15
by @maidambu41
ALAƘAR ZUCI
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
Littafin nan na kudi ne akan 1500
1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita
Domin tura shaida wannan number. *** ko wannan ***
Posting Arewapen da Telegram
SHA BIYAR
Wannan sumar ya haifar da abubuwa dayawa, domin Mama ta tsaya a gefena tsawon wunin da nayi a gadon tana tare ni. Tashin hankalin da Ya Hafiz ya shiga abin har ya wuce tunanin kowa. Abu kamar wasa sai gashi lamarin ya wuce yadda ake tsammanin domin hajiya take kara jagula take al'amarin ta hanyar da aka yi wani rikici a cikin family akan aurena, sai da ta kai an rabu gida biyu wasu suna ganin kamar naki Ya Hafiz ne saboda Yan uwana sun zuga ni, Yayinda wasu suke tare da ni saboda ciwon da yake jikina suka ce ai tunda ya yarda da ya aikata ,sai gashi haka ya kawo rabuwar kuma kowa ya amince da a rabun, banda Abba da ya kafe shi da Baba Malam sai na koma.
Wasa wasa har tsawon kwanaki uku ina asibiti, yau Mama ta shirya tare da faɗin. "Zan tafi karbo takardanki, na gaji da ganin yadda kome yake faruwa shi Babanku ya dage ni ma kuwa ina tare dake babu wanda ya isa miki dole!" Gyada kai nayi ina mai cigaba da kwanciya, nasan cewa ina cikin tashin hankali, amma a kasan zuciyata ina jin kamar ban mishi adalci ba, anya Ya Hafiz ya cancanci haka? Bayan fitar ta sai ga Abba ya shigo, wani irin tsoro ne ya cika ni nayi baya ina zare idan, zama yayi.
Gyara zama Babanmu yayi yana kallon yadda nake zaune a wurin guda, tunda ya shigo dakin, ya ga na kurawa window din idanu. "Lubabatu!" Ya kira sunana, a hankali na juyo ina kallonshi. "Nasan lafiyarki lau me yasa kike bawa Yan uwanki da mijinki wahala!" Kura mishi idanu nayi ina kallonshi. Turo kofar dakin Ya Ado da Ya Umar suka yi a tare, "me yasa kike bawa zuciyar kowa wahala?" "Baba bata da lafiya ka bar wannan maganar idan mun dawo ayi ta!" Inji Ya Umar da yake yana da zafin rai sosai. Rike shi Ya Ado yayi yana girgiza mishi kai. "Lubabatu Y'ata ce, akan me kuke kokarin shiga tsakaninmu?"
"Saboda ka fifita zumunci akan Rayuwarta, ka rabata da Mahaifiyarta kada tazo ta ga halin da take ciki. Ka nisantata da kowa nata, Abba idan ka sake ta mutu a wannan yanayin Allah sai ya nuna maka iyakar...." Tass ya tsinkawa Ya Ado mari, a zuciye yayi waje." "Abba zan koma gidansa!" Juyawa yayi yana kallon yadda nake murmushi. "No Lulu kada ki mana haka." "A'a zan koma Ya Ado, zan koma saura me ya rage a rayuwata? Farin ciki sai dai wasu su yi, amma ni na san nayi hannun riga da shi, Ya Ado na gode sosai ka ce likita ya sallame ni kawai na koma dakina."
Hankad'o kofar aka yi da karfi Mama ce tsaye tana huci. "Ba zaki koma ba, kin gama aurensa daga kotu muke ga takardanki."
"Salamatu" "Sai me? Uwarshi ta kai kotu me ya rage? Ai dama albarkacin zumunci ne zaku kashe min Y'a Uwar da tafi ƙarfin Mijinta zaka yi tsammanin zata bar Lubnah ta zauna ne? An bashi kudin wanke muni me ake bukata?"
Shima kamar wanda aka wurgo shi ya ce mana. "Wallahi ban sake ta ba."
"Kotu ta sake ta!" Inji Mama tana kara kallonshi. "Kaci albarkacin Ubanka, da sai na saka an maka abinda baka zata ba, Lubabatu kuwa ta haramta maka. Adamu kasan yadda zaku yi da ita zaman Bauchi ya kare kuma ka kuma kusantar inda Lubabatu take sai na saka an wulakanta min kai, idan kana jin rashin kunya da fitsara wannan cikin ta haifa min, lauya, magatakarda, Soja, da sojar kasa da na sama sun fika kwaya da tijara ahir dinka."
