Page 7
by @legendspen
*SAKATA*❤️⚓️
🌻Stroy and written🌻
By
Sayyid writer (Legend)✍️
*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*
*(FUWA)🖋️📚*
SHAFI NA BAKWAI.
(P.07)..
Sanarwa!
Ranar litinin zamu fara posting paid pages, posting kullum, za'a fara siyar da complt ma ranar litinin, zaku iya fara payemnt tun yanzu
Payment via.
8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.
Shaidar biya.
***.
بسم الله الرحمن الرحيم
"I love you too." Na faɗa tare da juyawa da sauri, har na kusa shiga gida ya ce."Am, Fulani kar ki manta ki kirani faa." Daga kai kawai nayi na huce, Mus'ab na tsaye bakin gate nazo zan huce, sai da na kalleshi wata sabuwar tsanar ta sake dirga a raina, sanan na ce. "Allah ubangiji ba danni ba, ba dan Halina ba, ba dan laifuka na ba, ka gama Mus'ab da katuwar Masifa ko iya duniya ne, masifa wacce za ta azbtar da shi."
"Ke wai baki san wanan masifar da like jawa Yaya Mus'ab ba, Mala'iku su na amsa da ce wa Walaki ba." Kallon Sadiya da ke zaune kan doguwar kujera a falon mu nayi sanan na ce. "Wallahi Sadiya ni dan ta tawa mai sauƙi ce, indai har Mus'ab zai shiga Masifar da nake masa fata."
"A'ah, dan Allah ki rage wanan muguwar tsanar."
"Wallahi Sadiya duk safiyar ubangiji, wata sabuwar tsanar Mus'ab ke huda zuciyata."
"Allah ya kawo miki sauƙi."Banza nayi da ita, sanan na miƙi zuwa ɗakin Ummanah. Wayarta da ke jikim chaji a soket na je ɗauka, amma ƙwalam ba ta nan. "Nasan tana dakin Abbanah, bari na je na ce tabani zanyi karatu." Na faɗa a raina tare da fice wa. Ban kai ga ɗakin ba naji muryar Ummanah na ce wa. "To yanzu zuwa yaushe zaku jira su?."
"Eyh, zamu jira su zuwa sati ko fi. Dole dai idan su ka gama shawararsu su nai me mu."
"Nima amma Alhaji, ciwon yaron nan ya mugun damana, gani nake kamar zasu ɓata mana lokaci. Kasan Likitan yadda ya nuna, yana buƙatar aure cikin gaggawa fa."
"Gaskiyya ne, ciwon nan na shi na buƙatar iyali kusa-kusan nan, Allah dai ya bamu yadda zamuyi." Abbanah ya faɗa, dai-dai lokacin da nayi sallama. Ummanh ca ta amsa da faɗin. "Salma shigo ma na." shigar nayi kaina a ƙasa, sanan na ce. "Ummanah ina son nayi karatun hadda, idan babu damuwa."
"To ai wayar na ɗaki."
"A'ah Umma, ba ta jikim soket."
"Eyh, ba nan na ajiye ba. Ki duba gefen fulo." Tashi na yi a raina ina ce wa. "Ko mai yasa ban duba nan ba oho." wani ɓari da ga zuciyata ya ce. "Rabon kiji wanan maganar ta su." afili na furta. "Mene haɗi na da maganar." kasancewar babu mai ba ni amsa, ya sa nayi shiru na ci gaba da tafiya zuwa ɗakin mu. Wayar na gefen gadon, hakan yasa na ɗauka na fara loda lambar ta shi, wacce tsabar yawan dubawa yasa na hadda ce ta.
Bugun farko ya ɗaga wayar, kamar ya san ni ce ya fara magana. "Fulani barka da dare." idan na ce banyi mamaki ba, kuma kusan ƙarya ne. Domin yadda ya kira sunan da ƙarfin gwiwarsa, irin yana da tabbacin ni ɗin ce."Ba ita ba ce." Na faɗa ina murmushi. "Haba Fulani, tun kafin ki kira zuciyata ke cemun Next call is your future wife." Murmushi nayi sanan na ce. "Yakake?."
"Not good." ya bani amsa, a ɗan tsorace na ce. "What's going on."
"Fulani I'm missing you, so badly."
"Same here, Vida mia."
"Oh what a sweet name, amma naji dadin sunan." kunya ta ka mani, na ce."Amma Fulani yafi daɗi."
"No, wanan ma yayi daɗi i really appreciate it."
"Thanks you." na fada, cikin ƙarewar magana. "Fulaninah." Sassanyar muryarshi ta sake faɗa. "Vida Mia." Nima na faɗa, cike da sabuwar soyaya, a raina ina cewa. "Ni kam na dace, a rayuwar soyayya, domin Masrur ko babu ci babu sha, zan zauna dashi ko dan kyakyawar fuskarsa. Duk da Walida ta ce wai rawar kai ce, amma nafishi kyau."
"Fulani, ina da tarin tambayoyi."
"Tambayoyi kuma?." Na faɗa kai tsaye. "Yeah Fulani, amma ba tambayoyi masu damuwa ba, na soyayya ne." Murmushi nayi sanan na ce. "Tom ina jinka."
"Fulani mai kika fara ji ranar da kika ganni." Shiru nayi ina sauraron zuciyatah. A hankali na fara ce wa."Ina zaune a harabar gida, na ji kamar ana kirana a waje, na tashi na fito, idanuwa na suka sauka a kan ka. Kyakywar farar fuskar ka ce ta fara burgeni." sai kuma nayi shiru. "Ci gaba mana Fulaninah."
