GUDUN AURE

8

by @bintaumarabbale

Na dube shi cikin tsanaki na ce." Bacci kuma karfe tara fa yanzu mun yini lafiya ya iyali." Ya gyara tsayuwa Yana amsawa ya dora da cewa ." To ai ban sani ba ko kina da saurin bacci." Shiru na yi ban ce komai ba. Sai ya cigaba da cewa." Malama Amina na ji dadin ganinki a yadda nake hasashe. Sule ya jima yana ba ni labarinki. Na farko ha'kurinki da tarbiyarki, wannan ya kara kwad'aita mini jin sha'awar auranki a raina, ina fatan zuciyarki ta aminta da ni, domin ni ba da wasa na shigo ba." Ba tare da na dube shi ba na ce." Na gode sosai da yabo da fatan alheri, amma don Allah ka yi hakuri da abinda zan fada maka, wallahi ba zan iya aure yanzu ba sai nan da wasu shekaru tukkuna, idan ma Allah Ya 'kaddara ba zan sake wani auran ba hakan daidai ne a wurinsa. amma dai yanzu babu shi a lissafina ." Ya gyara tsayuwarsa a karo na biyu ya fuskance ni sosai Ya ce." Wace hujja ce dake da za ki furta wannan maganar. Amina guda nawa ki ke da za ki jingine maganar aure, ki ce ba za ki yi ba sai nan da wasu shekaru. lokacin kin tsufa kenan, babu namijin da zai yi marmarinki, ai aure rahama ne kuma ni'ima ne ba don komai ba sai don idan sha'awarki ta tashi ki samu wanda zai kawar miki da ita. Wallahi a shirye nake da na aureki, kuma na kula dake yadda ya kamata, idan matsalar yaranki ne, zan ri'ke miki su, ai d'a na kowa ne, ni ma ina dasu a gida sai mu had'a mu ri'ke gabad'aya." Ganin yadda ya rikice Yana karyar da kai, da kalamai tausasa, sai jikina ya mutu. Na rasa abinda zan gaya masa domin ya gama kashe mini jiki, matsalata yarana kuma ya ce zai ri'ke mini su. A dan nazarin da na yi masa na hangi sona a tattare dashi. Kuma bai nuna 'kyama akan yarana ba kamar yadda wasu mazan suke yi idan suna son mace, sai su dinga k'yamar yaranta, suna nuna kishi, amma shi tashin farko ya amince zai ri'ke mini da alkawarin kula dasu kamar yaransa.. Jiki a sanyaye na ce." To na gode da nuna damuwarka, ina so ka ba ni lokaci zan yi shawara akan hakan, in sha Allahu duk abinda na yanke zan sanar da kai." Ya ce." Wannan ba matsala ba ce, amma ina rokonki don Allah ki yi shawara da mutanan arziki, domin kada ki yi da baragurbi su rud'a ki,wallahi da gaske nake auranki zan yi Amina, kuma zan kula da yaranki." Murmushi na yi na ce." In sha Allah, ni ba ni da k'awaye marasa tarbiya duk wad'anda nake mu'amula da su, sun san abinda suke yi, don haka kada ka damu." Ya ce." Ki ba ni lambarki zuwa gobe da safe idan Allah Ya kaimu, zan kira ki domin na ji Ina aka kwana." A nutse na fad'a masa lambar ya yi serving. Ya ce." Kin ga goma saura yanzu zan wuce gida, don Allah zuciyarki ta sa'ka miki alhari a kaina." Na ce." In sha Allahu, a gaishe da iyali." Na juya da zummar shiga gida ya dakatar da ni. Kudi ya d'auko a aljihunsa ya miko mini. Na girgiza kaina ina fad'in." Na gode amma ba zan kar'ba ba." Ya rausayar da kansa. " Don Allah ki kar'ba babu kyau mayar da hannun kyauta baya Amina, ki yarda da ni da alheri na zo miki." Hannu nasa na kar'ba tare da furta" To na gode sosai, A gaishe da iyalin." Ya amsa yana bud'e motar. Ni kuma da sassarfa na shige gida gaba na bugawa kad'an-kad'an. Ko da na shiga gidan zaman minti biyar ban yi ba. Babanmu ya shigo