15
by @surayyahms
1️⃣5️⃣
cikin sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai tsanananin sanyi ibaad yadauke kasalallen kwayar idanunsa akan kyakkwan fuskar ayaanah dake kwance akan gadon asibitin tana bacci har yanzu bata bude idanunta ba
jikakken sumar kanta ya mammanu agefen wuyarta da fuskarta da wani jarababben diso dison ruwan hawaye daya salkafe tun daga long curly eye lashes inta har zuwa kan dan ƙaramin lips dinta dat is blush pink in colour, perfectly lined da baƙin zanen baki kamar an zana matashi da gazal, kallon ta yakeyi cikin yanayin da baisan ma mayake ji akanta ba, haushi ne, tausyayi ne, shide duk rasa wanne yafi ji aransa..
..abubuwan da suka farun ne kawai suka shiga dawomasa kai gabaki daya yarasa tainama zai nitsu ya fara warwaresu.
shide yasan duk tsiya bazai taba iya komawa gidansu da ayaanah snn ya sanar dasu cewa anbashi matar aure kwasam awani gari ba, matar ma yar karamar yarinya kmr wann, he just cant imagine the scandalous chaos this situation will bring upon his life, kusan dolene kawai ya samu kakarsa hajiy mairo a warware maganan nan auren nan anan tun wuri.
yana cikin wann tunanin yaji karar bude kofa ya juyo ahankli wata nurse ce ta shigo a natse da sallama abakinta, jikinta sanye da All white uniform na nurses riga da wando da white hijabi me dan girma sabida yadda ta manyanta sosai, haukar da juma yazo yay musu dazun yasaka aka kira musu local gorvenment chairman na yankin yay maza-maza ya sa aka turo da security da kuma older nurses nd midwives for immidiete duty shift replcment wanda dai akasan zasu iya tunkarar kowani irin jahilin mutum musnmn ma irinsu juma masu shigowa gatsau cikin kananan asibitin gwamnati da maqami suna masu yin barazana.
Ibaad ya zauna a kujerar gefen gadon Hannuwansa a dunkule, idanunsa suna kan ayaanah harsuka gama gaisawa da nurse in ayayinda tafara duban jikin ayanahn sosai.
tana gama dubata ta juyo tace "Alhamdullahi, she is resting, sedatives in nan yataimaka mata sosai, “zaku iya tafiya sai Ku dawo da safe. Idan ta tashi lafiya,an tabbatar komai daidai yake, sai ku tafi da ita gida.”
atakaice ibaad yace mata toh mungode...
yan rubuce rubucenta tay ta miƙa masa papern snn ta wuce tabarshi anan, baiko karanta papern ba ya cusa a aljihun wandonsa kallo daya yay ma ayaanah da hazel eyes insa dat are piercing nd emontionless da bazaka taɓa iya banbance ko kallon tausayi yake mata ko na mugun jin haushi ba...
for abt 3 mints yana kallonta can snn yasaki karamin ajiyan zuciya ya fice ya samu hajy mairo tanata surutu a waya da matasa wanda suka fice jeji neman taawure da polisawa, duk ance mata ba aga taawuren ba dan har garin majiya anje amma ba aganta ba. police dinne ya kwantar mata da hankli yace sun baza idanun su snn bazasu bar jejin majiya ba har sai sun samu labarin inda taawure take snn hanklinta ya kwanta.
kallonta ibaad yake harta gama ta sauƙe wayar a kunnenta cikin rauni hawaye ya sauka acikin kwayar idanunta ahankli tabi ta share hawayen da bakin gyalenta araunace snn ta kalleshi tace ya jikin ayaanahn?
kureta yay da kallo for a while snn yace "sunce muje gida sai gobe zamu iya tafiya da ita.
kara rushewa tay da kuka tana girgiza kai tana cewa 'aa wallah ba'a isa ba. babu inda zamuje hakanan daga zuwa caji offis ko wani kwakwaran sallama banyi da inayah ba akazo akacemin wai ta rasu kuma juma yazo ya dauki gawarta, wallah wallah bazan je koina ba bare hakan ya kara faruwa akan ayaanah,inaa karya akeyi, ni anyama ba haɗa baki da nass din asibitin nan juma yay ba kuwa??...
