SAKATA COMPLETE

Page 6

by @legendspen

*SAKATA*❤️⚓️

🌻Stroy and written🌻
             By
Sayyid writer (Legend)✍️
  

   *FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)🖋️📚*

    SHAFI NA SHIDA
          (P.06).

بسم الله الرحمن الرحيم



Ƙarar tsayawar Napep ya samu ɗagowa tare, Su Ummah mu ka ga ni. Wani irin abun naji tsurum a zuciyatah, ga uban ledar alewa a hannuna, ga yara sun zagaye ni, su na faɗin."Allah ya bar ƙauna." 

Sakkowa su ka fara yi daga cikin Napep ɗin, idanu na suka sauka a kan sa, a raina na furta. "Ya dawo bai mutu ba." na ja tsakin da ya fito fili, har Walida ta kalle ni, sai kuma na sake ce wa. "Kai ka ɗai dai za ka ci tsiyarka, ni kam lokacin ta shi na daga gidan Galadima ya yi."


"Sadakar me a ke yi kuma?." Umnanah ta tambaya, bayan sun ƙaraso inda muke tsaye. Buɗe baki nayi zan fara wa'in- wa'in yaron da yake gaba na ya ce. "An gode, Allah ya bar ƙauna." da sauri nayi ƙasa da kai na, ban san da wane ido ne zan kalli Ummanah ba, Maman ciki kam ce wa tayi."Ƙaunar wa?." Shiru mu kayi nida Walida, nasan dai Walida ganin ina wajen yasa ba ta faɗi komai ba, amma da ba na wajen tuni ta shai da musu. Ummanah ce  ta ce."Ku shigo da kayan." sanan ta huce, Maman ciiki ma ta huce. Ido nasa na kalleshi, wata irin tsanarshi mai nauyi ta durga a ƙirjina, ni ke nan ba zanyi masa mugun fa ta ya kama shi ba, duk da haka ba zan gaji ba."Allah ka gama shi da masifar duniya da ta lahira." na sake faɗa ina daukan kayan. Ɓangaren Hajja suka nufa, mu kuma mu kayi bangarensu. A raina naji dadin dawowar Ummanah, ko ba komai zan ɗauki wayarta na kira Masrur. 



Ban daddara ba, na mai da lolipop ɗita jakar islamiya ta, a ce wa ta idan na fita nayi sadakar a bata, dan wallahi sai na nunawa Allah godiyata da yabani kyakyawan saurayin kamar Masrur. 


Ƙarfe ɗaya da rabi nayi shirin Islamiyya, bayan na ɗau jaka ta na fito falo na ce da Ummanah. "Na huce." tsaya ki mika wa Mus'ab doyar nan. Turɓune fuska nayi sanan na ce. " Na ma kara fa." 

"To sai kin kai, ko abinda ya fi makara kika yi. Wai ni Salma yaushe ne zaki dai na yi wa Mus'ab wanan ƙiyayyar ne?."

"Au ni ce nake ƙinsa?." Na faɗa a raina, a fili kuma na ce. "Ni ba ƙinsa na ke ba, kawai ba na son kowacce kalal alaƙa ta haɗa ni da shi." 


"Sabida ba ɗan-uwanki ba ne ko me?." 

"Umma kawo na kai."Na faɗa domin son tsayar da waccan maganar. "Salma ba fa ke ce kika haife ni ba, kin san da haka?." shiru nayi, ni ba na son a ci gaba da maganar, domin har cikin rai na ba na son wani abu da ya shafi Mus'ab a rayuwata. 

Ina tsaye ta gama soyawa ta miƙo mun."Sa a plast ki miƙa mai." ban ce uffan ba, na ɗau plast ɗin na zuba. Ga ba daya na juye  a plast din na kama hanya na fice, na fito daga ɓangarn mu zan nufi ɓangaren su na ga Sadiya ta dawo. Washe baki nayi da faɗin. "Ka ga amarya, shine kika kwashe ƙafa ki ka tafi, wato sai da a ka ce an basu shine ki ka dawo." Dariya tayi sanan ta ce. "Wallahi dazu Amina ta ce mun, Mal isah ya ce sai ya ɓallani, shine ki ka ga na kwaso ƙafa na dawo."

Dariya nayi sanan na ce."Ba kunya ki ka tafi gidan su saurayi ki ka zauna." 

"Yoo kunyar wa zanji, ina shan zumar ƙauna." ta fada ta na fari da ido."Uhm bari na mika wanan ɓangaren Hajja, amma kafin nan tsaya ki amshi sadakar ki." na fada ina a jiye plast ɗin a ƙasa. "Sadakar me?." ta tambaya ne da mamaki. "Allah ya kawo mun masoyi, na kece rai ni." Na faɗa ina miƙa mata alewan."Ki ce mun kusa barin gidan Galadima." 

"Mun kusa fa." na fada ina hucewa, ita ma tayi bangarensu. A hankali nayi sallama, amma ba'a amsa ba hakan yasa na shigo ciki kai tsaye. 

"Yanzu Mus'ab da wanna ciwon ya kashe ka fa?."  Naji muryar Hajja na faɗa.  Ahankali na ji ya yi magana cikin sanyin muryarshi."Hajja ai ina shan magani, ba zai kashe ni ba."

