GANIN IDO

PAGE 34

by @oumameer2671

GANIN IDO 🥀🥀

ADABI WRITER'S ASSOCIATION

AMEENA IBRAHIM

OUM-AMEER

*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671

FREE-BOOK

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

PAGE 34

Duk irin ƙarfin zuciya da Emraan yake da ita sai da ya fashe da kuka tsabar baƙin cikin wannan irin mummunan abun da ya riske su a yau mai cike da baƙin tarihi da abin faɗa a gare su muddin dai wannan maganar ta fita.

Kuka suke sosai wanda ta kai ga babu wanda ke rarrashin ɗan uwansa.

A raunane Lababi ta waigo ta kalle ta tana wani irin kuka ta girgiza kanta ta ce.

"Hajiya wannan wane irin mummunan labari ne haka? Wannan abun ya yi muni.... Wallahi ya yi muni Hajiya...Ina ma ace fatan mutuwa na da kyau.. Wallahi tallahi da na roƙi Allah ya ɗauki raina akan wannan mummunan rana da ta riskeni...Yay...yaya Mohaa...bamu taɓa ji ko a mafarki cewa shi ɗin ba ciki ɗaya muka fito ba. Tun tasowarmu har zuwa yau bamu taɓa samunsa da wani abun munanawa agareki ba ballantana mu zarge shi akan cewa yana miki ba daidai ba da har zai sa mu fahimci cewa ba ke ce kika haife sa ba....Wato ashe duk tsananin so da ƙaunar da kike nuna masa ashe duk na GANIN IDO ne Hajiya? Ke ɗin uwa ce a gaban idonsa amma a bayan sa ke ce maƙiyiyarsa ashe....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kai duniya! Wai ina za ki damu ne haka??"

Muryar Emraan suka ji yana faɗin.

" Hajiya! Wannan abun da kika aikata son zuciya ne kawai da ra'ayi irin naki! Dalilin da kika kawo Sam ba dalili ba ne. Ni,Labiba, Nadeeyah, Hairiyyah...tun da Alhaji ya faɗi ya mutu yaya Muhammad shi ne ya dawo komai namu, makaranta, magani,abinci, sutura...ya kula damu ya bamu soyayya Hajiya...yanda yake son ki yake ƙaunarki na yi imani ko mu nan iyakar son da muke miki kenan. Shi ne fa ya nema min aikin nan, ya nemawa Labiba ya nemawa Nadeeyah...shi ne yakai Hairi makaranta a Madina. Duk da cewa muna da hanyoyin samu, duk wata sai ya tura mana kuɗaɗe na Musamman. Abinci, motoci, abin hawa gida komai na rayuwa na jindaɗi ya tanada mana kuma bai taɓa yi mana iyaka akan komai ba...Hajiya duk ƙasar da kike so kai tsaye kike samun damar zuwa duk ta dalilin sa, idan kika nuna masa abu kika ce masa wannan fari  ne to yafi farin zama fari a wurinsa. Idan kuma kika nuna masa abu kika ce masa wannan abu baƙi ne to wannan baƙin  yafi gawayi baƙi a wurinsa...idan kince kin yi hakan ne saboda mu mi muka rasa? Idan kuma kin cutar da shi saboda ƙashin kanki miye ribar ki?.... "

Girgiza kai ta yi cikin gunjin kuka ta ce.

" Babu! Wallahi Babu Emraan! Sharrin shaiɗan ne kawai da zugin ƙawayena.... "

Cike da jin wani irin malolon baƙin ciki Labiba ta girgiza kanta ta ce.

" Idan kika ambaci ƙawaye a nan Hajiya to tabbas kina ƙara munana abun ne ni dai ta gefena,domin ni ɗin nan dai na san cewa ke ce kika haifeni kuma kina sama dani, idan na ce miki wai wata ƙawata ce ta zugani na aikata wani kuskuren to ko ke za ki yi Allah wadai dani ballantana ke da kike mahaifiyata... "

" Wallahi Labiba Sharrin shaiɗan ne da Hajiya Samiya... Ita ce wacce ta ɗorani akan wannan shawarar ta kuma tabbatar mini cewa duk ranar da na bari ya yi aure ya haifi 'ƴa'ƴa watarana sai ya gano cewa ba ni ce wadda na haife sa ba, kuma idan har hakan ta kasance to fa daga ni har yaran da zan haifa ko mutuwa ya yi sisi ba zamu tsira da shi ba... "

Cike da takaice Emraan ya girgiza kai yana faɗin.

" Oh Common Hajiya please Ki daina magana kamar wata ƙaramar yarinya. Ke kike maganar nan amma kuma ni kunya take kamawa wallahi.... Wannan abun da kika yi Hajiya wallahy Hairi gata nan ba za ta iya aikatawa ba Hajiya...Sannan yanzu dan Allah da wanne idon kike son na kalli Ya Muhammad? Da wanne ido kike so duniya ta kallemu idan ta ji abin da kika aikata masa??"

