RA'AYI NE KO BURI?

06

by @jamilaumarjanafty

RA'AYI NE KO BURI..?

NA

JANAFTY💞

Wattpad:Jamilaumar351

6

"Kishingida yayi jikin Kujeran Dayake Zaune Gefensa Ahiil ne Suna Zaune cikin Dakin Hutawar Matuka Jiragen Dake babban Filin jirgin Nmandi Azikewe Inetenatinal Aiport dake Abuja Sakamakon su suka Tuko Babban jirgin kamfaninsu zuwa Abuja suna Dakin Hutu ne Nan da awa Daya Zasu kara kwasan Mutane Zuwa Birinin na ikko.

Idanuwanshi na Lumshe yake Fadin"Na"am Asiya ce ko ,Aliimah..? Aliima na Mirmishi tace"Aliima ce ya Abba.."Sumar kansa ya shafa yana Fadin"Ah..Sweet Alimata ya gida..? ya sch...? Ina Asiya maman Daddy.....?

Cikin Jin Dadi take Fadin"Lafiya lau ya Abba ka manta yanzu bamu zuwa sch muna Hutu..? Tafada Lokaci Daya tana Ture Hannun Asiya Dake neman Fizge wayar hannunta..

Gefen Ahiil ya kallah yaga Hankalinsa baya kansa yana ga wayarsa,Dauke idanuwansa yayi yana Fadin"Na manta ne..?Baki bani amsana ba ina Asiya da Ummah..?

Aliima tace"Suna lafiya ya Abba Ummah Tana Dakinta ina Tunanin Ta Shiga wanka ne Asiya kuma gata kusa dani kamar zata warce wayar.."Yar dariya ya saka cike da nishadi yace"Saka wayar a speaker nayi mgana Daku duka.."Jin haka yasa Aliima ta Dago da wayar Daga kunninta ta sakata a speaker tana Hararan Alima.

Cikin Muryan Hargagi Asiya tace"ya Abba ganinan ina Kwana..? Yaushe kai zaka zo..? Yau daddy dasu Zuhra zasu taho ya Abba.."Baki Aliima ta Rike Lokaci Daya tana sakaarma Asiya wayar ganin yadda take rawan Jiki Mirmishi yasaki kaunar kannin nasa na Ratsashi kafin yace"Zan zo insha Allahu Lil Sis da zarar aiki yayinmana Sauki bana samun zama ne yanzu haka Muna Abuja tare da Ahill.."Cikin Jin Dadi Asiya tace"Shikenan yaya Don Allah kaima kazo wlh muna kewarka nida Anty Aliima kullum sai munyi Zencenka ko Anty Aliimah.."?tafada tana kallonta Daga kai tayi kafin tace"Eh mana kuma koda yaushe sai Umma ta ce mu Shiga Dakinka mu gyara maka,itama tana son ganinka bata nunawa ne kawai..."

Wani Farinciki ya Ziyarceshi ya mike yana Fadin"Da gaske kike Sweet Aliimah..?.."Bata kai ga mgana ba taji kyakyawan Rankwashi Bisa kanta Lokaci Daya Da Daka musu Tsawa da Umma tayi,Baya Aliima taja tana Dafe da kanta yayinda Tsoro yakama Asiya ta matsa baya da waya hannunta jikinata na Rawa tace"Allah Umma ba ruwana Anty Aliuma ce ta..."Bum Ta make mata baki har sai da Ta saki wata Siririyar kara wanda mutaddif Dake Rike da kan waya Sai da yaji Tuni Jikinsa yayi sanyi yasan Tunda Umma ta kamasu suna waya dashi Kashinsu ya bushe,Bata kaunar Taga suna Rabanshi balle har su saba Dashi.

Cikin Bacin rai take kallonsu kafin tace"Ni sa"ar wasanku ce da zan kafa muku Doka ku tsallake .?tafada Ranta in yayi Dubu ya baci Dama Tana cikin Bacin Ran Ubansu Yanzu kuma sun kara kunsamata,bayan shiryawanta ne ta fito Falo bata ga ko Daya ba kuma basu a kichen Hayaniyar mganarsu taji taNufo Dakin Daidai Lokacin da Aliima ke fadin wai tana sakasu gyara dakin nasa,Shi ya kara Harzukata har Abada bata kaunar wani ko wata yagane tana Begen D'anta kullum kwanan Duniya da kuka da Begen Rashinsa take,Bata gazawa wajen mai addu"an Fatan Alheri na Rayuwa Bata taba nunama wani afuska  Ta damu da Mutaddif ba, Alhalin Mutaddif Shine Jigonta D'a masu soyuwa acikin Zuciyarta wanda bata da kamarsa Sai dai Yau da gobe batar ba komai ba,yadda take kula da tsaftace Dakin Abban ko nata batamai Haka Ashe ya"yan nata suna Lura da ita.

