GANIN IDO

PAGE 31

by @oumameer2671

GANIN IDO 🥀🥀

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671

FREE-BOOK

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

PAGE 31

Yana nan a kwance kan Cushion ɗin ya saƙa ya warware ya saƙa ya warware har misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Yana nan ya ji saƙo ya shigo a private line ɗinsa wanda daga;Hajiya, Labiba, Emraan, Nadeeyah and Hairi. Su ka ɗai ke iya nemansa a wannan line ɗin a duk sanda suka so. Tun kafin ya kai ga ɗauko wayar ya yanke a ransa cewa yasan Wacece ta turo text ɗin.

'Jakadiyar wanzar da zaman lafiya.'

Kalmar da ya furta kenan a ransa sannan ya buɗe text ɗin ya karanta kamar haka:

"Ya Mohaa da fatan kana cikin aminci? Da fatan kana lafiya? If you are awake and safe please let me know....muna hanya gobe tare da Emraan da Hajiya...Muna kan plan ɗinmu kada ka manta, koda mun zo ba'a ɗaura auren ba sai next Friday coming."

"Ina cikin amincin Ubangiji Labiba. Thank you so much. Allah ya tashe mu lafiya."

Tashi ya yi bayan ya tabbatar cewa text ɗin ya shiga sannan ya wuce yaje ya yi alwala ya zo ya yi ta jera Nafilfili yana addu'a kamar yanda ya saba a kowane dare.

********

Washegari, bayan Labiba ta gama shiryawa a tare suka fito ita da Barrister ya kaita har gida. 

  Kafin ta fita daga motar ne ya kalle ta a hankali ya ce.

"Ni na ma rasa wane kalar tunani zan yi Labiba. Emraan ya ce yana sonta, ita kuma ta zo a uzurce ta auri Daddyn Raudah. Sannan shi kuma da akace Aljana ce ta aure shi tsawon lokaci ta hana mishi aure, sai ga shi cikin ƙanƙanin lokaci an ɗaura kuma yana zaune lafiya babu abinda ya same sa......Ta yi gargaɗin kada a sanarwa kowa a dangi har yanxu...."

Jinjina kan shi ya shiga yi still idonshi a kanta ya ce.

" Tabbas! There is something fishy Labiba! Dole akwai abin da ba daidai ba. "

"Ni kai na a rikice nake wallahy Barrister. Komai ya dagule mini wanda har na rasa ma wane kalar tunani zan yi. And kuma na gode Allah da har na ankare na bugewa Oga Sule warning cewa kada ya faɗawa kowa cewa ya kaini gidan su Beenafah, Kaga hakan kuwa ya yi rana."

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.

" Ba damuwa. Allah ya tsare yasa a dawo lafiya, Allah yasa kuma ya amince ya biyo ku ɗin."

"To Amin. Na gode sosai."

Tana shiga gidan ko ɗosana ɗuwawunta ba ta kai ga yi ba, Hajiya ta kalle ta jiki a sanyaye ta ce.

"Labiba kin tabbata auren nan zai yiyu da gaske? Labiba ni fa ina jin tsoro..."

Langaɓar da kanta tayi gefe a hankali tana mai marmaɗa idanunta sannan ta yi murmushi tana jinjina kai ta ce.

"I'm 100% sure Hajiya....muje ki zage ki haɗawa surukarki lefe. Sannan kuma..... what I suggest is that;tukuicin wannan Amaryar da iyayenta shi ne mun yafe musu kayan ɗaki, a kwashe kayan upstairs ɗin can nasa tunda Allah ya kaimu a zuba sababbi..."

Still zuciyar Hajiyar cike da doubting take kallon Labibar ta ce.

" Labiba kin tabbata auren nan zai faru?"

" Oh Allah! Hajiya Emraan fa ya shirya. Dan Allah ki zo mu tafi kada mu tsaya ɓata lokaci... "

Cikin nuna ƙwarin gwiwa jinjina kanta ta ce.

