GUDUN AURE

by @bintaumarabbale

Jin haka ya sanya yaron da sauri ya zo 'buya a bayana ya fara kuka. Ya kuwa janyo shi ya gwaura masa mari wanda ya gigitashi ya k'wallara ihu! Ya rike tsintsiyar hannunsa da kyau! Yana fad'in." Me kake so ka zama Kamalu? nawa shekarun naka suke a duniya da za ka dinga daga mana hankali, kai ba ka tausayin uwarka da take ta fadi tashi a kanku, ba zaka ri'ke maraicinka ba ko? idan ka yi wa Yaya Aminu haka ba ka yi masa adalci ba, sannan ba ka yi wa kanka adalci ba, kaf zuri'armu babu wanda ya ta'ba shiga hannun hukuma sai kai daga tasowarka zaka jaza mana abin magana." Bai dubi ihun da yake kurmawa ba ya 'kara kai masa wani marin a d'aya kumatun. Ya kid'ime sosai yana fad'in." Don Allah Baba Hamusu ka yi hakuri ba zan sake ba. Wayyo Allah Ummansu Saminu ki zo ki cece ni." Ya rike shi da kyau! Ganin yana ta kiciniyar fizgewa daga hannunsa. Ya ce.'' Wallahi ni ne maganinka Kamalu makaranta zan kai ka, a d'aure ka da sa-sari(mari!) ka je can ka zama almajira mahadaccin al'kur'ani, ba za ka d'orawa mahaifiyarka ciwo ba." Jin haka sai ya sake gigicewa Yana fad'in." Na rantse da Allah ba zan sake ba, Baba Hamusu don Allah ku yi hakuri." Ya juyo yana kallona " Mama ki yi hakuri ba zan sake ba." Yusi Yana kuka sosai kamar shi ya aikata lefin ya daddafa 'kafafuna har sai da na ji yadda jikinsa ya rawa. Ya ce." Mama ki yi hakuri, ki ce kin yafe masa, don Allah kada ki bayar dashi aka shi almajiranci kin ji mama." Wasu hawaye ne masu tsananin zafi suka kece mini. Tausayin yaran ya kara tsananta a cikin zuciyata. Haka suke yi a junansu. Mussaman shi Kamalun ya yarda ya ci zalin d'an'uwansa, amma bai yarda wani ya ta'ba shi ba. Ko a makaranta ne idan aka ci zalinsa a ajinsu ana tashi sai ya tare hanya har sai ya ramawa d'an'uwansa hankalinsa yake kwanciya. Duk lokacin da Kamalu ya yi lefi ina yi masa fada. Yusi shi yake shiga damuwa fiye dashi wanda ya yi lefin, ya dinga ba ni ha'kuri kenan. Ya je da rarrafe ya rike kafafun kawun nasa Yana cewa." Baba Hamusu don Allah ka yi hakuri ba zai sake ba, kada ka kai shi bara." Ummansu Hadiza ta le'ko tana fad'in." Hamusu Ya isa haka, ai ya bada ha'kuri, dukan ba zai shiryar ba sai dai addu'a, kuma dai kowa da irin k'uruciyarsa. Tasa ce kawai ta fito fili, amma duk abokanan nasa haka suke da 'kin ji, ku yi masa addu'a kawai Allah Ya tsayar iya nan." Ya sake shi. A guje ya je ya ri'ke Ummansu Hadiza Yana fad'in." Don Allah ki ce masa kada ya kai ni bara ba zan 'kara ba." Ta ri'ke shi tana cewa." Zan gaya masa, amma kai ma ka yi mini alkawari ba zaka sake k'wacen kud'i ba." Cikin kuka Ya ce." Ba zan sake ba na yi alkawari." Sai ta ja hannunsa suka fita tana fad'in." Idan kuwa hakane ni ma ba zan bari a kai ka almajiranci ba." Ya juyo yana kallona a sanyaye ya ce." Anti Amina don Allah ki daina kuka. Hakan zai sake jefa shi cikin wani yanayi. Ki dinga ko'karin sarrafa kanki. Wallahi tallahi ba ki fi mu shiga tashin hankali ba da damuwa ba, ba ki ga yadda Gwaggwo duk ta rud'e da jin abinda yaron ya aikata. Tana fad'in sai ta zo na ce ta zauna zan je ni na ji Ina aka kwana. Da kyar ta ha'kura. Ina zuwa kuma sai Usaini yake fad'a mini ai an kashe maganar. Ki yi hakuri ki cigaba da yi masa addu'a, in sha Allahu rabbi