ALAƘAR ZUCI

16

by @maidambu41

*ALAƘAR ZUCI*

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500*

*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita*

Domin tura shaida wannan number. *** ko wannan ***

Posting Arewapen da Telegram

SHA SHIDA

Da yake zuciyarsu ta cika da zalinci da mugunta, yadda yake shiga ba nan yake fita ba shi damuwarsa a maida Lubnah dakin Hafiz haka ne zai saka Hafiz ya samu nutsuwa, sai dai shi Baban Bauchi ya tabbatar mishi da cewa case ɗin bayana hannunsa yana hannun Baban Jama'are, wato mahaifin Hafiz, haka ya saka Hafiz a gaba har gaban mahaifinsa. Bayan sun zauna ba tare da dogon magana ba, ya ce ga abinda zai yi kuma Umarni ya bada ba ba kome ba. Shiru Baban Jama'are yayi tare da kallon Mahaifinsa. Sannan ya kalli Hafiz da yayi wani zuru-zuru. Ya ce mishi. "Baba ka tambaye tsakaninsa da Allah Lubabatu ta zalince? Idan ya ce eh yau ba sai gobe ba zata koma dakinsa idan kuma ya kasa ba ni amsar tambayoyin da zan mishi har abada ya rasa ta kenan."

A matuƙar razane Hafiz yake kallon Mahaifinsa, ya kuma kalli Baba Malam, kamar ya ce. " Don Allah Baba Malam, ja saka baki wallahi abubuwan ba sauki." Gyara zama Baban Jama'are yayi ya ce mishi. " Wallahi warabbul ka'aba idan har ka tabbatar sau daya Lubabatu ta cutar da kai tow yau zata koma dakinka! " Wasu irin zufa ke karyo mishi yana sharewa suna kara karyowa.

"Ka bawa Lubabatu maganin hana daukar ciki ko baka bata ba?" Baban Jama'are ya watsa mishi tambayar, kamar yayi kuka ya rike hannun Baba Malam. Yana me gyad'a. " Da bakinka zaka gaya min?" " Na bata" Hafiz ya fada yana shashekar kuka.

Murmushi Baban Jama'are yayi yana kallon danshi, cikin wani irin yanayi na Tausayi me zagaye da bakin ciki. Ya ce mishi. "Ka bata kwayar yan shaye-shaye ko baka bata ba?" Cikin wani irin kuka ya ce mishi. "Na bata?" Cizon lips dinsa Baban Jama'are yayi yana jin idanunsa na cika da kwalla.. "ka sayar mata da gidanta ko baka sayar ba?" Kanshi a sunkuye ya ce mishi. "Na sayar Baba!"

"Waye ya shiga tsakaninta da danginta?" Cikin wani irin gigita ya kalli Babansa ya ce mishi. "Baba ka gaya min ba zan same ta ba har abada, wallahi yanzu na tuba ina son Lubnah kamar yadda ta so ni a baya. Don Allah kada ka raba ni ita."

Zuciyar Baban Jama'are yayi laushi amma abinda ya saka Hafiz saduda na karamin al'amari bane. "Na san halinka na san waye kai. Da ka girmama kanka da yau an wayi gari duniya ta girmama ka. Shi girmama ana nimansa ne tun daga yarinta Yaro ya yi abinda Manya suke yi sai ka ga girma ya shige shi. Da yau ka mu'amala Lubnah da adalci ina ga da yanxu kuna da Yara uku zuwa hudu, amma haka ka kashe ta kana ta kwashe duk abinda ta mallaka bayan ta tsaya maka, tayiwa Uwarka, tayi maka, tayiwa Yaranka, tayiwa yan uwanka, wacce irin son zuciya ce haka? Me tayi maka da zafi haka? Na zata kaf duniya idan akwai wanda zaka bawa kariya Lubnah ce, iyayenta suka maka riga da wando suka dauki yarsu mafi soyuwa suka baka, a lokacin akwai wani bawan Allah da ya zo yana sonta da gaskiya yarinyar nan ta juya baya ta ce bata son shi sai kai, yau an wayi gari ka gama lalata mata rayuwa, yau yarinya da bata wuce shekaru ashirin da shida tana zuwa da bakwai tana can tana fama da jinyar bakin cikin da kayi ta cusa mata, Hafiz ni na haife ka amma ni ma ban tsira daga kaidinka ba, me yasa sai Lubnah? Me tayi da zafi ka mata haka? " Hawaye ne yayi ta zubo mishi yana faɗin n. " Don Allah ka yi hakuri ka rufa min asiri, Lubabatu ita ce rayuwata, ita ce arzikina. Baba don Allah ka yafe min ka bani lubnah a karo na biyu."

