PAGE 39
GANIN IDO 🥀🥀
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHIM
OUM-AMEER
*Wattpad:@Ummu-Ameer* Arewapen:@Oumameer2671
FREE-BOOK
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
PAGE 39
Sannu a hankali rayuwa ta shiga tafiyar damu wanda a yanzu mun shafe tsawon wata uku cikin na huɗu a tare. Wata irin shaƙuwa ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu wanda a yanzu na sake da shi sosai ba kamar farkon zuwanmu ba,musamman da na lura shi ɗin mutum ne mai ɗaukar abin da yake so da matuƙar muhimmanci, ya ɗaukeni tamkar wata aminiyarsa da ya kwashe tsawon shekarun rayuwar sa tare dani. Hatta wurin aikinsa sau uku yana tafiya dani da sunan rakiya,haka ma cikin gari mun fita sau biyu mukaje wuraren da suka sakani nishaɗi.
Kullum muna tare da juna sai idan zai yi tafiya ta barin gari irin ta kwanaki haka zai tafi ya barni cikin kewar sa, domin a yanzu idan baya nan ko baccin kirki bana iya yi a yanda na saba da kwana cikin jikin sa, idan ya nisance ni hakan yana mini wahala. Yasa na yi sabon da rashin sa a kusa dani yana sakani kasala,tun ina jin kunyar sa har na zo na saba wanda hatta cin abinci yanzu tare muke yi, dama duk wasu abubuwan rayuwa namu sun zamo ɗaya kamar yan da ya tsara. Gashi kuma Shi ɗin mutum ne kaifi ɗaya wanda bai iya lungu ba,komai kai tsaye yake gabatar da shi, duk abin da yake so na sani dangane da rayuwar sa ko wani abu, kai tsaye yake sanar dani tare da fahimtar dani da kyau yanda zan fahimta.
Yau ma bayan na yi sallar asuba komawa na yi na kwanta ban fito ba sai misalin sha ɗaya na safe. Da Wayata babbar Samsung ɗinda ya siyamin sati uku da suka wuce na fito a hannuna na shige Kitchen kai tsaye muka gaisa da su Madam Amima wacce ita ce ke kula da Kitchen ɗin na duk abincin da za'a sarrafa mana ita da sauran ma'aikatan. Bayan mun gama gaisawa cike da girmamawa ta tambayeni abin da zanci na ce mata ba komai zan duba abin da suka dafa ɗin da kaina tun da ni kaɗai ce a gidan, domin ya yi tafiya yau kusan six days kenan, abun da bai taɓa yi ba, duk ƙoƙuwar tafiyar sa kwana ɗaya ne ko biyu highest Idan ya daɗe ya yi spending 3days ya dawo.
Tea na haɗa kaɗan sannan na zuba abincin da suka dafa shima kaɗan a plate na zauna a kitchen island na ci, Bayan na kambala na ɗauki wayata na kira Ammie muka gaisa sannan na kira Aunty Labiba wacce naga miss calls ɗinta har guda biyu itama muka gaisa da ita. Bayan na gama na miƙe naje bakin fridge na ɗauko bottle water waɗanda basu cika sanyi ba sannan na duba kan fridge ɗin na ɗauko maganina na Folic Acid wanda na fara sha tun farkon dawowarmu daga asibiti bayan ya yi min bayani da cewa Dr. Ashman ne ya bayar kuma ya yi masa bayani na musamman akan cewa yana da matuƙar muhimmanci Macce ta fara shan sa atleast Wata uku kafin ta ɗauki ciki. Dalilin haka kuwa, shi ne;yana zama rigakafi daga hana samun nakasar ƙwaƙwalwa da ƙashin baya na jariri wanda ake kira (Neaural tube defects) kamar cutar da ake kira spina bifida wanda ƙashin baya zai rabu gida biyu ya kasa haɗewa da juna ko kuma Anencephaly wanda za'a haifi yaro babu murfin ƙwaƙwalwa ma'ana babu ƙashin kai. Wanda waɗannan cututtukan da makamantansu suna faruwa ne a makonnin farko na ciki a lokacin da ake haɗa halittar ɗan adam, wani lokacin kafinma mace ta gane tana ɗauke da juna biyu. Hakan yasa ake ƙarfafa Mata game da zuwa asibiti kafin ɗaukar ciki dama bayan sun ɗauki ciki sannan ake ƙarfafa su akan shan folic acid kowace rana.
