Page 5
by @legendspen
*SAKATA*❤️⚓️
🌻Stroy and written🌻
By
Sayyid writer (Legend)✍️
*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*
*(FUWA)🖋️📚*
SHAFI NA BIYAR
(P.05).
بسم الله الرحمن الرحيم
" I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba ba ce, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma.
"Doctor, kana firgita mu Menene matsala?"
" He have been diagnosed with a rare condition called Hypersexual Hormonal Disorder HHD. It means His body produces an unusual level of sex hormones beyond control. That’s why kake yawan jin wani irin zafi, idan kana ciwon cikin. Kuma irin wannan sha'awar ba irin wacce ake iya da ƙilewa ba ce,da ƙile ta da yayi na kwanakin baya yasa ta zama babba har haka."
"Wannan wace irin cuta ce haka, nifa bangane komai ba?." Mama ta tambaya cike da ruɗani. "Nima dai." Ummanah ma ta faɗa.
Yaya Ilayasu ne, ya kallemu ni da Walida yace."Ku fita." Sim sim sim kamar munafukai muka fice, ni dai burina a ce mutuwa zaiyi.
Bayan munfita ne likitan ya kalli su Mama yace.
"Yana fama da wata irin cuta mai suna Hypersexual Hormonal Disorder. (HHD). Ma'ana jikinsa yana fitar da wani nau'in sinadarin sha'awa fiye da kima. Wanan ne dalilin da yasa yakw yawan jin wani irin zafi, da kuma wata sha'awa mai ƙarfi wacce har ta kan iya kayarda shi ƙasa."
"Inullahi wa'inna illahir rajiun." su Mama suka shiga maimaitawa, likitan yakara da cewa."Tun farko bai bari anyi dogon bincike ba, a kan rashin lafiyar tashi, gashi har abun ya zama worst haka, ko kunyar ku yake ji oho."
"To amma fisabillillahi, ko da yanajin kunyar mu bashi da 'yan uwa maza. Kawai sabida rashin kula da lafiya." Ummanah ta fada cike da damuwa.
"To yanzu likita menene ai nayin maganin cutar?." Abban ciki ya tanbayeshi.
"There’s no drug-based cure yet. But in most studied cases, emotional stability and natural intimacy especially within marriage. help the body regulate the hormones over time. Auren na iya zama magani a gareshi."
"Shikenan likita, insha Allahu za'ayi." Abban ciki ya faɗa, likitan yakara da cewa."Yanzu za'a rubuta mishi drugs da zai na amfani dashi, zasu taimaka sosai da sosai."
"To mungode." Ummanah ta fada, likitan yasa kai ya fita, Mus'ab kam idonshi a kulle angama to na mai asiri yanzu kowa sai yasan halin da yake ciki.
"Yanzu fa Mus'ab da ka mutu d Wanan ciwon, baka da maraba da wanda yakashe kansa, kasani kuwa." Maman ciki ta fada murya a sanyaye, Ummanah ta dora da cewa. "Mus'ab, a duniyar nan babu kamar iyaye, ba'a ɓoye musu komai domin kowacce mafita tana daga garesu, ka bar ganin mun girma har mun haifi kamarku, duk wata matsala idan tataso mana, idan har mijinmu bazai iya magance mana ba, to iyayen mu muke nufa da ita." Tashi Abban ciki yayi ya fice, domin yasan duk abinda zai iya fada, Maman ciki da Ummanah zasu faɗeshi. "Kuyi haƙuri..." ya faɗa cikin sanyin murya, Ummanah ce tace. "Dan Allah ko dan gaba ku kiyaye baki ɗayanku."
"Tom insha Allahu." Yaya Ilyasu ya faɗa, sanan yace dasu Ummah. "Jiya masu neman auren Sadiya sun sake zuwa, a kace dasu sudawo yau."
"Lallai ne, Sadiya lokaci yayi." Maman ciki ta fada, inda Yaya ilyasu yace. "Saura Walida da kuma Salma, su kam kamar ma ba za su kai candy ba."
"Eyh kam, bazasu kai candy ba." Ummanah ta fada, Maman ciki tayi murmushi. Can sai ga Abban ciki ya shigo,rike da ledar magunguna.
" Gashinan, suma sai kayi wasa da shan su." Maman ciki ta amsa ba tare da ta cw komai ba.
