RA'AYI NE KO BURI?

03

by @jamilaumarjanafty

RA'AYI NE KO BURI...?

NA

JANAFTY💞

Wattpad:Jamilaumar351

Bismillahir Rahamanir Rahim

3

"Tunda ya dawo Daga masallaci ya koma daki ya kwanta barci mai Nauyi ya kwaseshi bai sani ba.,Saboda yana Da gajiya ajikinsa sai wajen Bayan la"asar kana ya Farka lokaci Daya yana mika bakinsa Dauke da Salati.

Kafafunsa ya fara zurowa kasa kafin ya mike Daga kan gadon gabadaya agogon Bangon Dake Dakin ya kafe da ido,Waro ido yayi yana istigafari acikin Zuciyarsa ganin Har Lokacin sallah ya wuce cikin Hanzari ya Fada Tiolet yana Danna Kafadarsa Ta hagu da Hannunsa Guda Daya alamar gajiya.

Bai Dauki Dogon Lokaci mai Tsawo ba,ya fito yana warware Hannun Rigarsa Ruwa na Diga Darduma ya Dauko saman Side Drower din gadon,ya shimfida ya kalli Alkibla ya Tada salla,Bayan ya idar ne ya Zauna yana Addu'o'insa,kafin ya mike yana Shafa gashin kansa,Kan gadon ya koma ya zauna lokaci daya yana Dauko wayarsa Dake yashe kan gadon Missed clls ya gani yana Dubawa yaga Ahiil ya kirashi har Sau 2 koda yabi bayan kiran Yaji Kuma wayarsa tana kashe bai Damu ba sanin Kila yana cikin Jirgi ne.

Wayar ya Saka cikin Aljihun Wandonsa,lokaci Daya yana Ficewa Daga Dakin nashi,Sai da ya biya ta kitchen ya bude Fridge ya Dauko Ruwan gora mai sanyi ya Sha fin Rabi kafin ya maida ya Fito kofar Shashen nashi ya maida ya Rufe kafin ya Fara taku zuwa Babban Falon gidan kafarsa Sanye cikin Budadden Takalmi na kamfanin Gucci.

Bai Tarar da kowa acikin Falon ba Sai Bose mai musu aikace aikace tana Kokarin kwashe Kololin Dake saman Dinning din Tana ganinsa ta Ramkwafa tana Fadin"Good Afterrnoon Sir..."Kallo Daya yayi mata ya Kauda kai ya cigaba da tafiya bai amsa mata ba,Bata damu ba sanin Halinshi ko Kanninshi ba kowa da yaushe yake amsa musu gaisuwar ba,Tabe baki tayi ta cigaba da Abunda take cikin Saurin Saboda ba kwana take ba zuwa take tatafi.

Yana Fitowa Haraban gidan yayi Tsam ganin Har yanzu Dad bai Dawo Gida ba,Karisawa yayi gaban Motarsa sai james ya taso Da gudu ya Durkusa bai mai mgana ba illah Hannu Daya mikamai ba bai damu ba ya Ciro makullin Mota cikin Aljihun Wandonsa ya mika mai batare Dayayi mgana ba ya bude Bangaren Direba ya Shiga Lokaci Daya yana ma motar key,Baya James yaja lokacin Dayayi ma Motar Riverse,Maigadi ya wangalemai get ya Fice da Sauri Suna Dagamai hannu ammh ko kallo basu isheshi ba suma basu damu ba indai Halin Mutaddif ne,Wahainiya ce mai chanza Launi.

*****

Sharifa ne da Ziyada zaune Bisa gadonsu kowacce ta Kuke sai Faman warware kitson kanta take Ammh kallo Daya zaka musu ka Fahimci Fuskarsu ba Walwala inda ma Allah ya Tarfama garinsu nono,Kitson ba kanana bane Suna da Girma,Ammh duk da Haka suna Shan Wuya Tunda basu saba Tsifan kai da kansu ba komai Shagon Saloon Suke zuwa agyara musu kai in ma kitso ne Achan ake Tsefe musu ayi musu komai sai dai Su hada Duka su biya.