za ki huta da shi." Na yi 'ko'karin dakatar da hawayen da suke zuba. Murya a dashe na ce." In sha Allahu zan yi 'kokarin yin hakan Hamusu na gode sosai da kokarin'ka, Allah Ya shirye shi.'' Ya amsa da "Amin Ya Allah." Kafin ya yi mini sallama ya tafi. Da 'kyar na iya cin abinci saboda tsananin damuwa. Wajejan takwas da rabi. Babanmu ya shigo dama idan ya rufe shagonsa ba gida yake dawowa ba yana tafiya bakin titin gidan 'kan'kara wurin abokanansa tun na k'uruciya su yi hira. Ya shigo d'akin Yana kiran sunana na amsa. Ya ce." Tun kafin na shigo gida jama'a suke yi mini jaje a hanya. Anya Amina yaron nan ba za ki mayar dashi hannun iyayensa ba, kada fa ya lalace a yi kuka da mu." Hanci na ja, a tausashe na ce." Baba ka yi hakuri da abinda zan fad'a maka don Allah ku bar ni na ri'ke yarana ba na so na yi ta jayayya da ku, Allah ne mai shiryarwa, in sha Allahu Kamalu ba zai lalace ba." Ya ce." Duk da haka dai. Kin san idan aure za ki yi babu namijin da zai ri'ke miki yara har biyu, ban 'ki ma 'karamin ba, shi wannan din da yake neman gagarar mutane ki mayar dashi can hannun kakarsa tunda tana raye." Shiru na yi ina nazarin maganarsa. Na san dama da wahala a samu namijin da zai aure ni da yara biyu. Wannan shine dalilin ma da ya sanya gabad'aya na ji auran ya fice mini daga rai, ba don komai ba sai don faruwar matsaltsalu bayan auran. Ba na jin zan yi aure a irin wannan yanayin gaskiya magana kenan. Maganarsa ta fargar da ni ashe Yana tsaye bai fita ba. Ya cigaba da cewa." Alhaji Muntari yana kan hanya zai zo ku gaisa idan kin amince ba za a ja dogon lokaci ba, tunda dake dashi duka ba yara ba ne." Cike da tsananin damuwa na ce." Shikkenan Baba zan yi bincike a kansa, idan ya kwanta mini a rai sai a yi." Ya ce." Hurumin bincike ba a hannunki yake ba, mun riga mun gama bincike a kansa. Mutumin nan sananne ne, Ubangidan Babanki Sule ne, kuma yana da rufin asiri da dattako, sai ki godewa Allah wannan karon ba ki yi jinkiri ba. kuma Ya ba ki miji mai wadata, idan Allah Ya yi ma don ya ri'ke miki yaran ba wani abu ba ne a wurinsa tunda Yana da hali." Shiru na yi ban ce komai ba. Ya kama hanyar fita yana fad'in." Ba za mu bari wannan damar ta wuce mu ba, ni kuma ba zan zuba Ido na dinga ganinki a gida kina yi mini shige da fice ba." Shimfid'a na gyarawa yaran ina ta nazarin yadda rayuwar duniya take kwatantawa da ni. Babanmu da d'an'uwansa suna hango wadatar Alhaji Muntari. Suna ganin idan na aure shi zan huta suma za su huta, ni kuma akwai abinda nake hange. Tara saura na dare yaro ya shigo yana fad'in." Wai ana sallama da Amina." Ummansu Hadiza ta yi caraf ta ce." To gata nan zuwa." Na juya na dubi Yusi da yake bacci a shimfid'arsu har lokacin Kamalu bai shigo ba yana can wurin Ummansu Hadiza. Hijabina na zura ba tare da wata kwalliya ko fesa turare ba nasa takalmana na fita. Yana jingine a jikin motarsa babban mutum ne don zai yi shekarun Baba Sulen. Yana da ki'ba daidai misali da duhun fata Amma ba can ba. Ga dai tumbi nan ya ajiye irin na alhazawa. Yana sanye da shadda riga tazarce da hula a saman kansa. Hannunsa kuwa manyan wayoyi ne guda biyu. Cikin nutsuwa na iske inda yake tsaye. Ya saki fuskarsa yana kallona tare da furta." Allah Ya sa ba daga bacci aka tashe ki ba."