SAKATA COMPLETE

Page 3

by @legendspen

*SAKATA*❤️⚓️

🌻Stroy and written🌻
             By
Sayyid writer (Legend)✍️
  

   *FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)🖋️📚*


بسم الله الرحمن الرحي

SHAFI NA UKU
          (P.03).

“Tabbas kuwa, wanan ba rashin kunya bace. Salma mai yasa kike haka?.”Cike da jin haushi na sake buɗe baki nace. “Wallahi, karya yake min. Kawai ya tsaneni ne.” ban rufe baki ba naji, an ɗaukeni da mari. 

Tabbas marin ya shigeni, domin har wasu taurari nagani. Suna yawo a sama, daga nan ɗaki na huce. Ban san mene zanyiwa Mus’ab na huce wanan kayan haushin, sai dai kuma ɗaukar fansar duk kusanci dashi ne, nikam ina neman tsarin ubangiji da zuwa kusa dashi, ni ko a laira idan za’ayi mana Hisabi so nake tazarar mu ta kasance nisan sama da ƙasa. Idan kuwa har akace sai nuna gab da juna, ni mai iya yafeshi ce. 

Duk lokacin da Mus’ab, ya matso kusa dani wani irin turnuƙuƙi nakeji daga cikin zuciyata. Wani irin zafi kamar ana soyata. Idan nace na tsani Mus’ab, to na tsaneshi, bana fatan ko da rana daya naji na samu sasssuci daga tsanar da nayiwa Mus’ab.

Yau ta kasance Lahadi, babu makarantar boko sai islamiyya. Muna zaune a compound muna wasa, har yanzu zuciyata cike da ɗacin marin da Yaya ilyasu yayimun jiya, kamar ance Salma fita waje haka naji zuciya na na fusgata. 

Kyawawan samari ne guda biyu, suna tsaye daga gefen gidanmu. Kyawawa ne sosai da sosai, cike da nutsuwa na fara tafiya zuwa inda suke, kamar wacce aka saka. ”Ƴan mata barka.” Daya cikinsu ya faɗa fuskarshi da murmushi. “Ina wuni.” na faɗa kasancewar sha-biyu ta kawo kai. 

“Lafiya ƙalau, dan Allah ko kin san gidan Alhaji idi me mai.” ɗaga kai nayi sanan nace. “Ai kuna kusa ma, gida na uku daga gidanmu.” 

“To inane gidan naku?.” ɗayan da baiyi magana ba tun dazu ya faɗa, cikin wata murya mai sanyi da zaƙi. “Kaji mazan arziƙi, ba irin su Mus’ab masu maganar mata ba.” na faɗa a raina, a fili kuma nayi murmushi na ce. “Wan can mai jan get ɗin shine namu, to daga na kusa da mu mai ƙofa, sai wancan mai ɓakin get na farko, to mai baƙin na biyu shine.” 

“Mungode Ƴan mata.” nayi murmushi, kamar an cemun juya idanuna suka faɗa cikin na Mus’ab, Ya harɗe hannye a ƙirjinsa yana kallonmu. Irin kallon da yakemun naji zuciyata ta buga da ƙarfi, da sauri nashiga gidansu Nana.

Sai dai ko minti biyar banyi a gidan ba, iki tazo tace wai nazo inji kawu Mudi. 

“Innullahi, mai wanan mutumin yaje yace nayi kuma ni.” iki dai ba tace mun komai ba ta huce, na bita jikin a sanyaye. A tsakar gidan mu, na tarar dashi hannunsa rike da bulala ga Mus’ab can tsaye. “Kawu gani.” 

“Tsugunna ƙasa.” 

“Kawu mai nayi.” 

“Bazaki tsugunna ba.” ban kai ga tsugunnawar ba ya fara dukana, da iya ƙarfinsa, babu imani ko tausayi. Yana dukana yana faɗin.

"Ke mara kunya mara tarbiyya ko, kina yin rashin kunya a gida ana kyaleki. Yanzu abun naki yakai harda fita waje, kiga mutane tsaye suna magana ki hau yimusu rashin kunya ko?.” zallan mamaki ne ya hanani cewa komai, wacce irin tsana Mus’ab yayi mini, mai nayi masa haka da zafi?, haka kawu mudi ya ci gaba da zabgamun bulal, har kuka shigo farkon labarin. 



*Cigaba*

Nanata addu’a ta nakeyi.”Allah yagama Mus’ab da masifar duniya.” na jiyi sautin Walida, tashigo bangaren mu tana rusa kuka, Abinda ya fara zuwa raina shine. Mus’ab ya mutu, afili na furta.

