17
by @surayyahms
⏯️1️⃣7️⃣Abunda ke ɓoye
bayan tafiyarsu hjy mairo na shiga gidanta ko aje mayafinta batay ba matasan majiya suka diro kofar gidantan yuuuu wai sunzo neman taawure haka hajiya mairo tabirkice da ihu tahau sauke musu bambalastar ruwan bala'i ta tara musu taron jama'a tabi tajuya maganan kaf akansu tace sune suka sace mata yar rikonta taawure dan haka kawai ace musu su fito mata da yarta ko kuma hukuma ne zata rabasu, haka akayi ta hatsaniya tsakanin matasan majiya da hajiya mairo, can dai da sukaga ta fisu bori tanace musu akan su susuka sace taawure tabita laka musu harda sharrin da ko shaidan bai isa ta ciresu aciki ba ahaka ahaka abanza aka bar maganan suka koma garin majiya batare da sun cimma komi ba, ga dumbin zargin su na tunanin taawuren tazo nan duk ya gushe, basusan kuma ina zataje bayan nan din ba, yau dayakamata ace ranar farinciki da samun daukaka ne awajen juma sai ya zamo masa tamkar wata baqar rana dan bakaramin muguwar asarar dukiya taawure ta masa ba,
shikansa dakyar ya tsira da ransa, sanadiyar wasu fatake masu fitowar jeji da sassafe da sukaga wuta na tashi a rumbun abincinsa suka kawomai dauki yau kaf garin majiya sai da aka tashi da labarin abunda ya faru da juma masu tausayinsa suna yi mahassadansa masu masa dariya suna kai, yau tsabar baqin cikin ganin konewar dukiyarsan kurmus koda aka kwanceshi ya fito sarari suma kawai ya dingayi ana yayyafa masa ruwa...
yarasa meke masa dadi, gashi yafi kowa sanin cewa da akwai kakkarfan aikin tsarin jiki na usalin fulanin daji ajikin taawure da yayanta, yasan koda zai dau fansa ta hanyar musu sihiri ko sammon da zaisaka rayuwarsu ya lalace bazai iya ba saidaima abun yadawo kansa..
iya ka dabbobinsa ne kawai tabar masa su araye ahakanma waidan bataso ne tay ma abu me rai azaba da wuta yasa bata konasu da ransu ba.
ranar gabaki daya duniyar juya masa ta dingayi yanata suma ana dagashi yana komawa musmn ma da aka dawo gida akacemai ba aga inda taawuren ta nufa ba duk anje har tudu suma can tudun nemanta akeyi har ansaka hukuma ajeji suna nemanta. yau ya kasance ma juma ranar tsananon bakin ciki da jimami wanda bazai taɓa iya mancewa arayuwarsa ba.
bayan komi ya lafa wajajen karfe daya da rabi saura ibaad ya shigo garin kano kai tsaye baije gidansu ba yawuce Al-eeman private hospital inda babban kawar mamansa take aiki a matsayin babban nurse snn ya damka mata ayanahn a hannu shikuma ya wuce private club dinsu domin halartar practical da sukeyi agefe nasu na yayan masu shi, few minute drive just few minutes away from his main school of medicine na buk, ya gaji sosai ga uban stress din hanya a jikinsa amma baidamu ba hakanan ya shiga aji ya fada aiki. yau ana kkrin koya musu sabuwar darasi ne game da introductory practical anatomy amma gabaki daya sqi yanaji kamar yarasa nitsuwrsa dan harga Allah baisan ma tayadda zaiyi ya cika dumbin alkwarun daya dauka ma tawure nacewa zai kula mata da rayuwar yarta ba...aiki sukayi sosai don komi practical ake nuna musu, har zuwa 3:30pm snn yaje yay sallahn asr aka koma lab still saiga wani visiting doctor yazo musu daga kasar india shima, shi yafara fayyace musu basics introdction naduka duka courses din da zasuyi a main cadre nasu da medicine gabaki daya, kai daga ganin yadda yake koya musun ma zaka san babu me iya karawa dasu a ajinsu yanzu, bcos they are far far advance, sun kamo hanyar wuce mates dinsu na aji sosai, kusan dukkan wasu abubuwan da ba a musu tukuna a ainin lectures dinsu ba shi ake ta kkrin koya musu anan just like private lesson. can da magrib aka sakesu sukabar wajen kusan kowa yagama gajiya. hanklinsa dam kwance dake yariga yagaya ma amminsa dasu bappa zaidu awaya cewa ya dawo kanon already amma bazai wuce gida ynxu ba.
