GUDUN AURE

6

by @bintaumarabbale

Kina Ina yanzu na ji kamar k'arar abin hawa." "Muna cikin adaidaita sahu ni da Sahura na rakata neman aiki a wani kamfani." Ta ce." To an dace dai ko?" Na ce." E, an dace anti." "Ki ba ni ita mu gaisa." Da sauri na mi'ka mata wayar. Bayan sun gama gaisawa ta mi'ko mini wayar muka yi sallama tana sake jadadda mini lallai na gayawa Babanmu maganar bikin da wuri idan da hali shi ma ya zo d'aurin aure. Ni ce na fara sauka a bakin titin gidanmu. Ita kuma aka wuce da ita. Ina sane ban kar'bi kudin da aka ba mu ba. Daf da zan shiga gida ta kira ni tana fad'in"Sis kudinki kin manta." Na ce." Ina sane Sahura ki ri'ke sai ki yi amfani da su." Ta ce.'" Amma ba ki kyauta mini ba wallahi. Kenan duk wahalar ke za ki yi mini." Na ce." Ina wahalar take ni ban ganta ba." Sai ta kashe wayar na san ranta ya baci da abinda na yi. Ina da kudi tunda ba a jima da yin salary ba, bayan haka kuma na yi jakkunkuna da yawa an kai mini kofar wambai. Don na barwa Sahura dubi biyar ba wani abu ba ne idan na yi duba da irin d'awainiyar da ta yi da ni a baya. Shaf na manta da maganar Ummasu Hadiza ina shiga gidan ko zaman minti goma ban yi ba ta leko tana cewa."Amina kin dawo?" Na ce." E, na dawo Umma." Ta ce." Babanku da ya shigo cin abinci ya sake jadadda mini maganar d'azu akan Alhaji Muktari." Na tashi zaune a nutse na ce." Umma kuyi ha'kuri don Allah ni fa ba aure zan yi yanzu ba, sai yarana sun girma tukkuna." Ta jim tana kallona kafin ta ce." Ni kuma sai na ke yi miki sha'awar auran Alhaji Muntari domin Yana da rufin asiri gashi da kula da gida." Shiru na yi ban ce mata komai ba yadda zuciyata take tiriri zan iya furta wata maganar ta yi mata zafi. Sai ta juya ta fita tana fad'in." Wani lokacin arziki Yana kiran mutum sai ya yi ta gudu, ina lefin Alhaji Muntari in banda abin Amina. Na koma na kwanta da nazarin yadda zan kawowa rayuwata da ta yarana cigaba. Da 'kyar na tashi na d'ora mana taliya Ina da miya dama na kan yi ta kwana biyu ko uku." Daf da magariba Yusi ya shigo shi kadai da ledar goruba a hannunsa. Na ce."Gwaggwo ce ta baka ne?" Ya daga kansa yana zaro kudi a acikin aljihunsa ya ce." Baba Hamisu ne ya ba ni dari da hamsin." Na ce." An gode masa, ina Kamalu yake?" "Mama tunda muka je gwaggo ta zuba mana abinci muka ci, sai aka neme shi aka rasa. Yanzu ma Baba Hamisu ne ya tsallako da ni titi, na 'karaso gida. Cikin fad'uwar gaba da fargaba na ce." Aka neme shi aka rasa kamar Yaya?" Ya yi shiru bai ce komai ba. Na d'auki wayata da sauri na nemi lambar Hamisu kanin Babansu ne. Muka gaisa na ce." Yusi ya dawo gida shi kadai, Yana ce mini tun d'azu ba a ga Kamalu ba." Ya ce." E, wallahi ni ma dawowata gida kenan gwaggo take gaya mini, tunda suka ci abinci ya fita, amma ki kwantar da hankalinki zai dawo in sha Allahu, kin san halinsa ba ya zama wuri daya." Na ce." Hamisu Ya zan yi ne? Kamalu ne damuwata a halin yanzu, ka dubi shekarunsa ba su kai sun kawo ba, amma Yana so ya fi karfina." Ya ce." Ki daina fad'in haka Anti Amina, duk yaran namu haka suke k'uruciya ce kawai, da ya kara shekaru zai daina. Sannan ki dinga tsinkaye kafin ki fad'i magana a kansa." A sanyaye na ce." Shikkenan Hamisu don Allah daga ya dawo ka kawo mini shi har kofar gida." Ya ce." In sha Allahu rabbi." Na kashe wayar na ajiye jikina duk babu kuzari na tace taliyar na juye a fulas. Idar da sallata kenan na ji kaya-kaya hayaniya na tashi a kofar gida. Yusi ya shigo da gudu Yana fad'in." Mama wasu ne suka daddaki Yaya har sun fasa gefan ido suna ta ce masa 'barawo, 'yansanda sun riko shi." Gabana ya yi mummunar bugawa. Na tashi da azama na fita. Lokacin matan gidan da yaran duk sun yi waje. Kofar gidan namu ta cika da jama'a, ga Kamalu ri'ke a hannun 'yansanda da wasu yara su biyu a tsakiya. "Wacece mahaifiyarsa ne?" Muryar d'ansandan ta daki kunnane. Saminu ya nuna ni da hannu yana cewa." Gata nan." Ya kalle ni." Yaron nan an kama shi ne yana yun'kurin 'kwacewa yaran nan kud'i an aike su sayan shinkafa a wurin mai awo na kan kwana." Shiru na yi ban ce komai ba illa kaina da yake mugun sarawa. Ya cigaba da cewa." Ku dinga kula da yaranku, duk dai yaran yanzu sai addua amma dai duk da haka sai iyaye sun tsananta kula