"Ni kuwa, matuƙar dai wannan auren ya faru da gaske,to na yimiki babban alƙawari Labiba... Amma ba zan faɗa miki yanzu ba sai idan an ɗaura auren kuma ta tare a gidannan."

"Na gode Hajiyata, ina marari da ɗokin jiran wannan lokacin. Allah ya tabbatar mana da alheri."

Suna cikin uzurin fitowa sai ga Munira ta shigo, bayan ta gaishe da Aunty Labibar sannan ta kalleta tare da miƙa mata wata leda ta ce.

"Aunty Labiba ga wayar nan da Ya Emraan ya siyawa Beenafah. A nan ta barta ɗakinmu ko buɗewa ba ta yi ba."

Jinjina kanta tayi sannan a kaikaice ta kalli Hajiya, ganin hankalinta baya nan ta kalli Munirar ta ce.

"ki je ki ajiye wurin ki, duk ranar da Ziza ta dawo ki ba ta ki faɗa mata yanda kika faɗa mini ɗinnan..."

Fitowa ta yi da gudu tana mai fashewa da dariya ta shige tana baiwa Haula labarin abin da Aunty Labibar ta ce.

Itama dariyar ta yi ta ce.

"Ni kuma In Sha Allahu a wannan ranar tare zamu tafi in raka ki muga wane kalar reaction ɗin za ta bada."

Girgiza kai Munirar ta yi tana faɗin.

"Allah sarki!, ko'ina Beenafah take?"

"Hmm! To kin gani dai? Duk abin da nake gudu sai da ya faru, nasan tun da ya furta mata wannan furucin dole sai wani abu ya biya baya. Kuma ni ina kyautata zaton Hajiya Korarta ta yi."

"To su suka sani Haula. Allah ya bata wani wurin wanda ya fiye mata nan."

"To amin."

Bayan su Hajiya sun wuce. Misalin ƙarfe ɗaya Nadeeyah ta iso gidan ita da yaranta. Isowarta ba'a yi hour ba aka shiga shigowa da kayayyaki ta gate ɗin baya mota tafi uku, kayan abinci ne birjik, kayayyakin aiki, turame da laces komai da suke buƙata na bukin shi ne ake ta jibgowa kamar hauka.

Zuwa Yamma sai ga Hairiyya ta iso itama. Tana shigowa da er Jakarta ta goyawa a baya ta rungume Nadeeyah tare da zubowa da ruwan hawaye ta ce.

"Aunty Nadee wai da gaske auren Ya Mohaa za'a yi a gidannan? It's just looking like a dream to me... I'm scared kada ace za a fasa....."

Cike da yaƙini ta jinjina mata kanta ta ce.

"In Sha Allahu za'a yi. Na siyo mana kaya amma ban kai ɗinki ba, sai ki kira Hazim ki bashi. Zan je in yi magana da baƙin ma'aikatan da suka iso a yanzu."

"OK! Bari na fara yin wanka tukun. Please ki faɗawa Dija ina ɗakina, she should come and meet me."

********

Koda na fito misalin ƙarfe bakwai na safe, na tarar da wata matashiya tana goge-goge da alama ta kambala shara ne, sannan ga wani ƙamshin daɗi yana fitowa daga ɓangaren Kitchen ɗinda ya nuna mana jiya.

" Ina kwana Hajiya!"

Matashiyar ta faɗa da ɗan rusunawa.

Hawayen da suka silalo mini ne na share da tafin hannuna sannan na jinjina kai ina kallonta murya a ƙasa na ce.

"Lafiya ƙalau! Sannun ki da aiki"

Hanyar kitchen ɗin na nufa ina mai jin mamaki a raina, wai yau ni ce Beenafah muke da mai aiki a gidanmu har tana kirana da Hajiya cike da girmamawa! Allah sarki! Komai mai lokaci.