Daga haka ya miƙe shima har yana haɗa hanya ya fice daga parlourn tare da ɗaukar motar sa ya wuce gidansa.

Ajiyar zuciya Labiba ta sauke a hankali tana mai ci gaba da share hawayenta ta kalli Hajiya ta ce.

" Kin san me Hajiya? Mafi munin kuskuren da kika aikata shi ne cutar da ɗan da ya ɗauke ki matsayin uwa. Hajiya duk abin da bawa zai samu Ubangiji ya riga ya rubuta masa tun yana Cikin mahaifiyar sa. Arzikin sa, ajalin sa, aikin sa, wallahi duk Allah ya riga ya gama ƙaddara komai. Wayonki ko kuma dubarar ki, babu ɗaya da zai fishsheki. Ko da Yaa Mohaa, ko babu Yaa Mohaa, arzikin da Allah ya nufeki da shi dole shi za ki samu babu wanda ya isa ya ƙara miki akan haka....... Munyi baƙin ciki da wannan abun,matuƙar baƙin ciki Hajiya. Na sani, da ace Alhaji yana doron duniyar nan da zai fi kowa baƙin ciki da wannan abun da kika aikata. Mun taso cikin haɗin kai da ƙaunar juna yanzu kin ɓata hakan Hajiya...."

Miƙewa ta yi a hankali ta shiga zagan kyakkyawan parlourn tana kewaya tana jinjina kai ta ce.

" Wannan gidan...lokacinda aka gama ƙerashi....mun shigo cikinsa muna farin ciki aka saka kaya lokacin da aka saka rai da auren sa da Hanifah, ƙarshe da auren bai yiyu ba, haka aka rufe shi cike da baƙin ciki na tsawon lokaci, babu wanda ya sake takowa cikinsa ko sau ɗaya sai yanxu da aka yi nasarar samun wacce za ta shigo cikinsa....Amma! Saboda son zuciya irin na ki, ko yau ga shi ba'a yi nasara ba domin haka za'a sake rufe shi cikin baƙin ciki kamar can baya."

Daga hakan itama ta fi ce ta koma ɓangaren Hajiyar, su Nadee na ganin ta fi ce suka miƙe a tare suka bi bayanta. Ta ɗauki tsawon lokaci zaune a inda suka barta tana ta kuka yayin da zuciyarta ta sarƙafe da wata irin nadama wacce ta ji ina ma tun farko ba ta fara aikata wannan aika-aikar ba. Ta yi ta tunanin lokaci makamancin wannan, amma kuma da yake shaiɗan ya nutsa zuciyarta sosai har ta yi nisan da ba ta jin kira sai taci gaba tana ganin za ta iya yin nasara musamman da ta ji ya ce ya bar ƙasa har Abada saboda ba zai iya zama babu Raudah ba....Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ina ma ace za ta iya dawowa da hannun agogo baya? Ina ma ace tun farko ba ta amince da wannan bahaguwar shawarar ba? Da yanzu mutuncin ta bai zube a gaban 'ƴa' ƴanta ba. Idan wannan abun kunyar ya fita ina za ta tsoma ranta ta ji sanyi?... "

A hankali ta ji takun takalmi a bayanta, hakan yasa ta waigo da sauri tare da miƙewa tsaye.

Hairiyyah ta gani tsaye tana ta kuka tana girgiza kai. Da gudu ta zo ta Rungumeta tare da fashewa da wani kukan tana faɗin.

" Hajiyaa! Haƙiƙa kin aikata babban kuskure mai muni da mafi girman kunya a duniya...Amma ni ban san kowa ba ban san komai ba idan ba ke ba Mahaifiyarta, da kuma Yayana Muhammad da sauran 'ƴan uwana. Kun bani tarbiyya yanda ya kamata musamman ke ɗin nan! A yanzu Ke ce wadda kika ɓata komai, amma ina roƙonki ki yi tunani mai kyau, kada ki sare....Ubangiji mai yafiya ne muddin bawa ya yi tuba na gaskiya...Ke ce kika ɓata, saboda haka ke ce za ki san yanda za ki  gyara. Kin fi kowa sanin waye Ya Mohaa..."

Murya a raunane ta ce.

" Hairiyya wallahi sharrin shaiɗain ne dan Allah ku yafe mini.. "

" Ba komai...Allah yasa mu dace yasa kuma mu fi ƙarfin zukatanmu."

Tana kambala faɗar haka ta ja hannun Hajiyar tana faɗin.

" Mu je... Mu je gida ki huta."