yana shiga motarsa asibitin inda yabar ayanahn ya wuce ya samu waje ya zauna yay shoru yanamai cigaba da zaman jiran jin me likitocin zasuce, anan yay sallan isha, ya fita yaje yaci abinci, kawar maman nasa har ta gama duty ta wuce gida, bashi da samun kan doc ba sai wajajen goma na dare, mace ce, nd she is a well know cardio doctor ana ce mata Haj sakeena shehu dakyar ake samun hanklinta sabida yawa da mutane suke mata. at arnd that time of 10pm na dare tay ushering ibaad cikin office inta ,yana zama suka gaisa a natse snn tafara mai cikakken bayani akan ciwon ayaanah
tacemai bincikensu ya nuna cewa yarinyar originally was born with a strange congenital heart weakness wanda baya nunawa kwata kwata sai inta shiga mummunan hali na tsorata, bacin rai me tsanani ,kakkarfan rauni, jimami me yawa, ko wani nau ikan intense fear ko emotional overwhemlness. daga zarar hakan ya sameta zuciyarta zai fara kokari wajen ganin yay coping da pain in amma akokarin hakanne yake kawo mata symptoms kala kala na raunin zuciya, kmr zafi da ciwon kirji,wahalar fitar numfashi da su panic attacks da zufa me dan banzan yawa har izuwa loss of counsiounes. hoto nan scan da suka dauka ta nunna masa snm takara da cewa Abu mafi muhimmanci ynxu shine a tabbatar mata da samun natsuwa. Kada a tada mata hankalinta. Kada a matsa mata tayi magana ko tana tuna wasu abubuwan da suka wuce mata abaya. snn Idan ta fara jinsu ko suka dawo mata kawai a zauna kusa da ita cikin shiru da bata kulawa cikin tausayawa,yarinyar yar karamace, so zata fi bukatar kulawa da kwantar da hankali fiye da duk wani maganin da zaa bayat yanxu..."jin yau shiru yasa ta kara kallomsa ahnkli tace 'are u her elder brother?babu yabo babu fallasa ya gyada kai, Dr tace okay, toh ga wannan. wano paper ta miƙamai ya karba tace" zaku iya komawa gida, there are the list of her drugs, snn zakuje nan pharmacynmu ku saya alluran sedatives amata su ynxu. idan jikinta bai sarara ba after 3 days adawo mana da ita. gyada kansa still yay cikin nitsuwa yace mata ya gode snn ya rike takardan ya fita dashi a hannu..
baije ya duba ayaanahn ba kai tsaye yajeshi pharmacy ya basu papern snn biya kudi akazo har dakin da ayaanah take kwance aka mata allurai har guda biyu...
hawaye ta dingayi sabida ta tsani allura har cikin kokon zuciyarta, but the more tana kallon fuskar ibaad a bakin kofa sai tanaji kamar ma tafi jin tsoronsa fiye da komi ynxu. jiri me dan banzan yawa takeji amma yadda ta tsaya kyam cikin shanye zafin alluran kamr wata soja yasaka nurse din data mata allurar tace masa
"yallabai zaku iya tafiya..
ibaad ya gyara zaman jakar laptop dinsa kallo daya yay ma aayanahn tay maza ta gyara zaman zaninta da dan kwalinta cikin saibin jiki ta saka takalmi, har saida yawuce gaba snn tafara takawa ahnkli tana bin bayansa yanayin fuskarsa da tazarar dake tsakanin su zai iya sakawa kai tsaye kace basusan junansu ba...