Ina shiga na tarar Ammie ita da wata dattijuwa haka na gaishesu a tare sannan matar ta kalleni da fara'arta ta ce.

"Wannan ɗin ita ce Amaryar da Alhaji ya faɗa mana kenan? To Allah yasa albarka."

Ammie ce ta amsa da amin, yayin da na juya kurum na koma tsabar mamakin da har yanzu ya kasa barina.

Ɗakin Bahrain na wuce direct wanda na iske ya yi ɗaiɗai a ɗan madaidaicin gadonsa yana bacci ga sanyin Ac mai daɗi yana hurashi.

Murmushi na yi tare da samun bakin gadon na zauna kawai ina tunani na cewa 'Shin familyn shi da yace suna tafe Ya ya za su ɗauki Ammie da mu? Idan har matarsa ta amince masa da ya auri Ammie to sauran en uwansa fa? Ya Allah ina tawassali da sunayen tsarkaka! Ya Allah wannan auren da Ammie ta yi don kawai taga cewa na samu cikar burina ya Allah kasa ya zama silar farin cikinta duniya da lahira.'

Ina nan zaune a hankali sai ga Bahrain ya farka. Wanka na ce ya je ya yi nima zanje in yi nawa yanzu domin bamu san wane lokaci ne za su zo ba.

Bayan na kambala shiryawa a tare muka fito har Ammie. Murmushi na yi na ce.

"Ammie kema kin shirya kenan?"

Jinjina kanta ta yi ta ce.

"Ya kirani a waya yace ƙarfe goma suna nan zuwa..."

Wata er dariyar ce ta suɓuce mini ina kallonta na ce.

"Waya Ammie? Ina Wayar take?"

Hararata ta yi sannan ta yi kwafa kawai ta wuce kitchen ɗin ta kawo mana abincin kari da kanta... Hmm! Wai duniya sabuwa. Muna zaune muna cin abincin Bahrain ya janyo wayar yana faɗin.

"Ga wayar nan Aunty Beena....wayar ma ai ɗaya ce daga cikin wayoyin da na gani a hannunsa."

"Allah Sarki Abbu!"

Ina faɗin haka shi kuma Bahrain ya fashe da wata irin dariya ya ce.

"Shike nan ba zamu ƙara cewa Dr. Basheer ba.."

"Ka sha giyar wake ne da za ka kira shi Dr. Basheer? Ka ɗauke shi ka girmama shi tamkar Abbie ne. Ka tsayu ka yi karatu Bahrain, sannan ka girmama duk wanda ya zo ta gefensa ka bashi muhimmanci...."

Duk firar nan da muke tana nan zaune tana cin abincinta uffan ba ta ce mana ba, muna nan sai gashi ya ƙara kiran ta, nan take ta miƙe kawai ta shige ciki ta barmu zaune a table ɗin muna ci gaba da shiririta muna dariya.

Misalin goma da rabi kuwa muka ji an buɗe gate ɗin gidan, jikin window na je na tsaya ina kallo. Motoci guda uku ne suka shigo jere da juna.

Ina ganin mutane na ta fitowa na kalli Ammie dake zaune jiki a sanyaye na ce.

"Ammie ga suna nan shigowa wallahi da yawa suke har da maza a ciki..."

Miƙewa ta yi tare da zura hijabinta cike da ƙarfin hankali ta je ta buɗe musu ƙofa tana musu maraba.

Hayaniya ce ta karaɗe ko'ina na parlourn wurin gaishe-gaishensu, daman kuma ga yara ƙananu a tare da su.

Bayan sun gama gaisawa da Ammie nima na kalle su na ce.

"Ina kwananku...sannun ku da Zuwa."

Matar Dr. Basheer ɗin wacce daga cikinsu ita kaɗai muka gane ce bayan sun amsa ta kalle ni tana faɗin.

"Ita ce Beenafah, Amaryaarmu..."