"Ba zan iya ba kayi hakuri, kaf duniya ni nake da iko da Adamu da Hindatu idan nace su dawo da ita zasu dawo da ita amma itama ina son ta shaki iskar yanci, ta san itama mace ce kuma mutum mai yanci, idan na ji labarin ka kuma d'ago maganar nan wallahi akan mahaifiyarka zan sauke shi. Kai na shiga tsakaninku da Lubnah har abada babu aure a tsakanin sai zumunci shima idan ta gadama idan na ji labarin wani abu ya faru sai ka gani a kwayar cin tuwonka!"

"Yanzu ni ban isa ba! Yaron nan yayi nadama!" Inji baba Malam!,

"Kayi hakuri Baba kai ikonka akanmu ne, Yaranmu kuwa ka barmu, akansu da ace tun farko ka amshi uzrin yarinyar nan da yau maganar bata dawo hannunmu ba, Baba ita gaskiya daya ce, don Allah ka bar yaran nan su dauki path din da kowa ya mishi duk wnada ya zalincin wani Allah ya bi masa hakkinsa." Rikicewa Hafiz yayi yana kuka yana rokon a bashi dama ɗaya. Babanshi kuwa ya ce ai yayi watsi da damarshi tun fil azal yanzu ya cigaba da hakuri kawai.

Wannan abin ya d'aga mishi haka, haka ya dawo wurin Hajiyarsu yayi ta kuka yana tambayarta me yasa tayi masa haka, me yasa ta shiga rayuwarshi da farko ya zata zai iya handle din matsalar sai ya fahimci ina kome ya lalace mishi, bai taɓa kawowa yana son Lubnah ba sai yanzu da ya rasata, haka yasa ya sha alwashin matukar bai same ta ba, har abada babu me samunta itama Hajiya ta kara tabbatarwa matukar basu dawo mishi da ita sai dai ta kare rayuwarta babu aure. Yadda suke kulla sharri matukar Lubnah bata dawo gare shi ba, abinda zasu mata sai ta zama abin tausayi. Wannan masifar da suke kulawa ya tsaya a tsakaninsu sannan itama Hajiyar zata je har Bauchi ta roke su idan suka ka ki kuwa sai dai su san yadda zasu da Lubnah. Wanann shi ne tsarin da suka yi, bayan sun manta da akwai Allah.

**

Lubnah

Rayuwa kamar littafi ne, yau idan wannan shafin ya bude maka gobe wani zai kara budewa, haka rayuwata ta shiga cikin jerin littattafan da ban san lokacin da na mallake su ba, kwanakina arba'in aka sallame ni, zuwa gidan Ya Tahir. Wanda shi ya fara nuna sha'awarsa akan na zauna a wurinsa. Aka gyara min dakina ba abinda ba a zuba min ba.

Tunda na dawo na samu nutsuwar zuciya da ruhi, shi yake bani magani ya kuma tsaya a kaina sai na ci abinci na sha maganin. Safe da yamma da rana kuma Matarshi tana bani. A hankali nutsuwa da kwanciyar hankali ya fara dawowa a rayuwata. Tseren da muka fara da kaddara ya dawo abu mafi sauƙin isowa. Mama gidan Ya Umar ta koma abinta, da suka mata maganar ta koma gidan Abba ta ce bata san da zancen ba, sosai Mama ta dauki wuta domin tafi kowa daukar zafi shi kanshi Abba sai da ta kai ta kawo yana shakkar mata magana, haka ya tafi har Jama'are yana samu Alhaji Ahmed Galadima babban wansu Mama ya roke shi ya saka baki Mama ya dawo, murmushi Yayi ya ce mishi ka zauna da ita tsawon shekaru arba'in ka san wacece ita ka je kai da kanka zata dawo! " Ba haka Abba ya so, Alhaji Ahmed Galadima ya tirsassa Mama ta koma sai gashi shima ya ce ya lallabata, kai karshe sai gashi ya kira Ya Ado tare da rokon shi da Yan uwansa su saka baki Uwarsu ta dawo dakinta. Ya ce mishi zasu mata magana in sha Allah.

Ai kuwa Ya Ado yana yiwa Mama magana ta ce ita fa ba inda zata koma ba sai dai yayi duk abinda zai yi, dukkanmu muka yi ta bata hakuri kafin ta amince ta koma amma shima Abba sai da yaji a jikinsa. Tsofaffin nan suna son junansu amma bakiɗaya sun koma kamar wasu kananan Yara sai wani jayayya suke. Haka muka cigaba da rayuwar a hankali ina ƙoƙarin zama mutum daga layin mahaukata zuwa jinsin mutane masu lafiya da cikakken hankali.