"A'a nidai Mus'ab, gwanda kawai ayi auren nan. Irin wanwn ciwon na ku, aure ne kadai mafita." Nan take kwakwalwata ta gano mun cutar da ke damunshi, kuma gashi ɗazu naji likita ya ce tayi Worst. "Chaɓ, irin su ne muke ji a Novel kenan? Wa'yanda matansu ke ramewa sabida yawan sha'awarsu." wata muguwar dariya ce ta tawo mun da ƙyar na iya tare ta, sabida tinawa buduruwar da zai aura nayi kamar tsinken sigari haka ta ke. "Sai dai ta koma tsinken kwa-kwa." na fada a fili, ina dariya ƙasa-ƙasa na shigo dakin. "Baki iya sallama ba." Hajja ta fada ta na hararata, nima hararar na mayar ma ta sanan na ce. "Kun can kuna hirar ku ai ba za ku ji ba." 

"Ke dalla me yasa baki da hankali." hararar na mayar kanshi, sanan na ce. "Ni ce ma kai." azabure ya ta so ya yo kai na xai da ke ni. Hajja tayi saurin riƙeshi, tare da fadin. "A'a Mus'ab na hana ka."  Koma wa yayi ya zauna ya na haki. "Ai da ka dake ni, wallahi sai ka yi da nasani, domin yanzu Allah yakawo mun mai tsayamun, wallahi Mus'ab idan ka dake ni har kotu sai mun je." Na faɗa tare da ajiye plast ɗin na juya. "Lallai yarinyar nan tabbata ki ke ji, to wallahi zaki zo ki same ni." Hajja ta faɗa, shi kuma ya ce. "Da kin barni na ɓallata." 

"A'a Mus'ab, ka dai na wanan saurin hannun." Shiru yayi bai ƙara ce wa komai ba. Ni kam ina fita na kaɗa kai na yi makaranta abu na. A hanya nai ta yiwa yara sadaka, haka 'yan ajinmu. Duk wanda na bawa sai na ce ya ce."Allah ya bar ƙauna." Kasancewar Ajin mu ba daya dasu Walida ba, ya sa ban fiya tsaya su tafiya ba. Allah bashii dawowa ma, ita kam Halima ba ma islamiyar mu ɗaya ba, ita hadda ta ke yi. 

A haka na shigo cikin layinmu, zuciyata fes sai dai ƙara hango Musrur da nayi ya ƙarawa zuciyar ta wa haske, a nuste na ci gaba da tafiya har inda ya ke. Da mayalwacin murmushi a fuskar sa ya tare ni da faɗin."Sannu da dawowa ranki ya daɗe." Wani sanyi na ji da ya ce ranki ya daɗe. "Yawwa sannu, Yallaɓai." na faɗa sabida kar na ce ranka ya daɗe ya zama kamar na kwaikwaiye shi gwanda na zo da sabon salo abuna. "Uhm, i apprecite this name." 

"You deserve it." na mayar mai cikin harshen turanci nima, domin ban son ya ga gazawa ta, ta kowanne fanni, domin yasan bani ka ɗai nayi sa'ar samunshi ba, shima ya yi sa'ar samu na. "So how was the school." 

"Alhmadulilah Yallaɓai, how was your work." 

"Everything great, ya mai jiki." 

"Jiki gashi can ya na fama." Na faɗa, in i don't care, ban son ma ya sake mun maganarshi.

"Tun ɗazu ina ta expecting kiranki." Murmushi nayi kafin na ce."Ina ta jiran Ummanah ta dawo da ga asibiti kafin na kira." 

"Ouh, bakya da waya!?." Ya fada da mamaki ƙarara a fuskarshi. Sai naji na zama wata kala, dama bance ba. "Yaka ma ta na sama miki." Da sauri na girgiza kai. "Abbanah duka ne zai yi, kaba ri with time za'azo lokacin da zaka bani." Murmushi ya yi sanan ya ce. "I'm so glad to have you in my life." Ƙasa na yi da kai na, sanan na ce."Same here." Kamar an ce Salma juya, idanu na suka sauka a kan shi, a raina na ce. "Ko uban me yake yi a nan, oho." 

"Fulani, wanan kamar mara lafiyan nan ko?." 

"Fulani.." na sake maimaita sunan, ya masifar yimun daɗi. Na ma manta da abinda ya tambaye ni. "ko ba shi ba ne?." ya sake tambayata. "Yeah, shine." Na faɗa. "Oh ya warke sosai, gida ɗaya kuke kenan?." 

"Uhm, family house ne." Na bashi amsa, ni ban son maganar wan can Mutumin. "But you look alike kamar blood brother na ki." da sauri na girgiza kai sanan na ce. "Godforbid, cousin brother ne." Dariya ya yi sanan ya ce."Mene na Godforbid ɗin?."

"Ni kam, i really hate this Mus'ab, mahaukaci ne fa ɗa zu fa ce wa ya yi wai zai dake ni." nan da nan ya haɗe rai, sanan ya ce. "Du ka kuma?." Na ɗaga kai sanan na ce. "Ai bashi da hankali." 

"Da'alama faa." shima ya faɗa. "Yallaɓai bari na shiga gida, Ummanah na jira na." 

"Okay, Fulani take good care I love you." 

"I love you too." Na faɗa tare da juyawa da sauri, har na kusa shiga gida ya ce."Am, Fulani kar ki manta ki kirani faa." Daga kai kawai nayi na huce, Mus'ab na tsaye bakin gate nazo zan huce, sai da na kalleshi wata sabuwar tsanar ta sake dirga a raina, sanan na ce. "Allah ubangiji ba danni ba, ba dan Halina ba, ba dan laifuka na ba, ka gama Mus'ab da katuwar Masifa ko iya duniya ne, masifa wacce za ta azbtar da shi." 


Legends pen.
(***/  ***).



Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete  ₦1000.

Ranar litinin zamu fara posting paid pages, posting kullum, za'a fara siyar da complt ma ranar litinin, zaku iya fara payemnt tun yanzu

Payment via.

8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.

Shaidar biya.

***