Sannan shan folic Acid yana ƙara lafiyar mahaifa da ƙarfafa ƙwayoyin halitta da kuma taimakawa wurin ɗaukar ciki cikin ƙoshin lafiya. Yana hana karancin jini abinda ake kira (Megaloblastic anemai) wanda idan akwai ƙarancin jini yana kawo gajiya, kasala, rauni kafin ko bayan samun ciki.
Sannan shan folic Acid yana inganta lafiyar jiki da jini gabaɗaya, yana taimakawa Mace ta samu lafiyayyen ciki ba tare da wata matsala ba. Sannan bayan cikin ya samu still shan folic Acid yana da matuƙar muhimmanci domin yana taimakawa wajen gina ƙwaƙwalwa da kyau da kuma jijiyoyin mahaifa domin ta samu ƙarfin riƙe jariri. Yana taimakawa wurin samar da lafiyayyun ƙwayoyin jini (Red blood cells) ga Uwa da kuma Jaririn. Yana inganta gina gaɓoɓin jiki domin yana taimakawa wajen gina DNA da kyau abinda ake kira Gene( wato ƙwayoyin halittar gado wanda ɗan adam yake samu daga uwa ko uba a lokacin halitta kamar, launin fata, gashi, ido, tsawo, da wasu siffofi dai na daga ɓangaren uwa ko na uba su gini da kyau ba tare da wata nakasa ba).
Sannan shan folic Acid yana da matuƙar muhimmanci domin yana rage yawan haɗarin haihuwar ciki wanda bai kai lokacin haihuwa ba abin da ake kira (premature birth) da Kuma haihuwar yaro wanda nauyin shi bai kai adadin yanda ake buƙata ba (Low birth weight). Ko kuma yawan mutuwar yaro a ciki abinda ake kira (Intra-uterine fetal death). Folic Acid Yana da muhimmanci sosai domin yana bada kariya daga cututtukan chromosal abnormalities musamman ga mai shekaru da yawa da yake buƙatar haihuwa.
Haka ya zauna ya karantar dani amfaninsa daki-daki wanda tun daga ranar ban taɓa tsallake rana ɗaya ba ba tare da nasha ba. A nan na ajiye kan fridge ɗin na musamman gudun kada ma na manta, idan kuma yana gari kullum shi ne wanda yake ɗaukowa da kansa ya bani nasha.
Ina tsaye bakin gangar fridge ɗin bayan na sha riƙe da ruwan a hannuna na shiga ƙoƙarin kiransa da numbern da naga ya yi min text daren jiya kawai na ganshi ya shigo ya tsaya gabana.
Gabana ne ya yanke ya faɗi ganin irin yanayin da yake ciki. Gabaɗaya idanunsa sun sauya kala, fuskar nan ta yi kajin-kajin, kwata-kwata dai Sam baya cikin karsashinsa da ya saba.
Hankali tashe na kallesa na ce.
"Subhanallah! Lafiya kuwa? Miye ya sameka haka??.."
Ƙarasowa ya yi gabana kai tsaye ya rungumeni sosai tamkar wanda zai mai da ni ciki. Shiru na yi nima a hankali na saƙala hannayena zuwa bayansa tare da ɗora kaina akan ƙirjinsa wanda har ina iya jiyo sautin yanda zuciyarsa ke bugawa a hankali. Bayan mun ɗauki tsawon lokaci sai na ɗan zame kaina a hankali na ɗago na kalle shi cikin tausasawa na ce.
"Allah yasa lafiya?"
A hankali ya binne fuskarsa a gefen wuyana sannan ya shiga gogawa yana sniffing ƙamshina har zuwa fuskata ya yi kissing lips ɗina lightly Sannan ya janye cikin wata iriyar murya mai cike da rauni ya kalleni ya ce.
"I'm sorry Beenafah....I'm so sorry da duk irin rayuwar da kikayi a baya....ashe kema haka kika rayu cike da ƙunci da baƙin ciki?? I... I don't know anything about you sai yanzu....na kasa Bacci na rasa abin da yake min daɗi. Ashe da ciwo haka sosai a rayuwarki...a haka kuma kika sadaukar da kanki gareni don kawai irin taimakon da Labiba tayi miki just because kiga ta yi farin ciki...Kin sha wahala Beenafah, abubuwan da suka faru dake sunfi ƙarfin ƙwaƙwalwarki da shekarunki..Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!... "
Bansan lokacin da wani murmushi ya suɓuce min ba akan mamakin yanda ya duk ya susuce ya rikice. Jinjina kaina na yi ina kallon sa still da murmushi da kuma hawaye a idona na ce.