cikin katseta ibaad yace toh me kikeso muyi ynxu bayan ga security ko a tsayawa kikeso muyi anan har gobe nifa agajiye nake . tana share hawayenta tace ni bance maka ka kwana a tsaye ba, ai akwai masallacin asibiti inda kaje kayi sallah muje can babu kowa aciki kagama hutunka sai ka kwana anan ni zan kwana agefen ayaanah
gyada mata kai kawai yay suka kama hanya suka fice harabar asibitin wani irin dan uban sanyi ne yasauka agarin tsabar ruwan sama da suka sha sai ɓari hajy mairo take ta riko hannun ibaad kam kam direct masallacin ya wuce da ita suka samu kuwa babu kowa aciki sai hasken fitilan solar tana zama ya fice yaje motarsa ya dauko jakarsa da basket din abinci da sauran aikan ya taho mata dashi.
samunta yay tanata kuka ahnkli tana maganganu, shide baice komi ya zauna gefenta yay shiru yana jinta har saida ta gama duk mitarta da masifarta akan juma da kuma mutuwar inayah da babu tantama kaidaga yanayinta kasan mutuwar tan yay mata zafi bana kadan ba
can tay shiru dan tariga dasanin cewa ibaad ba rarrashinta zaiyi ba, kusan sa'a ma taci dayake kulata yau sosai, yo dama ace jikanta mujaheed ne tasan shikam da har kukan sai yatayata yi shikuma maheer tasan sosai zai lallasheta, da haushin hakan ta harareshi yay kwafa yana kallonta girarsa na sama adage ahankli yace "Inkin gama kukan ga abinci nan ammi tace inkawo miki. tsinin baki tay kamar bazata amshi ba ganin ya kara dauke kai akanta yana daddana wayarsa yasa tay wuf ta jawo basket din gabanta tana budewa tana masifa "Allah wadarar naka ya lalace mutum sai kace dutsi kaga tsohuwa tana rabza kuka amma sannu common bazaka iya gaya mata ba, rayyanu wallh ka zanca hali dan babu wanda zai baka matar aure da wnn baqin halin naka ahto...
baice mata komi ba tana bude abincin wani dan uban qamshin kaza ya budeta cikin lumshe ido da budewa tace "masha Allahu.. wann koda bansani ba fatima ne tay min wnn bandashen, a raunace ta dan cijja labbanta sai kuma ta rushe da kuka "ohhh fatima, Allah ya miki Albarka fatima, yar albarka haihuwar ki ne kawai banyi ba wallh duk kinfimin su zaidu da muhammadu kedai Allah yakai haske kabarinki...ibaad ya mata wani irin mugun kallo a mugun dakile yace "au addua kike ma uwata ta mutu kome? adan hatsale ta kallesa "yo mexan fada ka kulani inba haka ba? rayyanu rasuwa fa akamin amma kocemin ya hakuri bakayi ba wann wani irin rayuwa ne kakeyi haka da dakkken zuciya fisballahi abu babu tsari babu tausayi aciki.
hade rai yay yace bazan baki hakuri ba kawai kici abincinki in mun gaisa zan miki duk wani abunda kikeso haba mutum yacemiki yagama gajiya kinzo kin zauna kinata cikamai kunne da koke koken banza
...baki bude take kallonshi tay kifi kifi da idanu zata amsa cikin katseta yace" kinga tsohuwa babu wani abunda zance miki face saikin nitsu kinci abincin nan...hawaye na zuba mata yarrrr a idonta ta karkada kai cikin kyabe baki tace "Allah ya fika rayyanu, wallah Allah ya fika tunda harni kake min fada kamar ban haife ubanka ba dadinta dai kaima kasan zafin mutuwa. batare da ya kulata ba ya karbe abincin ya bude very swifly cikin nitsuwa da tsafta yaje ya wanke spoon da plate ya dawo ya zuba mata isasshe, yasa mata ruwa da fresh juice din da aka hado mata dashi ya aje mata agabanta snn ya kalleta yace bismillah"
..hawayenta ta share ta dau abincin tay bismillh tana kaiwa loma daya bakinta jin dadin abincin yasa takara rushewa da kuka..ganin ibaad ya hatsala yaja tsaki yatashi zai bar wajen
tay wuf ta cakumo gefen rigarsa kamar barawo, cikin lumshe ido da budewa yace haba hajiya waime hakane kinga ainace miki nagaji kawai inbazakici abincin nan ba ne kigayamin in rufeshi what is wrong with u
tanakan tauna naman tace"toh shikenan mutum bazaiy kukan dadi ba uban waye yake ji dani a duniyan nan inba fatima ba badan ita ba ina ce saide in kwana da yunwa yau
yace toh saiki ce inkiramiki ita kimata kukan nide wallah kika sake baremin baki zan fita waje i am so tired..