Ganin yadda idanuwanta suka kada ne yasa Aliima Kaiwa kasa Tana Fadin"Don Allah Umma kiyi Hakuri bazamu kara ba.."Tafada tana matse kwallah ganin haka sai Asiya ma tabi bayanta itama ta Durkushe tana Fadin"Kiyi hakuri Umma bazamu kara ba.."Tafada tana Shesshekan kuka Saboda tafi Aliima Saurin kuka,kuma aduniya in suna kaunar mutuwarsu suna kaunar ganin bacin ran Umma wacce ta kasance Uwa wacce suke ganin Sunfi kowa Duka ya"yan Duniya Sa"ar Nagartattacen uwa...

Jikinta ne yayi sanyi ganin Yadda Asiya ke Share kwallah Cikin Saukar da Fushinta ta mika Hannu Tana Fadin"Ku kuka sani...Mikan wayata.."Tafada Lokaci Daya tana mika mata hannunta Jikin Asiya na Rawa ta mika mata wayar karba tayi tana latsa gefe sai haske ya bayyana nan Taga harzuwa Lokacin yana kan layi cikin Tsakin Takaichi ta Yanke Kiran Lokaci Daya ta Juya tana Fadin"In kun gama sai ku fita zuwa wanka kada azo a ganku Tun wankan Safe.."

Daga haka ta fice Daga Bedroom din Lokaci Daya suka Bita da kallo Asiya ta share kwallar idonta ta mike tana Fadim"Me yayanmu yama Umma mai zafi haka da bata kaunarsa kwata kwata..? batare bari ya rabeta ko kuma ya rabemu na rasa gane meke damun Umma Anty Aliima baki lura itama tana cikin Damuwa sosai Wani lokaci sai ki ganta tana kuka ita kadai..?

Mikewa Tsaye Itama Alima tayi Tana Fadin"Umh...Nikaina Asiya Abun na matukar bani mamaki kwata kwata Umma bata kaunar mu Furtama wani ya Abba Dan"uwanmu  ne,na uwa da Uba,kin manta har cemana tayi kar ta sakejin wannan Mganar abakinmu Sanda Daddy ya gayamana ya Abba d'an Umma ne na Farko ba Dan Mommy latifa ba.."Jinjina kai Asiya tayi zatayi mgana sai sukaji kamar motsi da gudu Alima ta Shige Toilet Tana Rawan Jiki Ita kuma Asiya ta hau Zare ido Jin Babu kowa ne yasa Asiya Fadin"Kinga watsa ruwanki anan ni bari na Shiga Dakinmu ba Umma ba ce motsin kuluyarta ne.."Tafada tana Dariya Itama Aliman Dariyan Take Daga cikin Tiolet din.

Umma kuwa Bedroom dinta ta koma bakin gado ta Zauna lokaci Daya Hawayen Dake cikin kwarmin Idanuwanta Suka Zubomata dafe kumatunta tayi Tana jin wani Daci acikinta ranta ko zata Shekara Fadan Cewa batason Mutaddif tama ranta da Zuciyarta karya,ita ta Dauki cikinsa Tun bata gama mallakan Hankalin kanta ba ta Reneshi har Zuwa lokacin Data kawoshi Duniya wanda Adalilin haihuwarshi Sai da ta Shafe Wata hudu asibitin koyarwa na mallam Aminu kano tana Jinya,Tataso da Soyayyarsa Domin Shine Yaron Data haifa Tana cikin kuruciyarta,suka Taso tamkar wani yaya da kaninta taci Buri kan inganta Rayuwarsa wajen Tarbiya da ilimin Addini Dana zamani Tun yana karami take da Burin yazama matukin Jiragen sama Shine Burinta ammh Rana tsaka Ya juyama Burunta baya ya manta cewa Itace ta Haifeshi Latifa ta Rabata da Danta bayan tayi Nasaran Kwace mata miji Taya ya zuciyarta zata manta da wannan Tabon ..?Har Abada bazata manta ba Shiyasa ta zabi yin Nesa da Duk Abunda ya Dangacensu Tunda har zai iya Zaban Latifa,ammh ita ya watsa mata kasa acikin idanuwanta.

