GUMBAR DUTSE

G_D - 01

by @khadeejacandy

***

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

SOYAYYAR KURMA KUMA HUNTUWA

Back again with another saga, you won’t regret reading, In Shaa Allahu.

Love doesn’t need words to be real. Sometimes, idan kalmomi suka kasa, zuciya ce ke magana. idan murya ta yi shiru, kallo ɗaya yana iya fassara duk wani abu da rai ke ji.

He fell in love with her silence.

She fell in love with the way he saw her heart, not her voice.

Tsari da zubin irin wannan tafiyar kenan.

Shimfidace ta wani sabon labari daga marubuciyarku Khadeeja Candy fatar za ku karbe shi hannu biyu.

Ban zan cika baki ba, amman ina da yakinin zai muku dadi fiye da sauran, domin labarin ma na dabam ne, jaruman cikinsa da digon tawadar alkamin ta dabam ce.

⚠️ Wannan labarin kirkirarren ne, idan ya ci karo da rayuwar wasu ko wata to arashi aka samu.

In collaboration with

JISMA INTERIOR DECORATION 🏡

YAR FILLO COLLECTION (Turenwuta, Humra, Body Milk & Air Fresheners) ✨

JISMA JEWELLERIES 💍

Za ku iya following dinsu ta Instagram:

@jismajewelleries01

***

@yar_fillo_collection

***

@jisma_interiordeco1

***

TikTok: @jisma_interior_deco1

***

Zaku iya Karanta GUMBAR DUTSE a Wattpad & Arewabooks @KhadeejaCandy

Stay tuned, my people.

This one will melt hearts, break silence, and redefine what love is truly means.

#KhadeejaCandySaga

#SoyayyarKurmaKumaHuntuwa

LITTAFIN NAN SADAUKARWA CE GA MACEN DA TA CANCANCI SADAUKARWA HAJIYA HABIBA MUHAMMAD, a beautiful sister from another precious mother, Allah ya cika burinki ya tsare gaba da bayanki. Wallahi ina kaunarki fiye da yadda kike kaunar farinciki da cigabana ILYSM

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣

Ya duba ko'ina be ga kowa alamar mutane ba, balle ya tambaya waye mai tulun dake aje ya roki alfarmar ruwan da ke ciki. Ya dan taka yayi gaba kadan ya leka ko zai hango wani, be ga kowa ba, ya dawo gurin da tulun yake without second thought ya dauki tulun da hannu daya ya juya hanyar da ya fito.

Duk abun da ake Butula na boye tana gani bata fito ba sai da ta hango ya dauke mata tulu, daga inda take boye ta biyo bayansa, tana daga masa hannu sai dai baya jinta domin be san da ita a bayansa ba, kuma a ka'idarsa idan yana tafiya baya waiwaye sai da dalili, gashi ita kuma bata da muryar da zata yi kira a jita, ba zata iya shan gabansa ba saboda ya mata nisa, hankalinta ya tafi gurin tulunta da kuma wanda ya dauke tulun hakan ya saka bata kula da hanya ba takawa kawai take tana gyara daurin karamin gyalen dake kugunta, tana jin wani abu ya soki kafarta amman bata kula ba sai bin bayan mutumen take har ya isa gurin katuwar motar dake fake, gefen hanyar mai cike da turbaya (Kasa)

Ta tsaya nesa da su bata karasa ba, a zatonta sace ta za su yi, musamman ganin motar mai bakin gilashi, ga kuma wani mutumen tsaye a jikin motar. Tana kallon lokacin da na jikin motar ya karbi tulun ya tara gaban motar ya zuba ruwan sannan ya dago ya wurgar da tulum, da wurgawar da kallon inda Batula take tsaye kusan a lokaci daya Ariz yayi haka.

"Kai Innalillahi, daman tulum mutane ne?"

Jawad ya dan tabe baki ya daga kafadunsa alamar be sani ba.

"Toh wacan fa?"

Ariz ya nunata, Jawad ya juya ya kalli gurin da Batula take tsaye tana hawaye.