Suna cikin tofa albarkacin bakin su ne Dr. Basheer ɗin ya shigo fuskar nan ɗauke da fara'a ya samu wuri ya zauna yana kallon Ammie ya ce.

"Hajiya Mulaifa kin gan su ko?....Wannan ita ce Matata wacce kika sani Hajiya Asma'u, ga Hashi yarona na biyu, Yayarsa Huda tayi aure tana Kebbi, sai ƙaninsu gashi nan Haidar.... Wannan kuma ta gefena Hajiya Sameera kenan ƙanwata da take bina..Ga Zubair wanda shi ma ƙanina ne....."

Haka dai ya shiga lissafamana duk wanda ke wurin da dangantakarsu. A yanda muka ɗauki abin ba haka ya kasance ba, domin mutanen sun karɓemu hannu biyu-biyu musamman Hajiya Asma'u. Yayin da kuma wasu suka ɗan sha jinin jikin su da alama dai bamu yi musu ba. Daman haka rayuwa take Komai zamowar ka mutumin kirki ba za ka taɓa samun so ba 100%, haka zalika ba za ka taɓa samun ƙiyayya ba 100%.

Duk yan da Ammie take ɗari-ɗari sai da suka yi ta janta da surutu suna ta yi mata fatan alheri da fatan zaman lafiya. Suna nan sai misalin ƙarfe biyu sannan suka tattara suka tafi sai Hajiya Asma'u da ta tsaya nan suka shiga tattauna yan da za'a gudanar bukina kamar yanda Dr. Basheer ɗin ya yi alkawari wanda a nan suka yanke cewa za'a yi Kamu ayi Walima da wunin buki, ranar Tuesday, Wednesday da Thursday, ranar Friday Kuma tun ƙarfe tara mu ɗauki hanya kamar yanda su ka yi wa Aunty Labiba alƙawari.

Washe da wuri ta sake dawowa gidan namu tare da Hashi da Mummy Sameera kamar yanda na ji Hashi ya kirata. Bayan sun gama tattaunawa suka shirya suka fice har da Ammie wai za su je kasuwa. Dr. Basheer kuwa yana can ya saka aje kama musu Hall sannan ya yi musu order ɗin duk abun da suka rubuta masa na buƙatar kayayyakin amfani.

*********

Tun da Mummy ta farfaɗo take sabbatu kala-kala marasa kan gado.

Duk yanda ake lallashinta ta ƙi ma ta kwantar da hankalinta ballantana a nema mata mafita. Sannan duk abin ya cakuɗe musu domin shi ma Daddy dai duk ya shige gashi tamkar wani marar lafiya.

Babu abin da take tunawa taji hankalinta ya tashi irin auren nan gashi ya matso saura kwanaki amma babu wata mafita. Sai dai kuma Uncle Ismaila ya ce ta kwantar da hankalinta ta bashi kwana biyu akwai abin da yake planning akai. Hakan yasa suka dakata da duk wani shirye-shirye suka zauna jiran Uncle Isma'il.

Gidan duk ya yi wani iri tamkar gidan mutuwa. Su Aysha suna nan dai sun zubawa sarautar Allah ido. Idan auren ya faru fine..idan ma bai faru ba sai ta tattara ta koma wurin Mijinta ta huta da ganin wannan baƙin cikin.

Yau ma Mummy tana nan ta yi zaune tana ta rusa uban kuka ta ji ƙugin Motoci suna ta shigowa gidan.

Wani irin ƙuuu! Ta ji sai da Hanjin cikinta suka koka, domin tasan cewa tabbas waɗannan ɗin Su Ameer ne daman sun ce za su zo, to amma Uncle Isma'il ya ce zai san yanda zai yi ya hana musu zuwa amma ta ya ya suka yi nasarar ƙarasowa gidan kenan??

Hankalinta a tashe ta shiga ƙwala kiran Daddy ba ji ba gani tana kiran ta shiga uku, shikenan asirinta ya tonu.

A tare suka shigo har da Uncle Isma'il ɗauke da sallama a bakinsu.

