02
RA'AYI NE KO BURI.?
2
LAGOS..
Murtala Muhammed International Airport Lagos
...⚡Shi ya tuko Babban Jirgin na kamfanin AERO CONTRATORS AIRLINES Dake Shake da Mutane kama Daga yan kasuwa da wasu kososhi agwannati da masu kudin Nageria Daga United Kingdom zuwa Babban Filin na Murtala Muhammed Dake garin na Ikko...
Jirgin Yada de da Sauka tun wajen 12pm na rana Har Ma mutanen Dake ciki Sun Firfita kowa ya kama kanshi Wasu Motar gida ce tazo Daukansu wasu kuma,Taxi suka shiga zuwa cikin gari.
Bude Kofar Babban Jirgin Akayi ya sawo kanshi Waje Yana sanye da Uniform dinsa Black din Wando Sai Farar Riga mai Dauke da Wasu igiyoyi ta saman Kafadun mai baki da Ratsin yellow,Hulan sa tana Hannunsa Gashinsa na Fara kallah yadda yawani Nannade waje Daya Duk da Shi din ba ma"aboci tara suma bane sosai Daga saman gefen Kirjinsa naga wani Dan Anani wanda yake bayyana Matsayin Uniformin din Jikinsa.
*PILOT A.S.MAINASARA* Naga an Rubuta a jikin Dan Ananin Dake gaban Rigarsa, da Doki na Bi Fuskarsa Da kallo Lokaci Daya da Tsarin Jikinsa kakkkarfan Namiji ne mai cike da Zati,kai tsaye bazamu kirashi Fari ba,kuma ba baki bane Choculate colour ne,Mai Faffadan Kirji da zati Fuskarsa ba Doguwa bace sai dai Tana Fadi kadan,sai Hancinsa Dayake Dogo wanda ya karama Kyakyawan Fuskarsa kyau,Sajensa baki shi ya taimaka wajen Zagayen Karamin bakinsa,idanuwansa Suna Lumshe ne da wasu Zararan gashin ido,sai da yadago naga Manyan idanuwansa masu Dauke da Fararan Idanuwansa masu Razana Duk wata mace mai lafiya.
Giransa tana Cike da gashi baki Silib kallon Farko zakamai ka Fahimci Ya hada iri ne da Fulani ko Ta bangaren Uwa ko na Uba,Tattausan Hannunsa na kallo Wanda ke sanye cikin Wani Rantsatsan Agogo na kamfanin DKNY,mai kyau da Tsari baki sai Kafarsa cikin Wani bakin Takalmi Sawu ciki mai kyau da yarari na kamfanin Rado.
Wayarsa ya ciro Daga Cikin Aljihun Wandonsa,Ya kunnata ya kira Direbansa Mr James akan yazo ya Daukesa lokaci Daya ya Sake kasheta,kafin ya Fara Taku cikin Haraban Filin Jirgi.
Abokan aikinsa Dake cikin Filin Jirgi yake bama Hannu suna gaisawa Sai lokacin Naga bayyanar Fararen Hakoransa masu karamai kyau da kwarjini Lokacin Da wani Dogon Namiji Fari sosai kamar Balarabe ya Daki Kafadansa yana Fadin"Babban mawakin mu kuma Babban matukin jiragen sama.."Fararen Hakoransa ya saki kafin ya waigo suka Sarke hannun juna Lokaci Daya suka Rumgume cike da Tsantsan Farinciki.
Sakin Juna sukayi kafin yace"Yaushe ka Daawo Ahiil..? U Suprises me..",?wanda aka kira da Ahiil ya Daki Kafadansa yana Fadin"Jiya na shigo koda nazo kuma kana sama,I miss u ya su mom and Dad hop kowa lafiya..?