Gwarama Ziyada tayi Abun kwarai Domin Takusa gama Tsifewa Gashin Attachement din Dasuke cirowa bisa kansu suna tarawa agabansu akan gadon,Sai ga Zuhra ta turo kofa ta Shigo tana kallonsu cikin Danne Dariyanta Ziyada ko Dagowa batayi ba Tacigaba da Abunda take Zuciyarta cike da Haushin ya Abba na yadda yake matsama Rayuwarsu....

Sharifa ce ta Dago tana Fadin"Zuh..plz come and help me..." Tafada Lokaci Daya tana marairaicewa Wata Uwar Harara Zuhra ta Makamata kafin tace"Wa...? Me...? Karma kin fara kin fi kowa sanin nafi ya Abba kyamatar wannan gashin Da kuke Dauka Adone,Ni wlh kun ma Batamin rai wlh,kuna fitar da Datti bisa kanku kuma taramana Bisa Bed din da muke kwanciya ."Tafada lokaci Daya tana kyabe Fuska.

Sharifa bata kara mgana ba, tacigaba da Tsifanta Tana Tura baki,Kai zuhra ta jijjiga tana Fadin"Plz ku kwashe wannan Abun Bisa gadonmu...Karfa ku manta Najasa ne,Har Allah yayi Tsinuwa damai sakawa da wanda ake sakamawa din nidai gaskiya ku sauko kasa ku tara Kazantarku,haka kurum kuna neman hanani kwana acikin dakin nan in ba haka ba Wlh zan je na kira ya Abba yanzu nan.."Tafada tana Rike kugu.

Da Wani banzan Kallo Ziyada ta Dago tana Fadin"And so wht zuh...Go....oya go...Now..."Take Fada tana wani yarfa hannu, wani Tsaki Zuhra taja Lokaci Daya tana Sakin Tsaki ganin kamar Ziyada zata taso ne yasa ta kwasa da gudu zuwa Falo tana kiran Mommy Tsaki Sharifa taja tana Fadin"Mumu kawai bata da karfin komai,ammh sai Tsokana sai za"a kamata da damu mutane da Shegiyar muryanta,ya Abba da Mommy sune karfinta.."Kwafa Ziyada tayi kafin tace"Nifa am tired...Wlh haka kurum Sai ya dinga matsama Rayuwarmu ko mommy bata mana irin Takuransa Daddy kuma yana goyon bayansa...Allah sa gobe yayi Tafiya.."Sharifa najinta bata tanka mata ba illah Lumshe idanuwanta Datayi tana mirmishi Da wani kallo Ziyada ta bita kafin tace"U are not Serious...Wawiya Sharifa.."Ko Bude idanuwanta Batayi ba Tace cikin Dariya.."yes...am i a fool..."Da karfi Ziyada tace"A big Fool..."Tafada kafin ta Sauka akan gadon Tana Tarrara gashinta lokaci Daya take Fadin"Am done..."Sharifa ta shiga wani yanayi bata bi takan Ziyada ba Har ta Fice Barin ma tsifan tayi ta koma ta Kishingida jikin Filo tana Dafe Saitin Zuciyarta Lokaci Daya ta Furta.

"I miss him...."

****

Sai da ya Dauki Hanyar gidansu Ahill ya Tuna Ahiil baya gida,Duk da Suma suna Victoria insland din ne Tsakaninsu babu Nisa ko gida goma bai kai ba,Ammh duk da Haka bai Fasa ba sai ya Karisa gidansu Ahill ya gaishe da Abbi da Ummi, tare da yi musu gaisuwar Rasuwar mahaifiyar Ummi kakar Ahill kenan,Sunji Dadi sosai sukaayi ta sakamai albarka agidan yadan jima Suna Hira fa Abbi Duk ba wani mgana yake ba Daga Kada kai sai Dariyan yake da Mirmishi..

