Page 4
by @legendspen
*SAKATA*❤️⚓️
🌻Stroy and written🌻
By
Sayyid writer (Legend)✍️
*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*
*(FUWA)🖋️📚*
SHAFI NA HUƊU
(P.04).
بسم الله الرحمن الرحيم
"Wallahi umma bani nayi komai ba, ko ledar ma sai a bakin ɗakin nan ta bani na riƙe."
"Ai shikenan, Ummanah ta faɗa tana kwance ledar.
Bude idanu tayi, ganin yamboll kuma ta tabbatar wanan din aiki na ne, domin kowa ya kwana ya tashi da sanin cewa. Mus'ab bai cin yamboll.
"Yunwa na keji." Mus'ab ya fada, wata dariyar mugunta ta tawomun wacce da kyar na iya tsaida ta, har sai da shi kanshi yaga alamun ina dariya.
"Salma, mene kikayi haka, kinsan baya cin yamboll ko?."
Hade rai nayi, sanan na ce. "Ummah shi ka dai ne damu."
"Eyh shi dake ba da doya akeyi ba ko?."
"A'a Ummah, yafi sauƙi ne."
"Ke zanci gidanku wallahi, a gama dafa doyar azo a daka shine zakice yafi sauƙi?."
"Wai menene?." Maman ciki ta tambaya, "Yamboll ta yo." Ummanah ta ba ta amsa, " Ai shikenan mu bari mu ci, ku kuma ku fita ku nemo mana tea, da kayan madara." Tashi nayi na amshi kudin, walida ta biyo ni har mun kai bakin kofa, Ummanah ta ce. "Saura ki siyo ruwan sanyi." Dariya nayi na fice, Mus'ab kam zuciyarsa kamar ta fito waje, ji yake kamar ya makeni da duka.
Mun siyo kayan shayin mun dawo cikin asibitin naji ana cewa."Ƴan mata." kamar nasan murya, amma duk da haka naki tsaya wa, duba da yanayin yawan mutanen dake wajen bai zama lallai ni din ake kira ba. "Ƴan mata, bakya jina wai." a ka sake fada kusa dani, da alama mutumin yazo inda muke. A hankali na waigo idanuna suka sauka a kansa, daya cikin matasan da suka zo layin mu jiya, suka tambayi Gidan Alhaji idi me mai. Wanda baiyi magana sosai ba, ina tuna lokacin da yace. "To ina ne gidan naku?." Murmushi nayi masa sanan nace."Ina yini." shima murmushin yayi, cikin zazzakar muryarsa yace. "Lafiya kalau ƙanwata; me kikeyi anan?."
"Ɗan-uwan mu ne ba lafiya, aka kwantar dashi anan."
"Ayyah, Allah sarki muje na duba shi." Wani irin abu naji a zuciyata, amma kuma baxan iya masa musu ba, hakan yasa na ce. "Toh muje." jerawa mu kayi muka fara tafiya, Walida ta shige gaba mu kuma muna baya, duk naji nayi wanan fiyau. Ya cika wajen baki daya, a raina na ce. "Idan wanan yace yana so na, wallahi sai nayi sadaka, sabida yana da kyau, gashi ɗan gayu, mai aji, murya mai zaƙi. Nipa an gama tashin kai na." A haka muka ƙara so daƙin, walida ce ta ce. "Bari na sanar da su." gyada kai yayi, ni kuma naji ni a ta kure. Ban yarda da abinda Walida za ta ce ba, hakan yasa na ce. "Bari na bi ta."
"A'ah ki jira mana." kallonshi nayi, idanuna sunyi wani kala na ce. "Ban san me za ta ce ba."
"Mai kike tsoro to?."
"Za fa ta iya ce musu, Saurayina ko wani abu." Murmushi yayi, sanan ya ce. "To menene a ciki, ko ki na da wani saurayin ne?." ƙasa nayi da kai na, ba tare da na ce komai ba. Shi kuma ya ƙara cewa. "Ko akwai ne." girgixa kai kawai nayi, dai-dai lokacin da Walida ta fito. Sai a lokacin na fahimci cewa, kofar bata yin ƙara idan a ka bude ta, shine yasa dazo banji lokacin da ummanah ta buɗe ba. "Ku shigo." ta faɗa, ni kam kamar munafuka haka na zama.
Idanunsa a rufe yana kallon sili muka shigo, Maman ciki ce ta. "Ga waje mana basai ka xauna a ƙasa ba."
"A'a Mama bari na zauna anan; ina kwana, ya mai jikin."
"Lafiya ƙalau, mai jiki da sauƙi." su ka amsa tare. "Allah ya ƙara lafiya."
"Amin, Mus'ab ga baƙo fa." Mama ta faɗa, a hankali ya buɗe idonsa ya sauke su akan mu, kasancewar ya tsugunna kusa da inda nake zaune. Kallo daya ya gane fuskar gayen, wa'yanda yaganni dasu jiya, tasowa gayen yayi zuwa idan gadon yake, tare da mi ƙawa Mus'ab hannu sukayi Musabaha."Ya ƙarfin jikin?."