"Shikenan." Na faɗa, shi kuma yayi dariya. "Ni kam Fulani idan na faɗamiki ranar da na fara ganinki za ki yi mamaki sosai."
"Yaushe?." Na tambayeshi. "Fulani, wajen 3weeks back. Na gan ki ke da ƙawayenki, kun dawo daga school. Tun lokacin na fara bin ki, ina ganin ki." Murmushi nayi mai sauti sanan na ce."Kasan maganar da nayi da ku, sai da Mus'ab ya ja a ka dake ni."
"Fulani, wai mai kika yiwa Mus'ab ne?."
"Nima ban sani ba, kawai dai na san ya tsane ni, nima haka."
"Amma ya kama ta ku daina haka, ba kya ganin yadda kuke kama ne."
"Ni kam har abada ba zan so Mus'ab."
"Nima bance ki so shi ba, amma ku fahimci juna." cike da jin haushi na ce."Ko da a kwai wani abu da fahimtar juna dashi za ta yi mun?."
"Ɗan-uwan ki ne fa."
"Dan Allah mu bar maganar shi haka." Na fada kamar zanyi kuka."Shikenan, yanzu tambaya ta gaba. Mutum nawa kika yi dating kafin ni?." Shiru nayi ina son tuna wa, sai kuma na ce."Wani yaro ne Hafiz, tun muna aji biyu a islamiya daga baya kuma mu ka rabu."
"Faɗa kuka yi?." Ya tambaye ni. "A'a, kawai yau da gobe da kuma girma."
"Okay, Wa kika fi so a ƙawayenki?."
"Ai ni bani da ƙawaye da suka huce 'yan uwana, Walida da Sadiya."
"Wacece wacca nagan ku tare a asibiti?."
"Walida, na bashi amsa."
"Okay, yanzu yi mun naki kafin na ciga ba."
"A wacce unguwa kake?." tambayar da ta fara zuwa bakina ba tare da na shiryawa fitarta ta ba.
"Gwari avenue." Na girgiza kai, alamun naji."Akwai wata?." ya tambayeni, na ce."Eyh, mai ya baka kwarin gwiwar zuwa layin mu."
"Zuciyatah." Dariya nayi sanan na ce."Na gama."
"Ina da wasu masu yawa, amma naga dare yayi."
"Uhm." Na faɗa, sabida bana son wayar ta kare. "Ki kwanta, sai Allah ya tashe mu. Kisani ina matuƙar ƙaunarki."
"Nima haka." Na faɗa tare da gyara kwanciyatah, fuska ta ɗauke da murmushi ya katse wayarshi. Haka na kwanta ina ta murmushi, kamar wata sabuwar kamun hauka.
Washe gari..
Da sassafe na tashi, sabida ina son zuwa boko duk da ba wani abu ake mana ba, sabida muna Ss2 ne kuma anyi exam ɗin third term har angama. Boko dai ajin mu ɗaya da Sadiya, amma Walida ta na Science ne, ni da Sadiya Muna art. Ita sadiya ma commerce take, kawai wasu subject ɗin mukeyi tare. Ni dai na ce ba zan wahalal da kaina a kan Karatun boko ba, dan yanzu ba wani aiki a ke samu ba, gwanda na karanci har kar kasuwanci abu na.
Zaune nake a cikin class, na ware gefe na zauna hirar mu da Vida mia nah ta na dawomun ina murmushi ni kadai abu na. Safiyya ce ƙanwar Samira wacce Mus'ab zau aura ta shigo ajin mu, wata muguwar dariya ce ta tawo mun, ganin ta na tafiya kamar cokali. To a haka ma tafi Samira ƙiba, ga mamaki naga ta na yo inda nake, kau da kai nayi daga saitin inda take tawo wa."Salma Galadima." ta faɗa, bayan ta ƙara so inda nake, cike da haɗe rai na ce. "Ya a ka yi?." murmushi tayi sanan ta ce. "Lafiya ƙalau, ai yanzu mun zama 'yan uwa."
"kun dai zama 'yan uwa, ni mene alaka ta da ku, har da wanda zaku aura."
"Ai ko ba komai ɗan uwanki ne ko."
"Kinga Safiyya, tashi ki bani waje." Na faɗa a tsawa ce, saukar da murya tayi sanan ta ce."Kiyi haƙuri, tambayar ki na zo yi fa."
"Me zaki tambayeni?."
"Dan Allah Kifaɗamun gaskiyya, nasan ba kya ƙarya kuma ba za kiyi ba." kallonta nayi sanan na ce. "Wai me zan fada miki."
"Nasan kin san Mus'ab su na soyayya da Samira, to amma tun farko ba wata soyayya ba ce ta a zo a gani, dan bai taɓayi ma ta maganar aure ba. Kawai dai soyayyar tasu ta bazo ne, kowa ya sani to kwatsam su Abbanku su ka zo da maganar aure, bayan su Babban mu sunyi shawarar ba shi, sai ga wani zance ya fito. Wai Mus'ab yana dauke da wata cuta, kuma duk macen da ya aura za ta sha wahala a kan wanan cutar tashi, dan Allah ki faɗamun gaskiyya, nasan ba zaki ɓoye ba, sanan kin san Yayata ba wani kiɓa gare ta ba, kuma wallahi ba xan taɓa cewa daga bakinki na ji ba, ko a gidanmu."
Legends pen.
(***/ ***).
Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ₦500 kacal ne sai kuma masu buƙatar complete ₦1000.
Payment via.
8129553971
OpaY
Sani Muhammad lawan.
Shaidar biya.
***.