Yaso yatafi Abbi ya hanashi sai da Sukayi sallar Mangariba Ummi ta matsamai yaci Abinci,Wacce suka taru suka Dafa ita da Kanwar Ahiil,Nihla bai wani jin Yunwa sosai domin Dama shi ba ma"abocin cin Abinci bane afarkon yunwa yafi so ya tara yunwa sosai kafin ya kawar da ita,har wajen Mota Abbi ya tako masa,kafin suyi sallama ya Shiga mota Megadi ya bude mai get ya fice da Hanzari.

Yaso ya koma gida ammh Baya cikin Mood mai Dadi Duk da Abbi ya Debemai kewa,Shawagi yayi tayi acikin Babban Titin Birnin na ikko,Bai koma gida ba sai da ya tsaya yayi sallah Isha"i kana ya Shigo gida Sai Lokacin yaga Motar Daddynsa ya shigo gidan kenan cikin katsaita yagama Daidaita motar a parking Space kafin ya kasheta ya Fito yana Takunsa cikin Sanyi Zuwa cikin Falon gidan inda ya Fara jiyo Shegen Zakin muryan nan na Zuhra kamar taci aku.

Da Karamar sallama ya Shigo Cikin Falon ba wanda yajisa sai Sharifa ce ta ankare Dashi Domin Tana Kujeran Dake kallon Kofar Shigowa cikin Sauri tace"Wlcm ya Abba..."Tafada tana kallonsa Jin Haka yasa kowa ya waigo yana kallonsa ciki harda kuwa Mahaifin nasu wato *CONTROLLER GENERAL SA"ED MAI NASARA*,  Dattijo ne mai akallah Shekaru 60 aduniya,Ba fari bane Baki ne sai dai yana da Fatar Murjewa,Yana da Fadin Fuska mai Dauke da Dogon Hancinsa yana Sanye cikin jallabiya da Farin glass mai kara karfin gani ne acikin idanuwansa Duk da yana Zaune ne na Fahimci yana Dan Jiki inaga wajensa Zuhra ta Dauko Jiki koda yake itama Hajiya Latifan tana Jiki sosai.

Gabadayansu suka sakarmai ido suna kallonshi Shima cikin Sanyin Jiki ya kariso garesu yana amsa gaisuwan su Zuhra cikin Ladabi yace"Mommy good evening...Dad Barka Da dawowa..."Yafada yana Tsaye ammh Kuma ya sadda kansa kasa.

Mirmishi mommy tayi tana Fadin"Evening my son...Ka Dawo..? Kai ya gyada tace"U are Wlcm..Zauna Ziyada ko Sharifa suyi Serving dinka..."Kai ya Rausayar kafin yace"No mommy am ok...Nabiya gidansu Ahill Ummi ta cikamin cikina.."Momy tana Dariya Lokaci Daya tana Fadin"Oh Dat great...May be gobe in na fita saloon Direba ya biya Dani na mata gaisuwa...".

Kai ya gyada kafin ya Kada kai yana Fadin"Dad...momy...gud Nite..."Yafada yana Bankama Sharifa harara wacce ta kafeshi da Ido  Da Sauri Ziyada tace"Kagani ya Abba mun warware Tun dazu.."Tafada tana Sabule Dankwalin Dake kanta wanda na Dole ne ta sanyashi Saboda Dawowar Daddy ne,Bai ko kara kallon Barayinsu ba Ya juya yafara taku zuwa Shashenshi Alhaji Sa"ed dake cin Abinshi a natse yadago ya bishi Da kallo kafin ya saka baki ya kirashi.." Baban Fatima....ABDULMUTADDIF..."yafada cikin Wani amo na so da kulawa.

Cak ya tsaya Cikin Mutuwar jiki Dama Abunda yake gudu kenan Shiyasa Tun Dazu yake Kauda idanuwansa ganin Yadda Dad din ya Kuramai ido,Juyowa yayi jin Da Sunan da Dad din ya kirashi Dashi alokaci Daya cikin Sagewar Murya yace"Na"am Daddy.."Yafada yana wani Gyara tsayuwarsa cikin Maida kai ga Abunda yake ya Furta"Wht wrong WIT u Baban fatima...?

