Page 1
by @legendspen
*SAKATA*❤️⚓️
🌻Stroy and written🌻
By
Sayyid writer (Legend)✍️
*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*
*(FUWA)🖋️📚*
🌻🌻🌻
_"Ƙungiyar Marubuta masu tasawa, Rubutunmu shi ne tafiyar da ke wuce lokaci, mu ne masu ɗaukar harshen gobe a yau. Marubuci ba ya zana kalma kawai, sai dai ya zana mafarki a zuciya, ya maida shi haske ga al'umma. Wannan shi ne alwashinmu a matsayin mu na matasan marubuta. Taken mu shine ɗaga darajar Marubuta masu tasawa."_
🌻🌻🌻
🌻Sadaukarwa🌻
Na sadaukar da wannan littafi ga ’yan’uwa marubuta na cikin ƙungiyarmu mai albarka — *Future Writers Association*.
Ku ne ginshiƙin kwarin gwiwa da hasken tafiyata a duniyar rubutu.
Wanan Littafin yafi ƙarfin Shafi ko alƙalami; wani ɗan ɓangare ne daga zukatanmu da ke ɗauke da mafarki, ƙalubale da burin da muke fatan cimmawa tare.
Allah ya ka ɗorar mana da haɗin kai, ka bunƙasa ƙungiyarmu, ka ba mu ikon sauya al’umma ta hanyar kalmomi.
*–Fatan alheri da ƙauna.*
*[Sayyid writer Legend]*
بسم الله الرحمن الرحي
SHAFI NA FARKO
(P. 01)
Durƙushe nake, gaban kawu Mudi yana zubamun bulalal da nake jinta kamar saukar ruwan dalma a jikina. Yata ƙarƙare sai zubumun bulalal yake iya ƙarfinsa, idanuwa na suna a murje kamar baza su zubar da hawaye ba. A cikin raina kuma faɗi nake.
“Ya ubangiji ka gama Mus’ab da masifar duniya, da ta lahira. Ya ubangiji kasa yayi saɓani da Alkhairi, yayi ido huɗu da tsautsayi , da asara.”
Wata bulala da ta shigeni ce, tasa ƙwalla fitowa daga idona ba tare da na shirya ba. Da sauri nayi ƙasa dakaina, ina goge ta da hijabi na. Mai na yiwa Mus’ab a duniyar nan ya tsane ni har haka?, a kullum burinshi yaga ana jibgata kamar sabuwar jaka, ko nace tsohuwa tunda na saba da dukan.
Tabbas nasan, ina da taurin kai, da kafiya, haka naci, amma kwata-kwata bani da rashin kunya. To yanzu ma ko ina da rashin kunyar, zan tsaya a waje na fara yiwa mutane rashin kunya ba tare da sunyi mun komai ba. Mahaukaciya nake ko me?, su kuma iyayen tarbiya, gidan da yafi na kowa tarbiya. Daga ance musu gani can waje, ina yiwa mutane rashin kunya. Shine zai sani gaba da duka.
“Tashi ki bani waje.” Muryar kawu mudi ta shiga kunnuwa na, tashi nayi na nufi cikin ɗakin mu. Nasan Mamana ba zata ce mun ko sannu ba, hakan yasa na kwanta kan doguwar kujera, ina kuka na a hankali, zuciya ta cike da ƙarin tsanar Mus’ab.
Ƴan mintina kad’an, Sadiya da Ummi suka shigo ɗakin namu, lokacin Mamana na cikin d’aki.
“Gaskiyya Yaya Mus’ab baya kyautawa, kullum shi burinshi yaga an dake ki, ko da yaga kina yin rashin kunyar ai shi mai yi miki faɗa ne.” Wani haushin Ummi ya ƙara kamani, ita yayanta bazaiyi ƙarya ba kenan, sai nice nake ƙarya tunda gashi sun yarda nayi rashin kunyar. Ni daga ganin mutane, suka tambayeni gidan Alhaji Idi me mai. Na nuna musu gidan, d’aya cikin su yace. “Mungode ‘yan mata.” Ni kuma nayi dariya shikenan kawai sabida Mus’ab ya tsaneni, yasa aka jibgeni kamar ba daren jiya yasa Yaya Iliyasu ya mareni ba.