Mainasara yace"Kowa lafiya,ya ka baro su Abbi..?!"Yace Normal wlh.."Da haka suka Rike hannun Juna suka Fara Tafiya suna Hira Har suka kusa Fita Daga Haraban Filin jirgin inda wata Bakar Mota Kirar Range Cover tazo tayi parking agabansu,tsayawa sukayi suka danyi mgana kafin su sarke hannun Juna kafin yayi kokarin Bude Motar James Yayi Saurin Fitowa Daga Bangaren Direban yana Fadin"wlcm Sir..."Kai ya gyada mai kafin ya Bude mai bayan motar ya Shiga Lokaci Daya yana Dagama Ahill hannu.
Cikin Abunda baifi Minti Daya ba Motar ta Bar Haraban Filin Jirgin,Ajiyar zuciya Ya sauke lokaci Daya yana maida kanshi ya jingina cikin Cussion din kujeran,Motar Lokaci Daya yana Shafa gashin kansa cikin Wani yanayi Wayarsa ya ciro Daga cikin Aljihun Uniform dinsa Wayace mai tsada Kirar Samsumg,kunnata yayi Domin Tunda zai tuka jirgi ya kashe wayarsa Tunda ka"idarsu kenan.
Sai da wayar tagama processing kafin ta Saitu Daidai wajen Contact ya shiga Lokaci Daya naga ya Tsurama wani suna ido... Ummah... Naga an Rubuta cikin Mirmishin yake, shafa Sunan da Hannunsa yana Fatan yaushe ne Umma zata kalleshi amatsayin Danta ta yafemai Laifin Datake ganin ya aikata mata...?
Dailing yayi nombar ta shiga Tafara Ringing Har Sai da Ta kusa katsewa Daga chan Bangaren Aliimah ta mikoma Hajiya Fatima wayar tana Fadin"Umma Ya Abba Na kiranki awaya.."
Kamar bazata karba ba sai ta Muskuta tana ijiye Littafin Gulubil Mara din Data ke karanta Gyara zaman mayafin kanta tayi tana Fadin"Kun karisa Abincin...? Kai Aliimah ta gyada kafin tace"Eh Umma ke kadai muke jira Asiya ta shiga wanka ne..."Kai ta kara gyadawa Daidai Lokacin Data Daga Kiran tana Fadin"ok kema kije kiyi wanka gani nan Fitowa yanzu.."Da hanzari yar matashiyar Budurwan ta Fice Tana Fadin"Tom Umma afito lafiya.."
Muryan Umma data Dakeshi Lokacin Datayima Alimah mgana Shiyakara Sakashi yaji wani iri cikin Sanyin Murya mai cike da Dattako ta Furta.."Assalamu Alaikum.."
Cikin Sauri Mainasara ya amsa da Fadin"Wa"alaikis salam Gug afternoon Mah..."Yafada yana Shafa Kirjinsa cikin Faduwar Gaba
Wani Takaichi ya kama Hajiya Fatima kamar ta Zubda Hawaye Ta kara Tabbatarma kanta cewa Hajiya latifa cutar data mata ba kadan bane,bayan ta kwace mata D'anta kwara Daya bai isheta ba sai da Ta gurbata mata Rayuwar Yaro ta Ruguje Burinta akanshi Ta saka yazama kamar ba nata ba,wajen maidashi wani chan Dabam,taci buri kan Rayuwar Danta Abdulmutaddif ammh Hajiya Latifa ta wargaza mata komai Ta hanyar Mara masa baya wajen cikar Burinsa na zama mawaki Abunda kullum in ta Tuna sai taji Zubar kwallah Tun Lokaci Taji gwara tabarma Hajiya Latifa Mainasara Zai fi mata Sauki Data Dinga kallonshi amatsayin Nata bakinciki ya kasheta Duk da yanzu din ya zama cikar Burinta bata taba jin zata Sauko Daga Hukuncin Data yanke ba.
Jin Tayi Shuru yasa ya kara Fadin "Hello mah.."Wani tsawa Ta dakamai tana Fadin"Kai wai ni Tsaran kane..? Ban hana ka kirana kana Cemin wata mah ba..?bana son Iskancin Banza da Wofi Daya yau in Bazaka iya Kirana Umma kamar yadda Sauran Ya"yana ke kirana ba Ka kirani Hajiya Fatimata.."Tafada cikin Fushi da Fada.