Numfashi ya sauke yana Fadin"Nothing...Dad...Am fine..."Dagowa yayi yana kallonsa na wani lokaci kafin yace"Ok...Alright.."Cikin Jin Dadi ya Juya kawai sai ya Tsinkaya muryan Dad yana Fadin"Ko baka Fadamin meke damunka ba...Nasan bai wuce kaida mahaifiyarka Fatima ko..?

Yafada yana Kuresa da ido Lokaci Daya kafin ya tashi yana goge bakinsa da Tissue,wani iri Yaji Cikin Sanyin jiki ya sake waiwayowa yana Kallon Dad wanda ya Kariso gabansa Lokaci Daya ya Dafa Duka Kafadunsa yana Fadin"My Son...Karka damu kanka game da problem din Fatima,Tana da Taurin kai da Zuciya mai tsanani Duk Da i know Zuciyar mahaifiyarka mai kyau ce mai cike da imani da Tsausayi nasan watarana zata yafe maka Laifin Datake ganin ka mata,Kuma ko yanzu Tana matukar sonka da kewarka Domin tafi sonka akan su Alimah kai Sanyin Idaniyanta ne, har gobe Kawai Dogin Fushi ne bazai bata damar Nunawa ba.."Yafada yana kallonsa,Wani ajiyar zuciya ya Sauke kafin yace"Hakane Dad..Nagode..."

Jinjina kai Dad yayi kafin yace"Naji Dadin hakan...Nothing to be Worry Mutaddif...Watarana Fatima zata fi kowa alfahari Dakai kaji ko..?"Ciikin Mirmishin Jin Dadi yace"Insha Allahu Dad..."Yafada har Hakoransa na bayyana waje Tsausayinshi ya kamashi baisan Lokacin Daya kamashi ya Rumgume ba sun Dauki Lokaci mai tsawo kafin su saki Juna Hannunsa ya Kama ya Sumbata lokaci Daya yana Shafa gashin kansa yace"Gud...Night Son.."yafada da Sauri yana Juyawa ya nufi hanyar Bedroom dinsa da kallo ya bisa Sanin Ya riga yaga Abunda yake boyemai Hawaye ne yake kokarin Boye wa Ajiyar zuciya ya Sauke kafin ya juya yana Fadin"Oh...Why Ummah..."?

Yake Fada cikin Damuwa kafin ya Shige Koriden da zai sadashi da Shashensu Duka biyun da kallo Hajiya Latifa ta bisu kafin ta kauda kai cikin Damuwa tafi kowa sanin Mijinta da Dan mijinta basu da wani damuwa illah na Hajiya Fatima,Ita tana mamakin Matar nan,Mai wata Zuciya mai bahaguwar Fahimta,Ashe nuna so ga D'anka yana kawo Tsana ita meye laifinta Domin ta Tallafa wajen Cikar Burin Mutaddif ko kuwa Laifin tane Domin ta Auri Alhaji Sa"ed.."

Zuhra ce ta Dora da Yanayin da Tashiga cikin Damuwa tace"mommy Meya faru ne...?Numfashi ta sauke kafin ta mike tana Fadin"Is ok..Nothing to be Worry zuh...ku kamallah ku kwashe komai ku maida ciki U make sure kun kwanta da Wuri Kunji ko.."?

Kai suka gyada mata kafin ta Wuce zuwa Dakin Dad Zuhra ce kawai ta bita da kallo Sharifa da Ziyada dama tun dazu suka gama cin abinci suka koma suna latse latsen waya,Daga karshema tashi sukayi suka wuve Daki suna hira kasa kasa harda Dariya.

Zuhra ta bisu da kallo ta tabe baki Ita ta kwashe Dishes din,da Flaks din zuwa kichen Falo ta koma ta Kunna Kallo Tashar Mbc3tana so ta kalli Cartoon ammh sai ta rage Volume saboda kar Momy taji,ammh kasan Ranta tana Damuwa da damuwar Dad da ya Abba.