"Tulunki ne?"

Ariz ya tambaya daga inda yake tsaye. Da kurmanci Batula ta yi masa alama da tulunta ne, yayi mata alama da ta zo sai ta lake kafada alamar ba zata zo ba, sai fada take da yarenta na kurmanci. Ariz ya nuna kunnensa ya nuna hannunsa ya girgiza alamar ita kurma ce sai ta daga mishi kai.

Ariz ya kalli Jawad

"Ka jangalo mana kurma, yanzu dai sai a biyata tulunta"

Jawad ya saka hannunsa aljihu ya ciro sabbin kudi ya kirga 1k guda biyar ya mika mata, a take Butula ta share hawayenta, har ta fara takawa sai kuma ta tsaya wata zuciyar na raya mata sace ta za su yi. Sai ya lake kafada daya alama ba zata zo ba. Jawad ya taka ya nufi inda take sai ta yi baya da sauri yana gaba tana baya har ya isa inda ta tsaya a dazun ya aje kudin a kasa ya daga karamin dutse ya dora sama saboda kar iska ta yi gaba da su.

Ya juyo ba tare da ya kalleta ba ya dawo gurin motar da Ariz ya rufe ya bude front seat ya shiga. Batula na ganin haka ya dawo da gudu ya dauke kudin tana dariya da hakoranta, domin bata iya da sauti, kukanta da dariya da magana dukansu babu wanda zai ce ya taba jin sautinsu balle kuma maganarta. Ta kirga kudin ta ga har 5k sai farinciki ya rufe ta, ta yi gobarar titi ita kan gaba ta kaita. Jawad ya sauke gilashin gefensa ya kwantar da kujerar ya kwanta yana kallon yadda take ta tsalle tana tafiya ta rawa kamar ba ta ji ciwo a kafa ba.

Ariz yaja motar suka fara tafiya da suka kawo daidai inda Batula take sai ta makale kudin a zanenta ta daga musu hannu biyu tana musu bye bye. Ariz ya tsaya da motar ya mata alama da ta zo, sai ta tako kusa da motarsu amman ba ta yarda daje daf ba. Ariz ya nunata ya tambayi sunanta da alamar kurmancinsa da be iya ba, ganin bata gane ba, ya saka shi nuna kansa yana motsa bakinsa a hankali.

"Ni Ariz, wannan Jawad"

Sai ya nuna ta. Ta nuna kanta alamar ita? Ariz ya daga mata kai. Sai ya matsa baya ta rubuta masa sunanta a cikin turbaya, (kasa)

"BATULA"

Jawad ya furta a ransa, Ariz kuma ya furta a fili, dukansu suna mamakin yadda ta iya rubuta, ya nuna kafafuwanta ya birkita hannu, alamar ina talkaminta.? Ta nuna kafarta da alamar tambaya, sai ya daga mata kai.

"Ni ba na yawo da talkami"

Ta rubuta masa a kasa. Ariz yayi mata alama da sun gode, ita kuma ta daga musu hannu tana ta bye bye, Jawad kallonta kawai yake kamin ya daga mata babban yatsansa 👍 yana ta kallon madubin gefen motar dake haskota, har sai da ya daina ganinta. Gurin da suka jefar da tulun ta nufa ta kwashe ta zuba wani cikin wani ta dauka cike da murna ta nufi gida, tana tafe tana tsalle da kafa daya irin tsallen nan mai kamar rawar dandali.

Tun da Batula ta kamo hanyar gida take murna da rawa har ta iso cikin garin, dake cike da gine ginen kasa da bukkokin zana. Babban gida ta shiga irin gidan nan dake nuna rufin asirin mutanen karkara, babban gida ne a suna haka kuma babban gida ne a yawa, kamar yadda yake babban gida a gurin jama'ar garin.

Gida ne dake dauke da mata hudu da yara ashirin da biyu, a karkashin inuwar mutum daya wato Malam Salisu Na Malam, wanda ya kasance mai garin garin rorau (kirkirarren gari ne) dake karkashin karamar hukumar mulkin Dange Shuni dake Sokoto Shehu.