tafiya take kirjinta na tsananin bugawa, with each step sai taji kamar akan rolling coster ball take yawo, kanta nawani irin juyawa kmr tana sararin sama cikin gajimare, kafin kace wani abu tafara ganin mutane bibbiyu, hatta dakin ya dawo yana mata duhu duhu hanklinta gabaki daya na neman gushewa
suna isowa daf da bakin kofar asibitin batare da ta shirya ba jikinta ya sake tayanki jiki ta fadi
wani securityne yay sauri yazo kanta da tunanin "she is all alone dacan har zai dagata sai kuma ibaad ya juyo, suna hade ido yace ma securityn its okay sir, i am with her. security ya masa wani irin kallo, "yace amma shine ka kabarta haka but you are suppose to hold her
ko za'a ko koma ciki a kira muku nurse ne..ibaad yace masa "a'a Allura aka mata bai saketa ba but she will be fine
...suna cikin maganan ayaana ta fara bude idonta cikin layiii tafara fulatanci tana cewa zata kwanta, ita tagaji zata kwanta, bazata iya takawa ba.."
yarensa ne shima yanaji sarai amma yay kamar be gane me take fada ba, wani cak taji ya dagata tay firgit kmr ta tsorata suna hade ido sai kuma ta lafe akan kirjinsa tare da tantame masa riga, qamshin turarensa atake ya bugar da ita saii luuuu ta koma bacci daga nan bata sake sanin me yafaru da ita ba.
yana fitowa waje ya ajeta seat din gaban motar ya saka mata seat belt ganin tana zufa ya kunna musu A C a low snn yafara driving dinsu calmy yana tukin very calm bazaka taba iya fayyace abunda yake rayawa aransa ba.
frm time to time yakan juyo ya kalle fuskar ayanahn cos u cant ignore the fact that she is girl with a rare beauty, kyau me dauke ido da sanyi irin wanda bai taba gani ba..ita abar tausayi ne, she is calm, and peacefull. any man in his good will senses may want to love nd spoil her bcos of her calm aura nd fragility, saidai shi aransa ba wann kadai yakeji ba, da akwai wani awkward feeling da yakeji akansa kmr wasu dabiaun ta yana mugun bashi haushi, he just can't seem to forget dat agabanta aka taru ana masa sharrin zina duk dama ya tambayeta gaskiyar abainar jama'a amma tay shiru takasa budan baki ta wankesa. yasan he is not even supose to be angry bcos of that amma wnn shegen rauni, da mugun tsoron dayake kallo acikin ayanayinta abune wanda bazai taba iya tolerating ba, inhar dagaske ne zaicika alkawarin daya daukarma taawure kusan dolene mishi ya kasance atskaninsu akwai kakkarfan ginin tarbiya, gyaran hali, da kuma ladabtarwa.
wajajen karfe sha daya saura na dare suka iso GRA cikin gidan bappa zaidu, tsabar gajiya har ji yake kamar bazai isa dakinsa ya kwanta ba, yana kammala parking kuwa ya juyo ya kalleta yaga har yanzu tana kan baccin ta peacefully.
kallon scnds biyu yay mata kafin ya dauki jakarsa da kominsa ya rataya snn ya zago ta inda take ya buɗe motar ahlkli yadda ya jawota jikinsa da karfi ya ratayata akafadansa nan da nan kuntacen dan kwalinta ya sulale kasa abunsa. haka wnn doguwar curly nd wavy hair dinta dat is so soft and shiny ya barbazu masa a fuska da kafada, ahnkli ya dinga takawa da ita har suka kai bed room dinsa snn yay saurin ajiyeta akan gadonsa tare da sauke ajiyan zuciya mai nauyi
yana tsaye amma idonsa gabaki daya nakanta dan bai taɓa ganin natural buzu hair irin nata ba duk dama dukan kannen sa suna da kyau da dogon suma.