Sadiya ce, ta bawa Ummi amsa. “Nikam gaskiyya abinda Yaya Mus’ab yake yayi yawa, shi fa bazai hanamu abu ba, sanan bazai sa a hana mu ba. Ita kad’ai yake sawa a daka, itama kuma ba sabida soyayya ba, sai dan ‘yar tsamar dake tsakanin su. Duk gidan nan Yaya Mus’ab ne kawai ke nuna ware, yana nuna ku kaɗai ne ƙannansa, kuma sauran yayin mu ba haka suke ba.”
“Sadiya gidan ku da wanan maganar, kar nasake ji kinyi ta. Gaba ɗaya gidannan babu wani mai ware, domin dukkan ku jini ɗaya ne, Hajja itace asalin ku. Kuma shi Mus’ab ai yanayin sa ne a haka, bai da son mutane kwata-kwata.” Ummanah dake cikin ɗaki ta faɗa. Nikam takaici ya isheni, na yadda Ummanah bata taɓa jin haushin Mus’ab, juya musu baya nayi na kwanta. Tun ina jin maganarsu sama-sama har bacci ya d’auke ni, zuciyata cike da tsanar Mus’ab.
Ƙarfe 1:45 dai-dai natashi, domin nasan da zuwa islamiya hakan yasa natashi a lokacin. Banɗaki na shiga na watsa ruwa, tare da ɗaura alwala na fito na tada sallar azhar. Ina idarwa na shiga Kitchen na lodo abinci, dan gaskiyya babu laifi Allah ya horemun ci, kamar yadda Mus’ab ke dizgani cikin mutane. Yake cemun (Gara uwar ci). To kam gaskiyya ina da cin abinci, sai dai kuma idan naci yanzu fa zai iya zama naci har na dare, dan bani da yawan cin abinci akai-akai, lokacin farko dai xanci har sai yabawa mutane mamaki.
Ina gama ci na zura hijabi na, nayi makaranta, a tsarin gidan mu (Gidan Galadima) duk lokacin tafiya makaranta sai an shiga ɗakin Hajja, an gaida ta, kama da makarantar safe, rana, da kuma ta dare, sabida ɓacin rai da hausin ɗan gaban goshinta, wanda nafi tsana sama sa kowa a duniya yasa nakaɗa kai na tafi banje na gaida ta ba. Ko a islamiyyar ma haka na zauna, kamar wacce aka yiwa mutuwa. Tsana da haushin Mus’ab na lugude a zuciyata. Ko da na dawo ma banje ɗakin Hajja ba, ɓangarenmu na nufa nayi kwanciyata.
A ɓangaren Hajiya Hajja kam, tana ganin kowa na shigowa gaisuwar tafiya amma babu ni, babu alamu na. Hakan ya matuƙar damunta, tana nan zaune ‘yan islamiyya suka fara dawowa. Ganin sun ƙare babu ni yasa tace da Iki.
“Ikirama, kira mini Salame.” Tashi Iki tayi ta nufo ɓangarenmu, ina kwance kan doguwar kujera tashigo ɗakinmu. “Salma, kizo inji Hajja.”
“Kice mata banzo ba….” ban ƙarashe ba, naji an make mini baki tare da faɗin.
“Zanci ubanki Wallahi, Hajja kike cewa ace baza kizo ba. Sai kin ƙara tabbatar da cewa baki da kunya ko.”
cuṅo baki nayi gaba, tare da sakkowa daga kan kujera, banko ɗauki mayafi ba na fice. Dabda ɓangaren Hajja, na hango Mus’ab yana tafiya a hankali, kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki. Idanunshi sunyi jazur, kamar gauta. A fili nace. “Allah yasa wanan ciwon kan ne ajalinka.”
A bakin ƙofar ɗakin Hajja na tsaya, tare da cewa. “Gani.”
“Naganki tijararra, naganki.” Juyawa nayi zan koma ɓangaren mu, ba tare da na ce ko ƙala ba, tunda ni yau bakina jinshi nake kamar an ɗora masa kwaɗo, babu abinda nake ji sai tsanar Mus'ab, Hajja ta ƙara cewa. “Yanzu salame, tafiya za kiyi.”