"Ni zan koma gida, zan samu Hajja nayi mata bayani, Muji abinda zata ce."
"Tom shikenan."Maman ciki ta fada, shikuma yasa kai ya fice.
Muna zaune daga gefe ya fito, da sauri muka taso tare da cewa."Abba zamu tafi muma."
"A'ah ku xauna mana, ko za kuyi musu wani aikin."
"Ai Abba zamuyi girkin rana, sanan mu na da islamiya." na fada sabida ni hankali na, na kan na koma gida nayi sadakar alewa, zan kaɗeɗen saurayi kamar Masrur ya ce yana so na, shine sabida nice nafi kowa butulci ba xanyi sadaka ba.
"Shikenan ." ya fada tare da fita, Walida ce ta koma daki tayi musu sallama, nikam bayan Abba nabi sabida tsoron karma ya tafi ya barmu.
Muna ƙarasawa gida na sauka nayi ɓangaren mu, ban ƙarasa ba naji muryarshi na cewa. "Ki cewa Abbanki ya same ni ɓangaren Hajja."
"Thom." na ce sanan na ci gaba da tafiya, shi kuma ya juya ga walida. "Kira mun sauran kawunnanki." itama "Tho." ta ce, ta tafi kiransu. Ina shiga na tarar da Abbanah ya gama shiryawa. "Abba mun dawo."
"Toh sannu da dawowa, ya jikin na sa?."
"ya warke." na faɗa a gajar ce, sai kuma na ƙara ce wa. "Abban ciki, ya ce ka same shi ɓangaren Hajja."
"Ya dawo?."
"Eyh, shine ya dawo da mu."
"Okay." daga haka ya fice, ni kuma nayi cikin ɗaki. A ɓangaren Hajja kam, gaba ɗayansu ne zaune sun sa Hajja a gaba da kallo. "Ni wai lafiyan ku?, kun haɗu kuma kun bini da idanu." Hajja ta faɗa, sai kuma ta ce. "ko dai Mus'abu ne ya mutu?."
"A'ah Hajja, ba mutuwa yayi ba amma akwai matsala."
"Tsarin ubangiji muke nema a kan kowacce matsala." Hajja ta faɗa, Abbanah kuma ya ce. "Yanzu Salma ke ce mun ya warke."
"Eyh hakane, su za su ga kamar ya warke. Amma a bayanin da likita ya yi mana, ya ce ba cutar ciwon kai ba ce ke damun Mus'ab tun farko, ya ɓoye mana ne."
"Waye ya ɓoye mana?." Abbanah ya faɗa cike da fushi, dan shi a tunaninshi likitan ne yanzu ya je suyi ɗauki ba daɗi, dan duk gidan Galadima babu wanda ya kai Abbanah fushi, da zafin zuciya.
"Shi Mus'ab ɗin."
"Innullahi wa inna illahr rajiun, yanzu wace cuta ce haka zata kashemun jika na, ɗan lele nah?."
"Mus'ab, na fama da wata cuta wai ita Hypersexual Hormonal Disorder. (HHD). Ma'ana dai jikinsa ya na fitar da wani nau'in sinadarin sha'awa fiye da kima. Shi ke haifar masa da wanan ciwon cikin."
Kuka Hajja ta saki tare da faɗin."Nashiga uku na, shiyasa nake ce wa yaron nan cike ke masa ciwo ba kai, sabida idan ciwon yayi zafi ciki ya ke riƙewa ba kai ba. Amma ya ce wai A'ah, yanzu idan ciwon ya kashe shi ina yake so na sa ka kaina."
"Kiyi haƙuri Hajja." kawu Mudi ya faɗa. Abban ciki ya ɗora da cewa. "A yanzu likita ya ce hanyar samun sauƙi guda ɗaya ce, ayi masa aure." Abbanah ne ya ce. "Abinda ke raina kenan, dama ai akwai yarinyar da ya ke nema ko?." gyaɗa kai Abban ciki ya yi, sanan ya ce. "Amma ya na da kyau idan anje neman auren a sanar da iyayen komai."
"Salan su hana shi, to wallahi ba da yawo na ba." Hajja ta faɗa. "Yaya ba fa cewa sukayi ya na da Mentel disorder ba, kuma ba cewa su kayi ya na sa yawan buƙata ba. Dan haka wanan ai ba matsala ba ne." Abbanah ya faɗa, Hajja ta cafeshi da ce wa."shine dai, yanzu ina so ku tashi daga nan kuyi gidan iyayenta a ba su komai da komai harda sadaki."