na ayanah nada wani irin cika ga yawa ga uban yauqi da tsayi , tagaban is so wavy nd damp, kasan lenght din kuma is curly nd very dark. yadda ya ajeta a ringine haka suman ya zubo yarrr ya rufe mata fuskarta kirif
it was hard for him to stop staring sai da yay minti uku atsaye cikin tunanin me zaiyi kafin ya dauke idonsa ya saukar da jakansa daga kafadarsa ya zauna akan chair ya ciro duka kayan ciki da suke da datti, snn yacire takalminsa da komi na jakan yay empting ya aje komi awajen zamnsa neatly
dan coridor dake tsakanin bathrom ya shiga da kayan ya jefasu cikin engine wanki, ya wanke 2 blood stained shirt din har da kayan dake jikinsan duka machiine din ya matse su, yay masa drying sama sama snn yay pressing dinsu so neatly kafin ya kaisu hanger ya rataye su.
blue shower trobe mai kauri ya nannade ajikinsa bayan ya kimtsa dakin kadan ya shiga wanka, he spends like 20 minutes just washing his hair and face kadai with this luxurious swiss brand na la praire, brand inda is excellent for lifting, firming nd anti aging saikaga kullum fatarka rass da karfinsa baiya yamushewa kamar dai bazaka tsufa ba.
BHA made face scrub da enzyme exfoliant dinsu yay using kafin nan ya shiga shower, wato idan kaga tulin kayan gyaran jikinsa ryt frm hydrants, retinols, SpF, sheet mask, da cleansers, shaves set ,dss. zakasan kowata ƴa macen ma bata isa tanuna ma gayen nan son gyaran jikinsa ba. he is a very neat guy dat priotise his looks nd skin health.
bayan kamar minti talatin ya fito a warm shower sulbabben fatar jikinshi yana qamshin sabulai da shampoos din la praire din cos all his men luxury items are of the same brand baya hada tarukuce, brush yay agaban sink yay rinsing bakinsa da ruwan kanunfari snn yay kamilallen alwala ya fito da wani sabon bathrobe din ajikinsa.
kallo daya yay ma kan gadonsan yaga kmr yadda ya aje ayaanahn haka ya dawo yasameta batako motsa ba banda sautin numfashinta dake fita ahankli ahankl. cikin kyabe baki ya dauke kansa walking gently kamr wanda baison ya tasheta yaje gaban mirrorn ya tsaya, after dabbing his skin with a clean white towel yafara jawo set na skin care items insa musmn na amfanin dare, kusan yadda komi na wanka, wanke kai da gyaran jikinsa ya kasance brand daya hakama komi na shafawa a jikinsa ya zama brand daya, he use only "la mer" for his body, hair nd face. a very luxurious american brand na mutanen da suke son zallan jikinsu yana glowing bana haske ko bleaching ba. with good skin barrier repair, rich hydration and luxury feel. anan ganinka ansan jiki duk madara duk A.C..
abu uku kawai ya shafa dake yasan dare ne is merely time for his serum, vitamin nd retinol kafin nan ya mulke jikinsa da soft soothing moisturizers, ya shafa turare ya gyara kansa tsaf ya jawo doguwar wando dark blue colour marar nauyi na CK da rigarsa me kamr t shirt yasa. yay lisafin duniyan nan a brain insa amma yarasa ta ina zai aje ayaana ta kwanta, gashi baison takuri shiyasa bai iya kwana akan kujera ba.
tsaftaccen cotton comfortersa ya jawo ya shimfida akan soft couch dinsa ya dawo zai dauketa wani cakk ta firgita acikin baccin ta kara cakuikuye masa riga kmr wacce za'a saceta, gently yariko hannun nata anashi, sann ajeta akan couch din tukun ya samu ya kwace rigarsa ahannunta ya dauko katon rigar sanyinsa da yake sawa in sunje holiday a united state me dauke da fur ya lallubeta da shi kirif.
kara gudun Ac yay jin kmr duka gabobin jikinsa na masa ciwo yasha kwayar magnessium glycinate for deep relaxation nd quality sleep, after like 5 minutes ya iddar da adduar bacci saiya kashe wutansa gabaki daya ya kwanta hankli akwance baijima ba wani bacci me nauyi ya daukesa...
