04
RA'AYI NE KO BURI..?
NA
JANAFTY💞
Wattpad:Jamilaumar351
4
SHEKARUN BAYA
""Sunana Aisha umar Ringim,Sunan mahaifina Mallam umar Ringim yadda Labari yazo mana Daga bakin Hajjo kusan Rabin mutanen Dake Ringim Duk yan"uwanmu ne, sakamakon muna da yawa Sosai.
Asalinmu mun fito Daga Tsatson Maigarin Ringim ne,Tun kakan kakaninmu,har zuwa kan wadanda suka haifi iyayenmu,Kamar yadda Hajjo ta sanar damu Ainihin Sunan Hajjo Aisha Sunanta naci, lokacin Maigari Zubairu mijinsu kenan matan Auransa Guda Hudu ne,itace uwargida kuma ita din ta kasance Abokiyar wasanshi ce, Tunda suna matsayin Dan mace Da D'a Namiji ne,Auran Saurayi Budurwa sukayi Tun Tana da Shekara 15 aduniya Tunkafin ma yasan za"a Nadashi amatsayin maigarin Ringim.
Dalilin kare karen Auren Maigari Zubairu Rashin Haihuwa ne,Tunda Har suka Shekara wajen Goma da Aure Hajjo bata taba Batan wata ba,Dalilin Dayasa ya karo matarsa ta biyu kenan ita ma tazo ta shafe Shekaru ba wani labari bai hakura ba ya sake yi suka zama su uku itama bawani labari,Auransa na Hudu lokacin Yana matsayin maigarin Ringim ne, bayan Mahaifinsa ya Rasu ganin har ya cike ne ba Labari yasa ya fara cire rai da Haihuwa yafara Dorama kansa Kila Shine baya Haihuwa.
Magunguna kuwa na gargaji da Saiwoyoyi,Su hajjo sun banka kamar Hauka,ammh Shuru ba wani labari,Haka dai suka Hakura Suka Zubama Sarautar Allah ido ganin har Maigari Zubairu,ya fara manyanta ba wani labari kullum yana cikin Takaichin Rashin samun magaji ko kuma kwansa aduniya.
Kwatsam aka wayi gari Hajjo ta Fara laulayin ciki,Sakamakon Lokaci Ilimin zamani bai wani yawaita ba,Sai masu anguwan zoma Haka su aka kira suka tabbatar da samun cikin Hajjo Wanda Labarin Daya isa kunnan Maigari Zubairu sai da aka yi karamin biki agarin saboda Murna da Farinciki Duk wani Tattali da kuma Kulawa Haka maigari Zubairu yake bama Hajjo kuma ya umarci Duka matansa da duk mai son ganin Farincikinsa ta Rika kula da Hajjo Koda suna jin Haushi Hakanan suka Danne suka Rufamai baya suna kula da Hajjo har cikinta ya tsufa ya isa Haihuwa,Wata ranar jumma"a da Safe Hajjo ta haifi Danta Namiji Bayan tasha Doguwar Naguda.
Murna wajen Maigari zubairu ba mgana bakinsa yaki Rufuwa Har suna kuwa shanayen Daya yanka ba Adadi zabbi,Kaji Tunda dama Yana da gidan gona Yaro yaci Sunan Hayatu,Hajjo ta cigaba da kula da Danta cikin Soyayyah da Kauna da kuma kulawar Maigari Zubairu,Hayatu nada Shekara 4 aduniya Hajjo ta kara samun wani cikin Shima Maigari Zubairu yayi murna sosai Shima wata tara ta kara Haihuwar Danta Namiji Ranar suna yaci Suna Umar.
Tun bayan su kuma Haihuwa bata kara zuwa ba,Basu damu suka Rumgume ya"yansu suna basu kulawa cikin Tattali,Sun taso cikin Tarbiya da ilimi,Karatun Addini ne kadai suke yi Tunda Lokacin babu yalwar ilimin zamanin in akaga ma kanayi tsanarka akeyi,Sai dai karatun allo Da Sauran Littafan Addini,Umar shine yafi Dauko Duka Halayan Maigari Zubairu Domin komai nasu iri Daya ne,Sabanin Hayatu kuwa Zaka ganshi mai Saukin Hali ne bai tsananma Rayuwarsa komai ba.