" Wai Kuka kake??"
Jinjina kansa ya yi yayin da ya kafe idonsa a nawa ya ce.
"Da ni kaɗai kika da ce Beenafahta domin nafi kowa sanin muhimmancin ki a duniya...idan zan tuna abun da ya faru dake sau dubu sai na mutu sau dubu akan baƙin ciki da takaicin yanda kika kasance.."
Jinjina kaina na yi tare da sauke ajiyar zuciya a hankali na ce.
"And that's what life is all about....Ɗan Adam ba zai gushe ko in ce ba zai huta daga dukkan igiyoyin ƙaddara ba har sai ranar da akace ya faɗi ya mutu...amma muddin yana raye...to tabbas, arzikinsa, sarautarsa, mulkinsa, wayonsa, dabararsa, ko kuma talaucinsa basu isa su hana faruwar duk abin da Allah ya ƙaddaro masa ba. Duk gatanmu sai da muka wayi gari cikin tsananin ƙunci, yunwa, azaba, da tauye haƙƙi...Kai kuma, duk kuɗin ka, girmanka, dangin ka da duk shaharar da kayi a duniya,hakan bai hana maka shiga cikin matsanancin ƙunci da baƙin ci ba, sannan wacce take zaman uwa a gareka... Sai gashi ta kasance ita ce ƙaddarar ka... "
Sake rungumeni ya yi muryarsa har tana sarƙewa ya ce.
" Haƙiƙa kin cancanci farin ciki da kwanciyar hankali na rayuwa Beenafah... Kuma na yi alƙawari....muddin ina numfashi a doron ƙasa to tabbas zan tsayu akan dugadugaina wurin baki dukkanin wani farin cikin da ya dace da rayuwarki.."
Janyewa na yi da guntun hawayena ina kallon tare da neman yanda zan kwantar masa da hankalin sa na ce.
" Thank you....yaushe ka dawo.?..sannu da zuwa!"
Ganin ya ƙura ido yana kallona baice komai ba yasa na ɗan shagwaɓe fuska na ce.
"Ni fa kasan bana son inga kana damuwa wallahy, hankalina tashi yake yi..."
"Dole na damu Beenafah..."
Hannunsa na kama ina murmushi na katse shi da faɗin.
"Komai ya yi farko yana da Ƙarshe watarana Ya Mohaa...Ubangiji ne kaɗai wanda bai da farko kuma bai da Ƙarshe...amma dukkan wani al'amari na duniya tabbas yana da farko kuma yana da Ƙarshe...kamar dai NI da KAI ɗinnan yanda al'amarinmu ya kasance..Ga shi yanzu ka same ni nima kuma na same ka...."
Kaina na mayar akan kirjinsa sannan na ci gaba da cewa.
" Abubuwa sun yi maka yawa, kullum cikin aikace-aikace kake. Idan kace za ka riƙa saka wasu damuwowi a ranka, to tabbas abin ba zai yi kyau ba. Na gode sosai da yanda ka damuna nima kuma ina alfahari dakai."
Ina gama faɗar haka na riƙe hannun sa muka wuce ɗaki ya yi wanka domin shigowarsa gidan kenan da alama a hanya ya kwana.
Bayan ya gama shiryawa na kawo masa abincin yaci sannan ya tashi ya ɗauki jakar sa ya fice office bai dawo ba sai kusan 9:pm. Sai da ya tsaya ɗakinsa yayi wanka ya shirya sannan ya shigo inda nake wanda ni a lokacin har na yi wankana nima na gama shirin bacci.
Yana shigowa na na sauko daga gadon na ce.
"Sannu da zuwa..."
Murmushi ya yi tare da kallon sleeping dress ɗinda ke jikina, ya ce.
"Beenafah."
"Na am."
Na amsa masa ina murmushi.
"Ya kika wuni? Ya daren? Koda yake kin faɗamin cewa bakya jin bacci...miye naga kina yi lokacin da na kiraki?"
Murmushi na yi na ce.
"Ina ɗakin can wanda muka shiga ranar, wani littafi ne na ɗauko...."