Gida ne da aka yalwata ta shi da Iyali da kuma girma, aka yi bangaren mai garin, ga bangaren da baki suke sauko, akwai bangaren da yake aje dabobinsa, sai kuma bangaren matansa guda hudu da kowace take da daki daya daya yaransa maza kuma dakinsu dabam, matan ma dakinsa dabam. Altine ce matarsa ta farko da yaranta 7, sai Umma Hindu dake binta mai yara 5, da kuma yar riko daya. Salamatu ce ta uku da yaranta 6 cikinta na bakwai, ta karshen da hausawa ke cewa cikon gida wato ta hudu Larai wanda ta kasance karamarsu ita ce da yara 4 ras duk maza. Gida ne da babu yunwa, domin Malam Salisu Na Malam ya wadata iyalinsa da hatsi kama daga masara, dawo da gero, shimkafa kuma idan an yi baki daga birni a dama musu.

Kishi a tsakanin mata biyu ma farilla ne balle hudu, hakan ya saka gidan yake cike da habaice haibace da yan neman ni na fi kowa komai.

Kowace kokarin take ta fi sauran, gasar haihuwa kuma kai kace a gidansu ya yanke cibi. Malam Salisu mutum ne mai kokarin kwatanta adalci a tsakanin matansa, haka ma ga yaransa da aka masa sirki maza da mata, ba sosai makarantun zamani suke wadatuwa a karkara ba, amman yayi iya kokarinsa waje ganin kowa ya samu ilmin addinin da na zamani ba ga yaransa kadai ba har ga yarinyar da matarsa take riko wato Batula, wacce ta kasance bata magana tun tana kankanuwa har zuwa yanzu da take da shekaru goma sha 14 a duniya.

Batula yarinya ce mai matukar far'a mai son jama'a kuma mai farin jinin mutane daga maza har mata, ko kadan bata da damuwa da kowa, kowa nata ne kowa ta gani zata waye kamar ta san shi, karatun ya taimaka mata gurin iya rubuta abubuwan da ba zata iya furtawa ba, ya taimaka mata gurin hulda da mutane sosai. Batula ta girma da wata dabi'a ta kyamar tafiya da talkami, saboda rashin kulawa na uwar rikon tata tun tana karama, sai ya zama ta girma ba tare da sanin dadin yawo da talkami ba, komai tsananin zafin rana ko hadarin guri, haka Batula take shiga babu talkami a kafarta, saboda ta fi jindadi, idan kana son ganin bacin ranta ka cilasta mata saka talkami, mutane sun yi magana har sun gaji, tun ana siya mata talkamin har an gaji saboda bata sakawa, idan har ta saka talkami to mashinshinta ne ya diro garin, domin ya san yadda yake fushi da ita idan ya ga kafarta babu talkami.

Wani iko na Allah duk wani abun da za a fada tana ji, amman a furucin ne ba a yassare mata ba, babu wanda zai fadi cewar ya taba jin dariyar Batula, ko kukanta, balle kuma maganar da kowa ya san ba zata iya ba. A cikin gidansu akwai saninta da wandansu suka girme ta, akwai kuma kanenta da kanen kanenta, amman ta fi kowa shiga ran jama'ar garin saboda lalurar da take tare da ita.

Akan tausaya mata, akan mata uzuri, akan daga mata kafa ko a taimaka mata ko'ina, ban da cikin gidansu musamman ga uwar rikonta da take ganin kamar Batula da fi yaranta farinjini kuma ta zame mata lalura tun tana karama, ba dan da taimakom Malam da wasu daga danginta sun yi ruwa da tsaki akan Batula ta zauna gurinta ba ganin ita tana da rufin asiri ba kamar su ba, da bata shirya karbar yar kanwar tata ba Batula, a lokacin da uwa da uba suka tafi suka barta a tsumma. Ba abun mamaki ba ne ka ga karamar yarinya da aure ko baiko a karkara, amman kowa yana mamakin na Batula da aka yi mata baiko da danyun shekarunta saboda lalurar dake tare da ita.