kara  Rushewa da  Kuka tayi Kamar wacce ake Duka kuka mai ban Tsausayi gamai Saurare,Shiko Dagachan Bangaren Mirmishi ya saki yana Fadin"Gaskiyar Daddy ne Dayace Uwa bazata haifi Da taki shi ba...Na yarda na amince haryanzu Ummata na sona.."Yafada Lokaci daya cikin Wani sanyin murya da Kewa Ahill Dake gefensa Sai da ya Dago yana kallonsa Cike da Tsausayin Halin da Amininashi ke ciki Shikanshi Shaida ne, sunsha Zuwa kano gidan Umma da Niyar Kwana biyu ammh dakyar suke kwana Daya su dawo Saboda Halin ko in kulan Datake nuna musu,Ya na tsausayama Aminin nashi  kuma yana Tayashi Addu"ar Allah ya Saussauta Zuciyar Umma ko shi ma zaiji kansa amatsayin ko wani Da na Cikin Duniya.

*******

Ihun su Asiya Taji Daga Falon Tayi Zumbur ta mike ta Shiga Tiolet ta wanke Fuskarta ta Fito kenan Shi kuma ya Bude Kofar Bedroom din ya Shigo Suka Hada Ido kallo Daya yayimata jikinsa ya karayin Sanyi Domin yafi Shekara 27 da sanin Fatima Yafi kowa karantar Duka yanayinta..

Mirmishi ta kakaro tana Fadin"Sannunku da zuwa.."Tafada tana isa gareshi Lokaci Daya ta mika hannu Tana karban Jakar Dake Rataye a kafadarsa ta Laptop dinsa baya zuwa da kaya kano ko lagos in zai koma Tunda kowani gida ya mallaki kayan sawa kuma in yatafi yana da wasu achan baya bukatar yawan Zirga zirga yana sanye da Shadda Harda Babban Riga ya kafa Hullarsa Zanna Bukar Bisa kanta afizge kamar Abdulmutaddif domin Alhaji Sa'ed Dan Boko ne sosai ba irin Shigar Dabayayi,Saboda yanayin aikinsa Yanzuma saboda zai zo kano ne yasa ya sanya manya kaya sanin Fatima bata sha"awar Ganinsa yana Saka Suit Batun yau bata tasha Fadamai haka

Sakarmata Jakar yayi lokaci Daya yana Sakarmata kiss atsakiyar kanta Ya Dago yana Fadin"Nayi kewarki Fatina.." yafada yana kallon kwayan idanuwanta Lum tayi da ido kafin ta saki mirmishi ta wuce batace komai ba zuwa gefen gadon Kan Side Drower ta ijiyemai Jakar ta Juya ta Shige Tiolet ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya kariso cikin Dakin cikin Ranshi yana fadin"Fatima bazata taba chanzawa ba.."Yafada Lokaci Daya yana kokarin Cire Babbar Rigarsa sai gata ta Fito Da Sauri ta karisa tana taimakai mai Lokaci Daya tana Fadin"Ina yaran..?tafada bata son kallon Fuskarsa Sakarmata yayi yana fadin "Suna Falo tare da yan"uwansu..."Bata kara mgana ba ta wuce Wardrope dinta ta saka Babban Rigar bayan ta Ninketa Lokaci Daya ta waigo Daidai lokacin Dayake kwabe Rigarsa tace"Kashiga kayi wanka Bari na Fita mu gaisa da yaran.."Tafada tana juyawa Mirmishi ya saki kafin yace"Ba za"amin wankan bane..?juyowa tayi Lokaci Daya tana Zabgamai Harara kafin tace"Au Ashe na iya Wankan miji yaushe na Fara koya..?Ai latifa ce kadai yar Boko Ita ta iya Soyayyah da yadda ake Tarairayan Miji Fatima bata son komai ba sai kauyancin Fulani da yarinta.."Daga haka ta Dauke kai zata Fice Daga Dakin Jikinsa yagama mutuwa muryansa cikin Sanyi yace"Latifa tana gaisheki.."Bata waigo ba illah Saurin Fita Datayi Jin idanuwanta na neman kawo kwallah Ajiyar Zuciya ya sauke yana Binta da kallo har yaushene Fatima zata daina Tuna wannan Al"amarin Dayafaru Tun Shekarun baya..? tace ta yafe ammh kuma Abun na ranta.

Jikinsa da Zuciyarsa ba Dadi ya Shige Tiolet ya Rufe.