Miƙewa ta yi lokaci ɗaya ita da Daddy suna rarraba ido suna wani yi musu yaƙe amma ba don suna cikin jindaɗi ba.

Bayan sun gaisa Ameer ɗin ya ce.

"Na zo ganin Beenafah ne...naga kamar abin zai yi wani iri ace ana ta zancen buki amma ni da ita bamu tattauna ba..."

"Uhmm! Ka gane ko Ameer....Dadd....daman ana shirya mata ne, tana can gidan gyaran jiki sai ana gobe ɗaura aure za'a dawo da ita.."

Kallon Ameer ɗin Uncle Isma'il ya yi ya ce.

"Ameer! Magana ta gaskiya ita ce; Beenafah an aurar da ita,daman kamar yanda na yi maka bayani tun can cewa marainiya ce, kuma so suke su aurar maka da ita saboda cutarwa to amma sai gashi Allah yasa mahaifiyarta ta samu wani ta aura mata...."

Wata irin tsawa Daddy ya doka masa cike da maɗaukakin mamaki ya ce.

" Isma'il!!! Isma'il kana cikin hayyacinka kuwa?"

Girgixa kai Uncle Isma'ila ya yi ya ce.

" Da hankalina Alhaji Mudassir adalci ne nake nema da masalaha. Daman bayan an nemi Hassana an rasa, na baku shawarar cewa ku aura masa Beenafah, to wani abun da ba ku sani ba shi ne; ni nan da kaina na je har gidan Alhaji Mansur Anka na yi masa duk wani bayanin shirinku da ƙudurinku da kuma cutar da marainiya da kuke da niyyar yi kamar yanda kuka ci amanar uwarta. Shi ne na roƙesu akan su haƙura su jingine burinsu da son auren en biyu su aura masa Beenafah da ita Husaina domin dukkan su mutanen kirki ne, sannan sai da ya yi mini alƙawarin riƙeta komai zai faru na ce kada ya yarda ya sake ta... To sai gashi kana naka Allah yana nasa iko Beenafah da mahaifiyarta sun fice daga tarkon ku..."

Wani irin gigitaccen mari Mummy ta sauke masa cike da wani irin sabon shock ɗinda ya fi kowanne ta ce.

" Isma'il ni za ka ci wa Amana? Ni yayarka uwa ɗaya uba ɗaya zaka ci wa Amana??"

Wani irin malalacin murmushi ya saki sannan ya Girgixa kai yana wani kallonta a sheƙe ya ce.

"Duk wani maci Amana Hajiya Zaliha ai bayanku yake...Mata daga mutuwar Mijinta kuka zalunce ta, kuka haye kan dukiyarsu kuka zauna a kai..."

"Isma'il miye yayi zafi haka da har ka shirya mana wannan cin amanar??"

"Because ni Hajiya Mulaifa ta fiye mini ke! A cikin kayan ta na samu gwalagwalai na kai aka bani milliyan goma sha ɗaya wanda da su ne na fara zuwa Lagos ina ɗauko kaya har yau inda na zama shahararre dukiya ta ninku. Ke fa? Ƙololuwar kyauta ta da ke shegiyar dubu hamsin ce...kin ko ga irin wannan gatan da Hajiya Mulaifa ta yi mini mi zai sa na cutar da ita? Ni sai daga baya ne ma na gane cewa banga laifin da ta muku ba kune azzaluman...saboda haka ni In sha Allahu daman na kuɗura a raina zan mayar mata da kuɗin ta sannan na roƙi gafararta, kuma ko yanzu ba zan sare ba, zan ci gaba da nemanta In Sha Allahu. Sannan abu na gaba da ya kamata ku sani shine... HASSANA ba guduwa ta yi ba kamar yanda kuka ɗauka. Nan garin ta zo inda muke muka aurar da ita ga SALMAN ɗinda take so yake sonta...."

✍️ OUM-AMEER ✍️