"Allah ka tabbatar.” shigowa tayi ɗakin mu tana faɗin. 

“Ummah, Yaya Mus’ab ne ya faɗi, ciwon kansa.” wani sanyi naji ya ratsa zuciyata, wanda kwata-kwata yau banji shi ba, tun bayan haɗuwata da wanan samari guda biyu. A gigice Ummanah ta fito, kamar wacce a ka ce mata, ni ko Yaya Asma’u sun faɗi. 

“Innullahi wainna illahir raji’un, Allah ka kawowa yaron nan saukin wanan ciwon kan.”

Ummanah ta fada tana ficewa, da ido na bita ina taɓe baki. 

“Allah yasa har mutuwarsa.” 

na fada tare da kwanciya abuna, ban farka ba sai kiran sallar asuba. Tashi nayi na shiga toilet, na daura alwala nayi sallah. 

“Ummah ina kwana?.” Na fada daga inda nake, amma naji shiru. “Ina kwana.” still shiru, tashi nayi nafito falo tunda ita Ummanah na anan take zama lazimi, tun sallar asuba har bakwai. Rashin ganinta a falon yayi matukar razana ni, dakinta ta nashiga kai tsaye nan ma batanan. 

A kid’imi na fito xuwa b’angaren Abbanah, dakinshi na shiga na tarar dashi xaune da carbi hannunsa. Kallo ɗaya yayimun yasan da damuwa a tare dani. “Salma lafiya?.” 

“Abbanah, ina Umma?.” Murmushi yayi sanan yace. “Yayanku ne ba lafiya a asibiti suka kwana.” A jiyar zuciya na sauke, ni kam na ma manta da wani Mus’ab ba lafiya. Hanya na kama zanfita yace. “Ki hada musu breakfast, kuje ke da walida.” cuno baki nayi gaba, tare da ficewa.

Kitchen na shiga na fara hada breakfast, cikin ƙanƙanin lokaci na soya doya da ƙwai, zuciya ta nayi mun tuƙuƙi. Nasan yadda Mus’ab ke mugun ƙaunar doya da ƙwai, domin ko a baya a ka kaiwa Hajja ba taci sai dai ta ajiye masa, har na zuba a plast sai kuma na tuna Mus’ab bai cin yamboll (Ƙosan doya), cikin hanzari na jawo doya  nashiga ferayewa. A gaggauce na dadatsa ta na ɗora ta a kan gas, tare da balbala uwar wuta. Zuba doyar nayi a plast tare da tea na miƙawaya Abbabah, na ɗibi iya cikina, na ɗibawa Hajja sai kuma wani bangare na zuciyata ya rayamun kar na kaiwa Hajja, domin ita ke daure masa gindi. Amma fa inason Hajja ko ya ne, fita nayi zuwa ɓangarenta hannuna riƙe da doyar. Tana zaune jigom kamar wacce aka yiwa mutuwa, ina kyautata zaton jiya batayi bacci ba.”Ina kwana?.” na faɗa, ina shiga dakin. “Lafiya.” 

“Gashi.” na fada tare da miƙamata. “Babar taki ta dawo ne?.” girgixa kai nayi, sanan nace. “Nina soya.”

“Menene kika soya?.” 

“Doya ne da ƙwai.” Murnushi tayi sanan tace. “Kin ɗibi na Asibiti.” a da kile nace. “Uhm.” daga haka na juya na fice. Ina zuwa na tarar doya ta tayi, aikuwa na sauke na fara dakawa, cikin ƙanƙanin lokaci na dake ta. Na yanka albasa da attatuhu na zuba a ciki, na kawo maggi da kuri na zuba a ciki, nasan baicin kifi hakan yasa na dakko kifin gwangwani na zuba a ciki, na hau mulmulawa. Cikin ƙanƙanin lokaci na mulmule ta tas, na kaɗa kwai na hau soyawa.

Ina gama soyawa na juye a plast, nasan duk masifa yana shan ruwan zafi hakan yasa naki da fawa dasu. Zuba tea din nayi a kofi, na zuba doya da yamboll dina, na hauci. Sai dana ƙoshi, na hade ragowar doyar na juye a baƙar leda, na jefe a kwandon shara, zuciyata fari tas. 


Abbanah ne ya kirani ɗakinsa, bayan na zauna ya kalleni yace. “Salma, kije ki shirya kuje asibitinan yanzu.” 