"Uhm. To kinci abinci?"
"Aa..ba kai ne kace in jira ka ba.."
"Ok to, muje."
Dining area muka je muka zauna kamar masu cin wani abincin kirki domin daga ni har shi ɗin ko plate ɗaya cikakke bamu ci ba.
Parlour muka dawo ya janyo table ya ɗora kayan aikinsa kamar kullum ni kuma na zauna a bayansa tare da manna jikina da bayansa na buɗe littafin da na ɗauko daga cikin kayansa wai shi the power of Du'aa.
"Beenafah!"
"Na am!"
Na amsa masa jin ya kira sunana ba tare da na motsa ba.
"I have something important to share with you....juyo ki gani."
Ajiye littafin na yi tare da zuro ƙafafuna na sauko na ce.
"Mine ne wannan?"
Wani babban file ne na fata dake gabansa ya buɗe ya ɗauko wasu takardu sannan ya ɗauko wani abu mai kamar sanda dogo ya warware wanda ashe babban Map ɗin Nigeria ne. Pointer ya ɗauka yana nunawa ya kalleni ya ce.
"Duba nan ki gani.....Da yammar nan na yi receiving business proposal daga multinational company a nan Dubai. They want me to supervise a new pharmaceutical plant construction in Nigeria. And location ɗin a Kaduna State ne..."
Ɗan wara ido na yi na ce.
"Kaduna? Za ka sake komawa Nigeria kenan?"
Jinjina kansa yayi ya ce.
"Yes, but amma ba yanzu ba."
Wata red marker ya ɗauko ya nuna min wani site yana faɗin.
"Suna so ne zuwa next month in tafi in yi inspecting ɗin wurin, Idan naga cewa wurin zai yi kuma na yi accepting...then the contract will run for two years.."
Ɗagowa ya yi ya kalleni yana jinjina kai ya ce.
"That's why I wanted to discuss it with you first...your opinion matters to me more than the offer itself..."
Shiru na yi tare da ƙure takardar da kallo ina nazari da kuma mamakin yanda rayuwa ta gangaro damu har ta kawomu wannan matakin wanda yanzu hatta harkar kasuwancinsa idan zai yi sai ya nemi shawara ta.
"Beenafah.."
Ɗagowa na yi na kallesa na ce.
"To idan ka je kayi Inspecting ɗin kaga wurin ya yi mi za a yi?"
"While....Aiki ne za'a yi babba...Basically, i will be the project consultant....i will design the layout for the research lab,production plant, and quality control unit...and kin san wani abu.?"
Girgiza kaina na yi alamar a'a.
"The payment is 1.2 million dollars for the entire contract."
Jinjina kaina na yi ɗauke da Mamaki a fuskata na ce.
"Duk da cewa ban san lissafin kuɗinba, amma dai daga ji suna da yawa sosai."
"Uhm! It's huge. But you know, money isn't always everything, Kaduna has its own challenges and the work is technical...i might have to stay long wani Lokacin..."
Wani kallon na jefa masa mai nuna zallar kulawa na ce.
"To me...your safety comes first...duk wani abinda zai saka ka wahala ko kuma ya zama barazana ga rayuwarka ko kuma lafiyarka ni ba son sa nake ba.."
Jinjina kansa ya yi cike da alfahari ya ce.
"In Sha Allahu babu abin da zai same ni Matata, addu'arki tana tare dani.."
Daga haka ya ƙara gyara zaman Map ɗin a kan table ɗin ya shiga nuna min wasu wurare da marker ɗin yana faɗin.
"This red zone here...represents the land area they have secured..and the blue lines show the water access for the factory, and this green mark...that's where the main admin building will be....."
Haka ya zage ya bayyana min duk yanda aikin zai kasance idan har abun ya yiyu sannan daga ƙarshe yace.
" Zan iya yi ko kuma kina ganin na fasa? What's your verdict?"
" While...shawara ta a nan shi ne, ka tsaya ka yi istihara a kai, idan har Kaga akwai alheri sai ka yi, idan kuma kaga babu alheri, sai ka bari.."
Jinjina kai ya yi yace.
"I will do exactly what you said Beenafah....thank for existing.."
Murmushi na yi ina mai duba agogon wayata na wani langaɓar da kaina a shagwaɓe na ce.
"Ni fa ina jin bacci..."