cikin yatsina tace toh naji naji Allah ya huci zuciyarka magajin babansa. cikin shareta ya dan kwace rigarsa ya dawo ya zauna kusa da ita daga nan sai bata kara cemai komi ba tanitsu taci abincin tanaci tana karkada kai ita dayanta tanakan tunawa da surkuwanta fatima...in sha Allahu zaidu saiya auri fatima haka kawai gidanmu bai koshi ba bazan kai fatima dawa ba.
.ita kadanta taketa raya hakan aranta har saida tay nakk da abincin ta koshi sosai, ibaad ya tattara plate din yaje waje bakin borehole ya dauraye tasstass
yazo da tsintsiya mai kyau daga waje yakara share wajen yay fesss yay kyan gani, tay tagumi sai kallonsa take tana kyabe baki itade duk ta rasa wani irin aljanun son tsafta Allah ya zuba masa.,
bayan ya gamane ya tura mata sakon anty safeeran agabanta tanata kallo tana yabawa sosai shikuma ya zuba makansa sauran abincin dan kadan yy bismillh ya fara ci anatsa, baiy kamr loma biyar ba ta matso kusa dashi tafara bashi labarin duk ydda ake ciki da lamarin juma da taawure from A-Z tana tashan mamakin ganin ibaad baiko girgiza da jin labarin ba ita kuwa dake bada labarin har tana kuka tana tara majina..
shiru yay har saida ta gama snn ya juyo ya kalleta cikin nitsuwa yace mata kukan ya isa haka kartaje tay ciwo. dakyar tay shiru saida ta nitsu snn shima yake gaya mata labarin abunda ya faru dashi, sosai tasha mamakinsa, tabi ta rushe masa da kuka kamar an bugeta tahau rufeshi da masifa najin irin taurin kan dayaje yy agaban sarkin fulani da na buzaye"
kai rayyanu na lura asirina kake so ka tonamin inba haka ba meye wann fisbillah, meye zaikai ka yin sa'insa da matsafa, jahilai, bokaye, baqaqn mugaye, azzaluman mutanen nan??? yo shikansa juman ai ba sallan yakeyi ba inba auren qaddara ba mema taawure zatay da jahili irinsa gashi gabaki daya ya lalata mata rayuwarta dana yayanta shine zai baka auren aayanah sadaka, lallai bansan juma ya tsane yarinyar nan har haka ba...toh ynxu inda ace bakaibane fa da saidai mu nema ayaanah a duniyar nan mu rasa ta har abada wayyo Allah, Allah ya isa, Allah ya isa tsakanina da juma Allah saiya saka ma taawure baiwar Allah babu abunda takwasa a auren nan sai baqin ciki da damuwa kajjje kacewa surkin naka Allah yafishi. mugu kawai azzalumi boka ma dashi, uban waye zaiy surki dashi inba irinka ba..
yadda duk ta rude tana masifar shirme tana rabza kuka tana bori yasaka ibaad yay shiru
baice komi ba, sai can daya lura kmr abun dagaskene ya girgizata yamata ciwo snn ya dan jawota jikinsa ta lafe ya rungumeta ya lallasheta sosai har saida ta nitsu tay shiru.
can sai ta dago kai ta kallesa tace "toy yanzu ya ake ciki? ka amshi auren kenan ko ya?