wajajen 2pm nayi cikin nisan bacci ayaanah tay firo da rigar sanyin daya rufeta dashi da alama allurar sedatives da aka mata ya fara raguwa, wani dan uban zafi da zufa tasoma ji ajikinta. tunda tay firo da bargon ta cigaba da sheƙa bacci me nisa ba ita da farkawa ba sai can ana daf za'a kira sallan farko da sanyin asuba ya hadu dana ac ya bugota, kallon dakin ta dingayi acikin duhu tana jin kanta wani iri kamar ba ta cikin duniyar, tsoro me matsanancin yawa sai ya riƙe mata kirji dan bata san yaushe sukazo nan ba, itade tasan sunbar asibiti gabaki daya sai taji ta rude sosai, fitsarin daya tasheta a baccin takejinsa kamar zai fasa mata mararta ya tsulalo waje duk sai ta rasa me zatayi.
lkcin is just few mins ya rage ma ibaad ya farka daga bacci amma dake yariga yasha wnn magani yasaka yau ko motsi bataga yanayi ba.
dake yaran taawure akwai jarumta inuwar sa kawai tagani acikin duhun tagane cewa shine yake kwance akan gadon, da kyar da karfin hali irin na mutumin kauye ta tashi ta dada lekensa kafin nan hanklinta yay sanyi ta miƙe tsaye jikin ta na rawa rawa dan kwata kwata batasan ina zata dosa acikin duhun ba ga fitsari ya mugun cika mata mara sosai
lalume ta dingay har saida ta isa gaban inuwarsan ta durkusa, hannunta dake rawa rawa ta miƙa kansa amma ta kasa taɓashi, tay hakan yakai sau biyar mugun tsoron sa datakeji ya hanata iya taba masa jiki.
nishi take fitarwa ahnkli tana dan mammatse kafafunta
jin fitsarin yafara jika mata pants,cikin dauriya ta dan taɓa jikin gadon da karamin muryan ta mai tsananin sanyi tace" umm umm dan Allah me mee..mme...mai..mota zan
..zanyi fitsari..ina jin fitsari sosai...maganan nata sai ya fara fitowa tare da maqudan hawaye masu zafi itakanta batasan mesa take yawan jin matsanancin kuka intaga ibaad ba.
a mugun shagwabe cikin fashewa da kukan tace ..mai mota..nifa zanyi ajikina dan Allah ka tashi ka nuna min wajen fitsari ...mai motaaaaa....
can cikin duniyar baccinsa yaji kmr ana jajjan masa bedsheet
yay tsam sai yafara ji harda sautin sheshhekar kuka da sauri ya bude idonsa ganin ayaanah agabansa ta durkusa tanata mammatse kafa tabi tazuba masa ido tana rabza uban kuka sosai..
gam ta rike bedsheet dinsa tana jajjansa tana cewa wayyo Allah na zanyi ajikina faaa
a firgit ya kunna bedside lamp haske yadan karede dakin fusknsa mugun daure yace "ke kuma meye haka..meye zakiy ajikin ki..uban wa ya bugeki kike kuka da tsakar daren nan..are u a child?
maƙe kafadunta tay a shagwabe tana hawaye tace
"nifa fitsari nakeji..
cikin galla mata harara yace "bakisan hanyar bayi bane...sai kuma ya tuna batasanin ba cikin dafe kansa yace shittt.. "tashi..
dakyar ta miƙe tsayen tana rawa rawa tana mammatse kafarta..
kai tsaye ya kunna asalin switch na wutan dakin wajen yay haske sosai kamr rana ya kalleta snn ya kalle kofar bathrum dinsa yace kizo kishiga kiyi fitsarin anan
da wani iri sauri ta gyada mai kai zata daga kafarta kenan sai zurrrrr fitsarin ya sace ya fara zuba mata ajiki..
ahnkli ta runtse ido tay tsamm jin fitsarin na bibiyar kafarta taki sam ta kara bude ido ga kalle ibaad daya zaro manyan idonsa waje yanamai shirin daka mata wani irin hatsalallen tsawa.
#SURAYYAHMS/***
ENJOY THE WEEKDNS
SAI MONDAY...IN SHA ALLAH!!