Yana na kan na ɗiɗiye map ɗin ba tare da ya kalleni ba ya ce.
"Idan zan yi sallah na tada ki?"
Girgiza kaina na yi ina dariya na ce.
"A'a ni dai....Ranar ma Kaga koda ka ƙarasa bacci ya sure ni..."
Ajiyewa ya yi yana min wani kallon yace.
"And kwana biyu ma da kika ga bana nan baccinki kawai kike ko?"
Hannu na saka na rufe fuskata ina dariya ina girgiza kaina alamar a'a. Kawai na ji ya janyoni zuwa jikin sa shima yana dariya yana tsungulata a hankali yana faɗin.
"Amma miye abin da na faɗa miki..iyeehh? Miye abin da na faɗa miki na ce..??"
Zillewa na fara ina jin ba daɗi still da dariya na shiga girgiza kaina ina faɗin.
"Wayyo Ammie...dan Allah ka yi haƙuri!..."
"To miye na faɗa miki?"
"Wayyo Allah na.. Wallahi cewa ka yi komai jin daɗin duniya da mutum yake yi ya kula da neman lahirarsa..."
"Na ce ta wace hanya kenan??"
"Wash... Wash... Allah na..kace sallar dare, azumi,sadaka,nafilfil...Wayyo Allah dama sauran su...wayyo ni...Wallahi na gaji dan Allah ka daina.."
Sama na ji an yi dani wanda bai direni a ko'ina ba sai a tsakiyar gadon ɗakinsa sannan ya dawo ya kashe mana fitilar ɗakin ya kunna dimlight ta bedside drawer a hankali ya hauro. Shiru na yi tare da ƙundudunewa don wallahy da gaske dariyar da na yi tasa na ji na gaji mamakinsa fal a raina domin bamu taɓa yin irin wannan wasar ba sai yau.
Janyoni ya yi na kwanta a ƙirjinsa kamar ko yaushe, a hankali ya kai hannun sa ya zare min ribbons ɗinda na saka na ɗaure gashina da su sai gashi ya bazo akan ƙirjinsa zuwa fuskarsa. Ɗagowa na yi na kallesa duk da cewa bana iya ganin sa da kyau sakamakon hasken ya yi ƙasa sosai, a shagwaɓe na ce.
"Ni wallahi sai ka ɗaure min tun da wahalar kamawa ne da shi..."
Cikin wata iriyar muryar da ban saba jinsa da Ita ba ya ce.
"I will...a hankali ai kina koyar dani wasu abubuwa da yawa kuma kin ga ina riƙewa...."
Daga haka ya zamar dani zuwa gefen damarsa ya ɗora kaina saman damtsen hannunsa muna fuskantar juna yakai bakinsa saitin kunnena ya raɗa min cewa.
"A wannan daren.....zamuyi musayar saƙonnin da suka jima suna dakon amintaccen lokacin da ya dace.....kin gama min komai a duniya Beenafah..wannan ɗin...shi ne abu mafi girma da ya rage ya kasance a tsakaninmu,wanda faruwar sa zai canja abubuwa masu yawa a tsakaninmu..... I promise to be gentle and nicer than you think....."
Bugun zuciyata ne ya sauya lokaci ɗaya, jin wasu irin batutuwa da ni ke jin kamar ina tare da wani mutum na daban.
Fuskarsa ya kai ya binne cikin wuyana inda ya haɗe da gashin nawa da fuskarsa muka haɗe wuri ɗaya...a hankali ya shiga aika min deeps kisses masu ɗauke da wani irin saƙon da lokaci ɗaya na ji na kasa jurewa domin wani irin ɓari jikina ya ɗauka tamkar an jonani a shocking...a hankali ya gangaro zuwa fuskata romantically ya shiga kissing ɗin lips ɗina tare da saka hannu a hankali ya shiga unbuttoning ɗin sleeping dress ɗita wanda Ko yau wasu riga da wando ne a jikina masu matuƙar santsi, sai dai su wandon a cinyata ɗina ya tsaya sannan hannun rigar kuma guntu ne....jin da gaske ya gama ɓalle maɓallan rigar gashi kuma babu komai a ciki yasa na girgiza kaina ina wani irin numfashi na riƙe hannun sa muryarta na wani irin rawa na ce.
"A'a... Yaya dan Allah...!! Dan Allah fa nace...."