Hayatu nada Shekara 20 Umar nada 15 maigari Zubairu ya rasu Kafin Rasuwarsa matansa Biyu suka rigasa tafiya mutuwar Data girgiza mutane Dadama musamman Hajjo Tafi kowa jin Mutuwar,Hakanan suka Fauwala ma Allah komai Ta Rumgume ya"yanta tana cigaba da kula Dasu Tafe tafe Rayuwa tana kara gaba Umar yana zuwa garuruwa Neman Ilimi,Saboda shi akwai Riko da addini Tuni ya Sauke Qur"ani kuma yayi Haddanshi Karatun Littafai garuruwa yake zuwa neman ilimi baya zama sakamakon Hayatu yana tare da Hajjo yana kula Da Ita Tunda Dayar matar Marigayi Zubairu ma Allah ya mata rasuwa.
Hayatu yana da Sauki kai Sosai Shiyasa Har karatun yaki da Jahilci yayi,Yasan wasu abubuwa,Sabanin Umar da ko zo in kasheka da Turanci bai sani ba hayatu nada Shekara 28 yayi Aure ya Auri Amina Bufallatanace gaba da baya Suna zaune ita da iyayenta A rigar hardo Dake Babban Hukumar Jahar jigawan Dutse Amina tayi Daidai da Ra"ayinsa Itama ta fito Daga Tsantson Fulani ne wadanda basu san Ilimin boko ba,Sai dai na Arabi kuma Yaransa suna kanana yake aurar dasu Duk da Yakasance malami ne sosai kuma Makiyayi Dalilin Cinikayyan shanaye suka Hadu da Hayatu Tunda Kiwo ya amsheshi yaga Amina mai Shekara 13 alokacin kuma ya Furta yana so Nan da nan ya bashi ba"a dauki Lokaci mai tsawo ba,aka gama komai Aka kawo Amarya nan garin Ringim.
Hajjo tafi kowa murna Domin tana jin Dadin Zama da Amina mace mai sanyi Hali da Kawaici Tana da Shakara 15 a haifi Yarta Ta fari ta ci suna Hasiya,bayan ita tazo tayi Zainaaba,sai Murjanatu,sai Lokacin kuma Hayatu aka nadamai Rawanin Mahaifinsu na zama maigarin Ringim duba da Chanchantarsa,Umar kuma ba Mazauni bane Domin bayan neman Ilmi yana Hadawa da kasuwanci Auren Umar na Fari mariyatu wacce ake kira Balaraba ya aura Rana Daya kuma aka Daura musu Aure da Hayatu wacce ya kara Aure da Maryam mairo wacce yar nan Asalin garin Ringim din ne.
Hayatu yana zaune ne gidansu mahaifinsu da suka sake gyarawa suka Fadadshi Shima Umar din nan yafara zama da matarsa Balaraba,Suna kula da Hajjo wacce ta manyanta tana jin Dadin zama da Surukanta Duk da Hajjo tana da Fada Tsiyan da Shiga Abunda ba Ruwanta ammh Haka suke hakuri da ita,Ba dadewa Amina ta Sake Haihuwan Sulaiman wanda tsakaninsu da Ya Nasirun ma ba Nisa kwana goma ne,Bayan Shi Wata Tara Innarmu ta kara Haihuwar Ya Gaddafi, bayan Haihuwarshi ne Suka tashi Daga gidan gadon suka koma gidan da Babanmu ya gida nan kusa Dasu ne ba Nisa Tunda yana samu akasuwanci kuma ga Gonakin Gado da Gidan Gona da Dabbonin da Suka gada shi Da maigari Hayatu,Basu koma ba sai Da Amarya Larai wacce Hajjo ta sanya Babanmu ya Aureta Sakamakon marainiya ce Bata da uwa bata da uba lokacin uwarta na Raye yar Dakin Hajjo ce
Tsakanin Haihuwata Da Haihuwar Maijidda da Aliyar Inna mairon Baba Hayatu duk yan wata Daya ne Duk acikin mu nice Babba kafin Aliya sai mai jidda,Bayan ni Sai Innarmu takara Haihuwan Mujadala,Daga lokacin kuma bata kara Haihuwa ba sai larai ce Haihuwa ta Budemawa tayi Sangiru da Auwalu sai Karaminmu Usman.
Inna mairo kuma Bayan Aliya sai Tayi Aliyu Da Nasar,Daga su itama bata kara Haihuwa ba in za"ayi kisayasi acikin gidanmu mu takwas ne Larai nada Hudu Innarmu ma nada Hudu gidan Baba maigari kuma Yana da ya"ya bakwai wanda Tuni su ya Zainab da ya Hasiya sukayi Aure anan garin Rimgim,ya murja itama anan garin tayi Aure.