kai tsaye ahnkli yace "a'a ban karba ba. akan me zan karba?? kijiki da wata maganan banza
tace "a'a ni karka haura min rayyanu lokacin da kukayi abunku ina nan ne? amma ai ynxun nan kace sun dauke agogonka sunyi sadaki dashi kenan kuma sun baka yarinya ka karba aayanan ta zama matarka kenan ai...
yace awani addinin ne ta zama mata ta..wann fa ba aure bane hajiya dan wallah bai dauru ba inkuma baki amince da hakan ba gobe sassafe ki kiramana malami yazo nan yamiki bayani kiji, ni badon walakanta yarinyar da ciwo danaga anayi ba da saidai su kasheni awajen amma babu abunda zai saka in kawota nan dan babu abunda ya hadani da ita..
wani irin harararsa tay kmr ruwan idonta zai duba kasa tace "tokai yanxu saima a dauke ayaanan abaka kyauta kuma ka karba? yarinya wankakkeiya kyakkawa, me ilimi, da asali wacce harka mutu bazaka same kamarta ba,karka ga juma yay maka bozonta ka dauka ko shi yana dakai ne, toh wallh wallahi barikaji kakanta da kakan kanta hanshakan malaman addinin musulunci ne shikansa uban taawure hamshakin manomi ne me arzikin gaske ciwo da yaki ne ya cinyeshi mutuwa kuma ya raba taawure da gatanta har qaddarar aure yafado mata akan juma. toh ka iye bakinka akan yar jikata ahtooh ayaanah tafi karfinka..
tunda tafara maganan wani irin kallo kawai yake binta dashi tana rufe baki yace "wann duk ke ta shafa nidai bana sonta. kuma bazan karbi wani aure ba. kawai kisan nayi akashe maganar nan tun anan. snn kisani ina da duk wani labarin abunda ke faruwa dake anan garin tun daga kan satar da ake miki har da yan ta'adda da kike case dasu kina kaiwa maganan auren nan gida wallah saina tona miki asiri dake da sana'ar taki duk za'a kwasheku akaiku gida inga ta tsiyar..
baki bude ta dinga kallonsa cikin tafa hannu ohhh ni mairo ashe har cctv aka saka min kenan toh uban waye ya gaggaya maka wann uban karya haka rayyanu har kuma ka yadda?wani case? ni har ina nagamu da yan kidnaping..
fuskarsa a dore yace "zaki sani...kinsan ni bana wann wasan. har police station zanje a dauko min file din cases dinki da yan daban garin nan harda wanda kike boye masu bappa
rushewa da kuka tay tafara maganganu masu tsananin ban dariya ko ajikinshi haka ya hade rai ya dinga razanata..da kyar dai suka gama case dinnan sukayi bacci.
washe gari kusan da asubah ta farka taga yadda ya cire rigarsa me qamshi ya rufeta dashi dan kartasha sanyi da uban sauro shikuma ahakan ya hakura ya kwana atakure duk data farka ta kallesa atakure sai taji mugun tausayinsa ya kamata sosai, tashi tay ta rufesa da rigar snn ta koma cikin asibiti taje dan tay sallah snn ta duba jikin ayaanah
samu tay ayanah harta farka but she is very weak dakyar ma take magana..ga yunwa ga gajiya ganin kanta kwance akan gadon da yar uwarta ta rasu shiya kara dawowa mata da radadin zafin mutuwarta sabowa.
dakyar hajya mairo ta sakata sukayi sallah snn tanemi ruwan zafi ta bata tasha tazauna ta dinga lallashinta tana tambayarta duk abunda ya faru dan gabaki daya so take tasake jin sauran labarin yiyuwar auren nasu da jikarta ibaad, Allah Allah take taji inhar ibaad amince toh bazata sake a raba auren nan ba kodan ta samu kwakkwan dalilu nawucewa da ita birni na har abada...
dagata dayan bangaren kuwa daga cikin zauren wani gida dake can can jeji taawure ta fito, wata yar tsohuwace agidan wacce koyaushe taawure ta haihu ita take zuwa tay mata wankan gida har tamata jinya sosai sabida tuntuni juma ya hana hajya mairo taka gidansa.