*******

Tun da ya daka mini wannan tsawar na sha jinin jikina na lafe wuri ɗaya a hankali ina ci gaba da raira kuka ba tare da sauti ba....Tsoro ne fal a ƙasan raina amma kuma ban san yanda zan yi ba. Abun da na yarda da shi shi ne har abada na san ba zai iya cutar da ni ba. Babu tunanin da bai zo mini ba musamman na su Aunty Labiba da Hajiya.....ina yi ina lissafi har bacci ɓarawo ya yi nasarar sa ce ni.

Ban san cewa na yi bacci mai nauyi ba sai da na motsa a hankali kwatsam na ji ni cikin jikin mutum ga wani irin ƙamshinsa da ya cika mini ƙofofin hancina, ina buɗe idona naga hannunsa ɗaya kewaye dani ina kwance kan ƙirjinsa ya ƙanƙameni sosai sannan ɗayan hannun kuma yana riƙe da waya a kunnen sa yana magana.

Janyewa na yi da sauri na matsa baya ina wani muzurai gabaɗaya jin yanda kunyarsa ta gama kamani. Shi kam Ko kallona bai yi ba ballantana ya nuna alamar cewa ya fahimci ma farkawar tawa,wayar sa kawai ya ci gaba da yi wanda yana yi yana kallon gefen windown da yake zaune tamkar bai san da wanzuwata a wurin ba.

Nima windown da ke gefena na ware ido ina kallon waje kamar yanda yake kallo. Duk da cewa rufe take ruf da duhu an sanya mata tinted ko'ina, hakan bai hanani fahimtar cewa garin ya gama yin haske ba. Ma'ana kenan tunda muka fito muke tsula gudu bamu tsaya ko'ina ba har gari ya fara haske. 'Sallah fa?' na furta a zuciyata domin tabbas ba mu yi sallar asuba ba.....shiru ni dai na yi ina ta istigfari a raina domin ba ni da laifi shi ne mai laifin, ko zunubi ne shi a za'a rubutawa ba ni ba. Hakan yasa na ƙara jinginawa jikin car seat ɗin tare da lumshe idanuwana kawai ina tunanin Ammiena ba tare da sanin inda muka dosa ba.

  Lakeview Crescent,

Asokoro, F.C.T., Abuja,

   Nigeria.

A hankali motar farko dake gaba mai ɗauke da jami'an Secret Tactical Guides da suka shahara wajen bada kariya da tsaro a wurin manyan mutane masu ƙumbar susa suka shiga sarrafuwa domin sun iso madakatar mai gidan na su. Motar ƙirar Range Rover sentinel ce ta Ƙarya corner in a slow motion ta shiga titin unguwar da gidansa yake. Sai mota ta biyu Mercedes-Maybach S680 Guard Edition wadda ita ce motar da muke ciki. Sai kuma A bayanmu, wa su G-Wagon Brabus ne guda biyu masu ɗauke da bodyguards ɗinsa waɗanda ke sanye da black tactical suits, earbud da kuma bulletproof vests.

"Eagle One approaching Asokoro zone, switch to Silent Protocol.....Repeat, silent mode activated."

Ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa ta hanyar sadarwar da suke tafiyar da aikin su (wannan wani yare ne na masu tsaro wanda suke amfani da shi a sirrince wanda da wuya mutum ya iya fahimtar abin da hakan ke nufi idan ba kana aiki tare da su ba ne. Ma'ana suna nufin Engineer Muhammad Attahiru Araam ya iso.)

Lokaci guda motar lead escort ɗin ta kashe na'urar tare da ƙara rage gudu fiye da na baya ta sulale cikin lakeview Crescent. Babbar unguwace mai gate-gate ɗinda ba ka isa ka wuce ba sai an tantance da zuwanka.

Muna isa, ƙofar gate ɗin katafaren gidan da ta kasance automatic ce sai ta buɗe kanta cike da wani irin sauti mai nuna alamar tsaro.

Muna shiga cikin zafin nama suka sauko suka buɗe masa ya fito. A hankali ya zago inda nake zaune ya buɗe da kansa ya riƙa hannuna a hankali ya fito dani. Ina haɗa ido da su na ji wani irin matsanancin tsoro ya kamani tamkar kace ƙyat! Na zura da gudu. Sai yanzu na ƙara godewa wannan veil ɗin da yake kaina, domin da ace babu shi da yanzu haka za su riƙa kallona kamar wata Stella. Ina ganin suna wani gaisheni na ƙara janyo veil ɗin na rufe fuskata domin bana ƙaunar ma haɗa idanu da su tsabar yan da suke firgitani.

Wani robotic sound na ji daga jikin bangon ƙofar yana faɗin.

"Security Level: Maximum....Intrusion mode:Activated"

A hankali cikin takunsa na zaratan Maza ya fara jana cike da nutsuwa ba kamar jiya da ya janyoni da ƙarfi ba muka taka muka shige gidan wanda yake upstairs ne mai hawa uku na ji da gani.