Idanuwansa suna lumshe ne lokaci Daya ya waresu yana Taune leben kasan Bakinshi cikin Sanyi Murya yace"Kiyi hakuri Umma..."Yafada yana kokarin maida kwallar Data cikamai cikin idanuwansa.
Shuru tayi tana Sauraran Bugun Zuciyarsa,Ganin yaki kara mgana ne,yasa tayi kokarin ijiye wayar tana Fadin"Zan ijiye wayar Tunda baka da Abun Fada.."Da Sauri ya Daga Hannu yana Fadin"A"a Umma plz karki ijiye Don Allah..."!Yafada cikin Muryan Biyayyah,Lokaci Daya yana Sauke ajiyar Zuciya.
Tsakanin uwa da Da Sai Allah Tuni taji Tsausayinsa ya kamata Sai ta fasa ya yanke Wayar jin yana Numfashi sama sama ne yasa tayi Saurin cewa"Lafiyanka meke damunka...? Cikin Damuwa da Sauri yace"Bakomai Umma...Dama na kiraki ne na gaisheki jiya ban samu na kiranki ba ina sama ne sai yanzu na sauka.."Kai ta gyada kafin tace"Nagode Allah ya taimaka..."Daga haka sukayi Shuru Dan mirmishi ya saki kafin yace"Zan zo Sati na sama Umma Nida Ahill ya Dawo...Nayi kewarki sosai..."
Cikin Sauri Hajiya Fatima tace"Kada ka kuskura kazo Abdulmutaddif......!!"Tafada cikin Fushi,Saurin Runtse idanuwanshi yayi kafin yace"Ummaaa...."!!!""Tsaya nace kada kazo...Ka zauna inda ka zaba da kuma inda mahaifinka ya zabar maka...Ni ba mahaifiyarka bace Latifa itace ta Haifeka domin Daka Daukeni Uwa da baka Biyema Mahaifinka da Zuciyarka wajen Zabar Abunda ni bana so ba!..tuni na yafe ka ga Latifa Mutaddif ni Hajiya Fatima bani da wani D'a bayan Aliimah da Asiya kai kana matsayin D'an Mijina ne..."tafada hawaye suna Taruwa cikin idanuwanta.
Dafe kanshi yayi Kamar zai Fashe da kuka Cikin Muryan Data Dade cikin Damuwa yace"Kiyi hakuri Ummah..."Daga haka bai kara mgana ba,sun dade suna Sauraran Numfashin Juna kafin Hajiya Fatima ta Datse kiran Lokaci Daya Tana fashe da kuka Saboda Takaichin Dake cin Zuciyarta ba,Shima Dagachan Bangaren Komawa yayi da kansa cikin Kujeran motar yana Fitar da Numfashi sama sama wayar ta Sabule bisa kunnansa zuwa saman Jikinsa.
_Shin Sai yaushe ne Mahaifiyarsa zata Koma kallonsa amatsayin Danta.