Sai da wata biyu kafin na fara jinin hailata domin shima daukewa yayi saboda tashin hankali, a wannan watan na fara kirga kwananki Iddana, da yake kwanaki biyar nake ina gamawa, na gayawa Aunty Hindatu da Aunty Innah, suka sani. Don sun ce idan yazo na gaya musu. Kamar da wasa na daina tunanin wani can Ya Hafiz, na daina tunanin kowa ni yanxu ai mazan tsoro suke ba ni, ba iya maza ba duk abinda za ayi tashin hankali da fada a kai take sai naji kamar zan mutu da tashin hankali. Shi yasa bana shiga ko hayaniyar Yaran Ya Tahir, suna fara zan gudu daki bana son tashin hankali ko yanayi sai naji kamar wani abu yana yawo a kaina. Haka yasa Uwar tana jin sun fara zata fara fada da kokarin kiran Babansu.

Wata hudu da mutuwar aure duk da ban gama idar ba, ranar na samu bakuntar Ruma Rabi'u Mai shanu ta zo min, Nafisa Sadi Gital, Hafsat Faruq Babaji, dukkansu Uku kowacce da Yaranta nayi mamakin da suka ji labarin ina gidan Ya Tahir.. "ladies a ina kuka ji ina nan gidan?" "Jalilah Kamil Jama'are ta gaya mana!" Lashe bakina nayi, sai kallon tausayi suke min. Yadda nake zaune kowa yasan yadda bana son kallon tausayi domin sai na fara jin wani irin tashin hankali. "Ku daina min kallon tausayi, ina da condition da mentally ill idan aka cigaba yanayin yana birkita min ƙwaƙwalwa Please." Yadda nayi maganar sai na ga suna kuka. Which mean sun san da haka, haka suka rungume ni tare sha faɗin. "Lulu in sha Allah zaki yi farin ciki, Ubangiji ya kawo lokacin farin cikin ne." Murmushi nayi ina shafa bayansu nace musu. "Alhamdulillahi Ubangiji ya bamu hakurin akan rayuwa." Daga nan jefi-jefi ina shiga hiran wani kuma nayi shiru nayi ta kallonsu kowacce take gaya min Yaranta da sauran nasarar da suka samu a lokacin suka bani shawarar idan na gama Idda na fara aiki, wani aiki zan yi? Ni da hayaniya yake d'aga min hankali, tow kadai nace musu anan suka wuce sai dare suka tafi bayan sun kawo min kayan alkhairi kala kala. Haka na yi ta shafa rayuwata a hankali har na gama iddana ina kuma ganin likita a kai a kai. A lokacin likitan shima yana jin dadin ganin yadda nake rayuwa cikin aminci da nutsuwa.

Ranar da Ya Hafiz ya ji labarin na gama Idda, sai da ya kwanta a gadon Asibiti. Yayi ta surutu Matarshi ce aka raba shi da ita har da fisge-fisge, abin da ba dadin ji domin sai gashi kamar mai cutar farfadiya haka yake wasu abubuwan.

Da na ji labarin na tausaya mishi amma idan na tuna yadda yaso kashe ni sai naji shi ba abin tausayi ba ne da ya samu wuri kashe ni zai yi da kwanaki na, gara da Allah ya yakin ce min shi da an barni da halina tabbas da na mutu.

Kwatsam ina zaune Aunty Innah ta nima min aikin koyarwa, wai ko dai rage min zaman da nake na kadaici, matata kuwa da Ya Hafiz ya rike sun karba aka sayar aka sauya min wata yar karama mai kyau, haka na fara zuwa aiki da ita. Bana shiga rayuwar kowa bana iya d'ago kai kalli mutum, asalima maza tsoro suke bani domin kallon Ya Hafiz nake su. Malamai mata ma sama-sama muke gaisawa.

Haka na cigaba da aikina yaran bani da matsala da su, musamman da suke ƙanana. Ina koya musu math, yadda na samu nutsuwa a yar wannan lokacin yasa hatta Yaran sun san bana son tashin hankali. Bana son magana bana son hayaniya. Sai Allah ya bani sa'a akansu yadda ko tari basu min nima da na fahimci sun fahimci halina, sai nake saya musu yar choco-choco ina bawa masu ƙoƙarin cikinsu, ina son Yara ina son ganinsu cikin farin ciki da walwala. Haka yasa yaran idan na shiga ajin sai su yi shiru kafin su mike su gaishe ni, sai na musu alama da da hannu suke zama na cigaba da musu karatu, kasancewar makarantar private ne sai Allah ya taimaka duk ranar Alhamis ina fita da su, PE physical education, saboda Yarar juma'a manya ke fita.

Yau da ya kasance Alhamis na isa Makarantar da wuri, nayi parking sannan na wuce staff office nayi sign sannan na nufi hanyar aji sai ga daya daga cikin malaman makaranta ya ce min. "Mrs Jama'are kina headmistress tana kiranki!" "Ok na gode!" Na juya na wuce office din, ina shiga da sallama idanuna ya fad'a cikin na......