Innata ta bani labari tun tasowata Ni mai Masoyace Domin Kowa yaganni sai ya Daukeni Saboda taso da kyau da Farinjini,Ga kirniya da Barna,gashi ina da sunan Hajjo ammh bama Shiri kodayaushe naje gidan Baba maigari da kuka nake Dawowa na mata barna ta Bugeni,ni kuma kamar mayya koda yaushe ina gidan,Dalilin Dawowar Hajjo gidan mu kuwa Tun Lokacin Rasuwar mahaifin Amina tatafi Rugarsu Hajjo tace ma Babanmu maza ya gyara mata Daki Zata dawo nan ta Zauna Shima Taga kamun ludayin zaman Auren Nashi wai Taga na Hayatu Saura na Umaru,Ba yadda Baba Hayatu bai lallasheta ba ta Tubure ba,daga karshema ta saka kuka Tunda Lokacin tsufa ya kamata Rigimarta kara yawa take,ko iyayen namu maza bata kyale ba balle matansu abu kadan zaka mata ta hau Tijara.
Dole ya kira Babanmu sukayi mgana Dama gidanmu muna da Dakuna bayan na waje akwai acikin gida domin katon Fili ne harda inda ma su ya Nasiru zasu iya yin gini su zauna da matansu,kafin Sati Daya aka gyarama ta Dakin Dake kusa da Innarmu Tadawo nan da zama Tunda kuma ta Dawo Shikenan muka Shiga uku barin ma ni Kamar Allah bai Hada jininmu ba,Bama Zama inuwa Daya ga Fadan Rashin Dalili,Larai kuwa Dama Tun Kafin Auren Hajjo na matukar sonta tana Tsausaya mata sai ta koma Yar Dakinta Tayi ta makirci Domin aga bakin Innarmu Ita kuma tana da bala"in Hakuri ga kawaici kan ya"yanta ko mai za"ayi baka jin bakinta sai dai kaji tana bada Hakuri Shike kashema Hajjo Jiki ko Tana so tayi Fitinarta bata samun Dama.
Nikuwa nasha Duka wajen Hajjo Saboda maijidda Domin Tun muna yara tacika tsokana ni kuma Na bugeta tunda nafita karfi,Hajjo kuwa takamani ta Daka tana kirana muguwa kamar ni ba Jikarta bace Shiyasa wani Lokacin nake tafiya wajen Inna mairo nayi zamana mu Rika Wasa da Aliya Tunda Muna da Shakuwar Jini Da ita tunmuna yara tamu tazo Daya Da ita.
Zuwa Lokacin da muke tasawa Babanmu yariga yayi suna amatsayinsa na malami,kaf garin Ringim da kewayanta ba inda ba"asanshi kuma ana zuwa Daukan karatu koda yaushe zaka ganshi akofar gida bisa Tabarma da Littafai Dalibai sun zayageshi,Baya Karban Dalibai ammh zaka iya zuwa ka nemi ilimi,mukuwa Koda yaushe karatun Dare Dana Asuba baya Wucemu Domin Babanmu yana da Zafi kamar shi ya biyo Hajjo a Fada Kana kin zuwa makaranta Asuba ko na Dare zai saka ya Nasiru ya zane maka jiki wanda zuwa Lokacin Su da ya Sulaiman suke Lura damu in muna karatun Azauran gidanmu gabadaya Da gidanmu da gidan Baba Hayatu.
Tun ina yarinya Jinina ya shaku Dana ya Sulaiman,Dalilin zama agidansu Danikeyi,komai ya samu nice Wanda Sunan Humairah awajensa na Fara samu haka zan Je Dakinsa nayi ta masa barna da Kirniya baya Damuwa,Zuwa Lokacin da suka Haura Shekara 15 aduniya Shi da ya Nasiru Turawa suka Shigo garin Rimgim Domin Wayar da kan Mutane game da Ilimin Boka,Babu wanda yafara amsan Mganar sai Baba hayatu dama kuma gidanshi suka sauka Lokacin Daya Nuna zai saka Sulaiman amakarantar Boko Harda Babanmu ayimai tawaye Hajjo kuwa kuka ta saka tana Fadin Turawa sun Asirce mata Hayatunta yayi kokarin ya Fahimtar dasu suka ki Fahimta Abun bai mai Dadi ba Saboda yana da Burin Sulaiman ya karatun Boko Ko domin ya Dogara da kanshi Watarana.