na hakika....?Yaushe zata yafemai laifin Daya aikata...?Yaushe zata gyara mu"amalanta da mahaifinsa...? Yafi kowa sanin Tunda Ranar Daya zo Duniya mahaifiyarsa Take matukar sonsa da kuma Burin ganin ya zama mai ilimin Addini da na Boko,...Ya taso cikin Zuciyar son Zama mawaki.....Waka da Sauraranta wani Abu da zai cewa daso yazo Duniya bashi da wani Buri sai na ganin ya zama mawaki in yana cikin Damuwa Sauraran Wakokinsa Acikin Zuciyarsa na sakashi cikin Nishadi Shin laifi ne Dan Daddy da Mommy sun Taimaka wajen cikar Burinsa..?Meyasa Umma bazata taba son Abunda yake so ba..? Koda ya zama matukin Jirgin sama ba Ra"ayinsa bane,Burin Ummah ne ammh Duk da Haka ta kasa kallonsa ta gane Abunda yafi so fiye da kowa? Allah na gani Waka Tanada cikin Abu mafi soyuwa cikin Rayuwarsa Don me Ummah bazatayi Tararraya cikin Burinsa ba,..?Yayi kudi Burinsa ya cika ya zama mawakin Harshen Hausa Dana Turanci,Ya yi suna kaf Nageria babu wanda baisan shi ba Koda mutum bai taba ganinsa ba yana jin Wakokinsa,gidajen Talabijin Din Daya zaga basu adadi gidajen Radion daya karbi Gayyatarsu babu Adadi...na samu Daukaka na samu suna Burina na zama mawaki ya cika ammh haryau zuciyata bata bar kuncina ba Saboda Ummah ta kasa kallonsa balle ta Fahimci Rauninsa..._
*******
VICTORIA ISLAND
Kwallar Dake cikin Idanuwansa yayi Saurin maidawa Daidai Lokacin da James ya saki Ahon Abakin wani babban get din gida mai kyau da Tsari Megadin su ya wangale get da Sauri yana musu Barka da zuwa.
Da hanzari James ya fito Daga bangaren Direba ya Budemai Kofar Baya ya Sawo kafarshi waje Lokaci Daya yana Maida wayarsa acikin aljihun Uniform dinsa Hulansa na gefen Hamatarshi Cikin Taku isa da Jarumta ya Nufi Kofar da zai sadashi da cikin gidan.
Da Sanyin Muryansa ya saka kansa Babban Falon gidan Bakinshi Dauke da Sallama Sharifa da Ziyada ne zaune Suna kallon Wani Horro Film atashar Mbc2 gefe Daya kuma manyan wayoyi ne ahannunsu suna Latsawa hankalinsu kaf baya kan ko"ina sai Abunda sukeyi da kallo ya bisu tabe baki yayi kawai yanufi Hanyar Shashensa Ammh Daga ganin yadda yake Taku zaka Fahimci baya jin Dadin Jikinsa.
Zuhra ce ta Fito Daga kichen Dauke da Filet Shake da Shinkafa mai Salt,Ta hangeshi yana kokarin Shigewa Koridon da zai sadashi da Shaahensa,Da Sauri tace"La ya Abba Sannu da dawowa..."Tafada cikin Farinciki,Da Sauri Su Sharifa suka waiwaya cike da mamaki Domin basu ji Shigowarsa ba.
Waiwayowa yayi yana kallonsu,Baiyi mgana ba Ziyada ta mike tanq kokarin Daukan Dankwalin Doguwar Rigar Dake Jikinta saboda kar Yaga kitson Attach din Dake kanta batason yagani batasan ya riga ya gani ba Itako Sharifa mikewa tayi Lokaci Daya tana sakarmai Manyan idanuwanta cikin Wani salo gashi tafi kowa Shigar banza domin wasu Riga da wando ne ajikinta sunkamata sosai sun Fito da Duka Suran Jikinta,kanta ba Dankwali sai gashin Attch din da sukaje akayi musu dashi ita da ziyada ya bayyana har gadon Bayyanta,Sabanin Zuhra Dake Sanye da Riga da zani na atamfa harda Dankwali da wani karamin Breziya hijab,kana ganinta zaka Fahimci tana da natsuwa sosai.
Kallo Daya yayima Sharifa ya kauda kai yana Fadin"Baku jin mgana ko..? Har saunawa zan Fada muku ku daina zama marasa amfani acikin gida.?.Don kun samu Hutun makaranta ai ba"a ce ku zauna kuna Shanshanci ba,yanzu don Allah lalli Abunda ke kanku Sharifa da Ziyada ashe ban hanaku saka Wannan Gashin Dokin ba..?