Tun da ya yi nasarar ciremin rigata yakai fuskarsa da hannayensa akan tsayayyun breast ɗina da lallausar fatar ƙirjina ya gigice min, har wani irin gurnani yake wanda ya ƙara gigitani da wani irin tsoro wanda na kasa riƙe kaina kamar yanda ya kasa controlling kansa shima.
Yanda nake jijjiga haka shima jikin sa ya ɗauki wani irin ɓari, haka ya shiga sarrafani bai ji bai gani kamar wani mayunwancin Zakin da ya shekara bai ci abinci ba.
Ban ƙara shiga cikin tsananin tashin hankali da ruɗani ba sai da na ji ya raba ƙafata biyu a hankali ya kai hannunsa wanda yana yi yana addu'a sannan ya ƙara gangarowa ya haɗe bakinmu wuri ɗaya a haka har ya yi nasarar kaiwa ga abin da yake muradi.
Jin wani irin azababben zafi na ratsani na janye bakina inata rusa kuka ina turashi ina faɗin.
"Innalillahi!... Wayyo Ammie...Wayyo na shiga uku..wallahi Zafi...Dan Allah Ammie ki zo ki ceceni zan mutu wallahi......Wayyo ka daina dan Allah wallahy bana so...Kai ne fa kace ba za ka iya cutar dani ba... Amma miye haka kake yi.. "
Wato wannan daren, shi ake kira daren ihun ka banza. Domin wallahy na gurzu ba ɗan kaɗan ba. Na yi kuka tamkar raina zai fita harda majina tsabar wahala da ficewa hayyacina. Mutumin nan ya mamayeni a lokacin da ban tsamma ta ba. Tun ina ɗari-ɗari ina zuƙewa ina tsoro, bai farmake ni ba sai yanxu da ya gama shashatar da ni yasa na gama sakin jiki da shi yay min wayo.
Bayan ya gama shan budurinsa can cikin magagin zafi na ji ya miƙo hannu ya janyoni...hannayena na saka guda biyu na turesa da ɗan sauran ƙarfin da ya rage min ina sheshsheka murya can ƙasa tsabar yanda nasha kuka duk ta dusashe na ce.
"Ni wallahi ka ƙyaleni...you broke the Promise you made..and kuma hakan ba daidai bane.."
Ko kalma ɗaya ya kasa furtawa, hakan yasa ya ƙara matsowa ya janyoni ina ta wani zillewa ya saka ƙarfinsa ya rungumeni cikin jikinsa a hankali yakai bakinsa saitin kunnena cikin wata irin kasalalliyar murya wacce da ƙyar yayi nasarar ƙaƙalo wasu kalmomi ya furzo su zuwa gare ni,ya ce.
"I'm sorry Bibi...I love youu"
Laƙwas! Haka na koma cikin jikin nasa na lafe tare da ɗora kaina akan ƙirjinsa ina jin kalmomin da ya furta a gare ni suna yawo a cikin kaina har bacci ya yi nasarar ɗaukemu. Baccin nake amma kuma ba don yana mini daɗi ba, sai wani juye-juye nake wanda daga ƙarshe na farka a hankali na buɗe idona. Jin kamar ina jin alamar zazzaɓi wanda ko ɗaga ƙafata bana jin zan iya yi yasa ni fara zubar da hawaye a hankali ina yi ina kallon fuskarsa cikin ɗan hasken da ya rage.
Jin saukar damshin ɗumin ruwan hawayena akan ƙirjinsa yasa a hankali ya buɗe idanunsa ya kalleni tare da kai hannu ya yaye gashin kaina ya mayar da shi baya ya shafo fuskata zuwa idona...ni kuma jin kamar hannunsa ya ɗauki ɗumi yasa nima na kai nawa hannun da sauri akan wuyansa da goshinsa, jin yanda ya yi zafi rau yasa na wani waro ido a gigice na ce.
"Na shiga uku...are you sick??...Huh!..ji..ji yanda jikinka ya yi zafi..miye abun da ya same ka.??"
*******
Gefen su Daddy kuwa, sai da suka shafe tsawon wata biyu a asibiti bayan ance an yi nasarar yi masa aikin amma kuma kullum babu wani ci gaba, domin har yau babu wanda yayi magana wannan ta fatar baki da shi kullum yana sanƙame da bututun shaƙar numfashi.