Ganin sunki yarda sai ya bar mganar,Ammh zuwa Lokacin da Kafuwar makarantar Boko agarin Ringim,yasa Sha"awar Abun yazo mai,ya dinga lallaban Hajjo Dakyar ta yarda Sulaiman yayi matukar Murna Dama Shi yana Son karatun Boko sosai,Sai ya bada Shawaran Baba Hayatu yama Babanmu mganar kan su Fara karatu Shida ya Nasiru yaji Dadin haka yaje ya samu Babanmu wanda ya Daka tsalle yace Allah ya tsareshi bazai Tura Nasiru boko ba Daya nemi ya matamai sai suka nemi su samu matsalama Dole ya kyalesa aka saka Sulaiman kadai,Lokacin Duk manya ne acikin Ajin bai Damu ba tunda sun saka karatun acikin Ransu Duk da basu da yawa alokacin
Ya sulaiman na SS1 Babanmu yama ya Nasirumu Aure da Rabi"atu itama Duk tana cikin Danginmu ya kuma gina mai Shashensa da Filin Dake gefen gidanmu sai aka Fitar musu da Kofa Daga Shashenmu,Zuwa lokacin Abubuwa Sun chanza ba kamar baya ba Tunda har Babanmu ya yarda ya Gaddafi ya shiga makaranta Domin Shima Babban Burinsa Shine yayi jami"a,Tunda ilimi ya yawaita ko"ina zuwa Lokacin muma An sakamu amakaranta ammh bayan sun karantu Sosai,kuma muna Maida kai akaratunmu,Ammh ya Nasiru baya Sha"awar boko kwata kwata kuma ko zo in kasheka baisani ba Illah kasuwancin Babanmu Dayake na Nomar Auduga.
Rayuwa tanata gangarawa Dadadi ba Dadi...,muna girma muna kara Fahimtar wani Abun na Rayuwa da Abubuwan Dake Faruwa mun kamallah primary lokacin ya sulaiman na gida ya gama Secondary sch dinsa Result dinsa ne baiyi kyau ba,yana ta kara Zanawa ammh kuma ba"adace ba,Tunda lokacin Jarabar Gama Babban Sakandiri Tana da Wuyar a Kasarmu na Nageria.
Zuwa lokacin Shi da ya gaddafi sun zama super star saboda yan gayu ne suna iya rubutu da karatu,kuma suna iya Turanci abakinsu koda yaushe zaka gansu Tsab dasu barin ma ya sulaiman mai songayu yan mata Dadama suna sonshi,nikuwa tuni yake burgeni,saboda nice mutuniyarsa koda yaushe cikin zuwa gidanmu yake yana kawomin su Sweet da kayan kwalama,Abunda ke batama larai rai da yarta maijidda rai kenan,larai bata shiga Bakinciki ba sai da ya sulaiman ya furtama Baba hayatu mganar Yana son abashi ni in yatashi aure zai Aureni,Mganar Da babanmu yaji Dadinta sosai hakama hajjo tadinga rawa tana Fadin gwara ya kwasheni su huta nikuwa lokacin inaa da kuruciya ban damu ba ganin Ai samun ya sulaiman amatsayin miji Abun alfahari ne.
Sun Dade agida wajen Shakaru Hudu har ya Gaddafi yazo ya cimma ya sulaiman, sai Ashekarar suka samu nasaran cin jarabawan Fita,basu sami Shiga jami"a ba sai da baba hayatu yata da mutum zuwa Cikin Jami"ar Buk kana da hanya da komai ya Gaddafi ya samu gurbin karatu ajami"ar Buk Dake kano yana karatan Kimiyar na"ura wata computer science,,Shi kuma ya sulaiman Dakyar aka samarmai gurbin karatu A jami"ar ABU dake zaria yana karantar chemitry,sunyi murna sosai burinsu ya cika Basu Dauki Lokaci ba kowannensu ya tattara zuwa inda zai yi karatu sai dai in sun samu hutu su zo gida in hutu ya kare su koma makaranta.
Mun samu damar shiga jss1 a makarantar Sabon gari Goverment Junior Secondary School Ringim mu uku Dani da Maijidda da Aliya Mu uku wanda Dama haka muka taso maijidda ce bama Shiri saboda bata iya mgana ba,Ta kuma kwaso Halin Uwarata Kullum mukaje makaranta muka Dawo sai ta kararmu wajen Hajjo,wai muna Wareta Nafison Aliya akanta Haka Hajjo zata Wuni zagina Wani Lokacin Har dakin innarmu take bina ta Mangareni Saboda Maijidda sai dai nayi kuka na Share Hawayena,Innarmu kuwa bata taba mgana ba sai in Hajjo ta sakota ne ta Bata hakuri ta wuce.