anan wajen tsohuwar taawure taji dukkan labarin yadda aka binne yarta inayah awalakance da irin zargin zina da juma ya laƙaka akan yarsun snn ta bata labarin komi daya wakana akan auren ayaanah tace mata ai wani kyakkwn yaro jarumi me mota shine ya tafi da ayaana.
taawure kamar zata zauce haka tay kukan rasa yayanta acikin wnn daren musmn ji datay an aurar da ayanah wa wani wanda batasan sa baa abubuwa sai suka taru suka mata yawa sosai
zuciyarta ya cika da neman fansa bata damu ko zata mutu ayau ko zatay rai ba saitaji ta gwammaci ma gara ace abata duniyar data zauna cikin baqin cikin sanin cewa inayah ta mutu snn ayaanah ta aure wani wnda basu sanshi ba batama san ta ina zata fara nemota ba.
ranar yadda taga rana hakanan taga dare, kuka kam batasan kalar wanda batay shi aranar ba, can da asubah da sukayi sallahn fajr tsohuwar tana dan runtsawa kadan taawure ta bar kan sallahya ta fice ta zaga ta dauko katon sandan bugun shinkafa, igiya, wuka, da roban kananzir da ashana idonta a bushe tabi hasken almuru babu shakka ko tsoro ayanayinta ta saita hanya sai gidansa.
as usual dake sune ata karshe karshen gari babu wanda yasan da zuwanta wajen da aka binne yarta ta wuce direct yadda taga kmr kasa aka shuhhure akan kabarin yasa ta sulale kasa ta fashe da wani irin kuka me balain tsuma ayayin da koinanta ya shiga karkarwa mai tsanani koinanta ya nuna alaman firgita da baqin ciki me tsanani, bude bakinta tayi da niyyar yima inayar addua atake sai kuma taji wani irin nakason zuci ya mamayeta.
daci da baqin cikine ya rinka bin jinin jikintta har izuwa sassan gabobinta sai tayi lagwas jikinta babu kwari sosai tamkar wata nakasashiya haka ta dawo, cikin yanayin rasa me zatayi da rayuwarta ta sulale kan kabarin rigib ta kifu a kan gwuwarta, sai a sann adduar yazo mata tanayi tana wani irin razanannen kuka mai tsananin tsuma zuciya da shiga jiki wanda bata shirya masa ba
kuka tay har saida baqin cikin abun ya ragu mata aranta snn ta miƙe jikinta na rawa rawa idanunta ya mugun rufuwa da baqin ciki da batun daukar fansa tana ganin kamr inta kyale juma tay makanta da y'ay'anta butulci,yadda ya mata asarar yaranta yau takejin ko ta kashe shi, ko tay masa asarar duk wani abunda yakeji dashi masu muhimmanci a duniyansa agabaki day. an eye for an eye
ji take...inhar bata lahanta juma ba gani take kamar bazata kai gobe ba itama..
da makaman yaqinta ta shiga gidan, aurensu shekara 12 kenan babu abunda bata sani gameda arziki da kuma rayuwar juma ba, gogan dama ba tashi yakeyi yay salla akan lokaci ba wata rana ma bayayi bare ma yau da akace za'a tattauna abashi a matsayi afadan majiya ya tabbata babban burinsa na zama namiji me daraja agarin majiya zai yau zai cika...
turakarsa ta shiga kai tsaye batay wata wata ba ta farmasa da dabara yana cikin baccin ta dauresa tam da jikin gadon tun daga kafa har hannaye da jiki irin daurin goron nan tay masa, tana gama kullawa kuwa ya farka a firkice zai magana ta watsa masa makahon mari snn tabi tasamai ihu tafara tsine masa da yarensu tana kuma zaginsa ayanayin da ya mugun bashi tsoro...
tace mai bazai taba yin farinciki arayuwarsa ba, yadda ya binne mata yarta awalaknce shima haka yayansa agaba zasu zo su binneshi a walaknce, kuma inde tana raye bazai taba yin arziki ba har abada...
