Page 2
by @legendspen
*SAKATA*❤️⚓️
🌻Stroy and written🌻
By
Sayyid writer (Legend)✍️
*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*
*(FUWA)🖋️📚*
🌻🌻🌻
_"Ƙungiyar Marubuta masu tasawa, Rubutunmu shi ne tafiyar da ke wuce lokaci, mu ne masu ɗaukar harshen gobe a yau. Marubuci ba ya zana kalma kawai, sai dai ya zana mafarki a zuciya, ya maida shi haske ga al'umma. Wannan shi ne alwashinmu a matsayin mu na matasan marubuta. Taken mu shine ɗaga darajar Marubuta masu tasawa."_
🌻🌻🌻
بسم الله الرحمن الرحي
SHAFI NA BIYU
(P.02).
Mu hudu ne wajen Mahafinmu, Yaya Asma’u ce babba. Wacce tana cikin ‘yan matan da aka aurar shekara da ta kare. Sai kuma Muhammadu dake bin ta, sai ni sai Mai sunan Hajja. Wacce itace autar mu muna ce mata Iki.
Itama Ummah bata gidan Galadima, amma kuma yaranta maza uku, duka a gidan Galadima suke, sai matan ne a wajenta, wa’yanda sune ƙanana dan muma nun girmesu. Aliyu, shu’aibu sai Kuma mai sunan Galadima. Sai kuma ɓangaren Alhaji ƙarami, shi ‘ya’ya uku gareshi, Yaya Khadija ce babba. Itama tana cikin wa’yan da aka aurar shekarar da ta ƙare, daman uku ne a cikin gidan Galadima. Sai kuma ɗaya daga gidan Mama. Sadiya ce ke bin Yaya Khadija, Sai kuma ƙanwarta guda daya. A cikin jikoki 27 da Allah yabawa Hajja, sai Allah ya jarabce ta da son guda daya, fiye da sauran jikokin. Har ake tunanin ta mafi son shi a kan wasu yaran na ta.
Mus’ab Galadima. Tun haihuwarsa take nuna masa muguwar ƙauna, fiye da tsammani. Dan ko sanda yana jariri yayi kuka, nan Hajja zata fara balbalin bala’i, Ƙarshe dai Maman ciki, ba tajira lokacin yaye yazo ba ta miƙawa Hajja abunta. A cinyar Hajja ya taso, ɗangata, ɗan lele, rigimamme, mara kuma jin magana, sabida gata da ya samu wajen Hajja, kowa bai kyale ba a lokacin ƙuruciyarsa, har da kawunansa wa’yanda basuyi aure ba lokacin.
Haka rayuwa tai ta tafiya, har a kazo lokacin da muka diro duniya, mu uku ne a set ɗinmu. Sadiya ce babba, sai kuma Walidah, ni ce ƙarama cikinsu. Tun tasowa ta, nake mugun son Kakata Hajja. Ina ƙaunar Hajja sosai da sosai, itama ganin haka yasa take ƙaunata. Sa dai Mus’ab ba ya ƙaunata ko kaɗan.
Haka rayuwa tai ta tafiya, har a kazo lokacin da muka diro duniya, mu uku ne a set ɗinmu. Sadiya ce babba, sai kuma Walidah, ni ce ƙarama cikinsu. Tun tasowa ta, nake mugun son Kakata Hajja. Ina ƙaunar Hajja sosai da sosai, itama ganin haka yasa take ƙaunata. Sa dai Mus’ab ba ya ƙaunata ko kaɗan.