Suna nan a wannan hali wasu daga cikin ƙawayen Mummy suka bata shawara akan cewa su fitar da shi ƙasar waje kada ya zo ya mutu a banza.
Haka suka shiga kicaniya wanda gabaɗaya mummy ta dawo tamkar wata mahaukaciya, ta gigice ta susuce ta fice daga hayyacinta.
Suna nan suna neman yanda za a yi Hafiz ya bada shawarar siyar da babban shagon da ta yi nasarar buɗewa, domin a yanxu basu da wasu kudi isassu da za su yi amfani da su wurin tafiya nema masa magani har ƙasar waje.
Da farko ta so ta yi tirjiya wanda sai daga baya bayan ta rasa yanda za ta yi dole aka soka shi kasuwa aka siyar sannan aka shiga fafutar tafiya.
Suna gida da yamma Ita da Hafiz, Aysha da kuma en biyu, daman ita Humaida tana can asibiti sun baro ta wurin Daddyn. Suna nan suna lissafin tafiyar gobe da za'a yi da Mummy da Hafiz sai suka ji ana sallama ƙofar gida.
Cikin mamaki Mummy ta kalli Hafiz ta ce.
"Waye ne Hafiz?"
"mummy ni ina zan sani bayan muna nan tare da ke.."
Jinjina kai ta yi sannan tace.
"Jeka ka dubo wata ƙila tallafin da muka nema ne muka samu."
Yana zuwa ya ga wasu abokanan aikinsa daga kamfaninsu na Wazeermed pharmaceutical tun daga Lagos sun zo tare da wasu mutane guda uku.
Cikin wani irin jin sanyin rahama ya miƙa musu hannu da niyyar su yi masabaha amma ga mamakinsa sai ya ga sun ja baya.
Wani daga cikin mutum ukun nan da bai sani ba sun miƙo masa envelope da uban stamping ta.
Karɓa ya yi hannu na rawa hankalinsa a tashe ya ce.
"Ta miye??"
"Idan ka karanta za ka gani."
Nan gabansu ya buɗe ta ya fara karantawa kamar haka:
WAZEERMED PHARMACEUTICAL COMPANY LTD.
Headquarter: 22 Wazeer Industrial Estate. Glass House, Lagos, Nigeria.
To:
Hafiz Mudassir Wazeer
Glass House, Lagos State, Nigeria.
Takardar tuhuma akan aiki ba tare da bin ƙa'ida yanda ya kamata ba.
Ƙarshen bincike da sashen doka da ladabtarwa na kamfanin Wazeermed Pharmaceutical Company Ltd. ya gudanar ya tabbatar da cewa kai, Hafiz Mudassir Wazeer, kana aiki a matsayin Manaja (Manager) a kamfanin dake Lagos ba tare da ingantattun takardun shaidar karatu ko ƙwarewar da ake buƙata ba.
Wannan lamari yana ɗauke da babban laifi na karya dokar kamfani da kuma rashin gaskiya a wajen aiki, kamar yadda aka bayyana a sashe na 8 (c) na Wazeermed Employment Regulation Act.
Saboda haka, bisa bin ƙa’idojin ladabtarwa na kamfanin, an kama ka tare da umarnin tsare ka ta hannun sashen tsaro na kamfani tare da haɗin gwiwar Corporate Affairs Investigation Board (CAIB) domin ci gaba da bincike.
An sanar da cewa ba za a sake ka ba sai bayan an biya tarar doka da kuɗaɗen gudanar da shari’a, waɗanda Alhaji Mudassir Wazeer, wanda ya sanya hannu a matsayin gwarzonka (guarantor) lokacin da aka ɗauke ka aiki.
Idan kuma ba a biya waɗannan kuɗaɗen cikin kwanaki bakwai ba daga ranar da ka riski wannan takarda ba, za a miƙa shari’ar ka zuwa ofishin Federal Corporate Crime Unit (FCCU) domin gurfanar da kai a gaban kotu.
Ana ba ka shawara da ka bada cikakken haɗin kai ga sashen bincike domin gujewa tsatstsauran hukunci.
Sign By:
Barr. Kabiru Lawal (LL.B, BL)
Shugaban Sashen Doka da Ladabtarwa
Wazeermed Pharmaceutical Company Ltd.
"Mummyyyy!!!"
Ya ambata a gigice jin abin da yafi ƙarfin tunanin sa......
✍️ OUM-AMEER ✍️