"Wallahi ban sake ta ba, ina son Matata kuma babu wanda! Ya isa raba ni da ita Baban Bauchi kana gani sun raba ni da Matata!" Ya dawo gabana ya ce min. "Luluna kina ganin sun raba mu? Luluna ki ce wani abu, ni ne Ya Hafiz dinki. Dube ni ni ne Hafiz ɗinki!" A hankali na zare hannuna a cikin nashi, zuciyata tana wani irin bugawa na ce mishi. "Alhamdulillahi Ubangiji da ka samar min yanci! Ka je na yafe maka kai da Karimcy ka je na bar muku kome na cikin gidan hatta suturata na yafe, Alhamdulillahi Ubangiji na gode maka!" Sai a lokacin na samu damar fashewa da kuka. Kuka nake da dukkan zuciyata.
Cikin irin haukar da ya saba ya ce min. "Idan baki dawo gare ni ba. Wallahi haka zaki kare rayuwraki babu namijin da ya isa kallonki!" Cikin fushi Mama ta ce mishi.
"Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure kuwa wallahi sai tayi, ka fita kafin na kira a ci mutuncinka." "Lubnah ki dawo? Wallahi ki dawo ko kuma kina ji kina gani ki kare rayuwarki a wulakance! " Dariya Mama tayi tana faɗin. " Alhaji ka ji abinda danka yake faɗa? Ka ji yadda yake ihu bari na nuna mishi nima ina da fitsararru irinsa, ta leko waje tana faɗin. "Kai Adamu zo kayi min waje da wannan ɗan iskan ka nuna mishi yadda ake rashin kunya!" Ba Ya Ado ba bakiɗaya Yayuna maza suka yo dakin wani irin daukar amarya suka mishi, zuwa waje suka ajiye shi.. "idan ka sake zuwa inda Lubnah take gara ka kira kanka gawa domin sai munci Ubanka shege mara kunya dan iska!"
Suka kore shi sannan suka dawo a lokacin Abba ya mike tsaye, kin yi yadda kike so da Yaranki ku je na sallame ku ke da ita Yar so dinku!" " Alhamdulillahi Masha Allah, na gode katuro min takardar da wuri domin ina gama idda zan yi aure in sha Allah! " Ashe maza ma na da kishi, cak Abba ya tsaya ya ce mata. " Uban waye ya ce zaki yi aure a shekarunki nan? " " Allah mana ya ce nayi koda ta dauki kwarinka! " " Kai Adamu ka gaya mata wallahi na dawo da ita kuma kada ta wuce yau bata koma dakinta ba, ita kuma kanwarku ba dai gidana ba. " Yadda Abba ya nuna baya bukatar ganina yasa min wani irin kunci, a hankali Mama ta d'ago hannu zata tab'a ni nayi maza na kare kaina, tare da cewa. "Don Allah ki yi hakuri!" Sake baki kowa na dakin yayi suna kallona har shi Abba da bai fita ba, juyowa yayi yana kallon yadda na kare fuskana. "Lubnah meke damunki! " Inji Ya Ado da ya tako gabana, " babu! " Na furta a hankali ina kallon Mama da itama mamaki ya kusan kashe ta. " Hafiz yana dukanki ne?" Rufe bakina nayi ina kallon Abba. " Gaya min dukarki yake yi?" Fadawa jikin Mama nayi na rufe idanuna, sake magana yayi ma kame-kame Mama ina ajiyar zuciya. " Wai a haka za a mai da ta wurinsa! Umar muje Bauchi a mai da ita asibiti she need treatment domin basu yadda ya dauka yana azabtar da ita ba. "
Kiransu Aunty Innah da Hindatu aka yi aka ce zaa koma Bauchi saboda mota daya aka dauko, a ranar aka bar Jama'aren, karfe tara na dare muka isa Bauchi, kai tsaya asibiti aka wuce da ni. Sai da muka isa asibiti bakiɗaya sai na kasa fita a motar, sai da suka fitar da ni daga motar, haka aka dauko keken marasa lafiya aka wuce da ni, zan iya cewa tun daga ranar sabon jinya ya same ni, hatta zuciyata sai da ta samu matsala.
Saboda nauyin damuwa dama can kaina ya jima da tabuwa, haka nayi ta jinya har wata guda kowa ya koma wurin aikinsa. Ya Umar da Tahir sai Sani da aka sake shi, Aunty Raliya tana zuwa a kai akai duba ni, da duk abinda tasan zan so.