Asanyaye ya karisa Shiga Bedroom dinsa Ya Fada bisa gado yana maida Numfashi ya Dauki Lokaci mai Tsawo a Haka kafin ya mike ,wayarsa ya ciro Daga cikin Aljihu ya ijiyeta bisa gadon yana Taku kamar zai Fadi ya Shiga Tiolet kayan Jikinsa ya zame ya watsa Cikin kwadon wanki kafin ya Shige cikin Jazucci ya kunna Shower,yana jin karan Saukan Ruwa Bisa kansa idanuwansa na Lumshe yana maida Numfashi ya Dade cikin Wannan Halin,kafin ya kashe Shower din yafito Bathrup ya Dauro bayan ya Dauki wani karamin Towel ya Dora Bisa kansa ya fito

bai shafa komai ajikinsa ba,illah dai ya Tsane Ruwan Jikinsa,Wardrope dinsa ya Bude inda Jerin kayan barcinsa suke ya Zaro Riga da wando na pjms masu Taushi Fari da Ratsin baki ya sanya Yana Taka cafet din Dakin Kafafunsa Farare suna lumewa Cikin Kasala Daya Zamar mai jiki ya Zame bisa gado lokaci Daya yana Mika hannu ya Dauko wayarsa Kurama wayar ido yayi kafin ya Shiga cikin Ma"adanan Hotuna wani Hoto naga ya Bude wanda ke Dauke da wata mata Akallah mai Shekaru 40 aduniya Fara ce Doguwa mai Doguwar Fuska Tana da kyau sosai Duk ko da Shekarunta Domin Sun boye Daka ganta zaka Fahimci Bufullata ne saboda Yanayin Jikinta kamar yarinyar yar Shekara 30.

Haka Yan matan Biyun Dake gefensa Suna matukar kama da Abdulmutaddif sai da na Kara kallo na Fahimci cewa Kamananin na Matan Dake Jikin Hotonan ne,Komai nasu iri Daya ne sai dai kawai yanayin Fuskarsa kamar ta Alhaji Sa"ed ne.

Ya dade yana kallon Hoton Cikin Wani yanayi kafin ya saka Hannu ya Shafi Hoton Lokaci Daya yake Fadin"Ina sonki Ummah...Ina mutukar kewar Uwa kamar ki.."Yafada hawaye suna Taruwa acikin Idanuwansa Wanda yayi Saurin Shanyesu Lokaci daya ya latsa gefen wayar Hasken ya Dauke,saman Side drower ya maidata kafin ya latse Wutar Dakin ya kunna Dumlight ta gefe ya kwana yana karanto Addu"ar kwanciya Daga Barci.

****

Awannan Lokacin Humairah na kwance Bisa gadon Karfen Innarta Balaraba Wayar da ya Sulaiman ne ya bata makale acikin Kunnata ta rage kara Tana Sauraran Muryan ganin nata cikin Wakarsa ta mahaifiya Gabadaya idanuwanta suna lumshe ne tayi Rigin gine tana Sauraran Wakar,Farinciki ya bayyana akan Fuskarta Kanwarta Mujadala yar kimanin Shekara goma ke gefenta tana Sharan barcinta..

Kara gyara kwanciya nayi Duk da ina jin gajiya Sakamakon yau ni nayi aikin yammah kuma Baba ya Siyo ganda na Dafa bayan Tuwon Shinkafar Dana Tukamana Miyar Shuwaka wanda Hajjo ta kafa bala"in shi take Muradin sha,Ban dade da gamawa ba nayo wanka Lokaci Daya da alwala nazo nayi sallar Mangariba da Isha"i aboye Ina Rawan Jiki kar Innata Data tafi Dakin Baba ta Shigo ta ganni Domin Tarbiyan gidanmu ne kome kake ka ijiyeshi ka yi sallah kafin ka cigaba,Duk da ko yadda iyayenmu mata suka mana Horo da aiki sosai,Kamar ni nan ina jina kamar Doki ne wani Lokaci bani da sanyi jiki wajen aiki Wanki ne kadai ke bani Wahala,Maijidda kuwa Alankosai kenan bata son aiki ko kadan ya Dangatan da irin Mahaifiyarta Larai mace mai son kanta.