yana fad'in." Kin je kun zanta to? Na fad'a miki da gaske yake, ina fata kun fahimci juna." Na ce." E, to Baba mun gaisa dai, amma fahimtar juna ai sai a hankali tukkuna, ina so ne komai a tafiyar da shi cikin nutsuwa baba gaggawar auran sai ya haifar da d'a mara ido." Ya ce." Ki dinga kyautatawa kanki zato na alheri Amina, wannan mutumin na yarda dashi d'ari bisa d'ari, domin duk wanda zai bude baki zai fad'i alherisa." Shiru na yi ban ce komai ba. Ya juya zai fita Yana cigaba da jaddada maganar. Na ce." Baba d'azu anti Yagana ta kira waya." Ya juyo da sauri yana cewa." To, to Ina fatan dai lafiya? "Bikin Babandi ne ya tashi sati mai zuwa shine tace na gaya maka ko zaka samu zuwa d'aurin aure, ni ma zan yi kokarin halarta tunda an yi hutun makaranta." Ya ce." Zan je mana Amina muddin za ki yi mini kud'in mota me zai hana ni zuwa." Murmushi na yi na ce." To Baba zan yi maka kud'in mota sai ka zauna cikin shiri." Ya ce." Idan da kara itama Murja ki yi mata kudin motar mana sai mu ruguntsuma mu tafi tare." Na ce." Baba idan na biyawa Ummansu Hadiza kud'in mota hakan zai haddasa maka rikici, Ummansu Saminu za ta nuna rashin jin dadinta akan hakan, kawai dai mu tafi mu biyun." Ya ce." Hakane kuma, to babu damuwa Allah Ya nuna mana." Na amsa da '"Amin." Shi kuma ya juya ya fita daga d'akin. Na dubi shimfid'ar yaran nan ga Kamalu a kwance kusa da d'anuwansa. Na girgiza kaina, wato tsoron shigowa yake yi sai da ya tabbatar da na fita tukkuna. Na so a daran na rage dinkunan mutanan da yake hannuna, amma damuwa da zullumin da nake ciki suka hanani katabus. Na yi zaune ina ta tufka da warwara akan lamarin da yake fuskanto ni. Na sake lissafa kudin da ya ba ni dubu goma sha uku ne, don duntso su kawai ya yi daga aljihu bai lissafa ba ya mi'ko mini sabbi kar dasu. Mutumin nan da gaske yake aurena zai yi. To ni ba na hangen wadatarsa yadda rayuwar aurana da shi za ta wakana nake nazari. Ya ce Yana da yara shin matansa nawa? wannan amsar dole tana wurinsa. Ya zanyi rayuwa a cikin gidansa da marayun yarana? Wace rayuwar zasu fuskanta. Wannan tunanin shi ya dami k'wa'kwalwata. Dukda Babanmu ya ce na dinga yi wa kaina zato na alheri. Amma ya zama dole ne na yi wannan nazari. Na dubi agogon da yake kafe a d'akin d'aya saura na dare. Gidan ya yi tsit. Na d'auki buta a nutse na fita Ina hirji. Na dauro alwala na ke'bance wuri d'aya domin kai wa Ubangiji kukana. Na jima Ina rok'onsa da ya kawo mini d'auki a rayuwata. Ya yi mini za'bi na gari. Na ninike daddumar. cikin nutsuwa na shiga cikin net din yaran, na sanya a hannuna a cinyarsa na dan buge shi, ina kiran sunansa. Firgigit ya tashi zaune Hakan ya tabbatar mini da cewa dama bacci da yake yi rabi da rabi ne, a tsorace yake yi. Sai hawaye shaaa! suka fara bin kuncinsa. Na ri'ke hannunsa da yake ta rawa Yana so ya fita daga cikin net din. A hankali na ce.'' Babu abinda zan yi maka Kamalu, ka samu nutsuwa tambayarka kawai zan yi, ga gaya mini gaskiya, idan kuma ka yi mini 'karya da kaina zan kai ka hukuma, idan sun hukuntaka sai na kira Hamusu ya zo ya tafi da kai tsangaya almajiranci." Hawayensa suka tsananta zuba. Ya had'a hannuwansa wuri d'aya Yana fad'in." Mamanmu ki yi hakuri don Allah." A hankali saboda ina gudun