Ko da yake mutane suna fadar Batula yarinyar ce mai hankali, da tarbiya, ga ta fara kyakkyawa mai far'a da son nishadi, rashin magana ne kawai nakasarta. Kusan duk wani aiki ko aikan Umma Hindu Batula ce take yi bata gajiya, tun mutane na magana har suka gaji suka daina. A duk fadin garin Rorau Batula bata da kawaye kamar Kande da Basira, kowa ma ya sani idan aka duba ko'ina ba aganta ba gidajensu ake tafiya nemanta har dandali da gona ko rafi tare suke tafiya, sai idan aikin ya mata rana ko kuma sun rigata gamawa take tafiya ita kadai.....

*** *** ***

Batula na shiga dakin Umma Hindu ta dauko littafinta ta rubuta abun da ya faru sannan ta yage takardar ta mikawa Umma Hindu tare da kudin da aka bata. Umma Batula ta mikawa yarta Mairo takardar yayinda ta shiga kirga kudin.

"Karanta min me aka rubuta"

"Umma... Na hadu... Da wani... Ya dauki... Tulunki ya zuba ruwa a mota sai ya fasa tulun amman ya bada kudi ya ce a siya wani"

Ta karanta mata da daidaya domin ba wani iya karatun ta yi da kyau ba.

"To ke kina me har ya fasa tulun mahaukaciya? Baki ga sanda ya dauka ba?"

Cewar Umma Hindu tana kallon Batula. Batula ta sake yin wani rubutun ta mika mata, Mairo ta karba ta karanta.

"Na zagaya ta cikin haki na yi fitsari na hango shi ya dauka, ni kuma na ji tsoro ban yi magana ba sai daga baya na bisu, sai suka biya kudin"

"Masu kudi ne halam Batula?"

Mairo ta tambaya, Batula ta daga kai da sauri alamar eh, tana musu alama da babbar mota da yarenta na kurmanci tana nuna kalar motar black.

"Kila masu zuwa hakon zinarin nan da aka ce za su zo yau, Malam yace yamma za su yi aikin kuma hanyarsu ta nan ce a dole za su bi, ke dai kin auna arziki sun biya kudi da sai kin ci ubanki yau a gidan nan, dauki wani tulun ki debo ruwa"

Batula ta yi murmushi ita kanta ta san da ba su biya ba, mai kwatarta a hannun Umma Hindu yau sai ya shirya. Sai da ta maida littafin ta aje sannan ta fita ta dauki wani tulun ta fice daga gidan, maya biyar ta yi da tulun sannan ta aje ta wanke kafafuwanta ta gyara daurin gyalen dake kugunta.

"Batula dauki fura gata nan ki kaiwa mai gari, yana can gindin ice a gona"

Kamar an dauke Batula an kawo wata haka yanayinta da fuskarta suka sauya, ta san bata ita tace ma Umma Hindu aa ba, domin shi kansa mai garin ya fi sha'awar a aika masa Batula ta kai masa sako ko abinci sama da yaransa, a cewarsa wai duk ta fisu hankali da kula.

Cikin rashin kuzari ta shiga dakin ta dauko kwanon ruwan dake cike da sabuwar fura ta dora a kai ta kama hanya kafa babu talkami fuska babu annuri sai turo baki take gaba kamar wata shagwababbiya.

_________________

Shim kun shirywa wannan tafiyar? Aje min ra'ayinku a karkashin page nan. 👌Kuma karku manta idan an karanta a tayani sharing.

Tsari da zubin irin wannan tafiyar kenan.

Shimfidace ta wani sabon labari daga marubuciyarku Khadeeja Candy fatar za ku karbe shi hannu biyu.

Ban zan cika baki ba, amman ina da yakinin zai muku dadi fiye da sauran, domin labarin ma na dabam ne, jaruman cikinsa da digon tawadar alkamin ta dabam ce.

Wannan labarin kirkirarren ne, idan ya ci karo da rayuwar wasu ko wata to arashi aka samu..