Yafada yana kafesu da idanuwanshi cikin Bacin Rai Jikin Ziyada na rawa ta mike tana Sosa kai Lokaci Daya take Fadin"Amr..Umh kayi hakuri Ya Abba bazamu sake ba.."Sharifa kuwa kallonsa kawai take Daure Fuska yayi yana Fadin"kafin na Fito Daga Shashena ku Tabbatar da Kun Tsife kitson Dake kanku in ba haka ba zan saka almakashi na aske kan naku gabadaya...Am i clear..?
Sharifa da Ziyada suka kalli juna Lokaci Daya suna Tura baki Zuhra Dake gefe Tana Kunshe Dariyanta karisowa tsakiyar Falon tayi ta ja karamin Center Table ta dora Filet din Abinci Tana kallo Su Ziyada da ido ya Raina Fata,Kai ya gyada yana Fadin"In kun isa karku tsefe...Ku bari na fito Wlh sai na Aske kanku tas...Mark my Word.." yafada kafin ya juyawa da Sasaarfa ya shige koridon Da zai sadashi da Shashensa.
Sai da ya kule kana Zuhra ta Sheke Da Dariya Harda Rike cike kallonta Sharifa tayi Cikin Takaichi Take Fadin"wa kike ma Dariya..? Da kallo Zuhra ta bita kafin tace"Wanda yaji Haushi mana.."Tafada tana musu gwalo ai kafin ta ankara Dukkansu sun Zaburo mata ta mike da gudu ta Nufi Shashen Hajiya latifa Dake yammah da Falon Domin Duka gida kasa ne ba uptairs.
Da gudu take Tafe tana Fadin"Wayyo Mommy...Come out Zasu taru su dakar miki Autanki.."Take Fada tana Dariya karaf suka ci karo da Hajiya latifa wacce ke Fitowa daga Bedroom Dinta,Gajeruwar mace ce Tana da kiba da Fadin Fuska,Kallo Farko zaka mata kagane ta Sirka da yare da Sigar karfi kamar Namiji sai dai Bata da muni afuskarta,akallah zata kai Shekara 42 aduniya ammh hutu sun Riga sun boye Shekarunta.
cikin Sauri ta tari Zuhra wacce tayi bayanta tana Haki Sai ga Sharifa da Ziyada sun bayyana suna haki Cikin Hararansu Hajiya latifa tace"Lafiyan kuwa..? Wai ku bazaku girma bane,Zuhra ba kanwarku ce plz bana son wannan Shanshancin Take note.."Tafada tana Riko Hannun Zuhra suka raba ta gefen Su Ziyada suka Wuce zuwa Falo Zuhra na musu gwalo.
Kafa Ziyada ta shiga Bubbugawa Tana Bin bayansu take Fadin"Haba mommy,Dariya fa tale tamana nida Sharifa.."Suna karisawa tsakiyar Falon Hajiya Latifa tace"cos of wht zata fara muku Dariya..? Tafada tana zama bisa Daya Daga cikin Kujeran Falo tana kuma Riko zuhra zuwa Jikinta.
Sharifa ne tace"Mommy Dariya take mana Saboda ya Abba yace mu tseefe kitson kanmu ko kuma yamana aski.."Hajiya latifa tace"Good..naji Dadi ba sai da nace kada kuyi ba..Kuma kunsan yana gida kuma kuna sane ya hana ku yi,sai ku kiyaye ku bari sai baya gida kuyi ko kuma indan Kunyi Kudaina yawo ba Dankwali.."Tafada ko ajikinta Zuhra kuwa tana jikinta tana Dariya Harda gwalo.
Sharifa ta tura baki tana Fadin"Toh ammh mommy plz Tok to him kinga fa Shekaranjiya mukaje akamana kitson.."Baki ta tabe kafin tace"U better go and Start...Bazan yimgana da Son kan wanman mganar ba He hv d Right da zai gaya muku gaskiya He is ur brother..kuma Dad dinku yana jin Dadin idon Dayake saka muku.."Jin Haka yasa Sumi sumi suka wuce zuwa Dakinsu suna Nuna ma Zuhra hannu alamun zaki zo ki samemu.