Da zarar nazo wajen Hajja, zai fara dukana, ni kuma Allah yasa mun taurin kai, kafiya, naci, da kuma rashin haƙuri. Shekaru d’ai-d’ai har goma ne tsakanin ni dashi, amma a wanan lokacin da nake da shekara uku, shi kuma yake da goma. Da zarar ya dake ni, ko ya buge ni, ko ya harare ni, kai ko kallon banza yayimun sai fa na rama. Wanan ramawar da nake itace abun da ta kara haifarwa da Mus’ab tsanata, ni kuma wanan tsanar tashi itace ta raini tawa. Mus’ab bashi da kunya, ko yayunsa maza ma yi musu yake. Wanan rashin haƙuri nawa, yawan faɗa da ƙarata da Mus’ab ke kaiwa Hajja. Shi yaja ta fara yi mun faɗa, har tana hanani zama a ɓangarenta, da nazo zata fara cewa.”Ni Salame, wanan halin rashin haƙuri naki ya fara isata na. Ke kenan bazaki zo ba, sai kin addabarmun yaro?.”
Cikin kuka nake cewa. “Hajja shine yake duka na.”
“Ke kuma da baki da kunya, shine sai ki rama ko?.” haka kullum muke fama da Hajja, har naji zuwa ɓangaren nata ya fara fita a kaina. Abinda na kwana, na tashi da sanin shi shine. Mus’ab yana masifar son ganin ya kai ƙarata, dan tu ina ‘yar mitsitsiya idan ya dakeni, nayi masa Allah ya isa, sai yazo ya ce. “Ya ganni a waje, ina yiwa wani Allah ya isa.” haka za’asani gaba, ai ta jibga kamar sabuwar jaka, nai ta kuka kamar marainiya.
Irin wa’yannan abubuwan, sune suka taru suka haifar da muguwar ƙiyayyar Mus’ab a zuciyata. Ƙiyayya irin mai girman gaske, sanan da yanda yake yiwa kowa rashin kunya, yasa na ƙara jin haushin sa. Sai da Ummanah ma Allah ya jarabce ta da ƙaunar Mus’ab. Ƙauna ta gaske, bata taɓa ganin laifinsa duk abunda zaiyi, ko da kuwa ya dakeni, ko yayi mun sharri an dake ni. Haka zan zauna nai ta kuka, amma ko a jikinta.
Kamar yanda na faɗa. “Gidan Galadima gidane na haɗin kai, ƙaunar juna.” gida ne da babu wani ware, kowa yana son kowa,sanan kowa yana da set na, sakwanin haihuwa. A bangaren rayuwa, gida ne na masu rufan asiri, ba zaka ce mana masu arziƙi ba. Amma duk wani ci, sha, suttura, wajen zama, wajen karatu, munfi ƙarfinsu. Muna rayuwa a nutse cike da tarbiya, kowa na ƙaunar kowa.
A ɓangaren kyau kam. Duk cikin gidan Galadima babu wanda yakai yayata Asma’u kyau. Duk da ance tana kama dasu Yaya Khadija, amma kowa yasan tafi kowa kyau A cikin wanan gidan. To ni da ita muna ɗiban kammani, ko da baza’ace nike biye mata a kyau ba. Bazan huce ta uku ba a cikin gidan Galadima. A maza kam a bayyane take, Mus’ab Galadima yafi kowa kyau, dan har wani shigen kama yake da wanan jarumin na indiya. (Aditya Roy Kapur) kawai shi Mus’ab yafi Aditiya faffadar fuska, kasancewar ta Aditiya ‘yar tsurut ce.
Amma ni bana ganin wanan, sabida girmam tsanar da nayi mishi. Nikam zance ban taɓa jin yakira sunana ko sau daya ba. Yoo mutumin ma da harkar arziƙi ba ta haɗa ku ba, ta ina zai kira sunanki?. A haka har mu kazo matakin gama firamare, zuwa sakandire. Mukam a gidan mu ba’a cewa mace ba zatayi karatu ba. Sabida iyeyenmu nan duk da iliminsu, sai dai kuma ba’a taɓa samun wacce taje gaba sakandire ba, domin da zarar sunje matakin siniya samari zasu fara ɓulɓulowa kamar ruwa. Hajja kam cewa take. “Tun da samarin nan sunzo, to aurar da yaran nan, sabida lokaci daya mazaje ki zu war wa mace, da zarar sun kare to tsiyayewa zasuyi kamar hawaye.”