Sai da ta tsaya akofar Bedroom din ta Daidaita kanta kafin ta kariso Falon Basu ciki sai dai tana jin Hayaniyarsu Adakin Baki Ta juya ta nufi Dakin Zuciyarta na Kuna ta tura kofar ta Shiga da Sallama sun kaure da Hira basu ma jita ba da Sharifa taci karo Daure da Towel ta Fito wanka Cinyoyinta Duk awaje ga Uban Kitson Attac nan Bisa kanta Zuhra ce kadai ke kan gado ita da Asiya Ziyada kuma tana cikin bayi tana wanka Kofar abude tana mgana suna Dariya,Bata su ji Shigowarta  ba,Sai da  ta Kariso Tsakiyar Dakin tana Fadin"Sannunku da zuwa.."Cikin yake.

Ganinta yasa Da Sauri Aliima ta matsa Daga bayan Sharifa wacce tace ta Daure mata kitson da Band,ita kanta Sharifa taji kunya Domin Ba karamin Kawarjini Umma ke mata ba,Zuhra ce tayi Saurin Saukowa Daga Gadon tafada Jikinta tana Fadin"Oyoyo Umma..Tundazu da muka iso nake Cigiyarki.."Bayanta ta Shiga Bugawa Tana mirmishi harga Allah tana kaunar Zuhra saboda ita Rayuwarta bata gurbata ba kamar na Ziyada Sharifa ba"a mganarta Tunda Dangine na Uwa na uba Saboda haka Gada Tayi ba Haya ba,Itama rankwafa tayi tana gaisheta taamsa lokaci Daya tana Dauke kanta kafin tace'Ke Aliima rufe kofar Tiolet din Ko bakusan mala"iku na Tsinema mai mgana acikin bayi bane..?

Da Sauri ta Rufe tana Fadin"Wai Umma tsoro take ji yanzu ma tare da Sharifa sukayi wankan fa.." Sai da ta fada kana ta Rufe bakinta Tuna barambaram Datayi wani banzan kallo Umma ta Wurgamata Daidai lokacin Da Ziyada ta Fito tana Fadin"Allah Umma tsoron Tiolet nake ji ko agida Tare da Sharifa mukeyi In ba Haka bazan iya Shiga ni kadai ba.."Salati Umma ta saki acikin Ranta tana Ayyana yadda zasu lalatamata tarbiyan ya"ya kafin su tafi Fuska ta hade kafin tace"Kul kar na sake ji...Chan Lagos ne in kunyi Abunda kukeso an kyaleku nan kano ne kuma arewa ce gidana gidan Tarbiya ne kan Tafarkin Abunda Addininmu ya koyar damu,Haramun ne Wata cikinku ta kalli Tsiraicin yar"uwa ko su Aliima bana bari suna Fitowa Wanka Da Towel karami na Gwammace su Daura zanin da Hijabi kafin su Shiga wankan,Kar ku sake kokarin yimin wannan Banzar Dabi"ar agida banaso.."Tafada Fuskarta ba walwala Dukkansu Jikinsu yayi sanyi Zuhra ce tace"Insha Allahu Umma bazasu sake ba.."Tafada tana Hararansu da Sharifa Sun gane metake nufi baki suka Hada wajen Fadin"Kiyi hakuri Umma bazamu kara ba."Fuskarta ta saki kadan kafim tace"Na hakura ku kara kiyayewa.."Suka amsa da insha Allahu Juyawa tayi tana Fadin"Ku yi maza ku shirya ku fito mu ci Abinci.."Tafada tana Ficewa Daga Dakin Sai Lokaci  kowanne ya saki Numfashi Zuhra tace"Ai sai ku gyara Hallayarku nan dai ba gidan Mommy bane,Gidan Umma ne ba"a kawo mata wargi ko Raini.."Daga Sharifa har Ziyada basu tanka ba Ransu bace yake ba Duk Zumudinsu na Zuwa kano sai ya fita kansu Domin sun Tsani takura Sun manta Halin Umma ne ko Fita ba"ayi agidanta kullum ana gida Daga makaranta sai gida bata yarda da yawon banza ba

Bata koma Bedroom dinta ba ta Isa Dining ta kara gyara komai Sai ga Alhaji Sa"ed yafito cikin Jallabiya Fara yana Fadin"Fatima kamar naji kiran sallah ko..? Dagowa tayi tana Fadin"Eh kira ne ba"a Tada sallar ba mu fara cin abinci Daga baya sai muyi sallar Tunda naga Daga tafiya kuke kilama baku karya ba.."..

