ba anacan dai ana nemanta....ibaad ya rasa meke masa dadi, gashi mutanen suna ta kallonsa wani iri da rashin yarda mussmn ganin jini ajikinsa baja baja. "yaso ya tambaye su kwatancen asibitin amma bai samu fuska ba. kawai sai ya musu godiya ya koma ya shiga motarsa, gabaki daya yanajin wayarsa tanata ringing amma ko kadam baida nitsuwar amsawa yawo yay kadan agarin yana tambayar asibiti toh dama karamin PHC ne guda daya bawani wahalar samu yake dashi ba.

wani matashi ne daya bashi dubu biyu ya amince ya shiga motar yakaisa har asibitin wanda tunkan ya gama parking ya hango hajy mairo curko curko da polisawa ta birkta wajen ta tada buhun barkwanon bala'i tana cewa kawai a fito mata da yarta taawure snn dolene su mata bayanim dalilin dayasa aka bar juma yazo har nan ya tafi da gawar inayah, inba haka ba kuma zatakaisu kara babban kotu acikin gari..

tsabar masifa har rirrike hajya mairo akeyi tana kumfar baki

polisawa biyu aka tura da matasa kusan su uku cikin jeji domin neman taawure wanda hajiya aranta tanada kyakkwan tabbacin cewa bacewar taawure a asibiti bana lafiya bane, kode zata je ta dau mummunan fansa akan mijinta juma ne ko kuma zataje ta dauko gawar yarta inayah a hannunsa tazo dashi.

cikin sauri ibaad ya sallame yaron da kudi snn ya taho wajen da ake hayaniyar da sauri

hajya mairo batama gansa ba saida ya fixgo ta jikinsa tay baya suna hade ido dashi ta rushe masa da wani dan uban kuka tace "Rayyan??? rayyanu wayooo rayyanu bawan Allah wai kaine nake gani ko mafarki nakeyi?? tunbe amsq ba cikin mugun kukan raki tace ohhh Allah nagode maka da ka aiko min rayyanu daga sama aigara dakazo kagani da idonka, dan banda cin mutunci da zalunta na babu abunda akeyi agarin nan....sabida da Allah gawar jika ta da yata sukutum fa aka sace asibitin nan, kawai ka gaya musu su fito min da ita yanxun nan ko mu hadu mu tada tarzoma...

ibaad yay rolling idanun sa amugun gajiye baice mata komi ba ya kama hannunta da wni irin mugun karfi ya jawota can gefe yace "hajiya dan Allah kimin shiru duk naji abunda ya faru wanda ya kawo nin yaban labari cewa uban yarinya ne yazo ya dauke gawar yarsa snn ai ance miki ficewa yarki tay dakanta ba sace ta akai ba kuma ba anje neman yarkin ajeji ba?? cikin yanke kukan rakin cak ta daga ido hawaye zuru zuru a idonta ta budi baki tana kallonsa "ohhh ohhh Allah wani dan uban magulmacin ne ya gaya maka haka kai kuma sarkin jin gulma ?? kai ammaaaaa akwai yan maganadisu kannen malaika jibirilu iyayen baza rahoto agarin nan

ibaad ya rasa meke masa dadi yace hjy ki tsaya dan Allah ki saurareni...kallonsa take tsaf taaf adan sashence tace ai ina jinka..ya budi baki zai magana kenan cikin raxana tace menake gani ajikinka haka rayyanu? yoooo kai kuma wani sabon gayen ne haka da jini kaca kaca ajikin riga, fisabillahi rayyan meye haka nake gani kaida nasanka da mugun son tsafta, tattabashi tafarayi tanajansa cikin haske sosai tana haskawa ta doka salati tareda cewa innalillah wa inna ilaihi rajiuna jini ne fa duk ajikinka?meya faru...ibaaad karde agarin zuwa kaje ka fadi a mota...wayooo Allahna na shiga uku ai saida nacewa ma zaidu yadena baku motarnan shikenan daga cewa ubanka ya mutu kaima aketa so kallai sai ankashe min kai..

tun be amsa ba tay wufff da sauri tabarshi zata koma cikin aabitin da uban gudu tana ihun sunan nurse tana cewa ..ke nass kee nasss..nasss..nasss, nurse tana fitowa ta jawota har gaban ibaad din tana cewa kiga jini ne kaca kaca ajikin jikana dan Allah kushiga ciki kiduba min shi kinji yar albarkata,.shine kadai mini gata na..na tabbata ji yaya ana so akasheni agarin nan shine yazo zai taimaka min gashi shima ansakosa min shi agaba da maita nashiga uku na tana fadin haka ta kara rushewa da kuka...