Yana shiga cikin Falonsa ya Daga labulen Dake window waje,ya tsaya kawai yana kallon Haraban gidan iska na kadashi,kafin ya saki ajiyar zuciya ya fara taku zuwa Tsakiyar Falon da ke Dauke da Wasu Rantsatsun Kujeru masu kyau da Tsari sai Katon Talabijin Din Dake Falon sai Kofar Kichen,sai wata kofa Dake gefe ammh kofar tana Rufe ne,Sai Daga chan kuma akwai wata Kofa itama tana Rufe.
Kansa ya kada zuwa cikin Bedroom dinsa mai Dauke da Makeken Wardrope mai gilasai,Da makeken Royal Bed Dinsa mai Kalan Fari da baki,Gabadaya Dakin cikin Tsari yake ba wani takarce sosai sai ma"ajiyar Takalmansa,Dake Shake da takalma Kamar za"a bude Shago,hulan sa ya ijiye hade da wayarsa saman Gado kafin yafara Sabule kayan Jikinsa saman wani mahanga naga ya Dauko wani Towel mai dan girma,ya Daurama kugunsa Lokaci Daya yana Sabule Wandon Dake jikinsa ya Tura Kofar Tiolet ya Shiga cikin Shower ya tsaya Lokaci Daya yana sakarma kanshi Shower din Bayan ya zare Towel din Jikinsa.
Ya Dade cikin Toilet din kafin ya Fito saboda dama yana Dadewa acikin bayi kafin ya Fito,yana Fitowa ya nufi Dreesing Mirror din Dake cikin Dakin ya Dibi manshi na Lotion ya shafa jikinsa lokaci Daya bayan yagama Tsane kansa da karamin Towel Daya Fito dashi Daga Tiolet din,Sai da ya Sauya kaya zuwa Riga da wando na Kirar Armani kafin ya koma cikin Tiolet din ya shanya Towel din Daya Yi amfani dashi.
Wardrope dinsa ya Bude ya maida Uniform dinsa kafin mai wanki yazo ya kwashe,Bai Saurari wayar Dake kan gado ba ya Fice Daga Bedroom din Hannayensa Duka Suna Cikin Aljihun Wandonsa,kofar Dake yammah acikin Falonsa naga ya Nufa ya Tura sai lokacin na Lura da Abunda nagani arubuce A.S. MAINASARA HOME STUDIO..
Tura kofar yayi ya Shiga Lokaci Daya yana Rufe kofar Wajen yayi Duhu kafin ya saka hannu ya kunna makunnin Wuta Haske ya gauraye wajen,Window nan Dakin ya Shiga Budewa yana Zage labulanyan Nan da nan haske ya cika wajen Baki na Rike ina kallon Ikon Allah da Abun mamaki,Domin gabadaya Dakin na Cike ne da kayan waka kama da Jita,Na"uran computer,Spekers,wasu manyan mayan Abubuwa wanda bangane ma ko miye ba,Daga chan gefe kuma Wani glass ne ya raba wajen,nan na hangi abun mgana mai Tsawon nan ma"ana inda mutum zai tsaya yana waka ko wani Abu,wani kuma Daga Chan waje yana Kallon Abun cikin Na"ura yana Tacewa.
Mirmiahi ya saki kafin yaja wata Kujera yazauna Lokaci daya ya kunna Soket din Computer,din sai dai komai na Wutar wajen ya kawo Tunda mahada Dayane, kana ya Shiga Sarrafa Na"ura Lokaci Daya naga ya sanya wani Abu mai kama da Abun jin Mgana acikin Kunnuwansa, Wata waka naji ya lalubo cikin Tarin Wakokinsa mai taken My Mother is my proud... Wakar yayi tane cikin Harshen Turanci Kansa ya maida Bisa Kujeran ya Lumshe idanuwansa yana Sauraran Muryansa cikin Sanyi da gardi,wakar yayi tane Lokacin da Kewa da kuma Kaunar Ummansa ya taso mai sai kawai ya Shiga Studion dinshi na cikin gida ya Rerata,Dama shi baya Rubuta waka,Zai dauki komai cikin Na"ura ya aikama ma"aikatanshi na Studion dinshi Dake kano Wato A.S.MAINASARA MUSICAL STUDIO KANO su zasu tace ta su gyara su Fitar da ita yana Fitar da albulm ammh baita Wallafa na Hoto ba Duk da Masoyansa suna Bukatar Hakan, ammh Shi kam baida Ra"ayi ko domin Sake bama Zuciyar Umma Damar yafemai.