Gabadaya Hankalina da imanina ya Tafi kan wakar Danake Saurara gefe Daya kuma na Zuciyata na Tunanin Shiko A.S mainasara wani irin so yake ma Mahaifiyarsa ne Gabadaya yawancin Wakokinsa Daga na Hausa zuwa na Turanci Duk kusan Saboda mahaifiyarsa yayita bai cika wakar soyayyah ba ammh yana Fitar da waka cikin Kowani lugga na kashema wanda ke Sauraranta Jiki Kai Daga jin Muryansa da Wakarsa kasan na mai aji ne,da kuma tarin Ilimi boko kodaga jin Turancinsa Uwa uba kuma ta Shaida Mainasara ba irin yan jagaliyan Sauran mawaka bane,Domin Bata taba cim karo da wanda ya mallaki hotonsa acikin Wayarsa ba Sai dai wakarsa,Daga yanayin sa kawai tagama Fassarashi acikin Ranta Mainasara na musamman ne Shiyasa wakarsa ta kasance na Musamman ne,Allah na gani Bata son yaushe ne ko kuma watarana ne ta kamu da Soyayyar Mainasara ba,ko kuma nace Soyayyarsa Dana wakarsa ba ammh Abu Dayane Tasani ta Shaku da Wakokin mai Nasara wanda ko karatunta batamai bitan Data ke musu Duk da Bata da wasa ta bangaren karatu ammh Tana girmama Muradin Ranta Dana Zuciyarta.

Har Innata ta shigo Dakin ban sani Baki ta sake tana Bina da kallo Ganin ina Mirmishi ni kadai,Sai da ta matso Taga waya Bisa kunnina,bani da Earpice Domin na taba siya Ranar kuwa da Baba ya gani sai da yasa ya Nasiru yacin min uwa Tundaga Ranar ban kara mararin Siya ba .

Batamin mgana ba illah kai Data gyada kafin ta Bubbuga gadon Firgigit na Dawo Daga Hayyacina na Dago kaina ina kallon Innarmu cikin Tsoro na boye wayar abayana ina Zare ido Kallona tayi kafin tace"Meye na boyewa Kuma Aisha...? Ke kika sani ni yanzu na Daina bata bakina akanki Duk wanda ya gyara Halinsa Don kansa ne...Nan gaba Aure zaki yi Kije Gidan mijinki kema ki haihu ki zama uwa...Saboda haka in kin gyara Rayuwarki Humarai don kanki ne ."

Tafada kafin ta Dauki Bargon Datazo Dauka ta Nufi Hanyar Fita tana Fadin"Ki taso ki Rufe kofa...Ki kuma Tofama mujadala addu"ar barci kafin ki koma ki cigaba da Sauraran Tafsirin karatun naki.."Tafada cikin gatse kafin tafice.

Da kallo na Bita Jikina yayi sanyi Tsaida wakar nayi lokaci Daya ina Saukowa Daga kan gado,na nufi kofa na Rufe kafin na Kashe Wutar Dakin Duk da ba Wuta ina Tsoron su kawota ciikin Dare Fitilar kwan na Ragema haske kafin na koma bisa gadon,Na gyarama Mujadala Kwanciya Lokaci Daya ina Tofa mata Addu"ar barci nima na shafa ma kaina ,Bargo na jamana Muka Rufa Tunda garin akwai sanyi kamar Da akwai Hadari.

Fadan Innarmu shi ya kashemin jiki na Kashe wayar na maida karkashin Filo na Koma na lafe ina Sauke Numfashi ina Tunanin Rayuwar Duniya da Abunda ke Cikinta cikin Haka naji Tarihin Rayuwata da komai na Zuwarmin cikin kaina Kamar ina bama wani labari