da addu'a. A dinga basu abinci duk rintsi kada a bar su da yunwa domin itama tana taka muhimmiyar rawa wurin gurbata tarbiyar yaro. Kasancewar shekarunsa basu kai matakin hukunci ba, za mu 'kyale shi. Amma da sharad'i idan ya sake shigowa hannunmu sai mun hukuntashi." Usaini 'kanina ce ya ce." Mun gode Yalla'bai in sha Allahu kuma za a kula, wallahi mahaifiyar yaron nan a tsaye take akansa maraya ne kuma mahaifinsa ya rasu, kawai rashin ji ne irin na mutumin yanzu." Ya zaro dari biyar a aljihunsa ya basu. Suka kama hanya suka tafi. Baba Sule ya 'karaso wurin Yana cewa." Tunda naga cincirindon jama'a a kofar gidan nan na san d'an iskan yaron nan ne ya janyo magana." Jin abinda yake fitowa daga bakinsa ya sanya na shige gida ba tare na tsaya gaishe shi ba. Gabad'aya suka shigo gidan har shi Kamalu da Yake rike a hannun Usaini Baba Sule yana kai masa duka yana ta zagi da aibata shi. Na kwanta hawaye masu d'umi suna bin gefen fuskata. Sai kawai na tsinkayi maganar Ummansu Saminu tana cewa." To dama ai ba dabararka ba ce ba kuma wayonka ba ne. Kullum dai ana ganin namu yaran sune lalatattu, to yau sai gashi kuma su Kamalu har da 'yansanda." Baba Sule ya ce." Shine dama d'an iskan cikinsu ai, za su zo su gurb'a ta mana zuri'a. Ita dai Ummansu Hadiza ba ta ce komai ba. Har ya gama zage-zagensa ya dago labulan dakina yana fad'in." Ke kina Amina." Shiru na yi ban amsa ba. Ya shigo d'akin sosai yana fad'in." Tashi zan yi magana dake." Na tashi ina goge hawayen da suka kasa tsayuwa. Ya ce." Ki mayar da yaran nan danginsu shi ya fi miki kwanciyar hankali, ki yi auranki tunda ba ki wuce ba, akan me za ki zauna ki lalata k'uruciyarki a banza, ba fa ke kike da hakkin kula dasu ba, dangin babansu ne suke da hakki a kansu. Ki kwantar da hankalinki, ki samu nutsuwa in sha Allahu idan ki ka auri Alhaji Muntari ba ke kadai ba, mu kanmu za mu ji dadi, domin mutum ne mai wadata da bushasha ko ni zan huta ta dalilinki." Na dube shi Ina 'kara ganin ba'kinsa a cikin raina. Na ce." Baba Sule ba zan yi aure ba, tunda ba farilla ba ne, musulunci da maslaha ya zo mana. Gaskiya yanzu Babu wannan ajandar a tare da ni, saboda inda da hujja. Bayan haka kuma ni ba yawon ta zubar nake yi ba balle ace ina neman janyo abin kunya, sannan ni nake wahala da kaina da yarana. Don Allah ku 'kyale ni da maganar auran nan haka." Cikin fushi Ya ce." Wallahi tallahi ba ki isa ba, sai kin yi aure Amina. Mu ba al'adar gidanmu ba ce haka, ba za ki zauna mana god'od'o a gida ba." Na dube shi cikin rashin shakku na ce." To shikkenan zan nemi Babanmu da maslaha sai na je na kama haya, tunda ka ce ba zan zauna muku a g.......Ya bi kuncina da mari mai tsanani! Jikinsa na kyarma yake fad'in." Kin samu kudi ko Amina, kina ji babu wanda ya isa saboda ba kya nema a wurin kowa shiyasa ki ke gaya mini maganar da duk ta zo bakinki, wallahi ba ki wuce duka ba, zan zage gabad'aya karfina akanki na nakastaki muddin ba za ki bi umarninmu ba." Ina kuka haikan na ce." Zan fi son ka nakastani Baba ni wallahi ka kashe ni ma, na gaji da wannan duniyar ba zan iya ba, me yasa lokacin da nake budurwa baku damu da aurena ba, sai a yanzu da Ubangijin da ya hallice ni ya ba ni za'bi. Ina da hujja Baba, ba wai Ina gudun auran ba ne, akwai dalilina." Kuka nake tu'kuru Ina fad'in." Baba Sule ka dake ni, idan hakan zai sanya ka huce! Ina so na mutu na riski Yaya Aminu a aljannar Firdausi." Kamalu ya zo ya ru'kunkume ni Yana kuka. Shi ma dan'uwan nasa ya zo ya zube a jikina ya fashe da kuka! [2/13, 7:40 PM] Aunty B: 10&11 Ya kama hanya ya fita daga d'akin Yana cewa." Wallahi tallahi Amina sai kin yi aure, ba za ki gur'bata mana zuri'a ba, don wanna ba ba al'adar gidanmu ba ce. Yadda ki ke ganin kin yi 'kwari a yanzu babu wanda ya isa ya gaya miki ki ji, to nan gaba idan ki ka fi haka za ki ce ba mu muka haifeki ba, sai kin auri Alhaji Muntari muddin ni ne waliyinki." Duk cikin maganganusa babu wadda ta razana ni. Dole dai sai da yarda ta tukkuna za a d'aura mini aure, ban guji auren ba sai da hujja mai k'arfi. Muryar Hamusu na tsinkaya a tsakargidan suna gaisawa da Ummansu Hadiza. Na ji dad'i da bai riski Baba Sule ba, lokacin ya tafi. Ya shigo d'akin Yana cewa." Ina Kamalun yake?''