Muna shiga a main parlour muka tarar da masu aiki maza da mata sun yi cirko-cirko suna ta faman miƙa mana gaisuwa.

Bai ko tsaya tanka su ba muka zarce a hawa na biyu muka yada zango a tsakiyar parlour inda a nan ne ya buɗe wani ɗakin da kansa muka shiga. Kallona ya yi a karon farka idanunmu suka sarƙe ya wani lumshe a hankali ya buɗe in a calm voice ya ce.

"Ki yi sallah a nan."

Daga haka ya juya ya fi ce.

Tashi na yi na zazzaga ɗakin wanda sosai na ji ya ƙayatar dani, sannan na wuce banɗakinda ya yi mini tamkar wani ɗakin bacci akan faɗin sa da tsaruwarsa. Hankali kwance na cire kayan jikina na gama duk buƙata ta sannan na yi wanka na yi alwala na ɗoro veil ɗina na fito.

Ina zuwa kan makeken gadon ɗakin na tarar da wasu shopping bag an zubesu a nan.

Janyowa na yi na buɗe wanda ba komai a cikinsu sai kayan amfanina da alama yanzu aka siyo su. Shiryawa na yi shaf-shaf cikin wata haɗaɗɗiyar Abaya peach colour na zuba hijabi na gabatar da sallah Asuba. Bayan na kambala ina nan a zaune tsawon lokaci ban ji ɗuriyar kowa ba wanda hakan yasa na miƙe a hankali na buɗe ƙofar na fito.

Zaune na gansa a kan 3seater ya  tallafe gefe-gefen kumatunsa yana kuka wiwiwi tamkar wani ƙaramin yaron goye. A gigice na isa garesa ina faɗin.

"Subhanallah! Ya Mohaa mi ka ke yi haka? Ka yi haƙuri dan Allah..."

Janyoni ya yi jikin sa har sai da na ji na tsorata ya ƙanƙameni gam tare da manna fuskarsa akan ƙirjina wanda har ina jin saukar ruwan hawayensa akan skin ɗina, ga kuma kwantaccen Sajensa da ke ƙara sa tsikar jikina tana ta shi yana wani gugar jikin nawa. Sosai jikina ya ɗauki ɓari amma kuma ganin yanda yake kuka ba ƙaramin tausayi ya bani ba. Haƙiƙa na san zafin cin amana fiye da kowa a duniyar nan, Hakan yasa duk da ina a tsoracen na saka hannayena na zagaye wuyansa cike da tausayinsa ni ma na fara hawaye ina faɗin.

"Ka yi haƙuri... Allah yana sane da kai...!!!"

Ya jima sosai yana kwararar da ruwan hawaye wanda sai da ya gaji don kansa sannan daga ƙarshe a hankali ya sassauta tare da janye jikinsa ya buɗe idanunsa da suka rine sosai suka canja launi ya kalleni cike da ƙwarin gwiwa ya jinjina kai ya ce.

" Thank you... Thank you for saving me..."

Daga haka ya janyo wata ƙaramar wayarsa ya daddana a hankali ya kai wayar saitin kunnena kurum ba tare da ya ce komai ba.

Jin muryar Ammie na yi tana mai yin sallama a cikin wayar. Cikin farin cikin jin sautin muryar ta ta na ce.

" Halo Ammie... Ammie ina kwana!"

"Lafiya lau Beenafah. Ya gajiya ya kuma tashin mai gidanki? Ina fata yana lafiya?"

Kallonsa na yi kamar yanda shima ɗin yake kallona ko ƙyaftawa babu, ɗan murmusawa na yi na ce.

"Lafiya lau muke Ammie, ga shi nan a zaune yana gaishe dake. Ina Bahrain, ina Abbu ina su Mama??"

Murmushi ta yi wanda har ina iya jiyo sautinta sannan ta ce.

"Beenafah kenan! Kowa yana nan lafiya, Bahrain bai tashi bacci ba kin san shi da samun wuri."

"To Ammie idan ya tashi ki gaishe sa da Abbu."

"Za Su ji In Sha Allahu... Su Aysha ma har sun ta so.."

Cike da mamaki na ce.

"Ammie tun yau za su koma kamar ana korar su??"

"To Beenafah, ke da suka je domin ki amma kuma tafiyar uzurin mijin ki tasa kin tafi kin bar su mi za su tsaya jira??"

Sake ɗago kaina na yi daga wasa da yatsun hannuna da nake na kallesa wanda har yanzu ya kasa ɗauke idonsa a kaina cike da mamakinsa na jinjina kaina kawai na ce.

" Uhm! Haka ne kuma. To Allah ya tsare. "

" Amin. Sai an jima na gode."

        ✍️  OUM-AMEER   ✍️