Yayi Nisa cikin Jin Dadin Wakar yaji Muryan Hajiya latifa tana Fadin"Son...!!."Da dan karfi Da Sauri ya Bude idanu yana kallonta kafin ya cire Abunda ke kunnensa Lokaci Daya yana Dakatar da wakar cikin ladabi yace"Gud afternon Mommy..."Kansa ta Shafa tana Fadin Fadin"afternoo my Son Ashe ka Dawo..?kai ya gyada mata yana kallonta cikin so da kauna.
Mirmishi ta sakarmai kafin tace"Oh ya aikin naku..? Jiya Dad dinka yace yana ta kiranta wayarka is not gaing nace may be kana cikin Jirgi ne..."Ajiyar rai ya saki kafin yace"Wlh kuwa mommy sai yanzu ba Dade na iso Airport dinmu,Jiya na tafi Engaland da safe Wajen gabd da Asuba na taso zuwa Nageria.."Mirmishin Jin Dadi Tayi kafin tace"Proud of u Son...May Allah Continue Protect ur life Now and Alyws Forever..."Cikin Jin Dadi yake Fadin"Ameen Ameen Mommy...Thank you..We proud of u."
Taji Dadi Sosai ta bishi da Kallo tana Fadin"Where is Ahill na kwana 2 banji sa ba..?"Cikin Sanyin Murya yace"Jiya suka Dawo Daga labanon Mummy kinsan Grandmah dinshi Ce tarasu So Tunda suka tafi sai jiya suka ya Dawo yace Duka na gaisheku Both of u.."Cikin Alhini tace"Oh Dadd dinka ya Fadamin Am srry For d lost zan kira Umminsa na mata gaisuwa...Ka Fito muyi Takin Dinner son.."Kansa ya Shafa yana Fadin"Am not Hungry mommy..Later."Bata Damu ba sanin Halinshi yasa ta juya tana Fadin"Ok Son...am going Enjoy ur Work.."Tafada tana Ficewa Daga cikin Dakin nashi ya Fita Da kallon Kauna ko ba komai yana kaunarta Don Allah Domin ta Rikeshi Tamkar D'anta ta kuma kula Dashi uwa Uba kuma tana da Wani matsayi mai girma acikin Rayuwarsa,Domin ta taimaka wajen Cikar Burinsa na zama Mawaki.
Bai koma ga Abunda yake ba ya kashe komai,bayan ya maida Duka Windows din Dakin ya maida Duka labulanya ya Zage,ya kashe Wutar Dakin ya kulle kofar ya Fito Direct Tiolet dinsa ya Nufa ya Dauro alwala Ya fito yana kokarin maida agogon Hannunsa cikin Sauri ya Fito Daga Bedroom din zuwa falonsa nan ma bai tsaya ba ya Fice Zuwa Falon gidan yana sawo kanshi Falon Ziyada da Sharifa Dake kan Dinning suna cin abinci Suka tashi Da gudu zuwa Daki har suna bige Juna Hajiya latifa da Zuhra suka bisu da kallo suna Dariya.
Yana kallonsu yayi kamar bai gane ba ya taka ya fice yana Tura hannayensa duka cikin Aljuhun Wandonsa Zuhra tabishi da kallo Cikin Damuwa Domin Tundazu ta Fahimci ya Abba baya cikin Walwalarsa Duk dama bamai yawan karammiya bane...