Mirmishi yayi yana karisowa kujera tajamai ya zauna yana Fadin"Coffea kawai nasha..Su Ziyada ma bana jin sun saka komai acikinsu saboda Murna.."Mirmishi kawai ta saki kafin tace"Ko na fara hadama Tea ne..?kai ya girgiza yana Fadin"A"a zubamin tuwo kinji Karki manta ni Tashin dawakinTofa  ne Rayuwar kauyen mun Saba da ita tun Safe zamu take ciki da kunu kafin Rana kuma mu kara Da Tuwo.."Yafada yana dariya itama dariyan tayi ta bude Coolar Tuwon Ta Ja Filet ta fara zubamai ta Turamai gabansa bayan ta Budemai tuwon Daga leda Miyar ta Zubamai tana Tashin kamshi baiyi mgana ba illah Kada kai kawai daya keyi Hannu ya ware yafara cin Tuwonsa Yana Fadin"Allah yayi miki albarka Fatima.."Da Ameen ta amsa tana zama gefensa sai gasu Alima sun Fito Dukkansu suka kariso suna musu sannu kowacce Taja kujera ta zauna Alima ta mike tayi Sarving din kowa nan suka Baje kowanne na kai lomar Tuwo su Ziyada anji chanji Hannu sai warba ake Dalilin Dayasa suke kaunar zuwa gida Umma Abinci Saboda ta iya abinci Sosai Ba kamar cham ba Da Bose take Jagwalgwalanta.

Atsanake suka gama cin Abinci Shi ya fara mikewa yana Share Hannnsa da Tissue yana Fadin"Bari na shiga na Dauro alwala naje masallaci nayi sallah naji an Tada.."Kada kai Umma tayi kafin ya wuce zuwa Bedroom din bai jima ba sai yashi ya Fito Fuskarsa Da Hannunsa da alamun Ruwa ya Fice yana Fadin"Sai na dawo.."Gabadayansu suka amsa da sai ka Dawo Daddy.

Yana fita yahadu da Hamisu Direba zai tafi masallacin Dake kusa Dasu tare suka Jera har zuwa masallacin Domin Alhaji Sa"ed koda ya taka wani matsayi Sam bashi da girman kai achan masallacin ma bayan an idar da sallah ya Dade yana gaisawa da mutane kafim ya Dawo gida sai da yaji bukatan wasu ya kuma mangance musu dama haka Abun yake indai yana gari Haka zaka ga kofar gidan Umma cike da mutane zai Fito kuma ya Sauraresu ya kuma Biya musu Bukatarsu Shiyasa Duk cikin anguwar kowa yabonsa yake da kyakyawan Hallayarsa na Taimakon Talakawa Gashi yana kokarin sama ma ya"yan Takala Aikin Costom din ba laifi ya Taimaki Mutane Dadama Ciki harda garin iyayensa Wato Dawakin Tofa Dake kano.

Wuni yayi agida bai kara Fita ko"ina ba, Suna Bedroom Shida Umma Su kuma yara suna Falo suna kallo Umma taso ta tura su Alima islamiya sai kuma ta kyalesu zuwa gobe,Sai bayan la"asar kana ta Fito lokacin Daddy ya samu barci Tace maza su tashi su Shiga kitchen ba yadda su ziyada suka iya suka mike Daga latsan latsan wayar da sukeyi Zuhra kuwa murna take saboda in tazo kano tana koyan Girke girke sosai Ita kadai ve bata da waya kuma ita tace abari sai ta gama Secondary Sch kana Daddy ya siya mata,sabanin Su ziyada tun suna jss suka mallaki manyan wayoyo wanda mommy ta siya musu su Alima kuwa Umma Batama da wannan Ra"ayin.

Dukkansu suka taru sukayi girkin Farar Shinkafa da miyar ganye sukayi su Ziyada dai ba Abunda akayi iya sai dai kallo Abun na basu mamaki ganin Su Asiya sun kware a iya girki Ga Zuhra ma ta Shige Cikinsu Kunun aya Alima tayi musu,Da suka gama Asiya da Zuhra da Ziyada suka Rinka Dauka kololin zuwa Dining Ita kuma Alima da  Sharifa suka gyara kitchen din Umma kuma ta Tafi wanka da sallah Daddy Tuni ya Fita sallar mangariba suma suna gamawa suka koma Dakunansu suka yi wanka sukayi sallar Lokacin Daddy ya Dawo suka fito Dinning suka ci abinci cikin Farinciki Cikin Ran Alhaji Sa'ed yana yaban kokarin Umma kan Tarbiya da Turba mai kyau karya ne,kazo gidanta baka tafi kana yabonta ba.