“Abba wallah, ƙafata ciwo takemun sosai…” wani kallo da ya watsamun yasa na haɗiye yawon bakina, da ragowar maganar tas, na tashi na nufi daki, dogon hijabin Ummanah na dauka na zura, aikuwa yazo mun har ƙasa ina jaa. Ban ko damu ba, nashiga kicin na dakko plast din nasa a leda, a bakin ƙofar dakin na tsaya nace. “Kudin mota.”

“Tasowa zanyi na kawo miki?.” a jiye ledar nayi, nashiga dakin ya bani dubu biyu, ba godi ba nagode na kadai na tafi, tunda dai bani na tambayeshi ba. 


Ɓangren su Walida na nufa, na sameta tsaye.”Mai kike jira?.” na tambayeta. “Lami nake jira ta gama abinci na tafi dashi; ina zaki ke?.” ta tambayeni , donin kowa zaiyi mamaki idan nace, Mus’ab zanje kai wa abinci. "Abba ne yasani girki, wai na kai asibiti, amma tunda ga wanan kawai kizo mutafi." na faɗa da biyu a raina, domin banason ya zamana abinda Ummi zata tafi dashi, Mus'ab ɗin nacin sa, anyi ba'ayi ba kenan. 

Ɗaki tashiga ta saka Hijabi itama, mu ka fice. A bakin titi mu kasami napep muka shiga, kasancewar kowa yasan asibitin da ake kai Mus'ab, ba ma shi kaɗai ba, kowa da kowa na gidan Galadima. 

A bakin asibitin mai napep ya sauke mu, naira duba daya na bashi ya ɗau ɗari biyar, yaban ɗari biyar. Muka rankaya cikin asibitin, har zuwa bakin ɗakin. A dai-dai na naja na tsaya, namiƙa wa Walida ledar nace."Shiga da'ita, idan kinfito ina bakin nan." 

"Haba salma, kishigo mana." 

"Wallahi walida ba zan shiga ba, ko da ace dubashi da xanyi, itace hanyar samun saukin shi da huri.” 

Ba tak’ara cewa komai ba, ta amshi ledar ta shige dakin ni kuma naja na tsaya, kamar wata mai gadi. 

Ina tsaye kusan mintina biyar, Ummanah ta leƙo sai ji nayi ance. "Sannu tabbatacciya." da sauri na juya, domin banma ji sanda aka buɗe ƙofar ba, da ruguwa zanyi a guje. "Ummah ina kwana." 

"Bansani ba, zaki shigo ko sai nazo nan na tsinke ki da mari." ta kowa na farayi a hankali, har zuwa bakin ƙofar ɗakin, a raina ina faɗin. "Lallai Walida da ni take zancen." 

Yana Kwance idanunsa na kallon ƙofa, aikuwa cikin rashin sa'a muka haɗa ido, aikuwa na murguɗa masa baki, tare da maka mai harara, game da yi masa gwalo a lokaci guda. Karo na farko a rayuwarsa da yaga nayi abu ya burgeshi, a cikin zuciyarsa yaji hakan. 

"Maman ciki ina kwana." 

"Lafiya ƙalau ɗiyar waje." kamar kullum dai dariyar mukayi, na matsa kusa da walida ko zama ban ƙarasa yi ba na maka mata mintsine tare da faɗin."Wallahi kinyi da ni." da sauri tace. "Wallahi bani na ce kinzo ba, Yaya Mus'ab ne." 

"Wallahi Walida ƙarya kike, aina yasan nazo." 

"To nima bansani ba, daga Mama ta tambayeni ya mutan gidan, nace lafiya. Sai ta ƙara cewa ke ya kike, nace ke kikayi girkin ma, shine Ummah ta ce mai yasa baki biyoni ba, ni kuma nayi shiru. Sai ji nayi yace tare kuke, na girgixa kai amma yace wai tare muke Ummah ta duba." Hararar ta nayi na ce. "Ni ban yarda ba." 

Ƴan minti na kaɗan na miƙe tare da cewa. "Zamu tafi." dai-dai lokacin shikuma ya buɗe baki ya ce. " Abinci..." Wani murmushi nayi tare da zama, Ummanah kuwa ta sakko tana faɗin. "Walida kun manta da tea."

"Wallahi umma ba ni nayi komai ba, ko ledar ma sai a bakin ɗakin nan ta bani na riƙe."

"Ai shikenan, Ummanah ta faɗa tana kwance ledar.

Legends pen.
(***/***).


Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete  ₦1000.

Payment via.

8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.

Shaidar biya.

***.