“Toh Hajja mene zance miki, bayan wanan kafirin la’ananne jikin naki, yasa ‘ya’yanki suna dukana, sun mai dani kamar wata jaka, kowacce a ka siyo.”
“Yanzu Salame,Mus’abun kike kafurtawa, har da la’ana. To fice ki bani waje.”
“Daman bani na kowa kaina ba, kice kika nemeni.” na faɗa tare da fice, a hanya na ƙara cin karo dashi, har yanzu bai kai ga shigowa ba. Dogon tsaki naja tare da cewa. “Duk wanda ya ɗauke zalunci a matsayin sana’a, rayuwarshi zata ƙare a jinya.” nikaina nasan da’a ce ba'a wanan halin Mus’ab yake ciki ba, da kafin na ƙarashe wanan maganar na kwashe haƙora na a hannu. Ci gaba yayi da tafiyarsa, nima nayi ɓangarenmu, a raina ina nanata addu’a ta ‘yar kullum. “Allah yagama Mus’ab da masifar duniya.”
*Asalinmu*
Dafarko dai sunana: Salamatu Yunusa Galadima. Kakan mu shine Galadiman, bawai Galadima na fadar sarki ba, a’ah sunane kawai yace. Mahaifina Yunusa shine ɗa na Uku wajen Galadima, Yakubu shine babba, wanda muke kira da Abban ciki. Sai kuma Aisha wacce muke kira da Mami, sai Mahaifina Yunusa wanda kowa ke kiranshi da Abba, sai kuma Halima wacce ake kira da Ummah, sai Abbas da ake kira da Alhaji ƙarami, daga shi sai Ilyasu da ake kira da yaya Ilyasu, shi kam shine baya son ace masa Kawu, shiyasa ake ce masa, Yaya ilyasu, sai kuma autan su Kawu Madu. A taƙaice da Galadima kakanmu yana da ‘ya’ya bakwai, maza biyar mata uku. Kuma duka wa’yan nan ‘ya’yan sun fito daga matarsa guda ɗaya, (Hajiya Hajja).
Kakanmu Galadima, tsohon mai kuɗi ne. Domin ko gidansa wanda muke ciki yanzu, yana da girman da kowanne part zau dauke mata hudu. Kafin rasuwarsa shiya bawa kowa ɓangaren da zai zauna, domin bayason yaga yaranshi su raba giadaje. Yace yana da burin ganin mun tashi a zuri’a ɗaya. Abban ciki ne ya fara aure, matarshi yar kano ce mai suna Jamila. Muna ce mata Maman ciki, idan mutunci yana yawa to ya yiwa Mamam ciki yawa, tana son mu, tana kaunar mu. Duk abu indai Maman ciki ce bata taba ware mu da yaranta, sanan mijinta shine babba. Kuma ta dau girman, domin har su Ummanah Yaya suke cemata, tana da yara guda biyar. Mai sunan Hajja ce babba, wacce yanzu take aure a Abuja, da yaranta guda biyu, yanzu gaba daya gida ance da ita, Yayar Abuja. Sai kuma Yaya Amira wacce ke aure a Zaria, ɗanta guda daya ne. Shekarar da ta ƙare ne, a ka aurar dasu, su hudu a cikin gidan. Daga ita Sai Mus’ab, shine babba a maza a ɓangarensu, sai kuma mai binsa Mai sunan kakanmu. Daga shi Sai Ummi dake auta a bangarensu. Sai kuma ‘ya’yan Mami guda shida, su kam ba’a gidan Galadima suke ba, kuma basa amfani da sunan Galadima kamar yadda mukeyi. A tsarin wanan gidan, yadda mahaifanmu ke amfani da Galadima haka muma mukeyi, kwata-kwata bama amfani da sunan iyayen mu, yadda mahaifina ke amfanu da Yunusa Galadima, haka nake amfani da Salma Galadima. Kuma kowa na cikin gidan haka yake amfani dashi.
Legends pen.
(*** / ***).