*
Flash back
Abinda ya faruwa kuwa, tunda Hajiyar Ya Hafiz ta ga kudin da aka kawo tayi lissafinsa zai kara musu wani abu da yake mugaye ne, ita da Yaranta Nana da Firdausi suka shirya a kai ƙarar Lubnah kotu, yadda dole a amshi kudin da yardan Hafiz ko kada ya yarda idan suka karbi kudin daga baya sai ya ce bai yarda ba, sai kuwa Tijjani yaji maganar shine ya gayawa Baban Jama'are, shi kuma da ya tabbatar an kai maganar kotu, shine ya kira Ado ya gaya mishi, shi kuma ya tura Hindatu, tana zuwa ta tabbatar dama case ɗin a Bauchi ake son ayi shi, amma tunda sun kawo ba tare da wani dogon magana ba, aka tattauna saboda abin na family ne a office din alkali aka yi magana take alkali ya sake Lubnah tunda uwar shi bata bukatar Lubnah sannan koda ace uwarsa tana son Lubnah dole Hafiz ya kyaleta tunda abin har da irin wannan rayuwar. Ana. Fitowa daga office din Tijani ya kira shi ya gaya masa, sai ga shi har kotun ana ta jajjanta lamarin, ihu yayi ta yi yana faɗin bai sake ta ba, wallahi bai sake Lubnah ba. Koda Hajiyarshi ta bashi kudin wanke muni watsi da su yayi ya ce mata. "Duk abinda ya faru ke ce kika lalata min kome na, ina son Matata kika yi ta saka ni a gaba na cutar da ita, wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba." Yayi ta rusa kuka har ya zo asibitin.
Wanann shine abinda ya faru.
**
A kwanakin da nayi ina jinya, babu wanda ya taba kira min sunan Ya Hafiz, nima kuma nayi ƙoƙarin danne tsoron da nake ji, sai dai kuma irin wannan tsoron baya barin Dan adam, domin abu ne da ruhi ya ginu akanshi, sai da ta kai ta kawo idan za a bude kofa da karfi sai na razana, ga wasu irin nightmare da nake yi,kamar dan mutu tsoro ya gama kassarani, karshe sai aka wayi gari amadadin jini na y sauka a'a jinina hawa yake kamar ana tula mishi gishiri, hatta likitan da yake duba ni sai da ya tambaye Mama ko tana bani wnai abincin da bai dace bane? Ta rantse mishi babu kome, shiru yayi kafin ya shiga tambayarta game da rayuwata kafin yau, bata boye mishi ba, amma yayi mamaki da ji ai ba a jima da kashe auren ba, don haka ya tafi da dare ina kwance ya shigo don Allah ya gani ko magana bana son yi ya shigo ya zauna tare da min tambayoyi, idanuna a rufe nake bashi amsa, abinda yayi matuƙar daure mishi kai, shine lokacin da ya mike ya matso zai duba ni domin ya ce na tashi zaune, wani baya da nayi saura kiris da na fado kasa. "Is ok ba zan miki kome ba,.amma ki kalle ni mana!" A dan tsorace na kalle shi nayi maza na rufe idanuna. "Hajiya haka take yi ne kullum!" Shiru tayi kafin ta ce mishi, "wani lokaci ba, musamman idan muna ta yawan baki masu zuwa gaishe ta!" "A dakatar dasu, su daina zuwa domin bata da lafiya sosai da sosai, jinya take bukata kafin ki tafi gida ku daura akan naku." Tabbas ni kaina nasan bani da lafiya, domin daga yadda nake razana da firgita.
Koda Yayuna suka zo Mama tayi musu bayani suka ga likita ya gaya musu halin da nake ciki, sai suke ganin kamar ba haka ba sai da Aunty Innah tazo ta fara musu bayani abinka da mai ilimin ta ce musu, ta gyara zama tana kallonsu kafin ta ce musu. "Lubnah tana bukatar kulawa a kowani irin Yanayi, Lubnah tana bukatar rayuwa me kyau no matter how tana bukatar faɗin ciki a ja ta a jiki." Sauke numfashi tayi tana kallon takardar hannunta ta ce musu. " Mun yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, Allah shi ya jarabci Lubnah da wannan laluran amma da ace tun farko da Hindatu ta fara min magana akan Lubnah zata samu wannan matsalar da tun lokacin aka kashe auren! "
"Dalla Malama ki mana bayani kin sa zuciyata sai tsalle take idan ta dirko ta fashe fa? " Inji Tahir da ya gaji da maganar da take yana son Isa ga point din. "*GAD*"
Ta furta muryanta yana rawa ta fara magana kamar haka. "GENERALIZED ANXIETY DISORDER, ake kiranshi a turance, cuta ce da take samun dan adam ta sanadin damuwa da tashin hankali tare da matsin lamba, wanda idan ta kai matakin chronic yake haifar da cutar hauka!"