nurse din tana kkrin tabashi yadan haɗe rai yace "kibari kawai, nagode.. please i have someone that may need urgent attention in my car.. nurse tace toh.. da sauri ya juya tunkan hajy mairo tacakumo rigarsa danyasan zata iya masa hakan suna kaiwa motarsa da nurse yay maza yabude gidan bayan agaggauce snn yajawo ayaanah da already bata motsi ya dauko cak ahannunsa...

hajiya mairo duk ta rikice tana bibiyrsu tana share hawaye tanata lallekawa tana binsa abaya tanacewa waye wann kuma rayyanu?? waye wann kamar ayaanah, laaaahhhh ayanahn ce, duk ta kasa nitsuwa sai binsa take tana cewa...kai kuma rayyanu a ina ka samu ayaanahn toh, ganin bai kulata ba ta dada rushe masa da kuka tana cewa innalillahi wa inna ilaihi rajiun kardai yar nan mutuwa itama tayi...

hade ransa yay bai ko kulata ba sabida uban attention din jama'a data jawo kansu da koke kokenta a cikin sauri yabi nurse din da ayaanan ahannunsa kai tsaye yakaita ciki aka bata gado snn ya dawo wajen biyan kudi ya ciro wallet dinsa ya kirga kudin ya biya kai tsaye..

yana juyowa suka hade ido da hajiya mairo tsabar ta damu taji bayani jikinta har rawa yakeyo dakansa da muryan kuka tace rayyanu dan Allah ka amsani kawai ina ka samo ayaanah??

a nitse yace kinsantane?

da sauri tace ehh mana, itama ai jikata ce anan garin, itace fa aka musu rasuwar gashi nan uwarta ma ta gudu. rayyanu inma kaine ka buge musu yarsu ta mutu ahannunka gara kawai ka fara gaya min gaskiyarka anan duka tsakaninka da Allah, ai shi Allahu gafhurahimi ne, saimu rufawa kanmu asiri mu roke taawure muyi biyan diyyya...dan wallah asarar yaya biyu arana daya bakaramin abu bane...

dan shiru yay yanata kallonta tareda jin wani irin intense relieve asaman kirjinsa sanin cewa hajy tasan yrinyar ma, shiru yay har saida tagama rakinta snn yace hajiya pls..nifa ba bugeta nayi ba she is just weak snn mahaifinta ne ya bani ita...in akayi stabilizing inta anan zan gaya miki komi akan haka pls kizauna anan kijira ni zanje ne nay sallah waje na dawo,

dan share hawayenta tay tace toh, toh muje sai in rakaka mana kayi sallahn..

kai tsaye ya juyo fuskarsa a mugun daure ya kalleta kmr wani boss yace "a'a kizauna nace miki hajya waike mesa kike min hakane kam duk kinsa anata min kallo kmr barawo

..cikin kyabe baki tace yooh to kaiwaye da ba za'a kalleka ba, cemaka akay dan adam abun yarda ne? yoh gadinka mana zanyi karkaje ka gudu binni abarni da gawan ayaanah ni bansan me zance ma taawure ba. cikin lumshe ido da budewa yace "saiki basu kanki akashe ki amadadi na

baki bude tace.."ehhhj yooo dama ai nasan ka tsaneni rayyanu, duk baqin cikin ganina araye da kakeji dan kar naga aurenka bqzai tqba yuwa ba inanan daram, toh ynxu de kaje ka dawo din kamin cikkn bayani dan wallah juma buzu ne kuma yafi ka rashin mutunci.

karamin tsaki yay baice komi ba ya kama hanya ya fice abunsa, acikin motarsa yabude kai tsaye ya jawo jakarsa yaciro wata plqin riga me tsafta snn ya nemi bayi a asibitin yay tsarki ya wanke jikinsa sosai snn yay alwala abune me wuya kaga yahada sallah biyu yaukam a dan dolensa ya haɗa magriba da ishaiii snn ya tura text ma bappa zaidu da mum dinsa...

yana idarwa still baibi takan wayarsan ba ya dawo cikin asibitin baiko kula kakar tasa ba yajeciki ya duba jikin ayaanahn, she is still unconsious amma bana suma ba, bacci kawai takeyi sabida alluran da aka mata na sedatives, yasan it will keep her alive till tmwr morning yasan duk ƙinsa da karban yarinyar kusan dole ne kawai yayi tunanin yadda zaiyi akaita babban asibiti gobe gobe dan amata proper treatment.

SURAYYAHM/***