haka ta bugeshi da sanda tay masa jina jina, snn ta fice da kalanzir din tabibiye dakin ajiya da kan rumbunan abincinsa daya tara dumbin kayan abinci buhunai hatsi sunkai dari uku banda kananan shanya na su barkwano da gyada, waken suya da baqin cikin jin ya rabata da duka yaranta idonta a rufe ta bunka ma duk wani abunda ya tarana arxiki da wahalansa wuta ta kuma tabbata yakama sosai yana ci bal bal snn ta zubar da makamanta ta arce da mugun gudu tay hanyar tudu godiyan Allah da polisawa basu ganta ba harta isa gidan hajiya mairo agalabaice tana haki...
daga bangaren hajy mairon kuwa duk bataji dadi da ayaana ta gaya mata cewa ibaad bai amshi auren ba, hasalima cewa kawai yay zai tafi da ita amma bai furta da bakinsa cewa ya amshi aurenta ba wanda tun anan jikin hajy yqy sany ta san cewa dagasken babu aure. duk dama batay tsammanin hakan zai bata haushi sosai ba sai kuma taji kmr abun bai mata dadi aranta ba sam. kyale ayaanan tay akan ta huta bayan an idar da sallahn fajr awaje salun alun tafita taje tanemo musu malami, ibaad yana kofar masjid din yana zaune suna waya da bappa zaidu sai ga kirar mujaheed ma ya shigo, sun fara magana kenan basuy nisa ba wata nurse tazo har wajen ta kirashi akan anemansa acan ciki dakin ayaanah sallama yay da mujaheed din snn yabita suka wuce ciki kusan atare.
da sassanyar muryan sa yay musu sallama ayaana tanajin muryansa tay sauri ta lunshe idonta da alaman bata son ma ta kara kallonsa ita har yanzu mummunan tsoronsa takeji ganin yadda jiya ya tunkare babanta da kuma yan kauyensu da mugun taurin kai da jarumta har kuma ya kareta duk dama bata wankeshi da zargin zina da aka masa agaban kowa ba.
babu ko shakka tafi kowa farinciki data ji cewa shima jikar hajy mairo ne sai kuma ta bari akan cewa Allah ne kawai yake kareta daya turosa wajen shiya sa tafado ahannun na gida da ynxu batasan ma ya zatay da rayuwarta ba
dama kuma addanta tay mata alkwari akan cewa kota mutu bazata bari wani abu ya cutar da ita ba.. cikin wann yanayin hawaye masu sanyi suka dinga sauka maga daga cikin lunshashun idanunta, tanaji ibaad ya rusuna ya gaida hajiya mairo a mutunce kamr ba itace abokiyar fadarsa ta kullum ba, snn ya gaida malamin nann suka fara magana akan auren agaban kowa su hudun anaji ibaad ya sake maimaita ma malamin yadda auren ya faru.
acikin kankanin lokaci malamin ya warware musu bayani...
daga hajiya mairo, zuwa kan ibaad har ayaanan duk sunajin bayaninsa yace shi siffan daura auren a musulnci yana bukatar Ijāb da Qabūl wato bayarwa da amsa, nd it has to be a mutual offer & acceptance which must be done willingly. muddin ibaad baice “ya karɓa” with his own free choice ba, then auren bai dauru ba, musmn ba da akayi auren while he is still very much uncounsious, bada cikkaken saninsa ba, bada izininsa kona iyayensa ba, given by this alone auren bazaiyu ba ko shariance ne there is no real nikah. yace koda kuwa duk duniya ne aka taru aka shaida, a musulinci irin wnn aure still remain (invalid)
bayan haka Islam does NOT accept a forced marriage for either man or woman musmn while unconsious.
tsadadden agogonsa sa da aka nuna a matsayin sadaki shima malamin yqce ya haramta tunda bada izininsa ya miƙa musu ba daukawa sukayi bada saninsa ba,shima kuma za'a iya alaƙanta musushi da lefin masa sata.
malamin yace tunda auren bai dauru ba babu saki tsakaninsu sai dai "Faskh" wato annulment
Ma'ana auren ya haramta legally not bounded a shariance, snn a addininace dede yake da auren da ba'ayishi ba..
##idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
AREWABOOKS
@SURAYYAHMS
WATTAPAD @SURAYYAHMS
WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025