Hakan ce ta faru kuwa, da zarar ‘yan matan gidan mu sunkai senior, zakiji anyi musu baiko. Suna kammalawa za’ayi bikinsu, wasu mazajen na barin su su ci gaba, wasu kuma basa ci gaba. Auren da’akayi shekarar da ta gabata, shine aure na uku da akayi, sabida idan aka tashi sai a hade mutum biyar, ko uku, maza da mata.
A yanzu mukam mun shiga Ss1. Mu uku abun mu, sanan an saka ran aurar damu tare dasu Mus’ab, da wata buduruwarsa Junaidiya. Yarinyar kamar tsinken sigari haka take, ni ina mamakin yadda Mus’ab yake son yarinyar nan, duk kudinshi, duk gayunshi, duk ajinshi. Sai kuma wani lokacin nace, menene nawa?.
A zuwa yanzu, tsanar Mus’ab ta danne ƙaunar da na kewa Hajja. Dan ko ɓangarenta banni xuwa, indai Mus’ab na garin. A kwanakin baya nai ta biyewa Mus’ab, ina zaginsa da masa rashin kunya, shi kam sai ya dakeni sosai, sanan yasa kawunnai na, ko yayumun su zaneni. Bansan mai yasa kaf ahalin Galadima, ake yarda da maganar Mus’ab ba, ni kuma ake kin yarda tawa. Ko dan shi yanayin magana cike da nutsuwa, niko da hayaniya nake magana. Sanan ina ƙaryatashi a gabansu. Haka za’aita jibgata kamar jaka.
Akwai wataran da nayi niyar daukan fansa a kan Mus’ab, Naje har ɓangarensu lokacin Maman ciki na kitchen. Da sallama nashiga Kitchen tare da faɗin. “Maman ciki, aiki akeyi.”
“Eyh, diyar ciki.” dariya nayi, sabida sunan da take kirana dashi kenan. “Ummi bata dawo ba kenan?.”
“Ke wai lafiyanki, kike mun tambayoyi haka.” Murmushi nayi sanan nace.”Babu komai, sai anjima.”
“Dawo mana, ɗiyar ciki.” Naji ta fada murya a sanyaye, alamun taji babu dadi. Haka kawai naji zuciyata ta karye, nafasa yin abinda ya kawo ni.
Abinda ya faru kuma, jiya da daddare har yaja Yaya ilyasu ya mareni. Mun dawo daga makarantar magariba, sai wani dan ajinmu Walid ya tareni a lokon baya. Yana tambayata a kan buduruwarsa, wacce take ƙawata. Muna cikin magana, Mus’ab yazo wucewa, da sauri Walid yace. “Salma ga yayanki.” kallon Mus’ab nayi nace. “Naganshi, yayi kyau kamar rago.” gyaɗa kai yayi yahuce, kasancewar lokon da mutane. Shi kam bazaiyi abinda xai zubda mai da mutunci gaban mutane ba.
Ina shigowa harabar gida, naganshi yafito daga bangaren Hajja. Da sauri na nufin ɓangaren nata, amma yarikemun hannu, juyowa nayi zan mai masifar da nasaba. Naji ya tsinkeni da mari.
"Allah ya isa, Allah yagamaka da masifar duniya.” addu’ata ‘yar kullum gareshi, wacce shi kan shi ya haddace ta. “Zaki ci gidanku.” ya fada tare da jana ciki, ihu na fara kur mawa, ko Allah zaisa maman ciki tajiyo ni, amma Allah bai nufita ba. Kai tsaye inda Yaya Ilyasu yake yakaini.
“Yayana, nagaji da abinda yarinyar nan keyi. Har ta kai ga abokaina sun fara mun magana a kan rashin kunyar da takeyiwa mutane a waje.”
Da sauri na ɗago, tare da faɗin.”Wallahi karya yake, Mus’ab kai azzaulumi ne.” Yaya iliyasu ne ya tare ni da cewa.
Legends pen.
(***/ ***).