" Bama depression ba?" Inji Ya Umar, hawaye ne ya zubo mata ta cigaba da cewa "A yanzu ta shiga mataki na biyu ga cutar, wanda daga shi sai hauka. Yawan razana da miyagun mafarki. Tun ranar da Mama ta kai hannu zata ta b'ata ta razana, ya fara jin shakku, idan kun lura ana bude kofar zata zabura." Kuka ta saka a hankali. " Tana kokarin fita daga staage ta shiga wancan da shine zata fara hauka. Tun da na ga tana yawan dariya ko tayi ta zama shiru nayi fatan ya tsaya a haka ashe har ya isa wannan matakin. "
" Kin ga ana warkewa ko ba a warkewa? "
Inji Ya Umar, cikin shashekar kuka ta ce mishi. "Ana warkewa idan aka hadu da therapy." Shiru yayi kafin ya ce mata. "Yanzu taya zamu iya magance matsalar Lubnah amma wancan dan kutumar uban na Ganshi sai na kusan kashe shi!" Mama da take bakin kofar basu san ta fito ba ta ce mishi. "Me yayi da za a kashe shi? Shi bai yiwa lubnah kome ba, nice a matsayina na uwa na kashe Lubnah na sha ganin damuwa a cikin idanunta amma na rufe nawa idanun bana son na karanta. Balle har na samu damar cewa tayi hakuri da ace na karanta ai da yau yarinyar nan bata nakasa har haka ba taya zan yi da Lubnah?"
Cikin kuka take magana, sanin cewa itama tana da laifi amma lokaci guda ta tsaya sai Yaran suka zagaye ta suna bata baki. Dakyar Mama tayi shiru.
Shigowa suka yi dakin, suka same ni kwance nayi rigingine, ina kallon sama ni kaina bana ce ga dalilin haka ba, amma na tsinci kaina da son kwanciya haka karar bude kofar yasa na rufe idanuna. "Auta!" Juyawa nayi ina kallonta. "Tashi ki ci abinci!" Duk yadda nake ji a zuciyata bana son ganin Mama tana damuwa balle yau ganin hawaye na zuba mata yasa na mike zaune. Abincin ta kawo min ta zauna a gefena tana mai diba ta bani a baki. Kallon cokalin nayi kafin na bude a hankali na amsa, hawaye na zuba mata tana bani ina ci, a hankali na kai hannuna saman fuskarta na goge mata. Murmushi tayi nima na mai da mata, na cigaba da amsa tana kuka har na kauda kaina domin idanuna yana cika da kwalla. Ruwa Aunty Innah ta bani na sha ina son Magana amma ban san me zance ba, a hankali na ce musu. "Amma ba zan koma gidan Ya Hafiz ba ko?" Ya Tahir ya matso gefena ya riko hannuna ya ce min. "Waye ya ce zaki koma gidan Hafiz?" Girgixa kai nayi matse hannuna yayi ya ce min. "Ki kwantar da hankalinki, babu inda zaki in sha Allah. Daga gidana babu wani wurin da zaki kin ji zaki zauna a gidana ko?" Gyada kai nayi ya ce min. "Kada ki kara tuna wani can da bai da amfani a rayuwarki da namu kin ji!"
Gyada kai nayi suka gaya min kowa ya shirya domin na zauna a gidanshi. Amma firstly lafiyata suke bukata domin sai da ita zan rayu. Tun daga ranar aka daura ni akan magani, idan Aunty Innah ta taso zata zo ta zauna tana kara tisa min karatun Alqur'ani da azkar. Haka yasa kullum ina cikin Alwala koda kuwa bani da tsarki ne, zuciyata ta samu nutswa. A cikin sati biyar da nayi a cikin babban asibitin Bauchi, duk wnada ya ganni sai ya san na samu nutswa sama da can baya.
*
Hafiz
Ya gigice domin har Karimah sai da ya koreta, kamar zai yi hauka sannan kullum yana hanyar wurin Baban Bauchi, tare da rokon ya saka baki Lubnah ta dawo amma baban Bauchi ya ce yana kan ƙoƙarin ta dawo ya jira a sallamota, domin har ga Allah tausayi Hafiz yake ji, yadda ya gigice har Jama'are ya je gaban Baba Malam yana kuka wiiwii da yake shima Baba Malam ya ɗan ji haushin abin da Hafiz yayi amma da yake zuciyarsa muguwa ce sai gashi ya kira Baban Bauchi..
*****