"Alhamdulillah." Mus'ab ya fada a da ƙile. "To Allah yaƙara afuwa."
"Amin."
"Zan huce, Allah yakara lafiya."
"Amin-Amin, an gode." Su Umma suka fada, shi kuma ya nufi ƙofa. Walida ce tayi magana da ƙarfi yanda kowa zaiji."Salma kije ki raka shi mana." kamar mara laka haka na tashi, ina raba idanu nayi waje.
A bakin ƙofa na tarar dashi. "Salma..." ya faɗi sunan, tare da ja cikin wani irin salo mai dadi. Sai naji kamar shi kadai ya iya kiran sunana. "Zan tafi, ngde da kulawa. Sunana Masrur, sanan wanan asibitin na mahaifina ne, kuma yana karkashin kulawata saboda haka, an dauke muku komai."
"Mun gode, amma da ka barshi dan wallahi ban san ta yadda zan fadawa iyayena haka ba."
"Salma..." ya ƙara kiran sunan na, a nutse na ɗago na kalleshi. "Ina sonki." Kara ɗagowa nayi na kalleshi, idanunsa suna kaina, da sauri nayi kasa da nawa a raina na ce."nima ina sonka." amma afili kuwa shiru nayi na kasa cewa ko uffan."Bazan ta kureki ba, zanbaki lokaci kiyi tunani. Ga lambata nan." ya faɗa yana miƙomin wani kati, hannu nasa na amsa sanan nace. "Nagode." ka ɗa kai yayi ya tafi, ni kuma na koma ciki.
Kamar wata ɓarauniyar da tayi sata aka kamata haka na shiga cikin ɗakin. Sai dai duk cikinsu babu wacce tace da ni ko uffan, hakan yasa nayi matuƙar damuwa. A hankali na ce."Umma, mai walida ta ce muku?." banza Umma tayi dani kamar ba taji ni ba, kuma nasan taji, hakan yasa na koma ga Mama. "Mama mai walida ta ce?."
"Mai kikaji wani yace miki?." Na girgiza kai na ce."Bakomai."
"To kuma, ko kinyi wani abun ne?." na girgiza kai kawai, can 'yan mintina na ce. "Walida ta so mu tafi." ba ta kai ga magana ba likita ya shigo ɗakin. Bayan sun gaisa yace da su Ummah.
"Ban san wane likita ke duba Mus'ab ba, kuma ko ma wane akwai matsalal da ba daga likitan mu take ba, dagashi yaron ku take."
"Matsala kuma likita?." Mama da Ummanah suka tambaya, har wani hade baki sukeyi. Ni kam a raina na ce. "Allah yasa matsalal mutuwa ce." maganar likitan ce tasa na dago na kalleshi.
"Eyh matsala, domin gaskiyyya ba aina hin ciwon dake damunshi ake fada ba, kuma da masaniyar sa domin ko magungunan da ake bashi, na asalin ciwon sa ne. Kunga kuwa sun hada baki da likitan suna ɓoye muku.
Wani daɗi naji a raina, domin nasan babban ciwon ne kadai ake boyewa iyaye ba'aso su ji sabida kadan hankalinsu ya tashi.
"To yanzu likita wane ciwo ne, na gaskiyya dan Allah." Ummanah ta fada kaman zatayi kuka, wani ƙululun abu ya tsayamun a ma ƙoshi yanda matarnan ta damu da Mus'ab ko ni bata damu dani ba, ji yanda take magana kaman zatayi kuka.
Abban ciki ne yayi sallama, tare da Kawu mudi da kuma Yaya ilyasu. Shigowa sukayi baki dayansu, nida walida muka koma can gefe muka basu basu waje, kasancewar dakin babbane.
"Kai ka sa tsohuwar mutane cikin damuwa." Yaya ilyasu ya faɗa. Likitane ya ci gaba da cewa."Kamar yanda na fada muku, matsalal shi ba ciwon kai bane kwata-kwata." da sauri Abban ciki yace. "To menene?."
"Matsala shi a ciki take."
"To amma mai yasa duk bayanan ku na baya yake nuna kai."
"A'ah ranka yadaɗe, ko a file na asibiti cike ne, sanan magungunan da yake sha ma na ciwon ciki ne, kawai su na ambatar kai ne domin ɓoye muku."
Ina daga gefe na fara addu'ar, Allah yasa afendes ne yanda za'a yanka shi karshe a ce ya mutu.
"To yanzu likiti menene cutar?." Abban ciki ya ƙara tambaya, Likitan ne ya fara duba takardun hannusa, nikam hankali na kanshi.
" I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba bace, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma.
"Doctor, kana firgita mu Menene matsala?"
Legends pen.
(***/ ***).
Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000.
Payment via.
8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.
Shaidar biya.
***.