kada sautin maganarmu ya fita. Na ce." Tona mini asiri za ka yi ko? Me na yi maka kake kuka Kamalu, ni ce fa zan zubar da hawaye, amma ban zubar maka ba. Kana so mutanan gidan su ji abinda yake faruwa tsakanina da kai kenan?" Ya girgiza kansa alamun "A'a. Na ce." To maza goge hawayenka ka nutsu sai mu yi magana." Ya goge hawayen tare da rungume gwiwarsa da hannuwansa. Na dube shi cikin nazari da tsantsar tausayi da fargaba. Na ce." Bayan kun ci abinci a gidan Gwaggwo da ka fita Ina ka je?" A sanyaye Ya ce.'' bayan Mun ci abinci sai Gwaggwo tace mu yi sallah. Bayan mun idar sai na ga tana gyangyad'i shine na fita. Ina tsallaka titi na ga Saminu ya ce na'ibawa zai je tsinto lemo ya siyar shine na bi shi muka tafi tare." "Kun tsinto lemon kenan?" "E, mun tsinto, amma ni ba'a sayi nawa ba wai duk ya ru'be ya lalace, shi kuma Saminu an sayi nasa amma ba duka ba shima akwai rub'abbu a ciki, ya samu d'ari shida, shine ya ba ni dari biyu." Na ce." To ya aka yi aka ganka za ka 'kwacewa Yara kudi an aike su auno shinkafa, Kamalu na yi maka sheda ko ni baka d'aukarwa kud'i idan ka gansu na ajiye, a garin yaya ka ke ko'karin jefa rayuwarka cikin wannan halin. Sata fa Kamalu kasan illarta kuwa?'' Hawaye ya kwaranyo masa ya ce." Saminu ne ya ce mini na je na k'wace musu sai mu raba, amma wallahi ban ta'ba yi ba Mama." Na zuba masa ido cikin nazari na ce.'' Kada ka yi mini 'karya fa Kamalu, ka san halin Saminu idan ya ji ka yi masa sharri ba zai yarda ba." Ya ce." Wallahi Mama shine ya tura ni. Shi yana samun kud'i sosai, haka yake yi, ko a makaranta sai an fita break idan wasu sun bar jakarsu sai ya je ya yi ta bincike idan da kudi ya d'auka idan babu sai ya kwashi littafai da biro. Muna tashi sai ya je ya sayar. Idona ya ciko da ruwan hawaye na yi kokarin dannesu saboda ba na son zubar masa dasu saboda kada masifar ta yi mana yawa ni dashi. Cikin wayo na ce." Yana baka kudin ne?" Ya ce." E, yana ba ni wataran kuma baya ba ni, amma dai idan mun je makaranta yana saya mana abubuwa." "A 'kafa ku ka je tsinto lemon har na'ibawa kuma ku ka dawo a kafa?" Ya daga mini kai alamun 'E' hawaye na zuba a kumatunsa. Na girgiza kaina jiki a mace na ce." To koma ka kwanta." Ya kwanta ya takure wuri d'aya Yana goge hawayen da suke karakaina a fuskarsa A hankali na fita daga cikin net din na jingina jikin bango(garu) ina nazarin abinda muka tattauna. Ba a shaidar d'an yau, Amma duk da haka zuciyata tana tabbatar mini da cewa Saminu Yana taka muhimiyar rawa wurin gur'bata mini tarbiyar yaro. Ya girmeshi ya fi shi wayo. Kuma muddin za su kwana a gida su wayi rabuwarsu za ta yi wahala. Duk lokacin da zan zauna da Kamalu na yi masa fada da nasiha yakan nuna nadamarsa ya yi ta kuka Yana ba ni ha'kuri akan ba zai sake ba. Amma ba a yin sati zai koma ya cigaba da d'auko mini magana. Babu yadda za a yi na fito na fadi wannan maganar a cikin gidan a yarda dalili kowa yana ganin fitinar Kamalu ta fi tsananta bayan ba haka ba ne. Ita Ummansu Saminu ta san yaronta ba ya ji, amma kullum cikin kare shi take ko abu suka aikata a tsakaninsu za ta cire shi tace ai lokacin da abin ya faru baya nan. Babban tashin hankali ne zai afku idan na fito na fadi cewa Saminu ne ya tura Kamalu yin 'kwace.