Suna kamallah cin abinci suka koma Dakinsu bayan Umma ta Jaddada musu su kwashe komai su maida ktichen din Su kuma gyara wajen suka amsa da Toh,Bai samu Fita sallar Isha"i tare da Umma sukayi jam"i bayan sungama suka zauna suna Addu"a Umma na gefe kanta na kasa Tana Jan carbi Daddy yajuyo gabanta Lokaci daya yana Fadin"Fatima.".

Tadago tana kallonsa Cikin Sanyin Murya yace"Alfarmarki zan roka kamar kullum yadda na saba duk da nasan tarin Laifina gareki bai kai matsayin da zaki man Abu ba sai domin alfarman da kika saba.."Ajiyar zuciya ta Sauke kafin tashafa Addu"arta tana Fadin"Sa'ed kenan..Ai ni na Dade da Yafemaka Duk laifin dakamin Tunkafin Rasuwar inna Asiya.."Tafada tana kauda kanta.

Hannayenta ya riko yana Fadin"Nasan da haka...Kin yafemin ammh kin kasa yafema Da'nki.Meyasa zuciyarki bazata waigo ta kalli Mutaddif ba..? karki manta ya Cika miki Burinki Fatima meyassa bazaki Dubesa ba Duba irin  na uwa da D'anta ba..."?Yafada yana Kura mata ido Itama cikin Rauni ta kafe shi da ido Lokaci Daya tana Fadin"Nasha gayamaka Alhaji kadaina kawomim mganar yaron nan in muna tare...Na Binne Amatsayina na mahaifiyarsa araina na barma Latifa shi har Abada..Ni fatima bani da wani Da bayan Alima da Asiya.."Tafada tana kokarin Dannen Rauninta hannayenta ya matse yana Fadin"A"a karki ce haka har gaban Abada kice Halastattaciyar uwarsa Fatima Latifa fa kara take miki ina laifin Wanda keson naka Don ta taimakama Abdulmutaddif yacika Burinsa na zama mawaki laifi ne..?

Da sauri ta Fizge hannuwanta ta mike tsaye Jikinta na rawa tace"Eh laifi ne mana Sa"ed...Meyasa bata Tabarmin Da'na ba...Lokacin Daya nuna min Burinsa na zama mawaki nina na Dakatar Dashi,Shine ita rabani Da D'ana dana fiso acikin ya"yana,Bayan kaima ka goyamata baya,kuna ganin zan yafe muku ne..? In na yafe muku Shi bazan yafe mishi ba domin ya manta ni Mahaifiyarsa ne da na Dauki Cikinsa na Tsawom Wata tara kafin nasha Wahalan Haihuwarsa ammh bai ji kunya ba ya tafi ya barni Lokacin da nake tsanananin bukatarsa ya Zabi Cikar Burinsa akaina...kai da ita kuntaba Tunanin Yinhaka laifi ne..?nace ka taba Tunanin hakan laifi ne awajena saboda kana Tunanin ni Bakauyiyace ban da ilimin boko ban da wayewa Saboda haka ban isa na Dakatar da D'ana kan Turban Da ya hau ba ka daukemin shi ka Damkama Latifa ta karbesa ta cikamasa Burinsa na zama mawakin Nanaye nikuwa in ban goge kaina amatsayin uwar Mutaddif mekake so nayi..Mekakeso nayi ehe..?

Tafada tana Fashewa da kuka kamar Zararriya cikin Azama ya mike yana fadin"Haba Fatima.."Ya mika hannu zai rikota ta Dakatar Dashi lokaci Daya tana Fadin"Karka kuskura ka tabani balle ka matso kusa dani kabarni nayi kuka bayan Amina bani da kowa agidan Duniyan nan sai Kai da Mutaddif da ku nafara girman sabawa Daku..kana Tunanin ban zan koka da kewarku ba Duka in Na Tuna kun man nisa ba..?tafada tana Zubar kwallah Lokaci Daya ta shige Tiolet tana kara Rushewa da kuka.

Kansa ya Dafe kan ya Sulale Bisa gado Lokaci Daya yana sakin Numfashi Kansa ya Dago yana Furzar da iska Lokaci Daya Tarihin Abunda ya Wuce Shekaru ashirin da Wani abu suka fara dawowamai Daki Daki kamar yana kallon a Magijin Bidiyo.