"Shikenan, amma ni ai babu ni za'a je ko?." Abban ciki ya faɗa da alamun tambaya ga Hajja. "Uhmmm." ta faɗa a gajarce, sai kuma ya ƙara cewa. "Su ma masu neman auren Sadiya fa?"
"Naga dangin Mahaifiyar ta ne, ɗan gidan Yayar Mahaifiyarta uwa ɗaya uba ɗaya. Ba najin sun cancanci a hana su, duba da Mahaifinsa kowa yasan shi, tarbiyar gidansu ba ɓoyayye ya baci." Abbanah ya faɗa.
"Sanan yaron yana zuwa nan sosai da sosai, haka mahaifiyarsa." Itama Hajja ta faɗa.
"Shikenan, sai a ba su watanni. Amma kuna ganin za' a haɗe dana yaron nan."
"A'ah kar ku fara, banason auren sa ya huce wata biyu fa." Hajja ta faɗa cike da damuwa. "Shikenan." kawai suka ce sanan suka fice, dole sai sunyi tasu shawarar a waje.
Ina shiga cikin ɗakin mu, nayi ɓangaren Ummanah. Ƙasan kayanta na shiga du bawa, nasan nanne wajen ajiyar kuɗinta. Cikin sa' a na gano su, naira dubu daya na dauka na ƙara da ɗari biyar cikin canji mota na, na fita siyo alewa sadaka. Shagon bayan gidanmu na je, na siyo lolipop mai tsinke, har leda biyu a cewa ta "idan zaka gode wa Allah, ka gode ma sa da babban masaki sai ya ƙara ma ka da wanda ya fi wanan girma."
Ina dawowa harabar gidan mu, na fara ƙwalawa yara kira ina faɗin."Sadaka, sadaka." cikin ƙan ƙanin lokaci yara su ka fara ta ruwa cikin gidan mu. Daga na cikin gida har na waje, ni kuwa faɗi nake. "Duk wanda ya karɓa ya ce Allah yabar ƙauna." ai kuwa da sun amsa za kiji suna cewa. "An gode, Allah ya bar ƙauna." na cafe da. "Amin." abuna, zuciyata shar, Allah ya bani zankaɗeɗen saurayi da ga sama.
Walida ce ta fito wajen da na ke sadakar, ta kalli ne ta ce. "Sadakar mecece haka kuma?." Jin wani yaro ya ce. "Allah ya bar ƙauna, yasa ta bi ni da idanu, ni kuwa na murje na ce. "Menene a ciki?."
"Ce wa yayi yana sonki?." ta tambaye ni. "Ba ke uwar munafukai ba, a faɗa miki kije ki ya ɗa mutum."
"Ya za'ayi na ya ɗa ki?."
"Walida da ban san halinki ba." na faɗa ina ci gaba da sadaka ta. "Wallahi ba zan fada ba."
"To ce wa yayi ya na so na, har da ba ni lambarsa." na faɗa hankali kwance.
"Lallai ne, ki na cikin Alheri. Kin san Sadiya ma an ba da ita?."
"Naji ƙishin-ƙishin dai." Na faɗa, ni dai hankali na na kan 'yan sadaka. Ganin kamar ta ji babu daɗi ya sa na ce. "Yanzu ke ma sai ki yi wa, Haidar magana kawai a kwashe mu."
"kina ganin Haidar zai yi aure yanzu?." ta tambayeni cike da damuwa.
"Mai zai hana shi tun da ya na sonki, ko ma ba za yi ba menene a ciki. Sai ki bawa wasu dama."
"Ni kam na fi sonshi."
"Sai ki zauna ki jirashi, ni dai wallahi ko yanzu a ka ce za'a ɗaurawa Masrur ne bin shi zanyi, na zauna na yi uban me a gidan?." Na faɗa ina murguɗa baki, kamar gaban iyayen nawa nake.
Ƙarar tsayawar Napep ya samu ɗagowa tare, Su Ummah mu ka gani. Wani irin abun naji tsurum a zuciyatah, ga uban ledar alewa a hannuna, ga yara sun zangaye ni su na faɗin."Allah ya bar ƙauna."
Legends pen.
(***/ ***).
Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000.
Payment via.
8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.
Shaidar biya.
***.