Aji daya aka samu nida maijidda Aliya kuma aka kaita B ne,Mu kuma muna A class,Dukkanmu muna maida Hankali akaratunmu Dani da Aliya munada kokari sosai saboda Tun muna gida kwakwalanmu sun bude da karatun Qur"ani,Maijidda kuwa banda Wasa da Biyema sabbin kawaye bata komai,In akayi jarabawa ta kusa Dana karshe Take Diba mu kuwa Nida Aliya in Bamu zo na 1 bazamu zo na 2,Saboda koda yaushe ya sulaiman ya dawo gida hutu cikin min Fada yake na Dage da karatu in mukayi aure ya samu aiki a kano zai tafi dani ya sakani a jami"a nima na zama yar gayu kamar kowa.
Abunda ke damun larai kenan ganin yadda kwanyata ke ja kuma Babanmu,kuma koda yaushe nayi kokari sai Babanmu yamin kyauta,Duk ko da Rashin Jina Domin nadaina kyale Hajjo Data min mgana zan maida mata Tayi ta Fitinata tana Fadin Innarmu ce ta Dauremin gindi ina iskanci,Innarmu tayi Shuru taki mgana sai dare yayi ta sameni cikin Daki ta Dinga min Fada Ammh Duk da haka bana jin Mgana.
Tsakani ga Allah mun horo a aiki Saboda mun taso cikin Tarbiya da Kulawan iyayenmu,Shiyasa muna Kawo karfi muka karbema iyayenmu mata aikin gida sai dai In mun tafi makaranta,Ko Abunda b"a rasa ba,Bama Wariya Dana Innata dana larai Muke Hadawa muyi Nida Maijidda muke rabawa Wata tayi da Rana wata tayi da Yammah Rabi matar ya Nasiru ita kadai ke girkinta,Sai dai in tayi Girkin ta Dibarma Su innarmu da Hajjo.
Babanmu nada Turakarsa Wanda Duk wacce keda Shi Ranar ita zata Je ta gyara Dakin Ta Share,Ta kuma jera mai abinci,mu kuma muji da gyara Cikin gida da kula da kanninmu.
Faruwar al"amarin na Da soyayyar wakar Mainasara Shine Ta Dalilin ya Gaddafi in ya Dawo yana bani wayarsa nayi ta game Dayake ina da karambani,na nace kamar mayya yana min Wulakanci,haka zai bani tun ina karba ina game har na fara Shige shigen wajen wakoki bazan taba mantawa ba wakarsa ta farko Dana fara ji awayar ya Gaddafi mai taken Muradin zuciyata❣️ina Sauraranta ina jin Dadi domin Banta jin Waka da murya data kwantamin irinta ba Duk mu ba ma"abota sauraran wakoki bane ina kafito karatu ina zaka karatu.
Tundaga lokacin dana gane wakokin A.S mainasara,shiikenan na Makalema Wayar ya Gaddafi sai yayi da gaske nake bashi kafin ya koma kano na gama Haddace wasu Daga cikin wakokinsa in ya gaddafi baya nan sai dai kawai in naji kewa aji ina Rairawa Innata tayi mamakin jin wakokin zamani abakina,Wanda ko Kayan kallo bamu dashi gwarama gidan Baba Hayatu akwai adakin Hajiya Amina,muna zuwa kallo NTA alokacin,Babu wanda ya taba lura da nayi zurfi acikin almaarin sai da na maida kaina kullum cikin jin wakar A.S mainasara,Cikin hakane ya Nasiru ya siyama Innarmu waya mai memoey,murna kamar zan suma Saboda Dadi nayi ta jiran Zuwan ya gaddafi hutu yana zuwa na saka ya lodamin Duka wakokinsa sai lokacin ma yake gayamin yana wakokin Turanci naji Dadin Haka sosai sai na samu Abun yi ko bayi zani da wayar Innata nake zuwa,Tun tana kallona batamin mgana har tafara min Fada banaji saboda Daukan wayarta har Duka ta saka ya Nasiru yayimin ammh ban kiyayi wayar ba in muka Hadu da Aliya ina bata labarin Iirin yadda nake mutuwar son wakar Mainasara lokaci Daya ina Wasashi,sai dai tamin Dariya kawai gani suke ina Shirmena ne Mgana har kunnin Babanmu Hajjo ta kaini kara wai ina damunsu da wakokin banza na zamani,Babanmu ya kirani yamin Fada sosai yace kar na bata wayau na ammh bai sa na Daina ba sai na koma yi aboye ganin ba mafita yasa na tara kudin Tara na,na siya Earpice ina sakawa ina ji ranar da Asirina ya Tonu Innata da kanta ta Dakeni Abunda bata taba min ba Tun bayan Girmana.